kawali Ne 12
*KAWALINE*
*Zahra Surbajo*
*Bissimillahirrahmanirrahim*
*wannan littafi nawa na kuɗine 500,yazo da salo na musamman acikinsa dagajin sunan kuma kun san zeyi maana,sannan na ɗauko wani ciwo dake damun mu ahalin yanzu na kawalci,so duk meso ya turo kuɗinsa 500,in siya zakiyi kifitarmin karku siya,Sannan suk wanda yasayi wannan littafin AJEE DOWN kyauta zekarantashi*
*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*
*07044600044*
*KUSHA LABARI HAUSA NOVELS tashace akan youtube wacce zaku samu complete ɗin littafin KAWALINE akai dama wasu sauran littattafan masu ƙayatarwa da nishaɗantarwa gaku masu sauraro kuhanzarta zuwa dan ɗebe kewarku,KUSHA LABARI HAUSA NOVELS ƊAYA TAMKAR GOMA*
https://www.youtube.com/@kushalabarihausatv
*12*
Tun daga wannan lokacin Rayhan ya koma kamar wani ɓeran masallaci shuru shuru ba yawan magana, tun mummy na magana har tadena yin maganar dan abun har ya zame musu jiki sauyin nasa.
Kullum jabeer in ya kirashi nuna masa yake ze dawo wani uzuri ya riƙeshi.
Yauko da jabeer yakirashi yace masa”rayhan mata har mata gasunan aƙasa vaka nan bansan wa dawa zan turawa suba tunda baka zo ka ɗanɗanaba”
“Jabeer na tuba na ɗauka zaka fahimci hakan ko ban faɗi maka ba to amma tunda baka fahimta ba yau nafito na faɗa maka,nadena kawalci jabeer,kaima ina maka adduar Allah yakawo sanadin da kaima zaka dena,duk dukiyar da muka samu ta hanyar duk na bar maka jabeer banason ko sisi”cewar rayhan cikin damuwa.
Wata dariya jabeer yake harda dira ƙafa,yace yana dariya”mu ba abinda akai da maza wallahi inde kawalcine,dan haka kyautar dukiya dakaimin nagode sosai,Allah ƙara ƙarfin imani”ya ƙarasa maganar yana dariya sosai
Girgiza kai rayhan yayi ya kashe wayar dan dama yayi zaton faruwar hakan daga gareshi,
Jabeer duniya sabuwa tuni yaci gaba da fantamawarshi da mata da mota da kuɗi yayinda kullum se yayiwa rayhan godiyar sakar masa mara yay futsari da yayi.
*********
To hajiya da mummy sunyi zama bisa damar da rayhan ya basu,kuma sun cimma matsayar haɗasu auran,inda sukasa watanni biyu masu zuwa.
Nusaiba sai murna take dama rabuwa sukai da wanda takeso ya koma gun ƙawarta shine takeso ta rigashi aure dan ta bashi haushi.
Anashi ɓangaran ko rayhan fatan alkhairi yayiwa abun yaci gaba da harkokinsa .
Su mummy ko shiri suke bana wasa ba,tun mahaifinshi na raye dama ta gina masa gida ma gani na faɗa a abujar dan haka sukasa aka buɗe aka wankeshi yayi tass,sannan aka fara decorating gidan dan zaman ango da amarya.
**********
A can jihar kano ko,jikin maman rayhana da sauƙi dan da wannan kuɗin da rayhan ya basu ta dinga biya ana mata abinda yadace,har yakai yanzu ana koya mata tafiya, Ako wanne lokaci zaa iya sallamarta.
Kasancewar suna asibitine yasa basu tattauna matsalar dasuke cikiba sabida gudun kar wani yaji.
Tsawon wata guda suka kwashe a asibitin,yayinda rayhana ta fara jin sauyi ajikinta,yawan bacci da yawan jin kasala ga ciwon kai da zazzaɓi.
Tun mama bata fargaba har tazo ta fara farga,tace mata cike da kulawa “rayhana lafiya kuwa kike kwana biyu naga duk kin sauya meke faruwa?”
Yamutsa fuska tayi tace “wallahi mama nima haka kawai nake jina wani iri jikina bemin daɗi”
“To Allah ya sauwaƙe ki sito magani kisha kar ciwon ya kwantar dake”
“To mama zan siyo insha Allahu”
Haka suka ci gaba da zama a asibitim har wata biyu sannan aka sallami mama dan yanzu tana tafiya seɗan abinda baa rasa ba kawai.
Koda suka dawo gida rayhana bata dena jin sauyin datake jiba wanda hakan sosai yake ƙara razanata.
COMPLETE ƊINSA NAKAN YOUTUBE KUJE KU SAURARA AKAN KUSHA LABARI TV,GA LINK CAN ASAMA.
*500 kacal zaku biya kusha karatu karku bari abaku labari*
Surbajo for life.