Hausa NovelsYar Zaman Wanka Hausa Novel

Yar Zaman Wanka 20

Sponsored Links

A dai dai bolar suka tsaya, wanda ke zaune a mai zaman banza ya fito da sauri ya buɗewa Inna ƙofa ta fito aka miƙo mata ledarta shaƙe da kayan marmari.

“Gashi iya” Ya faɗa yana durƙusa gwiwoyinsa a ƙasa.

“Ku ajiye a nan sarkin aljannu zai sa dogaransa aljannu su zo su ɗauka” Cewar Inna a fili a zuciyarta kuwa cewa ta yi.

Related Articles

“Yo Ina dalili zan hau bola da abun da zan ci”

Ajiyewar ya yi, gabaɗaya suna jin tsoro Inna kuwa dosar bolar ta yi tana addu’a a zuciyarta dan kar ta je ta yi gamo da magribar nan. Suna ƙoƙarin jan motar suka ga Inna ta fara wata girgiza da sauri ya ja motar suka bar layin a sukwane.

Sai da suka yi tafiya me nisa suka tsaya kowa ya kama gabansa dan sun ce sun bar garkuwa da mutane daga yau, sbd angamo da aljanar da suka yi yau, shi ma Ogan bayanin da suka masa a waya bayan barinsu wajen Inna ya sanya an maida me gadin kuma sun fasa ɗakko tsohuwar da suka yi niyya dan suna ganin kamar idan za su ɗakko ta aljana za ta iya rikiɗa su ɗauki aljanar a maimakon matar dan haka shi ma barin garkuwa da mutanen ya yi ya koma ya kama sana’a.

Inna kuwa tana ganin gilmawar motarsu ta gefen ido, sai ta ɗan dakata, sai da ta tabbatar sun tafi sanna ta baro kan bolar da sauri ta suri ledar kayan marmarinta, tana ta waiwaye tana cewa

“Ja’irai ƴan iskan ƙarya yo me na manta gashi na samu kayan marmarina ko banza ai na ƙwaci kaina, da yanzu ina can wataƙila ma wani daga cikinsu ya far mini tsakar dare tsofai-tsofai da ni, ya je ma ya goga mini cuta mai karya garkuwar jiki” Ta faɗa tana shigewa gidan Sadiya, sai da ta sanya ƙafarta a cikin gidan tsoron aljanin gidan da ya tsorata ta rannan ya faɗo mata, tana fatan kar dai yana jin yadda ta yaudari samarin nan, ya zo da dare ya tambayeta dalili.

“Assalamu alaikum, gafaranku dai masu gida” Cewar Inna lokacin da ta shigo gidan amma gidan shiru kamar ma babu kowa.

“Ikon Allah kun ji ina Halimar take ta barni ina ta faman rafka sallama” Ta faɗa tana shigowa tsakiyar falon amma babu kowa sai su Hassan da ke kwance kan gadajensu suna bacci.

“To ko dai bayi ta shiga, kenan Asharofa har ta tafi gida, to ai shikenan” Ta faɗa har lokacin ledar kayan marmarinta na riƙe a hannunta.

Imran da tun sallamar Inna ta farko ya jiyo ta amma Sadiya bata ji muryar Inna ba, hakan ya sanya ya riƙe hannun Sadiya da ke shirin fita ya hanata ta fita kuma ya yi hakan ne saboda ya yiwa Inna abin da za ta kunyata. Sadiya kuma da yake ta ga yana ta ƙuncin rai sai ta kasa tafiya ta dakata, tsaye suke a tsakiyar bedroom ɗin, ya riƙe hannunta babu wani abu da ya ce kuma bai mata komai ba duk da tana ɗan tsoron yanayin nasa dan ta san shi bai iya riƙe kansa ita kuma jego take babu damar yin hakan.

“Sa’adiyya ba dai baccin magriba kike yi ba” Cewar Inna tana dosowa bedroom ɗin da ƙarfin gwiwarta, Imran da ya ji takun tahowarta ɗakin ya yi saurin janyo Sadiya jikinsa ya rungumeta, hakan ya yi dai dai da bankaɗa labulen da Inna ta yi.
Ledar kayan marmarin ta saki ta faɗi ƙasa, ta fara rafka salati, tana tafa hannuwa kamar wanda ta ga mazinata turmi da taɓarya. Sadiya da ta ji maganar Inna ta shiga ƙoƙarin raba jikinta da na Imran, aikuwa Imran ya riƙe ta ƙam ya ƙi sakinta dan yanzu yake so ya ga yadda tsohuwar nan mai tsuru-tsurutun tsiya za ta yi, dan shegen shishshiginta da zalama ne ya sanya ta zo masa wani ZAMAN WANKA dole ya nuna mata bashi da kunya ko ta tattara komatsanta ta bar masa gida ta haƙura da ZAMAN WANKAN.

“Imirana, kai Imirana, wai Imirana ba magana nake maka ba” Cewar Inna a fili a zuciyarta kuma ta ce.

“Wannan an yi taƙadarin yaro wataƙila ma ba ya cikin hayyacinsa, sai na yi da gaske zai ƙyale ƴar mutane yo ban da jaraba ma yarinya tana jego amma ba zai ƙyaleta ba”

Sadiya duk kunya ta kama ta sai kiciniyar ƙwace kanta take, amma Imran ya ƙi bata haɗin kai nema ma yake ya haɗe bakinsu amma sai kauda kai take”

“Na shigesu ni Azumi me idanuna ke gani, Imirana riƙe da Sa’adiyya ko shamaki babu a tsakaninsu, yanzu ba za ka saka ta ba Imirana ko dan kunya ta ma ai ka saketa, amma ka runƙunƙume yarinyar da jego take ɗanye sharaf, ai abin da kunya yin tsirara a gaban uban miji” Inna ta faɗa kamar ta saki ihu dan jin nauyin yadda ta gan su, gashi kunya duk ta kamata amma tsegumi da kuma son ganin ƙwaƙwaf dan kar a yi katoɓara ya hanata tafiya daga ɗakin.

Imran kuwa jin yadda Inna duk ta rikice sai ya sanya hannunsa ɗaya ya riƙe ƙugunta ɗayan kuma ya kai wajen ƙirjinta a ransa yana cewa

“Ai tun da gane -gane gareki wallahi sai kin ga abin da ya fi ƙarfin ganinki, wa ya ce miki ana shiga tsakanin ma’aurata?” Ya faɗa a ransa.

” Na shigesu ni ɗiyar me daddawa jiƙar me barkono yau ina ganin abu , yo Imirana banda fallasa auren bashi ya za a yi ka rungumi me jego, tabbas shi yasa ba a baiwa kura ajiyar nama nima da gangan ne na fita na barku a gidan in ban da tsautsayi zagin mahaifi ai dama ba a bar mutum kamar Imirana ba da mace a cikin gida, yo me nema a duhu ne ya samu a sarari” Ta faɗa tana ɗan tako ƙafarta ta matso cikin ɗakin, dan so take ta san yadda za ta yi ta ƙwaci Sadiya kar a yi abin kunya.

Har lokacin nan da Inna ke ta karaɗi Imran ko niyyar sakin Sadiya be yi ba so yake ya ga iya gudun ruwan Inna za ta fice ta basu wuri ko kuma za ta cigaba da tsayuwa kamar an dasa ta har sai ta ga abin da zai turewa buzu naɗi.

“Yau na tabbatar da waye kai Imirana, dan tabbas gani ya kori ji, ni kaɗai na san abin da ya faru da ni a fitar nan tawa daga gidan nan, kuma ni na san abin da hannu na ya damƙa (Al’aura) ya Allah kai ka san karatun kurma Allah ka tsare min idanuna da gani na daga abin da zai ɗaga min hankali, yo banda ƙaddara ma ni da ba na ƙaunar ganin mazaƙuta in ba ta Malam ba, me ya kaini na taɓa mazaƙutar maza har uku da hannuna, ji nake kamar na sa wuƙa na gundule hannun nan nawa da ya taɓa al’aurar da ba halalinsa ba” Cewar Inna tana sakin kuka, dan gabaɗaya sai ta ji birnin ta fita a ranta yau ta haɗu da maza da abin da ta musu kaɗai ne ya ƙwace ta gashi kuma yanzu ta dawo gida ta tarar da wata katoɓarar.

Imran kuwa furucin Inna ya sanya dariya ta kusa ƙwace masa, amma haka ya daure ya cigaba da ƙoƙarin kai hannunsa wajen ƙirjin Sadiya ita kuma tana ƙoƙarin bige hannunsa.

“Amma wannan yaro an yi me wankekken ido, bayan ƙwaƙumarta da ka yi babu shamaki tsakaninku, hallaw na shanunta kake so ka damƙo, to wallahi dai ka bi duniya a sannu a gaban idona baka jin kunya kake waɗan nan abubuwa kamar wanda uwarsa ta ce jeka ka ganiz shi yasa ashe ko zamana baka ƙauna a gidan na kafi so a barka ka ci karenka ba babbaka, ai dama idan ka ji makaho yana cewa a yi wasan jifa to tabbas ya taka dutse”

Imran juya Sadiya ya yi yake neman kwantar da ita a kan gado.

“Halima wai duk a gaban idona fa ake sarrafa ki kamar wata injin kaɗin taliya, amma kin kasa kataɓus ki ƙwaci kan ki so kike sai sheɗan ya masa linzami ya haike miki da ɗanyen jegon, wallahi ki kiyayi biyewa ɗa namiji Sa’adiyya ina rabaki da kiwon kyalle kina kyalle ta haihu, , ni nan yanzu na ƙwaci kaina daga hannun maza ƙartai uku, bayan haka harda yaudarar kayan marmari amma ke a hannun namiji ɗaya kin kaya ƙwato kan ki kin barsa sai waricinsa yake a kan ki, sai ka ce wata matar shige, ai matar shige bata daraja amma ke kuwa da ba matar shige ba kya biye masa”

Ganin Imran ya kwantar da Sadiya a kan gado Inna ta saki ihu me haɗe da kuka.

“Dan Allah Imirana na roƙeka dan darajar iyayenka ka rabu da yarinyar nan, kar amana ta ci ni, duk wacce taje ZAMAN WANKA tamkar an damƙa mata amanar me jego ne a hannunta, so kake ka je ka sa ƴar mutane ta yi ciki da goyo, ka farke mata ɗinki a shiga uku, bayan ɗinki bakwai Amina uwarka ta faɗa min an mata a mafitar ɗa (HQ) Sai ka ce wata ƙwarya amma kake neman maida hannun agogo baya, dama duk abin da aka yi da jaki sai ya ci kara, kuma ai dama abin kirki bai gaji kare ba, in ya yi ma dukansa ake”

“I luv u baby) Cewar Imran cikin wata murya da ya yi da gangan.

“Ƙarya yake miki wallahi yaudara ce kawai irin ta maza, duk da ban san fassarar abin da ya faɗa ba, amma na san magana ce me daɗi dan na ga a kan gado ya yi maganar kin san kuwa maza kalamansu basa tashi sai suna neman biyan buƙata to a nan za ki ji kalaman soyayya har da na siyarwa”

“Ina sonki masoyiya” Cewar Imran shi ma yana ƙoƙarin hayewa gadon, sai da ya hau gadon ya kife a kan Sadiya ɗare-ɗare, kicinyar tashi Sadiya ta shiga yi amma ya hanata.

“Lahaula wala ƙuwata illah billahi aliyal azim, Imirana kan ruwan cikinta za ta hau a gabana” Inna ta faɗa tana sauri ta yi taku ɗaya biyu sai gata a gaban gadon a sukwane, aikuwa ta shiga kiran Imran da ƙarfi tana cewa.

“Imirana kai, kai Imirana tasata (Ɗaga ta) tasa ƴar mutane, wallahi ban bari ka yi wannan aikin da na sani, azo ayi abun kan ji alawo, sai daga baya ake wallahi tallahi” Ta faɗa tana jan rigarsa, amma Imran ko gizau be yi ba, cikin sauri ta juya ta bar ɗakin har tana haɗawa da gudu -gudu ta yi tsakar gida gabaɗaya a gigice take.

Imran kuwa ya ɗauka kunya ce ta sanya Inna ficewa daga ɗakin dan haka sai ya fara ƙoƙarin tashi, ai sai ya fara jiyo ƙaran gudun Inna kidif-kidif kamar an biyo ta, da sauri ya koma yadda yake ya yiwa Sadiya rumfa.

“Bari dai na yi maganinka na yi maganin sheɗan ɗin da ya rufe maka ido kake neman aikata aikin da na sani” Cewar Inna da ta dawo ɗauke da taɓaryar da ta ɗakko a kicin, ɗaya hannun kuma muciya, Sadiya da yake ita ce a kwance Imran kuma ya baiwa Inna baya bai ga abin da ta ɗakko ba, sai Sadiya ta ce cikin ƙaraji.

“Abban twins tashi taɓarya” Ta faɗa tana turashi da ƙarfi da hannunta dan ta san kaɗan daga aikin Imna ta ɗaga taɓarya da muciyar nan sa rafkawa Imran dan tsaf za ta sauke masa su a gadon baya ta je ta lahantashi a shiga uku a zo ana a’i ina indo. Imran turawar da Sadiya ta masa sai gashi a gafe rigingine a kan gadon, hango Inna ɗauke da madokai ta iyu kukan kura za ta hau kansu ya sanya ya yi wata adungure ya dira daga gadon sai gashi ba shiri tsaye a kan ƙafafunsa. Sadiya kuma da sauri ta tashi zaune ta miƙe tsaye dan dama ita dan ya mata nauyin kuka ne kuma ya hana ta ƙwatar kan ta amma dama da ba za ta yarda ta yi wannan abin kunyar ba a gaban Inna ta barwa kanta abin gori da abin faɗa marar iyaka a wajen Inna Azumi.

Ita ma Sadiya dirowa ta yi daga kan gadon ganin duk da Imran ya ɗaga ta amma Inna kamar bata fasa abin da ta yi niyyar yi ba, ganin da gaske tana shirin farmusu da taɓarya da muciyar ya sanya Imran yin wani uban tsalle ya bi ta bayan Inna ya fita daga ɗakin a sukwane, Sadiya ma da gudunta na bara ta fice suka bar Inna a ɗakin tana sababi tare da rufa musu baya cikin gudu -gudu sauri -sauri.

Back to top button