Hausa NovelsYar Aikin Karuwai Book 2 Hausa Novel

Yar Aikin Karuwai Book 2 Page 21-25

Sponsored Links

Nawwar ficewa yayi daga part din Mami wayarsa ya dakko ya Kira Auta,Yana dagawa yace ka samu Baffa ku warware matsalar Mami wlh ta damu, Auta yace kana ganin ba matsala yanzu? Kai karka raina min hankali ka fadawa Baffa mana, Alright yace Auta ya nufi part din Baffa sanye yake cikin gajeren wando da yar rigarsa wasu farare ya saka hannaye biyu a aljihu wando haka ya shiga part din Baffa,Ya samu Baffa da Papa a Palo suna hirar su ta zumunci,Auta gaida su yayi,Baffa yace Auta ya akayi ne? Yace Baffa zaka iya zuwa daga yau,Baffa yace to Nawaf dina farin ciki ya ishi Baffa bakinsa yaki rufuwa har sai da Papa ya tambaya Wai lafiya dai ko? yace Mamin Nawwar kasan tayi Idda to yarana sun wuce min gaba yanzu haka a saukake za a maida auren nan,Papa yace mashaallah na tayaka murna Yaya ashe har tayi Iddar, yace ae Mana yau ma,yace to tun kafin zawarawa su fara kawo hari ka koma ko ka turani na Fara share maka hanya ko abokinka Alhaji Muaz,Baffa yace a’a ni kadai ma zanje gwara naje Ido da ido, Papa yace to ba damuwa ka bari sai gobe ko ka Kara Mata kwanaki tunda yau ta Gama Idda,Baffa yace hakane a bari to ta Kara kwana ukun zai fi
Bangaren Mami kuma Jin Baffa bai zo ba shuru Shuru sai hankalinta ya sake tashi a Haka ma tana kokarin dannewa sabo da kunyar yaranta.

Auta ne ya shigo bayan Sallar Isha da Sallama anci wanka cikin kana nan Kaya hannunsa Daya a cikin Aljihu Daya Kuma da ledarsa,Mami tana Palo a zahiri kallo take Amma a zuciyarta ta fada tunani,Auta ta gani tace Nawaf daga ina haka? ya gaida Mami ta amsa ya ajiye Mata ledar yace Mami gashi siyo Miki nayi,Mami tana dariya ta bude ledar ta duba sai taga tsire lafiyayye yaji hadi da fruits salat da wasu snacks,Mami tace Autana na gode Allah ya maka Albarka a Ina ka samu kudin? Ni shike nan ban Isa nayi abu ba sai ace Ina na samu kudi to Baffa ne ya bani,Ni yanzu sai abinda nake so a wajen Baffa yace zai siya min mota kwana nan,Mami tace to na gode Auta a wajen ta bude tsirenta tana ci Mami akwai son tsire,tace ka je wajen Nawwar yace yanzu zanje ,jeka ka dawo muyi hira yace to ya mike ya fice, motar da kankabarsa ke sawa ya dakko ta ita ya koma ya Bude ya dakko wata ledar ta su Nawwar ma tafi girma Wai su ba mutum daya ne zai ci ba,Muna Palo Nawwar yayi matashi da cinyata Muna kallo Muna hirar mu Auta ya dinga Danna door bell sai da Nawwar ya kule yace wai waye ya shigo Mana,Auta ne ya shigo yace wlh nasan sai kai,yace to gidanku na ango da Amarya ai ba tsari na fado muku ciki Baku shirya ba ko,Uhm munji sarkin iya zance cewar Nawwar,Nawaf Zama yayi ya kalli Nawwar yaki tashi Yana kwance yayi matashi da cinyata,kasa kasa yace da wani ne da yanzu an dame shi ance bashi da kunya, Aunty Ina yini? Nace lafiya kalau Auta ya gajiya ya labarin aurenka ne,Auta yace hmm ya Mika min Leda tare da cewa gashi Aunty,Nawwar yace ya fasa Auren ai,inji wa? Auta ya tambaya da sauri yace aure Yana nan ba gudu ba ja da baya,Nawwar yace yaro rikon aure da wuya kawo kawo ma ta isheka me aiki babba ma yaya ya Kare bare Kai,yace karayayye ba shine ke tsoro ai Allah ne yake ciyarwa ba dabara da wayon mutum ba,Kai nufinka kudinka ne yasa kake ci da Aunty kana bushasha, Nawwar yayi dariya yace a’a kudinka ne Auta, yace Allah ne dai da badan Allah yaga dama ba sai ya baka kudin Kuma ya hanaka ka bawa iyalinka Aunty da yanzu kyawun Nan ya fece ta dagargaje ta lalace da idan ance ma ka kwanta a cinyarta baza ka je ba,amma yanzu Allah ya baka ikon kula da ita shine zaka ce ni bazan iya ba to Allah ne zai bani nima,Nawwar yace 1-0 Auta Ina ta dariya na dauki ledar nace Auta mun gode,yace kullum ke ba a Maganar kirki dake sai yawu sai kace maye yaga wani ransa ya biya,nace Nifa bana son wulakanci Auta Kai ba a abin kirki da kai sau daya fa kazo kaga yawun nan shike nan ka sani gaba,Nawwar tashi yayi ya bude tsiren Auta Muka durfafi tsire da ci,yace Yaya yau anci madari,Nawwar yace Allah naso na kalli wasan nan,yace Wasa yayi baka ga yanda aka wulakanta Madrid ba yau,modric duk kyansa yau jahilci yayi, suna ta hirar ball har Auta ya tashi yace wajen Mami zai je,Nawwar yace to mun gode Auta yau anyi abin kai,Naga alama ko na mutu Auta zai rike matata,Auta yace in aureta kuwa wlh ba ruwana mantawa zamuyi da Kai tsaf,Nawwar Yana dariya yace to bazan mutu yanzu Dan Iska Ina nan sai na tsufa tukuf ni da ita,Nace Inshaallah aniyarka ta bika Auta,yace Ameen tunda aniyata me kyau ce ni bana gudu ta bini, yau a bangaren Mami ya kwana dakinsa daban bai koma gida ba Suka Sha hirarsu.

Iyamami ce taje Kauye ta samo yarinya bazawara sakin Wawa a danginsu ta kawota har gidan bangarenta tace ta samowa Papa matar aure lallai sai ya aure ta,Papa yace wallahi bazai Aura ba Iyamami ta dage sai Papa ya Kara aure ga Sabreen ta samu Iklima sun hade kai sai sun kori Wise,sun hana Wise sakat a gidan nan tun bata damuwa har ta fara damuwa a ranta,Seraline ta Kira tace tazo Dan Allah sabo da Indai Shawara ce sai Seraline Allah ya bata fasahar yin abu cikin hankali idan Kuwa Star ce cewa zatayi Kawai aci ubansu a musu dukan tsiya,Nima Haka zance,Yar Zabil ma bare Mandula mijinta ne Kawai ya Isa da ita shima darajar so ne tana mugun sonsa shi yasa sai yanda yayi da ita,Seraline ce ta Kira Sabeer ya tafi Katsina wajen Yan Uwansa baya gari tace Baby dan Allah yau zanje gidan Wise,yace ban son yawo kin sani kullum fa sai Kun hadu a makaranta,da shagwaba tace kirana tayi fa matsala ce shi yasa yace to shike nan kije da motata karki kai dare tace to,da Yamma ta shirya taje,bayan sun dan taba hira Wise ta bawa Sera labarin komai,Seraline tace ki kyale su tunda uwarsa tana ciki kin San uwa tana da power zata iya yanke hukunci ko shi Mijin naki sai ya Mata biyayya ke me ya dameki suyi ta Yi miji shi Zaki rike duk abinda zasuyi a banza yaran dai idan Suka Miki kici ubansu wannan Sabreen din naga Alama bata daku bane,Wise tace zanyi bariki a gidan nan,Seraline tace a’a karki Yi please dariya Suka Yi tace kinga Iyamami da ace ba uwarsa bace da yanzu na canja Mata kamanni Mata da budurwar zuciya kullum zo kiga kwalliya ta wani saka jambaki harfa kitso ake Mata da Attach wallahi Rannan cewa tayi sai an sa Mata Attach,Seraline ta dinga dariya tace na gani ai,tace ni ai da dangin Sabeer sun Fara min wulakanci ya taka musu birki da Kansa ya kwatar min yanci shike nan ai Yana Jin harka a local government yaci ubansu kaf.
Wise da Sera suna Hira Suka ji hayaniya lekowa Suka yi Suka ga Auta da Iklima bakuwa matar da za a aurawa Papa suna kokawa, Namiji da mace karfi ba daya ba sai gashi Auta ya fasa Mata Hanci da baki jini Yana fita,Fitowa sukayi da Sera suna tafawa Auta wise tace Auta another punch Auta Kamar dan China haka yayiwa Iklima budu budu tana ta ihun agaji,Iyamami ce ta fito da gudu tana zagin Auta tace ubanka ta maka yanzu zaka Yi kisan Kai Dan iskan yaro marar tarbiyya dama uwarku bata muku tarbiyya ba,Auta yace ai ke shi yasa naga tarbiyar ce dake ke naki Iyayen tarbiyyar Suka Miki ai da sun Miki tarbiyya da baki abinda kike ba Kuma wallahi ta sake cewa zata aikeni sai na karyata baras,au au yanzu dama akan Kawai tace zata aikeka shine ka Mata wannan dukan,yace ae ni sa’anta ne ko kece bazan je ba bare wata kucaka kazama,ta kirani wai Kai yaron nan nine yaronta ko kanin ubanta ne ni,ko Papa kanin Ubana baya min wannan Kiran sai ita sabo da kin kawota Zaki cusawa Papa ya aureta baya so ta tafi gidan ubanta wallahi baza a sata a gidan nan ba ai ba gidanki bane kema Iyamami,Dan ubanka ko ubanka bai Isa dani ba bare kai,ai Ubana Yana tsoronki aljanarsa tana kafarki ni tawa a kafarki take? a kafar uwata take bazan biki ba idan Kinga dam ki tsine min ma,ai Kuwa idan na tsine maka sai ta kamaka yanda na Sha wahalar rainonka da goyaka a bayana ga shegen kukan tsiya haka nake goyaka kayi min fitsari da kashi duk na wanke maka,Auta yace Iklima take ko wa bata da waje a gidan nan baza a aureta ba, Iyamami tace to na gani idan ka Isa sai mu gani mace daya tayiwa Dana kadan wannan Karuwar ce zata bar gidan nan bana kaunarta.

Auta ya nuna Wise yace wannan da kike gani hadin Allah kenan mace Daya tamkar da dubu ai akan ki aurawa Papa Mata goma to gwara ki bashi Wise guda daya,baki ji sunan bane Wise ta ko Ina Wise ce duk ta cike gurbinsu su goman ,kainuwa dashen Allah ita da Papa sai Allah, yau naga dan iskan yaro haka ka koma cewar Iyamami, Auta yace Kuma sai ta haifo mana yara Papa ya samu yaran kirki masu Jin Kansa ba irin Sabreen ba ciwon Kai hawan jini da Kansa to Sabreen kenan, Auta ya kalli Wise yace kina haihuwa na zama Dan raino, ki share su Iyamami ba Arabic ba boko baza su gane ba ko Papa ya sakeki Ina nan zanyi ciki dake ni a haka ma Ina so,Iyamami salati ta saki tace au kwarto ka koma Kuma to wannan sai an sa Ido a kanka tunda ka Fadi haka zaka iya zagawa dama kaga Karuwa ce shike nan kwartonki a gida, Auta yace ke ma da kinyi wa ya san irin zalamar da Kika Yi a zamaninki, ki dai gyara tsufanki ko Kya samu ki cika da Imani yanzu mutuwa ma Yara dauke su take ba sallama bare ke da kin tafi gangara idan baki tuba ba sai yaushe, kin girma kisan kin girma,ki sani gadararki ke Kika haifi yara to suna da hakki a kanki wallahi sai Allah ya tambayeki tunda Amana ya baki,Dan Adam guda aka zabeki aka baki su gasu nan har Mata da maza aka hada Miki matan sun gujeki sai sunga dama suke zuwa daga su sai yaransu sabo da duk kinbi kin watsa Kan yaranki da kanki Aunty Rukayya da Aunty Binta ko gaisheki basa zuwa sai suyi shekaru sai da dalili suke zuwa Babu zumunci Sam yaransu basu sanmu sosai ba muma Haka to a haka kike so idan kin mutu muyi zumunci zuriarki su hada Kai a haka,yanzu Maman Sabreen duk kin jawo yanzu anyi baran baran,komai kin lalata Baffa ma da Papa badan Allah yasa ba da yanzu sun farrake to a haka ke son yaranki kike Yi? Ai ke ce ma makiyiyarsu,kina ta shiga hakkinsu kin hanasu zaman lafiya da matansu,takala na bala’i me kudi nayi mene amfaninsa sabo da koshi ya Miki yawa Zaki ci abinda kike so Allah ya bawa yaranki kudi, wani abin ma samun waje ne koshi ya Miki yawa da ace Zaki tashi ki wayi gari ace ta Yaya ma Zaki ci ki rayu kike da baki tsaya wannan abin baki da lokacin wannan abin,ta cikinki kike Yi,for God sake ki kyale mutane su sakata su wala Ki ja mutuncinki ki ja girmanki ke yanzu dadine Kamar mu ace mu zauna Muna fada Miki magana yanda muka ga dama,kin Sa surukai duk sun rainaki kowa ya tsaneki idan Kika mutu waye zai miki Addua me kyau ko yabon halinki baza muyi ba sai dai muce Allah raka taki gona wallahi sai na raka makara ina tsaye Ina latsa wayata Ina chat,kin San dai yanzu haka akeyi ana makarbata tsabar bushewar zuciya Zaki ga mutane ba ruwansu waya ma suke dannawa suna chatting abinsu,ko mutum ya hau tiktok akan kabari Yana kallon shirme da fitsara to yanzu haka akeyi,Ki kyale mu Dan Allah mu sarara,ki fadawa bakuwarki ba a aikena idan bata sani ba ta sani me aikena sai ya shirya ba kowa ba wlh sai Ina ganin mutuncin mutum bare tazo tana ce min Kai yaron nan sabo da ita bazawara ce wa ya san me tayi aka saketa maybe ma uwar mijinta tayiwa dukan tsiya ke kin kawota sabo da son zuciya danki ya aura kina nan za a aureta ta karyaki ta Miki buju buju ba ruwanmu Kuma Kuna Yi Muna Shan Ginger juice mu ba ruwanmu,har wani Galavanting take a gidan mutane.
Auta Yana gamawa ya karkade rigarsa yace sai nayi wankan tsarki ta shafa min najasa,Dariya su Wise Suka yi Wise tace ni da Kai Amana ne Auta you be better person,Auta yayi gaba abinsa ya bar Iyamami a tsaye Kamar gunki,yaro ya zage yaci mutuncinta haka ashe fadan ma duk wannan bala’in da yake Dan ance Masa yaro ne za a aike shi,Amma maganganun Auta na karshe sun taba zuciyar Iyamami,wa’azin Auta ya shigeta tabbas abinda ya fada gaskiya ne iyaye da dama suna raba Kan yaransu su watsa zumuncin zuriarsu da kansu gashi kowa ya tsaneta babu me sonta sai yaranta su ma Dole ce ta sa.
Sera dai tace to ke Auta ya Gama Miki aiki Saura naki idan basu hakura ba ki karasa da kanki,Wise sai Murna take Yi tace ai Dole nayiwa Auta kyauta.

Umma Umma na dawo fito ki sauke min markaden geron,matar ce ta fito da sauri,dittujuwa ce Fara kyakyawar gaske ta saukewa budurwar da baza ta wuce 18yrs ba katuwa da ita kyakyawar burdurwa zankadaziya son kowa kin Wanda ya rasa Yar jajir da ita,markaden aka sauke Mata,tace Umma Aunty Cele Ashe sunfi wata uku ma da tafiya ita da kaka,Umma Murmushi tayi tace Omaira kyale Rufaida bata Jin magana amma ni Banga laifinta ba ko kadan mahaifinku ne da uwarsa sune da laifi duk abinda tayi tana da hujja laifinta Daya da take hadawa dani,dariya Omaira tayi tace kin San Rannan daga naje nace Cele ta bani awara da kudina fa Umma wallahi ta kamani da kokawa Wai ubana nane ya bata jarin nima kin San bani da hakuri naki kyaleta Muka Yi ta kokawa a titi shine ta fasa min goshi ta min dukan tsiya Wai na rainata shike nan duk inda ta gani sai taci ubana har bana so mu hadu a hanya da Cele sabo da bata gajiya da fada Allah ya taimaka ma ta tafi makkah,Umma tayi dariya tace ku dai na rasa inda kuka yo gadon masifa sai dai ubanku kuka yo, ku goma na Haifa cif duk Mata Kuma duk Babu me sauki duk da ban San dayar ba tana raye ko tana mace oho ko tana gidan marayu Ina aka jefar min da ita oho sabo da Kawai Ina haifar Mata amma ai Alhmdllh tunda dai Ina da guda Tara na suna nan bazan yiwa Allah Butulci ba akan daya ta bace,Cele ai Dole tayi masifa an cuceta ne bana ganin laifinta wlh,Nima Kuma an shiga hakkina an yiwa Allah shishigi,Omaira tace karki damu Umma gamu dukkan mu zuciyar maza ce da mu mace daya ma gayya ce a cikinmu dan ma duk sunyi aure yanzu mu hudu ne Kawai a gabanki Banda Cele da taki aure yanzu maga shegen da zai taba Mana uwa da anyi tsiya.

Gyaran muryar me gidan suka ji ya shugo Yana muzurai wani fari dogo me Dan jiki tun kafin ya karaso ya fara tsawa Kai Kai….hayaniyar me nake ji ne haka ne baki da aiki sai dai kisa Yara a gaba kina zance gashi Nan duk yaranki ba na gari aikin banza wannan ba tarbiyya bace ki dinga munafunci da yaranki,duk Wanda yaci namana ban yafe ba nasan gulmata kuke yi,Umma tace na rasa gulmar Wanda zanyi sai Kai Ina abin gulma a wajenka,Hanifa ce ta shigo sanye da uniform ta dawo daga school tayi sallama ta wuce dakinsu,Can sai ga Rahma da Raheema sun shugo su biyu Yan matasan mata sun shugo suna fada akan biro daya ta sacewa daya biro,Omaira ce babba a ciki tsawa ta musu Kai dalla kuyi Mana shuru muna fama da talaucin mu Kun dame mu,Abbansu ne yayi magana yace ai ni rabon da naji dadi a duniya tun kafin nayi aure gaba daya banyi dacen mace ba,gashi yaran ma banyi dace ba gaba Daya an cika min gida da gwari Mace ai gwari ce, Ni kenan kudina su Kare a siyen gado da katifa kullum a bikin Yara nake har an gaji da zuwa daurin aure gidana,gaba Daya Kuma ba wacce ta auri me kudi duk talakawa suke kawo min ko wacce da kyar take Sha a gidan aurensu Ina za a iya taimakon Iyaye, Uwa ce ta fito daga dakinta mahaifiyar Abba kenan tana wani gadara tace Kai Kam sai dai Allah ya biyaka a lahira mace bata da aiki sai haifo Yara mata da wannan haihuwar ai gwara babu, sai da tayi Yan biyu a jere sau uku sabo da bala’i, su yaran ma da suna da kashin arziki da sai ace da sauki amma duk talakawa suke kawo mana, gashi duk wacce ka aura Suma duk matan suka haifo ta Gama cinye su da baki, Abba yace ai gashi nan wlh sai an aurar dasu tas Zan dinga ciyar da ita tunda haihuwar Mata ta zaba to sai dai su ci da kansu abinda Naga dama shi zan bayar a gidan,Umm ta kalle shi tare da tabe baki tace jahilci yafi hauka ciwo Allah ya ganar da ku, dake Umma itama bata da tsoro bata barin ko ta kwana Indai aka Mata.

Maheerah tayi tayi ta fita Cele ta tare hanyar haka ta juya ta koma Palo ta zauna tace Kuma Ni Zan fita ba ke ba gantalalliya Albakaratun,Al Himarun jaki to ke jaka ce me kawo mazan banza tana jinta Maheerah tayi Shuru tana saka muguntar da zata hadawa Cele,Cele Kuwa shiri tayi cikin Abaya tayi rolling ta bude kofa ta fice tare da cire key din kofar ta kulle Maheerah ta baya tayi ficewarta daga gidan gaba daya, ta fito taga hadadden gari ta bude hannaye tare da daga Kai sama tace iskar yanci haba har naga rana ai na samu sinadarin vitamin D a jikina,ta Fara tafiya tana nishadi tana zaga layin gashi layin manya ne tana tsoro Kar ta bace sai da ta gama yawonta mutane sai dai daiku ta gaji da yawon ma tace bari na koma gida Banga kowa ba ta juya kenan taji ance ke daga ina,sai data tsorata ta zaci gamo tayi ta juyo da sauri taga mace dattijuwa bahaushiya baka da ita tana yawo da katuwar jaka,harshen larabci ta juya taga Cele Fara ko ruwa biyu ce bata Jin hausa,Cele tace Sannu bakuwa ce ni ban fara Jin larabci ba,matar tace kin San a state din nan kazamin kame suke Yi idan Baki da sheda wallahi ki daina fitowa,Cele tace asibiti nake so naje wallahi bani da lafiya Kinga cikina kullum sai Naga ya Kara girma Kuma ayi ta motsi a ciki,Matar tace ni kin ganni Yar Jigawa ce ni mijina ne ke aiki a nan ya taho Dani muke zaune Amma unguwar da muke ba irin wannan bace ta manyan larabawa unguwa ce ta Yan fake fake, Cele tace okay Ashe kina Jin larabci? Matar tace ae Ina ji ni,tace Dan Allah ki Zama Aunty na Zan dinga zuwa kina koya min,Matar tace hmm baki da shedar Zama a kasar su wlh kamaki zasu yi matsayinmu na hausawa Zan dai dinga zuwa duk sati Ina koya Miki ki tanadi biro da takarda Cele tace na gode,Matar tace Sunana Hajiya Hauwau,Cele tace Rufaida Cele sunana,Zo muje na nuna Miki inda nake aiki Ni Yar aiki ce,Hajiya Hauwa tace to Suka taka Cele ta nuna Mata gidan,Matar ce tace muji cikin naki da yake girma ta taba cikin Cele tace Kan Uba ai ke ciki ne dake,waye ya Miki ciki Yar Nan? Cele tace ban gane ciki ba nifa bani da lafiya wallahi ban san da Namiji ba ma Sai dai idan ciwon koda ko Hanta ne ya kamani ko ciwon sanyi,Hajiya Hauwa tace wanne irin ciwon koda haihuwata bakwai nasan ciki nasan komai haba yarinya

Me yasa kuke zubar Mana da mutunci a idon duniya ne gashi nan kasashe duk sun Raina mu kadan ne ake samun na gari a takari me yasa haka da kuruciya da komai ki kwanta ki bawa Namiji kanki haba gaki wayayyiya,Cele tace ahhh karki kaini inda banje ba nace Miki na rantse da Allah ban San Namiji ba,Watanki Nawa rabon da kiyi al’ada? Sai lokacin Cele ta tuna rabonta da period ta Kai wata uku tunda tazo garin Saudi bata yi jini ba,tsoro ya kamata tace sai dai idan Aljani ne ya min ciki ai Rannan dama nayi mafarkin Ina sex Aljani ne idan cike ne to Aljani ne ya min wallahi bazan yafe musu ba Indai Aljanu ne idan ba su ba waye to.
Hajiya Hauwa ta kalli Cele Kawai tace muje ciki na rubuta Miki wasu kalmomin ki rike kafin na dawo,suka Shiga ciki tare Maheera ranta idan yayi dubu ya baci Cele ta hanata fita,sai ganin Cele tayi ta shigo da mace gidan Kuma ta sake kulle kofar ta cire key,tana kallonsu,Hajiya Hauwa tayiwa Maheerah magana da larabci tana gaisheta, Maheerah ta samu me Jin larabci sai zagi Kawai Wai ta shugo musu gida ba Izini,Cele tace kyale banza muyi abinda ya kawo ki ta shiga daki ta dakko littafin data gani Diary din Maheerah da take rubuta tarihin rayuwarta kaf ta dakko ta bude page din da ba rubutu ta mikawa Hajiya Hauwa tace rubuta nima tarihin koyon larabcina nane, Hajiya Hauwa tayi dariya ta Fara rubutu da Hausa larabcin ma da Hausa take rubutawa yanda Cele zata gane kalmomi masu ma’ana Wanda ya Dace mutum ya iya su ta koya Mata sabo da Zama da masu yare,Cele tace ya sunan ciki da larabci ciki na haihuwa ta rubuta mata,tace cuta fa Nan ma aka rubuta mata tana ta tambayoyi ana rubutawa sai da Suka Yi da yawa sannan Maheerah ta lura Diary dinta aka lalata Mata,tazo tana masifa da bala’i,Hajiya Hauwa tace wannan gidan naku bana zuwa bane Rufaida idan nazo Zan shigo na kiraki mu dinga haduwa a iya tsakar gida,Cele tace to ba damuwa ta rakata ta tafi ta dawo ta dauki Remote ta kunna channel din da ake nuna dakin Ka’abah ana ibada,Maheerah wani Tsaki ta ja ta fisge remote tare da canja channel ta Kai tashar larabawa masu rawa da damammun kaya, data gaji ma tashar turawa ta Kama me saka wakokin disco ta tsani a kamo Mata tashar Dake nuna wani addini.

Cele shareta tayi har Ahsan ya dawo driver ya shigo da shi har ciki,Yana shigowa Cele ta mike ana cewa marhabah marhababika ya Ahsan dariya yayi ba shiri Cele tana kashe Larabci, hannunsa ta jawo harda cewa ta’al ta’Ali na’am shuwayya tana rikeshi suna tafiya tana cewa shuwayya Shuwayya a kujera ta zaunar da shi tace Ijilis,Yace Jalasna Wai ya zauna,Cele tace ya gane ya Gane na Fara iyawa a tafa min tana tafawa kanta Yana ta dariya Idonsa sanye da glass baya gani Wai, Maheerah Tsaki taja da larabci tace bata iya komai ba Babu abinda ta iya sai lalata Mana yare,tasowa tayi zata ta dawo kusa da mijinta Ahsan,Cele da sauri ta kankane shi tace karki zo Mana mu,Maheerah Takaici yasa ta tafkawa Cele mari Ahsan da larabci yace plate ne ya fashe haka? Maheerah tace Marinta nayi na gaji da abinda take min idan ciki ne nace bana so na hakura a sallameta Ni wallahi Zan iya zubar da cikin ma kowa ya huta,Ahsan yace mari haka wanne irin zalunci ne wannan ki mareta,ciki baza a zubar ba Ina son abina,Cele tace bashi Kika ci wallahi Kuma bazan tashi ba mijina ne ta kwanta a jikin Ahsan Yana kokarin janyeta yace Haram ya Subhannallah ya Subhannallah, Cele tace kaji da shi ta sake narkewa a kirjinsa tace Ina nan ta Sosa kumatunta tace fata gata Fara ashe karfi ne da ita kamar bayan kada,Ido suka hada da Maheerah ta Mata gwalo tace ke dai ta ko Ina baki hadu ba fata kamar bayan kada, Ahsan Yana so ya janye jikinsa Cele tace Kai dai baka San Dadi ba kafi son waccen me duwawu Kamar shape din Albasa, tashi tayi taje kitchen zata kawo Masa shayinsu da Suka Saba Sha,Maheerah ta koma jikinsa ta kanmake mijinta Cele ta fito ta ajiye shayin tasa hannaye ta fisgo Maheerah,ita Kuma ta manne a jikinsa,Ahsan yace shayi zai Sha Cele tayi sauri ta ebo shayin a spoon ta Kai bakinsa Maheerah tace wlh bazan yarda ta kwace min miji ba sai dai muyi ta yi ta Shige kitchen itama ta hado shayinta da snacks ta kawo Suka tsaya su biyu akan Ahsan Cele tana bashi Shayi Maheerah ma ta ebo nata ta Mika Masa shi kadai yake dariya a ransa dukkansu ya dinga karba ko wacce ta bashi ya karbe Yana Sha,Maheera ta dauki Snacks Ana shafa Masa gashi noorul Qalbi ta Mika Masa ya gutsira Yana ci,Cele ma ta shafa gashinsa tace ni harda gemun Zan taba duk da ni Haram ce to nace Haram nima ta shafe gemu da gashin Kansa shi kuma Alhaji Salmau Yana zaune kurum abinsa,Maheerah ta duka zata Masa kiss a lips,Cele ta durma mata duka a gadon baya ta bangajeta ta kwace Snacks din itama Wai ita zata bashi Ahsan Yana ji Yana ta ci shi kam Mata biyu akansa suna ta masifa,Maheerah tana zuwa ta fisge shayin ta Kai kitchen ta zubar duka ta dawo ta kwace Snacks din ta maida kitchen tace ya koshi da larabci,Ahsan yace shi bai koshi ba Yana masifa,Cele ta fahimci me yake nufi ta Shige kitchen ta Dora indomie tana Mata hadin Nigeria Amma bata sa yaji ba,Maheerah ma kitchen da shigo ta dasa tukunya tana girkinta na larabawa itama Cele tana nata duk a cikin Ahsan za a bashi, Cele ta riga Maheerah gamawa.

Tana zuwa ta kawo Masa ta dawo dashi kasan carpet ya zauna tasa fork tana bashi a baki yana ci sai ga Maheerah ma da nata a plate ta zauna suke jere ita da Cele,Cele ta matsa jikinsa Kamar zata shige cikinsa Maheerah Kuma ta biyo da abincinta ta saman Kan Cele ta shallake zuwa bakin Ahsan,Ahsan ya gaji ya shiga surfa bala’i da masifa yace baya cin na kowa a cikin su sun dame shi ya mike Yana lalube da kyar ya koma bedroom shi Dadi ya isheshi Mata sai fada suke a kansa.
Maheerah ce ta bi bayansa harda sawa kofa key Kar Cele ta biyo ta,Cele tace zaki fito ma.

Kannen Wise su Uku Mata ne Suka zo wajen Wise sun kawo Mata Ziyara,Tunda Auta yayiwa Iyamami fata fata bata sake Shiga Harkar Wise ba sannan Iklima ma tsorata tayi ta gudu garinsu Amma har Yanzu Iyamami da sauranta,Kannen Wise Suka ce Aunty yau kwanan mu hudu ko kofar gida bamu je kisa a kaimu yawo,tace Zan kaiku da kaina amma Bari nasa Nawaf ya kaiku gidan su Rabi ku gaishe su,Wise a waya ta Kira Auta tace Autan mu,yace Ina jinki dan Allah su walida zaka Kai gidajen kawayena su Star,yace karfe nawa? tace 11am dai tunda yawon nasu da yawa,yace to su shirya Amma Kar a barni da jira, sun ma shirya su Kai suke jira kaga yanzu 10am yace to gani Nan.
Auta wanka ya dauka cikin kana nan Kaya kamar zai bar kasar 11:30am yazo yace ku fito Suka fito suna ta kallon Iyayin Auta,Walida tace gashi kyakyawa haka shi dai Auta bai San suna Yi ba har Suka je jikin mota yace Babbar ta shigo gaba,Suna kunshe dariya Walida ta shiga gaba,Yana shiga ya kunna uban kida,Walida tace wow haka nake son mota da kida amma sululu motar wasu ba dadi,Auta yace wannan motar manyan Yara ce ai,Suka ce munga alama,Iyamami ce ta wuce tana musu kallon banza a cikin mota tace ai fa mun shiga Uku an auri jinin kudi kullum dangi suna Nan Kai Kuma bawan Mata da kaga Mata shike nan sai ka kasa zaune ka kasa tsaye,Auta yace ya ranki ya rufe mota yaja yayi gaba,Walida ta zake da yawa ita a Dole sai ta nuna ita wayayyiya ce a wajen Auta,Bata San maza Indai mutum na kirki bane me zakewa da nuna ta waye bata birge su,Yan matan yanzu da yawa haka suke burinsu su nuna su fa sun waye suna wani fitsara Wanda wannan baya birge mazan.

Gidan Star ya Fara kaisu tana kitchen tana girki Malam Abhulkhair Yana ta yanka Mata salat ya zauna dirshan a kujera,ana Sallama Suka amsa Auta yace baki ne mu shigo,Malam yace Muna zuwa yace da namiji Nawaf ya balaga saka Hijab,Star tace to ta saka hijab har kasa ya bude kofa yace ku shigo Nawaf Kaine ka kawo kannen namu kenan? Yace ae suka zauna,Star yace Dan duniya shine baza a dinga zuwa gaishe bi ko ya Jin Dadi? Auta yace Jin dadi ai sai me aure Abhulkhair ya dinga dariya,Star ta kawo musu kayan ci da sha, Abhulkhair ya koma kitchen Yana kula da girki su kuma suna ta hirarsu,Auta yace Malam guda a kitchen ko ni da ba Malam ba ai baza a min wannan rainin ba,Star tace wlh karka cika baki yaro,sun dade a gidan Star sannan Suka tafi gidan Yar Zabil,Nan ma sun dade,sai gidan Mandula da Sera daga Nan Suka yada zango a gidan Nawwar daga nan sai dare ya maida su gida harda siya musu kayan makulashe.

Sabreen yau tana gidan Santana tana kallon soyayya Kawai burgeta sukeyi sai taji wani haushin kanta da Dana sani da yanda ta samu Miji na kirki ta tsaya shirme gashi yanzu Kamar Santana ma ta rasa, Bayan Santana ya fita Jamcy ta rakashi ta dawo tace sai rayuwarku take birgeni Jamcy idan na tuna abinda nayi Ina nadama gashi na rasa kowa ko me matar ma ban samu ba Kuma auren nake so,a shirye nake idan na samu Miji Zan daina Shan komai cuta dai na Riga na cuci kaina,Jamcy tace Ni kaina da ban zaci Zan so Santana ba sai gashi zabin Alkhairi kullum cikin nishadi nake sai Naga shaye shayen da Muka dinga Yi rayuwa ce Kamar ta dabbobin da Basu San me suke ba,a da har mijinki na so Sabreen na so na Miki kwace sabo da kin kasa fahimtar gaskiya shaye shayenki yayi yawa Amma hakan Bai faru ba Nima ban cimma burina ba Allah yasa aka hadani da Santana wannan rayuwar ta fimin daraja da mutunci akan shaye shayen da ya Zama ruwan dare ga Mata da maza Ni Kam na daina Ina Miki Addua kema Allah yasa ki daina, Sabreen tayi mamaki tace yanzu da Nawwar yace Yana sonki sai ki yarda? Da gudu wallahi ke dai Allah ya kiyaye Kawai,Sabreen ta Sha mamaki tace rayuwa kenan gashi na rasa kin rasa shike nan,gobe Zan tafi garin su Mama zanje nayi sati daya,Jamcy tace Allah ya kaimu Dan Allah ki gaishe min ita,zata ji Inshaallah.

Mami yau taji Baffa zaizo Auta ya fada Mata tun sassafe take gyara part dinta tana kalkale kalkale sai kamshi da sheki ko ina,ta shirya girki lafiyayye taci kwalliya cikin hadadden leshi sai kace wata budurwa harda sa Riga da skert sai kace wata matashiya haka Mami ta koma ta kafe dauri,Nawwar bai sani ba ya dawo daga Office part dinta ya wuce direct tun daga Shiga yake karewa ko Ina kallo dan gyaran na daban ne,Mami ya samu a bedroom ta tsaya jikin mudubi tana ta kallon kanta tana zancen zuci ita kadai,shiga yayi da Sallama ta juyo da sauri,ya bita da kallo yace amma party Zaki je ko? Party Kuma bana son Iskanci yau ka taba gani Ina saka Riga da skert,Uhmm Nawwar yace ko dai bako zakiyi,ban sani ba karka dameni da tambayar masifa bana son irin wannan Auta ma Nema yake ma ya fiku hankali, Nawwar yayi dariya yace Baffa yace Auta ya fini kema kince Auta ya fimu ai shike nan,Duk yarana babu me sanin yakamata irin Auta Kai ai girman banza ne dakai,Nawwar yace yau Kuma Mami,Allah ya baki hakuri ga Auta nan Indai shine,Kudin da Kika ce na tura Miki tace na gani na gode Allah ya Kara budi yace Ameen ya juya ya fice, Yana shugowa bangarena na buya a bayan kofa na tsorata shi

Dariya yayi yace Dan cikinki Zaki tsorata ba ni ba Muka haura sama,nace yau akwai show a gidan nan yau Baffa zaizo inji Auta,Nawwar yace no wonder ai naji a jikina bako Mami zata yi irin wannan kyau haka yau,ba a dade ba Driver ya kawo Baffa sai kace wani Ango ya Sha fararen Kaya harda babbar Riga sababbi gal,tare da Auta aka zo shine dan Kira shine me iso,Palo Suka shiga da sallama Auta yaga gyaran Mami sai dariya yake boyewa ya haura sama yace Mami yazo fa ki fito,Mami harda bata rai Wai aji tace gani nan,Auta ya dawo yace Baffa gata nan,Baffa yace to jeka abinka,Auta ya fice ya dawo part din Nawwar ya barsu.

Bayan sati Daya Maheerah ta shirya da dare zata fita Ahsan Yana Main palo Cele ma haka da littafinta tana bitar larabcinta a gabansa idan ta fada da yarensu sai ya gyara Mata yanda ake fada dai dai tana fassarawa da Hausa shima sai ya rike hausar yasan me ake nufi a haka suke karatun,Cele ta kalli Maheerah tace da tsohon Daren nan Zaki fita gidan uban wa zaki je wato kwartanci Zaki tafi kenan to baza ki fita ba,Maheerah ba Jin hausa take ba ta juya zata fita Cele ta riko rigarta tace wlh sai dai ki Kira kwarton gidan nan yazo na ganshi idan da rambon Zan masa bille kaciyarsa to yazo,Maheerah bata sani ba ai kuwa ta koma daki tace da Saurayinta yazo gidan tunda dai mijin Nan nata baya gani ita a bukace take yaga wancen karon yazo ya fita lafiya,wannan karon ma sai yazo a gaban Ahsan Suka wuce ciki,Cele dama labewa tayi a dakinta suna shiga ta fito ta dakko sabuwar reza data gani a dakin, Maheerah ta nemi key din dakin ta rasa haka ta kulle ba key sunyi tsirara a dakin suna Masha’arsu Cele ta Shige ciki,Balaraben nan yayi mugun tsorata,da larabci yace wannan wacece? Maheerah tace wacce aka yiwa dashen ciki ce ta dameni ta hanani sakewa Ina ganin Nan gaba gidan nan Zan bar mata shi Kuma Ahsan baya so a taba ta ko kadan na gaji,Saurayin yace Yana makahon ya Zama miskini Amma ya dinga takuraki,Cele taji ance miskini tace na miskinawa Uwarka zagi,tace yau sai na maka bille a kaciyarka shege me Kan fir’auna ta nufe su Suka tsorata sunga ta zaro reza tace wlh sai na Miki bille a Fuska irin na Nigeria Zaki ci ubanki yau,na taba ganin Yar iska irinki da mijinki sabo da baya gani ki koma kawo kwarto,rayuwa Kamar ta dabbobin dama haka kike yi ku ba kunya ba tsoron Allah,na taba ganin tashin hankali irin wannan wannan wanne irin masifa ce wallahi yau baza ku tafi free ba.

 

BAN YARDA A MAIDA MIN DA NOVEL AUDIO BA BABU IZINI NA,MASU AUDIO KAR KUCI HAKKINA

GA MASU SIYAR MIN DA LITTAFINA BAN SANI BA KU SANI KUN CI HARAMUN WLH KO NI KYAUTA NA BAYAR KUNA SIYAR MIN DA NOVEL

 

 

 

AsmaBaffa
08061929616
[8/9, 10:59 PM] +234 806 192 9616: ‘YAR AIKIN KARUWAI 2
MATAFIYA

BOOK 2

26-30

Official

By
AsmaBaffa

SADAUKARWA NE GA
ZAINAB USMAN

MASU AUDIO DUK WACCE TA MAIDA MIN NOVEL AUDIO BA IZININA TACI HAKKI NA TACI HAKKIN WACCE TA SIYA,KUJI TSORON ALLAH.

PAKE NAKU NE

 

Ina masu bukatar unique kitchen utensils . fabrics adult and children’s wears shoe’s and bag’s.
Da masu bukatar ahada musu lefe ko masu bukatar iya luggage’s din kawai duk inkazo
R&U EXCLUSIVE KITCHEN AND MORE.
Zaku samu duk abinda kuke bukata ko a awanne state kake zaa kawo

Masu bukata ga number. 0703 455 9202

https://chat.whatsapp.com/LAizQA6PofSLoFhQ7XeaQx

Check Also
Close
Back to top button