Hausa NovelsYar Zaman Wanka Hausa Novel

Yar Zaman Wanka 28

Sponsored Links

Ɗan jim ta yi tana jinjina ƙoƙarin mutumin, shi da ya zo barka, barkar ma daga maƙota amma har yake neman ruwa, haka dai ta kama hanya ta fita tsakar gidan tana addu’ar Allah sa dai shek ya tafi ba tare da matsalar da suke ciki ba ta bayyana kanta.

Ƙoƙarin sanya takalminta take amma kuma ganin Hassan na warware jelarsa sai ta dakata, tana ɗan kallon Ustaz ɗin da fatan Allah sa kar ya lura.

“Ɗan kula Sthadiya kin san daga nan wajen wani wa’azi zan je da ake gabatarwa a can masallacin sama damu duk laraba da yamma” Ya faɗa yana ɗan satar kallonta, tana shirin bashi amsa sai ganin micijin ta yi ya taso kamar wanda yake tafiya a kan iska, bai yi masauki ba aai a tsakiyar gidan, ya ɗaga kai sama ya fasa kansa alamar sara tare da sakin wani ƙara me kamar hamimiya.

“Allahu akbar! Sthadiya wato ainihin ki bar ruwan nan kawai, na yi ɗoren azumin nafila” Ya faɗa a ɗan gigice yana miƙewa tsaye daga zaunen da yake, a ransa ya ce.

“Ashe dai Barira da gaskiyarta da take bani labarin an ce yaran ɗayan miciji yake zama, da na aan gaske ne da sai dai na yiwa Imran barka a waya ko a hanya in mun haɗu amma babu abin da zan shigo yi gidan nan saida rai”

“Azumi kuma yau fa laraba” Sadiya ta faɗa dan ita kawai ƙoƙarinta ta ɗauke nasa hankali kar ya ga micijin bata san ya gani ba, bare kuma ƙaran da micijin ke yi ma tuni ya sanya hantar cikin Shek ɗin ta kaɗa.

“Bari kawai dai kowace rana ma ai mutum na iya azumin nafila” Ya faɗa da magana kamar yadda kowa ke magana ya manta cewa sai ya yiwa maganarsa kwaskwarima irin ta Ustazai.Ganin rikicewar da ya yi sai Sadiya ta fahimci ya ha micijin, a hankali cikin sanɗa ya nufo ƙofar falon, Sadiya ta koma gefe ɗaya ta takure a jikin bango dan ta bashi hanyar. Idanunsa a kan micijin ya tsugunna yana lalumen ƙasa takalmansa yake so ya ɗauka amma ruɗewa ta hanashi nutsuwa bare ya fahimci ko inda takalmin yake hannunsa bai kai ba.

“Ɗaya mafarin ƙirge, biyu idanun dabba, uku duwatsun murhu, huɗu ƙafafun tebur, biyar na yatsun hannu” Cewar Shek hankali tashe ganin micijin ya iyo tsalle ya sauka a gabansa.

A hankali ya ɗaga kai sama ya fasa a lamar sara.

“Shida ranakun aiki, bakwai kwanakin mako, takwas goma ba biyu kenan, tara daga ke sai goma, goma biyar biyu kenan” Ustaz ya faɗa yana sakin kuka kamar ƙaramin yaro dan tun da yake bai taɓa ganin miciji me girman wannan ba, kuma a gabansa haka yana neman saran sa, in ba tsautsayi ba zagin mahaifi me zai kawo sa barkar mutum ɗaya miciji ɗaya.

“Dan Allah Shek ka yi addu’a wallahi tun wajen ƙarfe ɗaya yake a haka so nake ma ya koma mutum amma har yanzu shiru, gidan nan kusan mutum goma ne amma duk sun ɓuya sai ni kaɗai, kai da yake malami ne ko ka masa addu’a” Cewar Sadiya tana kuka.

Shiru Shek ya yi sai lokacin ma ƙwalƙwalwarsa ta fara taryo masa cewa ashe karatun hausa ne na irge da aka koya musu tun suna primary yake faɗa ba addu’a bace, so yake ya tuno wata addu’a ko da ɗaya ce amma ya kasa sai danna carbinsa yake kamar zai maida madannin ciki, ga bakinsa har kumfar yawu yake kan magana amma bai san me yake cewa ba.

“Labbaika lahumma labbaik, labbaika lashari kala labbaik, innalhamda, wanni’imata laka wal mulk laaaaaaaasharikalak” Cewar Shek da mugun ƙarfi dan har la ɗin lasharikalak ya ja duk ya karaɗe gidan ganin miciji zai bi ta tsakanin ƙafafunsa dan tun lokacin da micijin ya tunkarosa ya tashi tsaye daga durƙuson ɗaukan takakalmansa.

Sulululuuuu micijin ya bi ta tsakanin ƙafar, Shek ai kafin micijin ya fito ta tsakanin ƙafafun Shek fitari ya rigasa fitowa, fitsari ne kawai yake kwaranyowa kamar an buɗe famfo, duk ya zuba a jikin micijin amma Shek bai ma san ya yi fitsarin nan ba kawai tashin hankalinsa micijin a tsakiyar ƙafafunsa. Haka micijin ya bi ya fito ta baya, ya ƙara gewayowa zai shige ta tsakiyar ƙafafun nasa

“Innal halala baiyyinun, wa innal harama bayyinun, A ƙarama A babba Ba ƙarama Ba babba, ca ƙamara ca babba, an, in, un, ban, bin, bun, tan, tin, tun” Ustaz fa sai bitar karatu yake a matsayin addu’a ko gaga baya yi. Amma micijin nan sai da ya bi tsakiyar ƙafarsa sau uku sannan ya dawo gabansa, ya juya masa baya ai da ya ɗaga jelarsa bai sauke a ko ina ba sai a kan ƙafar Shek, Shej yadda ka san wuta aka ɗora masa haka ya ji.

Ai da ya wani buɗe murya ya dage ƙarfinsa ya ce.

“Assalatu kairum minannaum, Allahu akbar la’ilaha illalllaaaaaaaaaah” Ya faɗa yana kuka har da dariya.

Inna da tun karatun Shek na farko ta jiyo daga maɓoyarta, hakan ya bata tabbacin akwai wanda ya kawo kansa gidan dan haka bata yi sanya ba ta taka bencin ta leƙo ta window dan haka duk abin da ake a kan idonta, dariya kwa ta yi ya fi cikin carbi, babu abin da ya bata dariya sama da yadda zilaikar Shek ta yi sharkaf da fitsari, sai kwaranyowa yake.

“Jama’ar unguwar nan ku zo ga limaminku na fitsari a tsaye, da a ce wani ya gani yana fitsari a tsaye wataƙila sai ya masa wa’azi” Cewar Inna a ranta tana dariya har da ƙwallarta.

“Allah, Allah, sayyadina Muhammadu, wa ala alih sayyidina Muhammadu” Ya faɗa likacin da ya daddage yana bugun ƙirji irin yadda maulidi ke yi.

“Bari na biya maka karatuna ni ma sanda na samu kaina a wannan halin har Imirana ya tuna min wani wajen, zan ji ko kai za ka karɓa” Cewar Inna tana dariyar ƙeta.
“Alif, anbaki, wawzal” Cewar Inna da ta leƙo kanta daga windown ta sako bakinta. Ai hakan sau ya tunawa Shek da makarantar allo lokacin yana ƙarami, a take ya karɓe har yana neman yin gaga.

“Baaaa, aliiiiif, baƙiiiii, lallaaaaaan, hakuriiiii” Ya faɗa yana jan kowane ɗaya daga ciki. Dariya sosai Inna ke yi har ta kasa magana jan dariya, yana gama faɗar wancan sai ya fara.

“Book littafi kenan, chair kujera kenan” Yana ta jero sunayen abubuwa da turanci tana fassarawa da hausa, dan har lokacin jelar tana kan ƙafarsa. A guje micijin ya yi hanyar zaure be tsaya ba sai da ya dangana da ƙofar, ai Shek na ganin haka sai ya ɗakko hiramin wuyansa ya durƙusa cikin sauri ya ɗauki takakmansa ya naɗe takalman a cikin hiramin ya ci uban tumuri da shi a tsantsa, sai da ya ɗaure hiramin sosai a tsantsarsa sannan, ya zura da gudu, wurin Sadiya, yana zuwa ta yi saurin natsawa ganinsa dab da ita, ƙara matsawa ya yi, ta kuwa sake matsawa ta bar jikin bangon ai Shek sai ya koma yake ƙoƙarin laɓewa a bayanta.

“Haba Shek ya za kake matsowa kusa da ni, baka ganin matar aure ce ni”

“Haba Sadiya wato ainihin babu banbanci tsakanin jinsi da jinsi idan a halin ceton rai ake ” Ya faɗa yana neman kai hannunsa jikinta, dan shi gani yake tun da uwar micijin ce ita to ba zai masa komai ba in ya gansa a wurinta.

“Me ye hakan wai?” Ta faɗa tana mata rai.

“Ki ceci limamin masallacin unguwarku mana Sadiya, kin san dai in micijinnya ganni tare da ke zai ƙyaleni” Ya faɗa dan zuwa lokacin duk ya daina maƙale-maƙaken murya Sadiya ma yake faɗa sak, ba kamar zuwansa ba da yake cewa Sthadiya.

“To dan gwafar ubanka Imirana da ya haifi micijin yana tukunya a ɓoye, ka ga kuwa ai bai bar ubansa ba ma bare kai” Cewar Inna da ke window. Ganin micijin ya dawo daga zauren sai kuwa Shek yake neman damƙo Sadiya cikin ficewar hayyaci da tsoro.

“Ihuuuu kwarto, jama’a ku kawo ɗauki kwarto a gidan nan zan yi fyaɗe” Cewar Inna gabaɗaya kowa ya ji maganar duk sai suka ƙara tsorata da maganar kwarto dan haka, Hajiya sai ta ƙara totsuwa cikin ƙatakwaye, har tana buga kanta a jikin fikankin gado.dan kar kwarto ya ritsa da ita da girmanta, Mama da ke cikin drower sai ta ƙara totsuwa duk da matsin da take ciki, can ƙarshe ta matsa ta miƙa hannu ta kwaso kayan Imran wanda duk siglet ne da gajerunan wanduna, a inda ta sanya hannun nata, ta kwaso ta jibga a kanta, duk da tana jin nauyin ɗora gajerunan wandunan da singiletin amma haka ta daure dan kar a mata fyaɗe a gidan siriki.

“Wayyo Allah, ga raɗaɗin lalle a fuska da wuya, ga miciji, hallaw ga fargabar shigowar kwarto, wayyo ɗan budurcina da nake tattalawa zan kai gidan miji, haka kawai ina ganin ƙawayena suna bin maza amma na ƙi san in kai mutucina gidan aure amma gashi a neman halal wani ƙaton zai karɓe min” Cewar me ƙunshi da ke cikin kayan wanki.

Ƴan cikin loka kuwa kuka suka fara haiƙan jin wata ƙaddarar ta shigo gidan. Ashrof da ke bayi ita kaɗai tuni gumi da hawaye sun daɗe da mata sallama.
Imran kuwa jin abin da Inna ta ce sai ya koma ya ƙara lumewa a cikin ruwan, har yana shiga hancinsa amma gani yake da ace ya fito wurin micijin nan gwara kowa ta yi ta kanta dan ya san dai ba Sadiya ce kaɗai a gidan ba.

Inna sakkowa ta yi daga saman bencin, ta ɗakko ashana tare da buhun shinkafa marar komai, ta ɗaga ƙafa ta doki jikin lokar da matan nan je ciki, aikuwa suka ƙara sakin wani kukan, tsaki ta yi, ta juyawarta ta buɗe ƙofar kicin ɗin ta fito, ganin Hassan daga gefe ɗaya, ga kuma Shek tsaye bayan Sadiya dan tana motsawa yake take mata baya. Hanyar murhu ta nufa tana zuwa ta ce .

“Ihuuuu kwarto” Sai da ta tabbatar Imran ya ji da gangan ya ƙi fitowa, aikuwa ta sanya buhu a murhun dama cike yake da ita ce ta kunna ashana ta sanya nan sa nan wuta ta kama ci galgalgal, dariyar ƙeta ta yi tana jijjiga kai ta koma gefe ta tsaya ta ce.

“Kamar yadda na fara jin sanyi lokaci guda ya baibaye firinji, haka kaima za ka ju zafi lokaci guda ya baibaye tukunya”

Imran da ke cikin tukunya, ya ji wani zafi ya fara ratsa tukunyar, gyara rungisan sa ya yi amma sai ya ji abin na ƙaruwa, amma aai ya daure, jim kaɗan sai ya gabaɗaya kamar an sanyashi a ovin.

A mugun firgice ya bugi murfin tukunyar ba shiri, ji kake gwagwaraf, ya yi jifa da murfin, sai gashi yana fitowa jargaf da ruwa a jikinsa ga kuma uban gumi kamar an masa wanka …
[24/03, 5:14 AM] Mom Mashkur First class: *MAMAN AFRAH DATA SERVICES*

Back to top button