Yar Zaman Wanka 37-38
*IMRAN*
Bayan an idar da sallar ya kira Sadiya a waya suka yi magana a kan snacks da zai siyo wanda za a raba a suna, dama saboda ma Hassan sai suka shawarta ba sai an zo gidan an yi wani abin rabo ba dan haka sai ya ce a sayi lemuka kawai in ya so sai a haɗa da snack dan hatta jakar da za a saka kayan duk ya bayar a yi yanzu zai je ya karɓo. Bayan sun gama wayar Inna ta kalli Sadiya ta ce.
“Halima ki tabbtar dai kin ɗauka min kyak (Cake) Ɗin mai yawa da dannat(Donot) Ɗin nan dan wallahi ina so Tsahare ta tafi da kayan sunan nan himili guda dan bana so ta je ƙauyenmu babu kaya mai yawa ƙwara ta je da abin arziƙin da za a daɗe ana batunsa a ƙauyen” Ta faɗa tana tashi ɗauke da kwanukan da ta ci abinci. Da kallo kawai Sadiya ta bita.
Bayan Inna ta wanki Husaini ta shirya shi lokacin Sadiya tana bayi tana wanka Imran kuma bai dawo ba, ƙaran bugun da ake yiwa ƙofar gidan da alama ma ba wai da yatsu ake ƙwanƙwasawa ba, hannu kawai aka jimƙe, ake faman doka ƙofar Inna tana zaune ta yi ɗai-ɗai tana ji amma ko alamar tashi bata yi ba bare a sanya ran za ta buɗe. Hannu ma ta sanya ta ɗakko wani lemo a frige da ta sanya wanda ta fasa ɗaya daga cikin cartoon ɗin da za a raba, buɗewa ta yi tana sha tana lunshe ido.
“Kai duniya budurwar wawa, wallahi daɗi da sanyin lemon nan har tsakar kaina, wayyo Tasalla gaskiya ana yi ba ke ni bana jin ma Tasalla ta taɓa shan lemon roba amma dai zan daure in danne kishi na in baiwa Tsahare robobi guda biyu wanda aka shanye lemon ta kai mata ta tsage ɗan ƙasan robar da ake bari da bai fi cikin cokali ba, ta suɗe in ya so ta ajiye robobin take ganin hoton lemon na jikin robar tana jin haushin ina ma tana da ƴan uwa a birni take shan lemo” Cewar Inna a ranta tana dariyar mugunta, tana ɗaga lemonta tana sha hankali kwance.Wani uban bugu da aka yi wanda ya sanya Inna zabura har lemon ya tafi wa Inna ba shiri har yana biyo wa ta hanci, robar ta ajiye ta tashi a fusace ta yi hanyar ƙofar gidan, tana zuwa ta ce
“Wai uban waye yake wannan bugun kamar wanda yake binmu bashi?”
“Buɗe ƙofa uban Jamila da Jamilu ne Malam Isuhu mai haddar izufi sittin wata kan wata” Ta ji an bata amsa. Shiru ta yi tana son gano inda ta ji wannan sunan kafin ƙwaƙwakwarta ta tuno mata ta sanya hannu ta cire jamlock ɗin a fusace ta buɗe ƙofar Idanunta ne suka sauka a kan wani ƙaton mutum da manyan kaya har da babbar riga ga wani hirami ya naɗa a kansa sai ka ce gammo ga wani carbi irin mai dubun nan guda biyu yana riƙe da su hagu da dama. Sai wasu manyan ƙartin maza guda biyu suna tsaye su ne ke bugun ƙofar shi kuma yana tsaye ya kame sai jan carbunan yake hagu da dama bakinsa yana motsi mismis. Mazan guda biyu ɗaya yana riƙe da manyan dorina guda biyu ɗayan kuma galan irin na mai da wata hula da alama wani abu ne a cikin hular.
“Ikon Allah kun yi ɓatan kai nan ai ba turu bane, ba kuma gidan maza bane(Gidan yari) Cewar Inna tana galla musu harara tare da sanya hannu a hancinta ta fato sauran lemon da ya biyo mata ta hanci dan har lokacin bata daina jin zafinsa a hancinta ba.
“Ke tsohuwa ki iya bakinki ba a faɗa mini magana” Cewar Malamin daga inda yake tsaye ya cigaba da jan carbunan kamar ba shi ne ya yi maganar ba.
“To fa lallai yau ake yinta to buɗe idonka da kyau ka gani Azumi ce ba matarka bace, har ni za ka kalla ka wani ce in iya bakina yo Allah na tuba kai har ka ma isa, yo meye a cikin ido banda ruwa”
“Ki kama bakin ki Iya” Cewar ɗaya daga cikin Mazan nan.
“Oh abin da ya sa kuka riƙo dorinai dan ku daki mutane to indai zan daku ga wurin nan, dan wallahi sai uwaku ta yi da na sanin haihuwarku”
“Ba ta duka ake ba tsohuwa muna jiye miki Malam ya fusata ya maidaki tsuntsuwa” Cewar ɗaya yana kallon Inna da ta yatsina fuska tana kallon Malam ɗin da ke ta jan carbuna, a shelaƙe.
“Ah jemage zai maidani, ko baka ji ba na ce jemage zai maidani, ko ya maidani ɗan tsako in hakan bai masa ba ma zai iya maidani tururuwa”
Gabaɗaya sai suka maida Inna kamar TV kowa kallonta yake cike da mamaki yadda ta haƙiƙice take magana babu tsoro ko ɗarr a tare da ita bayan kuma sun san Malam ɗin yana yiwa mutane kwarjini.
“Ki faɗawa masu gidan Malam Isuhu ne da ya zo cirewa Hassan aljannu wanda Hajiya Amina ta turo” Cewar Malan dan ya ɗan ji shayin Inna ya ga kuma tana neman kunyata shi a gaban almajiransa, manyan almajiransa ne da ya riƙe tun suna yara har suka girma yanzu sun zama manyan garada amma da yake ba wani karatun kirki ake a makarantar ba har yau ba su yi sauka ba, kawai ya ajiyesu in zai je yin ruƙiyya ya tafi da su suke danne masa mai aljanin saboda majiya ƙarfi ne.
Shiru Inna ta yi sai lokacin ta tuna da inda ta ji sunan wato wanda Amina ta faɗawa Imran a waya zai zo. Kallon Malamin ta yi ta ga yadda ba ya barin bakinsa ya huta da mismis ko ambaton Allah yake ko kuma dan a ce yana yi ne shi dai ya sani.Jibgegiyar babbar rigarsa ta bi da kallo sai wani baza ta yake yana wani bada faɗi shi a dole Malami. Wata ƴar dariya ce ta suɓuce mata wacce a ranta ta so yinta amma ta kufce ta fito fili.
“Dariya kuma?” Cewar Malamin yana kallon Inna dan ya ɗauka ta gane shi ba wani Malami bane kawai dai yana son a ce ya yi suna amma ko almajiransa ba wani tsayawa yake a kan su, su yi karatu ba kawai dai ya ajiye su ne dan yawanci duk su ke ci da masa gida idan sun samo abinci. Da kuma aikin ƙarfi da suke duk wajensa nemansu ke ƙarewa.
” Lah dariyar farinciki ce na yi ganin babban Malami ya zo gidan nan, ashe kai ne Malam Isuhun da ake ta labari, yo da na san kai ne ma ai da tuni kuna cikin gidan nan kuna gabatar da aikin” Cewar Inna a fili a ranta kuma ƙwafa ta yi tana fatan Allah kai damo ga harawa.
Wani uban washe haƙoransa da basa samun wanki Malamin ya yi, ya ƙara gyara zaman babbar rigarsa jin Inna ta ce ana labarinsa ai tuni ya ji kansa ya fashe ya masa wani gingirim.
“Haka ne ai duk yankin nan da ni ake ji kuma da ni suke ƙafafa a matsayin babban Malamin da ya yi fice”
“Gaskia dai na ga alama” Ta faɗa a ranta a fili kuma ta ƙara washe baki ta ce.
“Allah ja da ran Malam ai na yi komai cikin rashin sani ne, bari na maka iso dan babban Malami kamar ka ba ya shigo ba tare da an kintsa ba saboda girmama wa” Ta faɗa tana juyawa ta koma cikin gidan, tana zuwa ta ɗauke robar lemonta ta shanye tas, ta ɗauke Husaini ta mayar da shi ɗaki, shi dama Hassan yana ɗakin bata fito da shi falo ba dan ba wanka za a masa ba dan yana siffar miciji. Kallon Hassan ɗin ta yi ta fashe da dariya har da ƙyaƙyatawa ta ce a ranta.
“Yau akwai daru” A fili kuma ta ce.
“Hasanunu bawan Allah kana da baƙon Malami”
Suna nan tsaye sai gata ta dawo ta ce su shigo. Matsawa gefe samarin suka yi Malam ya shiga gaba su kuma suka take masa baya suna wani wasa shi tare da koɗa shi sai ka ce wani basarake. Har falon Inna ta shigar da su Malam ya samu wuri ya zauna a kan kujera haka almajiransa ma suka zauna a ƙasa dan girmamawa. Inna da ke ƙoƙarin zama a kujera almajiran Malam suka ce.
“Iya ba a zama a sama idan Malam yana zaune sai dai ki zauna a ƙasa”
Galala Inna ta saki baki tana bin su da kallon mamaki, shiru ta ɗan yi ta dakata da zama a kujerar ta kallesu ta ce.
“A min afuwa ƴan samari jikokina, ai ban sani ba, kuma ni ma na yi tunanin hakan ai girman Malam ne a masa komai” Cewar Inna tana neman ƙasa ta zauna. Malam Isuhu kuma sai ya fara wani gyara zama yana wani ƙara jan carbunansa bakin nan kwa sai mismis yake.
“A wane ɗakin aka kulle marar lafiyar? Dan yau ƙaryarsu ta ƙare sai mun fitar da kowa daga jikinsa” Cewar Malam yana wani gyaɗa kai.
“Eh gaskiya kam da ana samun irinku ai da aljannu ba za su yarda ma su zauna a jikin mutane ba” Cewar Inna tana ɗan ƙunshe dariyarta.
“Hakane kam ai nan da kika ganni ba na barin aljani sosai muka zuba artabu da su har sai sun gaji sun sakar min ragamar tare da bani haƙuri da kuma yin alƙawarin barin jikin mutum har abada” Cewar Malam yana nannaɗe hannun rigar kamar wanda aka ce za a hau dambe da shi.
“To Allah gafarta Malam yanzu za a fara aikin ne?” Inna ta faɗa cikin ɗan girmamawa.
“Haba tsohuwa ya ba a tsadance ba za ki ce a fara aiki ai sai an tsadance tukunna mun daidaita na ji nawa za a bani”
“To gafarta Malam kai kake yanke abin sadakar da za a baka kenan”
“Eh” Kawai ya ce yana wani ɓata rai ganin Inna ta ce wai yana yanke abin sadaka, ita ma Inna baki ta taɓe ta ce.
“To bari matar gidan ta fito daga bayi sai ku tsadance”
“To” Kawai ya ce ya ɗauki carbunansa wanda ya ajiye lokacin da zai naɗe hannun riga ya cigaba da laziminsa.
Suna nan zaune sai ga Sadiya ta fito daga wanka da sallama ta shigo da yake ma ta shiga da hijab wanka sai ta sanyo abinta gaishe da Malam ɗin ta yi sauran samarin suka gaishe ta, haka kawai ta ji haushin ganin su musamman da ta ga uwar dorinan da suka zo da su, ban da sirikarta ce ta turo Malamin nan da babu wanda ya isa ya shigo mata gida da sunan wani abu.
Ɗaki ta shiga ta shafa mai ta sanya kaya ta ɗoro hijab ta fito da yake Inna ta ce ita ake jira falon ta dawo tana ƙoƙarin zama a kan kujera Inna ta dakatar da ita tana nuna mata cewa Malam ni kaɗai ya kamata ya zauna a sama. Mamaki duk ya hana Sadiya cewa komai ita abin da ya fi bata mamaki ma yadda Inna ta yarda ta zauna a ƙasa kuma take wani kaffa-kaffa da su tana wani sanyaya murya sai wani baiwa Malam ɗin girma take.
” Wato jiranki dama muke tun da me gidan naki baya nan za mu ƙididdige abin sadakar da za a bayar na aikin fidda aljanin”
Wani zaro idanu Sadiya ta yi jin wai ya ce za a fitar da aljani gabaɗaya ta diririce amma kuma Inna ta mata alama da kar ta furta komai kan hakan babu yadda ta iya ta yi shiru da bakinta.
“Wato za a bada dubu hamsin sannan ƙwaryar nono mayan manya guda biyu, da ƙwaryar zuma ɗaya sai kuma ƙwaryar dabino dukansu manya” Cewar Malam yana wani gyara zama. Daga Inna har Sadiya sa kallon mamaki suka bishi, Inna ce ta yi karaf ta ce.
“Haba Malam sai ka ce wanda za ka ɗauki aljanin da hannu ka fitar dashi, in ce dai addu’a za ka yi ya fita kawai to wannan kayan ko aljanin ne zai tafi da su wato toshiyar baki za ka bashi” Cewar Inna tana kallonsa.
Wani irin haɗe fuska Malam ya yi ya fara wani zazzare ido cikin kaushin murya ya ce
“Babu wanda zai muku wannan aikin in ba ni ba ko da kun samu wanda zai muku to ba zai muku aiki kamar ni ba, ko da an fitar da aljannun to za su dawo ne”
“Ikon Allah to wallahi da sake dubu hamsin fa ga ƙwaraken nono da na zuma kai wai har da dabino, yo ai ka manta ka ce da manyan zabbi riƙaƙƙu guda bakwai” Inna ta faɗa ita ma tana ɓata ran.
“Idan baku da kuɗin mu za mu tafi”
“Yo Allah na tuba ku fi ruwa gudu mana, indai kuɗin nan da ƙwaraken abubuwan nan za a bayar wallahi ƙwara mijina Malam ya zo ya yi aikin a bashi kuɗin ni ma in san na mori wani abu nono da zumar kuwa da dabinon ma tsakurawa Tasalla a farar leda ladan ganin ido mu ajiye muna cin kayanmu, da dai a baka kai kaɗai da ranka ni ma ai matar Malam ce kai ni da kaina ma sai in yi aikin”
Wata uwar harara ya jefawa Inna ya ce
“Babu mai ja dani sai wawa, dan duk mai hankali ba zai ja da Malam Isuhu ba dan hukuncin Malam ba ya yin kyau” Ya faɗa yana kallonsu.
“Yo Allah na tuba ni zaka faɗawa haka? To kalleni da kyau fara nake ba baƙa nake ba ruwan sama ne ya wanke ni ruwan datti ya ɓata ni da zaman ƙauye ne ya mulke ni, Allah na tuba me zaka min wallahi ni Azumi matar Malam na sha tabara na sha lahaula”
“Allah gafarta Malam a bar aikin kawai” Cewar Sadiya cikin sanyin murya dan dama ita bata son wani aiki kawai an tashi an ɗakko wani Malami tausayinka sa sauƙi har da wasu uban dorinai ko wa ma za a duka da dorinan.
“Gidanku Sa’adiyya babu mai fasa aiki Malam indai aikin ka ya yi to za a baka duk kan abin da ka buƙata” Cewar Inna da ta danne fushinta tana ɗan murmushi.
Shi ma murmushin ya yi ya ce
“Yawwa ko ku fa ai duka abin da na lissafa haƙƙina ne a bani dan Allah kaɗai ya san artabun da za a yi da mu da su”
“Babu komai ai komai ma aka bada ba faɗuwa aka yi ba” Cewar Inna cikin sanyin murya. Sosai Malam ya ji daɗin maganar Inna yana wani jin kamar ya tashi ya taka rawa dan murna dan tun da yake ko aikin dubu uku bai taɓa yi ba amma gashi zai yi na dubu hamsin har da wasu kaya a ka.
“A kaimu ɗakin mu fara aikin” Ya faɗa yana gyarawa carbinsa ruƙo a hannunsa.
“To Malam bari ina zuwa sai na muku iso” Cewar Inna ta tashi Sadiya kwa da kallo ta bita dan ta san dai ba a ƙarƙewa ƙalaw da Inna. Tana shiga bedroom ɗin sai gata ta ɗakko Husaini da gadonsa ta kawo shi falon.
“Ikon Allah haihuwa ka yi a gidan ma kenan?” Cewar Malam yana kallon Husaini.
“To kenan Hajiya bata masa bayani ba ko me ?” Cewar Sadiya a zuciyarta.
“Eh haihuwa aka yi har gobe ma suna ” Cewar Inna a fili tana ƴar dariya. Azuciyarta kuma ta ce da alama dai Amina babu abinda ta sanar maka”
*Masu fitar min da littafi ku sani haƙƙina ne, kuɗin karatu kawai kika biya, ke ma da kike karantawa haƙƙina ne tun da baki biya ni ba ina so ku san da haka!*
09030283375
[24/03, 5:14 AM] Mom Mashkur First class: *MAMAN AFRAH DATA SERVICES*
*BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===150
1GB@=====250
2GB@=====500
3GB@====850
5GB@====1,400
Dial *312*4*7*4# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Act details FA’IZA ABUBAKAR unity bank 0020281885
Whatsapp OR
Call 09033283375
Wannan littafin kuɗi ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa’iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134