Garin Dadi Hausa NovelHausa Novels

Garin Dadi 7

Sponsored Links

©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION.*
_(Home of expert & perfect writers?)_

 

*GARIN DAƊI……!*

 

_*NA*_

*_UMMI A’ISHA_*

*Wattpad:ummishatu*

From the writer of

KAMAR DA WASA
KUMALLON MATA
MIJIN MATACCIYA
SO DA ALAƘA & REST…..

*7*

 

~~~Hawaye ne kawai ke faman sintirin kaiwa da komowa akan kumatu na yayin da bakina ya kasa furta koda kalma guda,

“Abba hakan da kayi shine daidai, haka kawai yarinya tana neman ta mayar da mutane ƙananan mutane…..” yaya Abdul hakim ya faɗa bayan ya miƙe yana ƙoƙarin fita daga cikin falon, ni ɗinma mama kamani tayi muka fita har lokacin ban bar zubar da hawaye ba,

Kai tsaye sashen mama muka shiga wadda dama tun can ni a sashenta ɗakina yake, zaunar dani tayi kan kujera sannan itama ta zauna kusa dani ta soma rarrashi na,

“haba widat…. Ya ina yi miki kallon mai hankali kuma kina ƙoƙarin ɓata rawar ki da tsalle? Ringiɗi ringiɗi aka yi maganar nan sai yanzu zaki dawo ki cewa yaron nan kin fasa auren sa bayan duka burikansa sun ta’alaƙƙa ne akan ki….. Ai Kinga kamar ba a kyauta ba idan aka yi masa haka ko? ”

Cikin shassheƙar kuka na ɗago kaina na kalli mama,

” mama wallahi bana sonshi, ban taɓa son yaya Faisal ba koda na aure shi kawai zan zauna dashi ne amma ba dan wai ina son shi ba ”

Jijjiga kai mama tayi tace” na fahimceki amma kin san abin da nake so dake? ”

” a’a…. ” na faɗa cikin kuka,

” ki kwantar da hankalinki ki cigaba da addu’a, kin san sau dayawa muna son abu amma kuma ba alkhairi bane atare damu, wanda kuma muke ƙi sai kiga daga ƙarshe ya zame mana alkhairin, dan haka abin da nake so dake shine ki daina wannan kukan ki share hawayenki kiyi addu’a akan Allah ya tabbatar miki da koma menene in dai shine alkhairi agareki duniyar ki da lahirarki…. ”

” to mama”

Sai da ta ɗan sake yi min nasiha sannan na tashi na wuce ɗakina naje na cigaba da kuka na, ina yi ina tuna hashim yanzu kowacece zata iya sonshi har ta aure shi ta bashi irin kulawar da nake mafarkin bashi a koda yaushe? Da zarar na tuno wannan lamari sai inji na kasa jurewa.

Yinin ranar haka na yishi cikin damuwa da koke koke domin wuni nayi cur ina cikin ɗaki in banda kuka babu abin da nake yi a haka har ƙawalli ta zo ta iskeni, ganinta sanye da hijabin makaranta hakan ya tabbatar min da daga islamiyya ta dawo ko gida bata je ba ta shigo wurina,

Ganin yanayin da nake ciki yasa ta faɗin “subhanallahi, ƙawalli lafiya kuwa? Ko dai baki da lafiya ne?” ta ƙarasa maganar tana zama kusa dani, murya ta a dashe na tashi zaune kuma har lokacin kayan bacci ne ajikina dan yau ko wanka ban yiba,

“ƙawalli gara rashin lafiya da wannan halin da nake ciki…. Su Abba sun yanke shawarar aura min yaya faisal duk da na faɗa musu gaskiya cewar bana sonshi…… Saboda jiya da daddare na faɗa masa abin da ke raina cewa inada wanda nake so shine ya zagaye yaje ya fadawa yaya hakim, shi kuma ya faɗawa su abba….. ”

” gaskiya ƙawalli lamarinki yanzu yana bani mutuƙar mamaki….. To menene abin damuwa dan su abba sun yanke hukunci akan ki…. Ki sani fa duk zaɓin da zasu yi miki ba zai taɓa zama sharri agareki ba sai dai ya zama alkhairi…. Dan Allah ki daina irin abubuwan nan na marassa ilmi, ni wallahi har kin sa naji raina zai ɓaci….. ”

Jajayen idanuwana na buɗe na kalleta, lallai duk yadda aka yi ƙawalli bata san zafi da raɗaɗin rabuwa da masoyi ba shiyasa take furta irin waɗannan kalaman, ni dai har ta ƙaraci faɗanta ta tafi bana fuskantar abin da take cewa, bayan tafiyarta ina zaune kan sallaya bayan na idar da sallar magariba mama ta shigo cikin ɗakin,

“ƴar mama taso mana…. Zo muje maza”

Tashi nayi nabi bayanta har zuwa falonta, abinci ta nuna min babu musu na zuba na fara ci ba wai dan yana yi min daɗi a bakina ba, bayan na gama mama ta sake yi min nasiha sannan tace in je inbaiwa Annie haƙuri dan da alama fushi take dani kuma fushin iyaye akan ƴaƴansu babu kyau, kamar yadda tace haka na tashi naje na samu Annie tana zaune kan carpet ɗin salla da carbi a hannunta tana ja, durƙusawa nayi agabanta na fara bata hakuri amma har nayi na gama bata kulani ba, tashi nayi na fita na koma ɗakina na cigaba da zaman ƙunci.

Har weekend ɗinnan yaci ya cinye cikin damuwa nayi shi ranar Monday kuwa ban iya fita aiki ba nidai duk gani nan ne damuwa ta taru tayi min yawa, daren ranar ban san me ya faru ba kawai dai naga mama ta shigo tace in je abba na kirana, hijabi na nasaka na fita, yana zaune falonsa yana cin tuwon dare, tuwon biskin masara miyar taushe zama nayi gabansa na fara gaishe shi, ɗagowa yayi ya kalleni,

“maimunatu….. Har yanzu wannan maganar tana ranki tana damunki?”

Girgiza kai nayi alamar a’a sannan cikin sanyin murya nace “a’a abba na yarda da duk zaɓin da kayi min”

Murmushi naga yayi ya cigaba da cin tuwonsa kafin daga bisani ya sake ɗagowa ya kalleni,

“maimunatu kina son faisal? Ma’ana zaki iya zama dashi a matsayin miji agareki ko zuciyar ki bata aminta da shiba?”

Girgiza kaina nayi alamar zuciya ta bata aminta dashi ba, abba bai ƙara magana ba har sai da ya kammala cin abincinsa sannan yace dani,

“maimunatu bazan yi miki auren dole ba, domin mune a koda yaushe muke yi wa mutane nasiha akan kar su aurar da yaransu ga wanda basa so, mu alƙalai mune muka fi kowa sanin haɗarin dake tattare da wannan al’amari domin mune ake kawowa ƙara muke ganin cases kala kala sanadiyyar auren dole, ko yau ɗinnan sai da nayi shari’a makamanciyar wannan, tunda bakya son faisal to bazan tilastaki ba, kije Allah yayi miki zaɓin miji na gari ki kawo duk wanda kike so in dai mutumin kirki ne zan aura miki shi….. Allah yayi miki albarka ”

Wani sanyi naji yana ratsa zuciya ta cikin farin ciki na sunkuyar da kaina nace” nagode abba, Allah ya ƙara lafiya da tsawon kwana ”

” amin tashi kije ”

Tashi nayi ina fita na ruga a guje zuwa cikin ɗakina ina shiga na dungura akan gado na sake dungurawa haka nayi ta yi dan tsananin farin ciki, yau kam faɗar irin halin murnar da nake ciki ɓata baki ne,bacci kuwa harda minshari dan har makara nayi.

Washe gari kamar koda yaushe lokacin da naje gaida Annie bata amsa ba dama kwana biyu bata amsa ni, har na juya zan fita naji tace “zo nan”

Dawowa nayi na tsugunna,

“widat haka kika ga ya fiye miki ko? Kin fi so kiyi ta zama agabanmu babu aure ko, yanzu menene laifin yaron nan faisal, inane zai je neman aure a hana shi? Baida wata makusa sai awurinki da kikace bai yi miki ba”

“Annie kiyi haƙuri, ki cigaba da yi min addu’a insha Allah zan kawo wanda yayi min”

“Allah ya zaɓa miki mafi alkhairi ya baki nagari mai sonki da gaskiya”

Tashi nayi na fita naje na ƙarasa shiryawa domin tafiya aiki, yau ma ta gidan su hashim na fara biyawa na kuwa iske shi yana nan bai fita ba,

“yau ma na zaci ba zaki zo ba ai, gashi ban san inda zan je in nemoki ba, lafiya kuwa jiya naji shiru?” ya faɗa bayan mun fito daga gidan domin tafiya,

“lafiya Lau hashim, jiya dai ban ji daɗi bane sosai shiyasa”

“ayya shiyasa ashe naji jikina nima babu daɗin, ashe ƴar kyakkyawata ce bata jin daɗi”

“hashim kenan, wai waye ya faɗa maka ni kyakkyawa ce? Kama cire wannan tunanin daga cikin ranka dan bana so ranar da idonka ya buɗe ka ganni ba yanda ka zata ba”

“hmm maimunatu kenan…. Wallahi a duk yanda kike kin yi min, ko yaya kike ina son ki kuma bazan taɓa dainawa ba, ko duk matan duniya kinfi su muni to ni awurina kinfi kowacce mace kyau… Bana jin zanga wata mace wadda tafi ki kyau a idanu na”

Irin waɗannan kalaman na hashim sune ke ƙara min ƙwarin gwiwa wurin ganin na cimma ƙudurina na taimakawa rayuwar sa musamman ma yanzu da maganar aurena da yaya faisal ta gama rushewa, so da ƙaunar da muke nunawa junanmu abin ba a cewa komai, koda yaushe muna tare, sau da yawa na kan gayyaceshi muje film house cinema duk da ba idanu gareshi ba amma hakan na lura yana saka shi farin ciki sosai, duk inda na san zai ɗebe masa kewa ya sanyashi farin ciki ina kai shi, wuraren shaƙatawa da tanɗe tanɗe gami da lashe lashe duk mukan je kuma babu wanda zai ganshi yace makaho ne dama kuma na siya mana wasu glasses masu kyau ta jumia iri ɗaya baƙaƙe koda yaushe shi yake sakawa.

Yau dai na shirya tsaf domin aiwatar da ƙudurina da na jima ina shiryawa akan hashim, sai da nayi musu siyayyar kayan abinci kamar yadda na saba duk ƙarshen wata sannan naje gidan, kamar koda yaushe godiya da albarka iya keta faman saka min bayan ta tsagaita na kalleta cike da kunya nace,

“iya dan Allah zan ɗan yi miki wata tambaya, wai dama hashim da wannan lalurar aka haife shi ko daga baya ya haɗu da ita?”

Shiru naga tayi kafin ta nisa tace dani,

“a’a lafiya lau ras aka haife shi da idanuwansa… Saida ya fara girma ma ya kai kimanin shekaru takwas sannan wani al’amari ya faru dashi wanda shine kamar silar makancewarsa….. Wani mafarki yayi wani abu adunƙule mai duhu yazo ya daki idanuwansa shikenan ya tashi babu ido… Magani mun yi har mun gaji tun mahaifinsa yana raye, kuɗin da muka kashe ba zasu lissafu ba dan kayan ɗakina duk anan suka ƙare wurin nema masa magani amma ba ayi dace ba, sai lokacin da mahaifinsa yana kwance yana jinyar ajali wani amininsa ya iyo masa aike daga ƙasar chadi cewa an samu mai magani acan wanda insha Allah ana saka ran wai idan aka kai hashimu wurinsa to zai samu waraka amma mu dai har yau ba mu samu zuwa ba domin kuɗin da aka yanka sunyi yawa ba kaɗanba. ”

Ajiyar zuciya na sauke ina godiya ga Allah acikin raina domin insha Allah komai yawan kuɗin a shirye nake in nemo inbada in dai idanuwan masoyina zasu buɗe zai ganni kamar yadda yake mafarki kullum maganarsa yana son yayi tozali da kyakkyawar fuskata koda sau ɗayane a tarihin rayuwarsa…………..

*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*

*_Ummi Shatu_*

Back to top button