Hausa NovelsYar Zaman Wanka Hausa Novel

Yar Zaman Wanka 19

Sponsored Links

Sai da Inna ta tabbatar ya damƙu, sannan ta sake shi, dafe jikin motar ya yi yana sauke numfashi, kallon kallo aka shiga yi shi da sauran yaran nasa, amma babu wanda ya ce wani abu. Inna ce ta warce dorinar hannunsa ta ce.

“Faɗa da aljani ba daɗi wa ya faɗa muku barno gabas take, ni dama duk ina jiyo abin da kuke faɗa tun daga inda nake, hakan ya sa na sawaya daga halittar asalin aljana na koma halittar mutum, kawai fitowa na yi a wurin da kuka ganni a zaune amma ba ni bace wacce kuke nema” Cewar Inna afili cikin wayincewa dan ɗazu da suka taho a mota bayan an ɗaure mata ido ta ji suna zancen mahaifiyar me gidan ce ita, hakan ya sanya ta gane sawun ɓarawo ta taka, a zuciyarta kuma cewa take.

“Wallahi ba zan bari ba ku min lahani dan idan kuka san ni bil adama ce yaudararku na yi to na san na lahira ma sai ya fini jin daɗi, in ya yi aiki me kyau amma idan na nuna muku aljana ce ni tun da na ji mahaifiyar me gidan kuke son ɗakko wa kuka ɗakkoni a shegen son ganin gida me kyau irin nawa, da ban yi dibarar cin kwalar mazaƙutarku ba da wallahi na san sai yadda hali ya yi”

Ai fa gaba ɗayansu da suka fuskanci aljana suka ɗakko jin furucin Inna sai suka shiga kallon kallo kowa jikinsa na karkarwa. Ganin sun yi dim basu ce komai ba sai Inna ta ɗauka mgnart bata samu shiga bane, cikinta har ya fara kiran ciroma, tana hango yadda za su mata ɗaurin goro a dajin Allahn nan inda babu wani wanda zai taimaketa cikin azama ta yi wuf ta ce.

“Me kan agwagwa ku jirani ina nan zuwa, wani abu ne ya shiga tsakanina da bil adama amma ku je birnin sin ɗin ni kwa same ni a bangon duniya” Ta faɗa tana ɗaga murya ta canja muryarta ta zama kamar ta wani gardin da aka shaƙeshi, ita ala dole magana take da aljannu.

 

Ganin yadda take magana sai suka ƙara tsorata, cikin bada umarni ta ɗaga dorinar nan ta ce

“Duk ku fito daga cikin motar idan ba ku yi saurin fitowa ba sai dai ku ga na maida samanta ya zama a ƙasa ƙasan kuma ya zama a sama” Da sauri suka fara fito su duka a layi kamar masu neman taimako, sai da suka fito su duka suna karkarwa Inna ta dubi ɗaya wanda ya ƙulle mata ido ya danne mata baki ganin ya yi wujiga wujiga kamar an tsamoshi a ruwa ta ce.

“Tabɗi wai kai nan wuya ce ta sa ka yi tsuru -tsuru ya wannan? Dole mana ka jigata ka ji damƙa kamar a sanyawa akuya dabaibayi, tare da datsa maka haƙori masu tsini dole ka ji jiki ai daga jin cizon ma ya wuce na bil adama ko ba haka ba?” Ta faɗa tana kallonsa kai ya shiga gyaɗawa kamar ƙadangare, ya ce

“Hakane iya aljana” Ya faɗa a fili a zuciyarsa kuma ya ce.

“Wallahi ji nake kamar hannun ba a jikina yake ba”

wannan haƙorin naki me tsini kamar mashi, ai daga ji ma ba na bil adama bane, sai dai naku aljannun”

“Ku zo nan kowa ya yi kamun kunne yau kowa sai ya faɗawa aya zaƙinta, yo ina dalili za ku mini cali-cali kamar wata gawa, haka kawai da raina ban mutu ba ku min kama -kama, ina ji ina gani, ai na muku ma da sauƙi”

Haka ta sanya su suka kama kunne tsoro kuma kamar farar kura kowa ji yake kamar ya tashi ya zura da gudu saboda tsananin tsoron ganin gashi ga aljana.

Haka Inna ta sanya su a gaba ga magriba ta kawo kai amma duk wanda ya yi wani motsi sai ta ɗaga dorinar ta zabga masa sai dai ka ji sun saki kuka kamar ɓeran daji. Babban nasu ne wanda shi ne direban da ya yi motsi sai Inna ta daddage ƙarfinta ta zabga masa dorinar har sai da ya durƙushe sannan cikin sauri ya tashi ya kama kunnensa.

“Kai dalla ka yiwa mutane shiru ragon banza da wofi, yo Allah na tuba da ƙarfinmu na aljannu na dage na dake ka ai da sai dai gyatumarka ta haifi wani, Allah na tuba jika dai jibgege amma mazaƙutar yara gareka abu kamar lagwanin fitila, in banda ma larura me zai sa ni taɓa jikinku ai ba zan iya ba ma, Allah tsari gatari da saran shuka”.

A can wajen Ogansu kuwa sai jiran zuwansu yake amma shiru kake ji maye ya ci shirwa, yana shirin kiransu a waya sai wayar me gadin nan da aka ɗakko daga gidan da za sato tsohuwar nan, ta yi ƙara Ogan nasu ne ya ɗaga kiran dan dama a hannunsa wayar take, ganin an sa Hajiyar Alhaji, sai ya ɗaga aikuwa ya ji muryar tsohuwa tana cewa.

“Wai me gadi ina ka shiga ka barwa mutane get a buɗe” Cikin mamaki Ogan nasu ya cire wayar daga kunne ya kashe ta, jin maganar matar da ya sanya a kamo mamaki ma ya hanashi magana a take ya ɗaga waya ya kira wayar direban su Baaba aikuwa wayar ta shiga ringing Inna ta ɗakkota a mota ta kawo wa direban ta miƙa masa, yana ganin sunan Oga ya ɗaga da sauri Ogan ne ya fada magana

“Kuna Ina ne?” Ogan ya faɗa cikin ɓacin rai dan yana ganin sun raina masa hankali sun ce sun kamo tsohuwar a gidan amma gata tana waya.

“Oga gamu a nan dokar daji za mu ƙaraso kuma Allah bai yi…

“Dallah rufe min baki, ashe ku duka, dukan iska ne, kai banda sha ka tafi ne me yasa baku ɗakko matar nan ba ka ce kun je gidan kun ɗakko ta?” Oga ya katse masa magana tare da bashi labarin wayar da suka yi da matar a wayar me gadi.

Wannan maganar da Oga ya faɗa musu a waya da yake handafree aka kunna kowa yana ji, a take suka fara maƙyarƙyata dan hakan ya tabbatar musu cewa Inna aljana ce.

Jikinsu ɓari ya shiga yi suna ta kuka tare da baiwa Inna haƙuri.

“Oga ba yin kanmu bane wallahi ashe angamo muka yi muka ɗakko aljana ka ganmu sai wahala take bamu kamar an aikota ga ƙarfin bala’i kamar raƙumi, ban da ma da kwananmu a gaba ai da sai dai wasu ba mu ba” Cewar direban a zuciyarsa a fili kuma ya ce.

 

“Oga iya ce muka ɗakko kuma za mu maidata gidan”

Mahaukata kawai” Ya faɗa yana jan tsaki tare da kashe waya,dan shi bai san cewa aljana suka ɗakko ba. Sai da Inna ta basu wahala sosai dan har goyo -goyo ta sanya suka rinƙa yiwa junansu.

“Da kun san ni bil adama ce na san yau kuma kashina ya bushe yo in kun min da arziƙi ku min rigijib (duka) Ku barni in ƙarasa mutuwa da kaina amma na san dai ba za ku barni a yadda na muku wasa da hankalin nan” Cewar Inna a zuciyarta.

Sai da ta gama zane su tsaf sannan ta ce

“To yanzu inaso ku maidani inda kuka ɗakkoni dan yanzu idan na ce zan ɓace guguwa ce za ta taso kuma wataƙila ta kwashe har ku a nemeku a rasa”

“Dan Allah kar ki ɓace ki taimaka mana ” Suka haɗa baki wajen faɗa.

“Ina da sharaɗi”

“Muna jinki”

“Daga yau babu ku ba garkuwa da mutane ko da kuwa sauro ne ”

“Ai wallahi mun tuba mu da muka yi garkuwa da aljana ai ba ma ƙara ba”

“Ba aljana ba ce Inna Azumi ce matar Malam, kishiyar Tasalla ni ma da za mu ga aljanar yanzu da sai dai a shiga ceton rai dan ƙafa mai na ci ban baki ba za a yi” Ta faɗa a zuciyarta a fili kuma ta ce.

“Ku shiga mota mu tafi, ɗaya ya shiga gaba ni da ɗaya mu shiga baya ɗaya kuma ya tuƙa” Ta faɗa tana saurin shiga motar ta zauna dan tunowa ta yi da aljanin da ta gani a bayi , hakan ya sanya ta ji wani mugun tsoro dan bata manta karonsu ba. Haka suka shiga suna zazzare ido saboda tsoro Inna kuwa da ta shiga baya ta zauna a setin kujerar direban ta ɗaga ƙafafunta ta ɗora a kan wuyan direba, a haka yake tuƙin rai duk ba daɗi wuyansa ɗauke da ƙafar aljana.

Haka ake tuƙin sun yi dif kamar ruwa ya ci su suna shigowa cikin gari ana fara kiran sallar magriba, dan haka wani wurin mai saida kayan marmari Inna ta nuna musu.

“Maza ku tsaya ku cikawa sarkin aljannu leda da kayan marmari san wannan ledar da kuma sa ta faɗi lokacin da kuka kinkimeni kamar kun samu tukunya alkakinsa ne da bakilawa, to yanzu ku ramawa kura aniyarta in ba haka ba kuna komawa gidajenku za ku ga an mayar da ku dajin da muka baro yanzu, in sau dubu za ku komo nan sai an maida ku”

“Za mu siya ma” Suka faɗa suna ɗakko kuɗi kowa ya bayar aka cikawa Inna ledar viva da kayan marmari masu yawan gaske, dan cewa ma ta yi gorubar bature ta fi yawa (Apple) Haka aka ɗakko kayan nan aka sanya a mota, har ƙofar gidan da suka ɗauki Inna suka dosa za su kaita amma sai ta ce, dama ai ita aljana ce kuma ba a nan take ba, nan ta ce bangon duniya za ta je amma sai sun kaita kan bola ta nan za ta bi ta tafi, haka ta rinƙa nuna masa hanya, a haka dai suka kama hanyar gidan Sadiya sun kusa ƙarasawa sai ta ce su ajiyera a wajen wata bola saboda a nan za ta bi ta koma hanyar aljannunsu, ita kuma ta yi haka ne dan kar a a je wucewa ta ƙofar gidan Sadiya Imran ya ya ganta a motar ya tona mata asiri dan kaɗan da aikinsa.

 

Back to top button