Auren Gado 31-32
3⃣1⃣&3⃣2⃣
08032252760
08175479641contact this numbers for more information
Ya dade zaune yana bin kofar da kallo, “babe that’s our room tunda shi kika zaba mana. Yafada yana murmushi mai kayatarwa saida yaji ya d’an dawo normal ya mike tareda mayarda rigar shi bayan ya kalli yanda taja duk wandon yayi squeeze, cikin gidan ya koma tareda kiran maid yace tazo side din su ta hada musu breakfast idan tagama tayiwa madam magana tafito taci shi ya fita.
Naziya bata kuma fitowa ba saida taji bugun kofar maid tace “Aunty nice kifito ga breakfast. Bude bakinta tayi cikeda kasala tace ” ba kowane a cikin gidan? “Eh Oga ya fita yace ki karya sai ya dawo. Ajiyar zuciya tayi ta mike tareda cewa ” kije nagode. Saida taji ta tafi tafito falon ta dauki d’an kwalinta dake kan kujera ta kalli wurin tareda tuna what ever happened yanzu, mamakin shi takeji halin shi daban ya mugun canjawa kuma she understand know, khaleel bayaji domin ta lurada baiko tsoron kalaman momy like Ahmed dake mugun gudun fushin ta, zama tayi na tsawon lokaci tana tunanin banbancin halin su tareda irin nashi ra’ayin I don’t care, da kuma bin son zuciyar shi,
Sai karfe shadaya ta karya ta kwashe kayan ta nemi kitchen, yanzu ta lura komai na part din sabone bazata manta ba lokacin da Ahmed kenan ba wainnan bane a ciki, wainnan sunfi haduwa ko kitchen din kamar Aljannar duniya bare kuma bedroom din data shiga, kawai jitayi Abun ya burgeta taji tana son taga gidan baki daya, dakunan sunyi matukar burgeta duka sai daya dayafi kowane haduwa da shan ado ga akwatunan ta sunkai saiti shida masu kyau da tsada waldrp din ta bude taga yanda ya tsara komai kayane yan gida da waje birjik kowane side kaya daban harda iners kamar wani small shopping mall, samun fuskar ta tayi da saki ta zauna tareda zubawa ko Ina kallo tana tunanin shi just like that tafara hasaso rayuwar shi, daga jiya zuwa safiyar yau he changed all her thinking, duk wani baki nashi da take gani ya goge sai wasu kyawawan halayen shi dake maye mata gurbin duk wani kiyayya datakeji tashi, me ma yayi mata tunfarko? Takasa tunawa sai wata zuciyar ke fada mata kanin mijinki ne this is not right, girgiza kai tayi tareda tunawa da ya’yan manzon Allah da ya Aurar da ya ta mutu yakuma bashi wata itama ta mutu yace da da wata da zai kuma Kara mai, don haka tasani ba haramci a cikin Auren su sai dai zata dauki dogon lokaci kafin ta iya sakin jikinta dashi, karar wata sabuwar waya taji a gefen gadon ta mike tareda daukar wayar ta zuba mata ido kamar tana tsoro domin wayar nada matukar girma da kuma kyau, saida tayi ringing sau biyu ana uku tayi shahada ta dauka,
Shiru tayi domin batasan wayar waye ba kuma ba suna, “Hmmm madam kinga wayar ki kenan, that’s your phone ita zaki rike madam khaleel, and this is your husband number save it. “Nidai bana son waya inada tawa. Tafada cikin wata irin murya da batasan tafito ba. Ajiyar zuciya yayi yace ” Hmm you are my wife I can buy the whole iPhone company for you if you want, kinfi karfin wannan wayar, ni zanfada miki how wealthy I am, your husband is a rich man take it or leave it, but that the fact, and ki shirya very soon zamuje honey moon domin I have a lot to offer to you madam Ibrahim, I want to fulfill All my brother dreams, kullum so yake yi yaganki cikin farin ciki, bai samu dama ba, ni inada dama what ever you want just tell me I will do it right away, I don’t mind if you call me your savernt.
Kalaman shi sunyi matukar tasiri a zuciyar ta saidai kalma daya data tsaya mata da tasa ta bude baki batareda ta shirya ba, ” kanayin komai saboda Ahmed? Shiru yayi na d’an lokaci kafin yace “yes shine ya bani umarnin Aurenki, and bazan iya tsallake wa ba koda bana so zan iya takura rayuwa ta for my brother happiness. Kalmar batayi mata dadi ba taji wani iri Abun ya tabata wato saboda Alfarmar Ahmed yake Auren ta? “Me yasa zaka takura kanka kayi Auren da bazai taba Baka farin ciki ba? Ni baso nakeyi ba da kabarni na Auri Wanda nakeso. Wani irin d’aci yaji a kirjin shi, “Wanda take so? ” oh wannan Almajirin ko I no it, but last warning daga yau tunda igiyoyina na wuyan ki kar inkuma jin irin wannan maganar a kunne na, bazan dauka ba, any way is nice talking to you on phone, bazan dawo da wuri ba aiki ya rikeni daga lekawa office kinsan Yaya na keyin komai yanzu responsibilities sun hau wuyana da yawa,mata biyu gida uku Momy na office our business zaki taimaka min ai ko? “Mata biyu? Ta samu kanta da tanbaya batareda ta shirya ba kalmar ta fito, “yes two wife’s idan naga da hali salifa ma zata dawo kuzama ku uku but kafin nan zangina muku gidan da yafi wannan yanda kowacce zata wala.
Sauke wayar tayi, taji she can’t talk anymore just like that ta datse ta Ajiye,
Wayar shi ya bi da ido tareda cewa “what? Idanun shi a waje domin he can believe it, kishi takeyi batason kishiya? Or what? Tafara sonshi ne daga small touch daya bata daga jiya zuwa yau or what? Ko kawai ta gaji da magana dashi ne? So much question da yake bukatar Amsar su, dafe goshi yayi tareda cewa “babe if you are really jealous saboda ni I swear I will divorce fauzy I promise you, but I will find out first. Jinshi yakeyi kamar yayi tsuntsuwa ya bar office yagan shi agida this is very hard time for him he needs time saboda ita,
Ta dade rikeda wayar tana tunanin meke faruwa daga jiya zuwa yau, takasa kamo bakin zaren mikewa tayi tareda kwabewa ta daura towel domin tayi wanka kafin lokacin sallah, katon mirror din dake bathroom din ta zubawa jikinta ido tana kallon kirjin ta da yayi wani irin ja saboda murza, Ahmed ta tuna dayayi mafarkin tabasu har yabar duniya, tace you miss my Ahmed you really missed. Tuna yanda ya kafa soft lips dinshi akansu taji wani iri Abu nabin jikinta, yanda yake squeezen dinsu ta tuna, namiji baida kunya domin ita a irin zaman su za amutu bazata iya koda rike hannun shi ba Amma shi daga zuwan ta first night ya murjeta tsab a gado yanda yake so ko a kwalar rigar shi.
Saida ta kwashe kusan hour guda kafin ta fito ta samu kanta da murje ko Ina najikin ta da kamshi da mayuka masu tsadar gaske da gyara fata, ta fito zuwa cikin dakin, inda tasamu kanta da zabo wata doguwar rigar Abaya Baka mai d’an kwali kato ta ciro Iner wears ta saka masu kyau bakake suma ta zura rigar ta shafa powder da wet lips saboda ita irin matan nan ne masu natural beauty ba saida make up ba.
Nade gyalen tayi kamar balarabiya, fadin kyau da tayi bata bakine, hijabi ta dora a kai tayi sallah, ta dade kafin taji karar wayar ta, dauka tayi tasan shine domin ba Wanda zai kirata, ” madam nagaji kuma inajin yunwa, please set food for me and water for bath I will be home in fifteen minutes insha Allah. Batace komai ba ya datse kiran. Tashi kawai tayi ta nade daddumar ta fito zuwa cikin kitchen, ko Baka ra’ayi zakayi sha’awar yin girki a cikin wannan kitchen din, don haka ta baje tareda hadamai lafiyayyan dishes din da yakeci, Wanda gidan ya cika da mugun aroma, ganin zobo dasu Abarba taji tana son ta hada, domin ko a gidan su sana’ar inna ce, cikin minti shabiyar ta hada komai ta zuba kankara tareda zubawa cikin lafiyayyan jug ta saka a firij,
Gyara wurin takeyi tana tunanin ba wannan kudurin ta shigo dashi cikin gidan nan ba, duk Ina tsarin ta da kuma kiyayyar Auren khaleel daga jiya zuwa yau ya zage ta girka mai Abinci, and this wanka, no ba saboda shi bane saboda ta bi maganar iyayen ta dasu Aunty, kuma tana tsoron wutar Allah, banbancin mutum mai ilimi da jahili kenan, Wanda shi kullum idan zai aikata laifi yasan makomar shi amma jahili yi yakeyi batareda tunanin gobe ba, don haka Allah yabamu ikon aikata mai kyau.
Motsin da taji ne yasa tayi saurin Ajiye towel din da take goge goge dashi, a tsaye yake ya nade hannu tareda zuba mata ido kamar zai cinyeta tayi mai matukar kyau ga wani irin Aroma da yayi mai welcome tun shigowar shi falon, dukar da kanta tayi duk ta diririce domin duk ya cika mata ido da kitchen din, ga wani killer smile da yake watso mata Wanda ke Kara hanata tabuka kudurin zuciyar ta. Ganin ta daskare ya bude hannun shi Alamar tazo gareshi ta ki tareda juyawa ta bashi baya. “Ni dole inzo madam bazan iya ba ai. Yafada yana cire hannayen shi a saman kirjin shi ya fara taku a natse har wurin ta bai yi wata wata ba ya zagaye west dinta tareda dora habar shi a wuyanta yana lumshe idanun shi. “Wow wannan kamshin daga cikin gidan ki har kitchen din ki, Hmm I can’t express, you are amazing, you are beautiful adorable and Angel from god Alhamdulillah, kinsan ance wai idan namiji yazo gida ya tarar da Matar shi duk gajiyar shi na bajewa, Amma ni ba haka bane, duk lokacin da zanganki jikina Kara mutuwa yakeyi you are my weakness.
Kalmar tayi matukar tasiri a zuciyar ta, sannan yanda yake magana hucin shi na bugun gefen wuyan ta tuni ya saukarwa da nata jikin kasala, she can swear shine weakness dinta domin duk lokacin da ya matso gareta ta tashi aiki, sun dauki lokaci idanun su a runtse yace “A bani Abinci am hungry. Saurin cire hannayen shi tayi ta matsa tareda daukar tray ta bude firij ta dakko jug dinta ta dora mai komai yana kallon ta har tafita gefen kitchen din da ke daukeda dining ta Ajiye yana biye kamar rakumi, jan kujera yayi ya zauna tareda cewa ” nafa gaji kezaki ciyarda ni da kanki. Dago kanta tayi tace ” Aa ni bazan iya ba.
Kasheta yayi da wani irin salon kallo ya karkace tareda ciro wayar shi yayi dialing number fauziya, ringing daya ta dauka yace ” come to Naziya side now. “Why zanzo side dinta? “Inbazaki zoba karki dameni da surutu you can pack up and leave. Ya datse kiran, ya jingina a jikin kujera ya runtse idanun shi batareda ya kuma ko kallon taba, tunda ya Kira Fauziya fuskar ta ta sauya tuni ya zubawa handsome and well shape face dinshi ido dake dauke da wani irin kyakkyawan saje dayake karamai haiba da haduwa ido, girar idanun shi zaro zaro sunfito, pink lips dinshi, jin shigoqar fauziya yasa tayi saurin waigawa tareda zuba mata ido, mugun kallo ta watsawa Naziya Wanda itama akaron farko taji ta tsane ta. Tareda mayar mata da kallon tayi saurin matsawa zata fara ruwan fada” ke ni sa’ar kice zaki harare ni wallahi…… “Enough banson hayaniya zoki bani Abinci am hungry. Yafada fuskar shi a tamke, tuni kanta yayi wani irin kato tafara kwarkwasa ” OK baby ai badamuwa, matsowa tayi tareda jan kujera dab dashi ta bude Abincin tayi serve ta dauki fake tana zokalo prawns din tana bashi a baki,
Sai wani irin shigewa takeyi cikin jikin shi , shukuwa he is enjoying each and every spoon na favorite food dinshi kamar ita tafi kowace mace iya sarrafa tukunya,
Takasa koda motsi wani irin Abu taji ya danne kirjin ta kamar sanda yana sata jin wani irin kakarin mutuwa ko miyau ta kasa hadiyewa Wanda tarasa dalilin, wasu hot tears da bata shiryasu ba suka biyo kuncin ta, a gefen fuskar shi yake kallon ta Wanda jiyake kamar ya buga tsallen murna is true she is jealous, Amazing.
Juyawa tayi tabar falon gudun karma yaga metakeyi ta shige dakin tabarsu anan, tana shigewa ya karfi fake din yana wani irin murmushi mai kyau ” tank you dear, Yafada cikeda nishadi tareda saka mata abaki ta bude ta karba jinta takeyi a sama yau.
Saida yaci yayi kat ya janyo jug dinta ya tsiyaya zoban da kanshi, kamshi ya bugi hancin shi nasu cucumber da abarba, kurba daya yaji wani irin kuzarin shi duk yadawo, best juice ever, yana gamawa ya ce “I need to bath muje can dakin ki hadamin ruwa, ya nuna mata wani daki daban, jikinta na rawa ta mike tayi dakin ta hada mai ruwan ya shigo tareda kwabewa ya rage dagashi sai boxer ya ce ta nemo mai kaya kana na ya shige fuskar shi a tamke yanzu domin bayaso ta shigemai.
A dakin Naziya kuwa samun kanta tayi da kasa sukuni taji Sam bata gamsu da shigowar ta dakiba, kukan me takeyi to ai Matar shi ce kuma tare tagansu meye nadamuwa? Toh me ya hana ita ta dafa mai da kanta sai yaci fuskar ta? Wayar ta ta janyo ta Kira Aunty Raliya, tana dauka tace “Alhamdulillahi Naziya kin Kira duk hankali na natashe haka Inna Ina gudun injiki cikin matsala hope ba wata matsala ko? ” Aunty ba komai. “Kifadamin ba matsala keda Abokiyar zamanki koda mijinki ko uwar mijin ki? ” Ina gefena yanzu ta shigo. tafada wani kuka na kufce mata na rashin dalili, “Innalillahi, me tayi miki, ni Raliya, Abinda nake tsoro kenan wallahi. Saurin hadiye kukan ta tayi jin Aunty Raliya ta rude, ” Aunty batayimin komai ba shine yakirata. Anan dai dole ta war ware mata komai tareda fada mata duk Abinda zai iya faduwa a tsakanin su. Ajiyar zuciya Aunty Raliya tayi tace “Alhamdulillah, kingani ko Naziya, insha Allahu zakiyi farin ciki, a tsaye khaleel yake inada labarin shi saidai yanzu matsalar na wurinki ki gane kishiya gareki duk wata muguwar akidar ki da hango haramci da kikeyi ki cireshi ki dage ki mallaki mijinki zaman ku bamai karewa bane don inaji akwai Abinda Allah ya boye a Al’amarin ku. Ta dade tana bata shawar wari kafin su katse, Ajiyar zuciya tayi tareda sawa zuciyar ta kwatan tawa batason tayi kuskuren baya, zaman ta da Ahmed wannan ce damar ta,
Sai da la’asr ta fito, suna zaune a falon, fauziya ansamu sake ta wani dora kanta a cinyar shi tana bacci Wanda haryagaji saboda neman magana yana gab da tureta yaji fitowar ta, wani irin saurin dora tafin hannun shi yayi akan fauziya yana wani shafawq kamar mai lallashin kwai, turus tayi kadan kafin tayi saurin danne ranta, domin ta canjo salo, ta matso fuskar ta a sake tace “me zakaci a dinner ko zata dafa maka ne? Wani mugun kallo ya watsa mata ba haka yake soba shi fadan ta yake kwadayin gani da sunan kishin shi that’s means he is mistaken, don haka cikeda takaici yace bazanci komai ba, ya ture kan fauziya ya mike, zabura tayi yace ” zoki wuce part din ki malama, daukar dankwalinta tayi tace” muje tom. Har zai kuma gwaleta ya dai bita waje Wanda daga nan yayi mosque ko lekawa baiyi ba, cikin gidan momy ta shiga da gudu saboda takai gulma, tana zaune tana faman wayar tafado kanta cikeda farin ciki, ” momy aiki yafara kyau, yau yakirani har agaban ta ya nata jidani kuma naga harda kuka tayi, “kai Y’ar Albarka, kice dole mukara wa Malam kudi irin wannan zafin aiki kamar yankan wuka, bari kiga mai zai faru ma nan gaba dani take zancen, tashi kije ki shirya mai dinner ki caba ado ki baza kamshi yau zakiga mai zai faru. “Kinfa san ban iya girki ba, uhm ki hadoni da mai aiki muje ta mun gyara. “Toh ke a haka zaki Kama mijin yakama ta ki gano halin khaleel Abinci yafi bukatar girkina tunda kina nan ki koya kamar wannan yarinyar rana daya ta iya dafa Abincin shi. “Nidai kidaina min kwatance da ita ni bantashi a wahala ba ita kuwa jikinta ya horu, nidai turon mai aikin muje. Tayi gaba abunta. Momy ta bita da kallo Sam bata ganin girman ta fauziya magana gatsau gatsau take fada mata.
Bai shigo gidan ba sai karfe takwas domin saida yaje ya gaida kawu da Malam Wanda bakomai ke kaishi wurin Malam ba sai neman karuwa da kuma nasihohin shi a kullum, Wanda yakejin dadin su, saida yayi kamar bazaije part din nata ba, Amma zuciya ta ki barin shi kamar ana ingiza shi, baida zabi haka yabi son ranshi, a zaune take a falon ta canja ado zuwa wata silky gowan fubu mai kyau da karamin d’an kwalinta, ya shigo cikin sallama har wani irin sanyi yakeji yana ratsa jiki da zuciyar shi saboda hango ta a zaune a cikin gidan shi a falon shi ta saki jiki tana danna wayar da yabata gefe daya ga tsohuwar tata, zaman da tayi kawai Abun burgewa ne a wurin shi, ta lankwashe kafarta akan kujera, daga nesa ta dago kai tagan shi cikin jallabiya ta dukar da kanta kasa tanaci gaba da hira da Aunty Aisha, saida yazo gab ya zauna nesa da ita ya zuba mata ido yana shafa sajen shi cikeda damuwa, kulawar ta yake bukata very badly bazai iya hakuri da wannan ba he needs her, “Ina wuni. Tafada tareda sauke kafarta kasa,
Kallon ke bakya ganewa yake aika mata kafin ya ce “Hmm, yatsunta farare take murzawq kafin cikin dauriya tace “a dafa maka Abincin? ” Wai ke… Sai ya mike kawai yace saida safe ki kulle kofarki zanje wurin da aka damu dani, wurin da ake sona basai na nemi a mun abuba in ansan Ina so. Ya fita kai tsaye saboda haushin ta. Binshi tayi da kallo kirjin ta na bugawa, ko yanzu shawara Aunty Aisha ke bata akan Abinda kefaruwa domin sun lashi takobin sai sun sa Y’ar uwar su akan hanya, kiran da taji ne yasa taga takira saboda taji Shiru ba reply tace “ke lafiya ko yadawo ne inkyale ki? ” ya ma fita Aunty wai… Sai tafada mata Abinda yace.
“Kedai anyi banzar yarinya wallahi ace Sam bakida wayau kullum muna babatu saikace Y’ar kauye meye amfanin wayar ki bakya wtsp ne? Yanzu mata sun waye shiga grps sukeyi na sanin sirrin gidan Aure ki bari zan hadaki da wata marubuciya tana tareda mata da suka san sirrin rike miji ba boka ba malam kissa tafi magani, tunda ke ba kida wayau. “Aunty wacece wannan?”sai kinyi hankali tukuna, yanzu dai bari inturo miki littafan Aunty feenah dana karanta zaki tsinci wani salon in kin so kiyi wasa. Ta datse kiran ta watso mata su ta wtsp ta sauka, kallon jerin su tayi tareda kurawq kuskure na ido Wanda taji sha’awar karantawa domin sanin meye kuskuren tauraruwar?
Saida tayi nafila like Always ta haye gado tareda daukar wayar ta domin batasan tayi tunani akan me yakeyi Ina yake, Amma wani gefen zuciyar ta nafada mata cewa yana can suna wasa kamar yanda yayi da ita jiya, wani iri taji ba dadi kamar mashi ne ya caki zuciyar ta, saurin bude littafin tayi ta fara karantawa domin kawarda tunani aranta,
Batayi bacci ba har Asuba saboda sakai Wanda ta fahimci sakonnin cikin hikima, duk da itama ta lura tana so tayi kuskuren ta hanyar wancakalar da damarta, ba inda Abun ya burgeta sai ranar da Abdullah yafara romancing Ummu Ruman, tsigar jikinta saida taji ta mike , kuma taji tsoron yanda suka kare a daren farko har tafara hasaso idan hakan yafaru da ita, zaro idanun ta tayi data tuna lokacin da yasa ta rike gaban shi, dafe kirjin ta tayi ta tuna how thick taji Abun a tafin hannun ta, tashiga uku idan yace zaiyi, wata zuciyar tace Naziya stop dreaming momy bazata taba barin shiba kamar Ahmed, tashi tayi tayi sallah ta maida baccin da batayi ba.
Gefen khaleel kuwa yana fita da daren part din Fauziya ya wuce domin bayaso momy tagano akwai matsala tsakanin shida Naziya, tana nan a hakimce a falon anci lingerie guntu ana jiran Oga, sai gashi, fuskar shi Sam ba walwala ya shigo ya zauna, yunwa yakeji, gashi yayo fushi yayo nan, tasowa tayi tana karai raya ta fada jikin shi, “baby welcome back, muje ka kwanta, tafada tana shafo kirjin shi, zuba mata ido yayi kamar ya watsa mata Mari yakeji domin tabashi da takeyi karamai bakin ciki tareda kewar Naziya takeyi, yanajin inama inama……. 🖊