Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 45

Sponsored Links

*Talented writers forum*

*45*

Yaya Yusuf Bai kawo inna ba sai da ya shirya Kuma ya zayyanawa Mai martaba komai ya masa fada akan Bai kyauta ba ya nuna sonkai saboda Bai nemi sanin wane Hali tsohon mijin inna ke ciki kafin a warware auren donhaka ya yafewa inna tun kan tazo garin , cikin bangaren da yake ganawa da manyan baqi suka samesa tare da ya Muhammad da wasu yayun inna Yan uwan ya Yusuf su biyu sun gabatar da gaisuwa cike da girmamawa hajjo ta rakube gefe anty Balqis na kusa da ita, bayan sun gaisa da tambayan bayan rabuwa nan Mai martaba yayiwa inna fada akan meyasa Bata dawo gida ba bayan tafiyar mijin nata cikin muryar kuka inna tace ” ka manta da furucinka Baba , shiya hanani dawowa bansan Yaya zaku karbeni ba ”
“Kiyi hakuri Aminatu bayan auren naki nagane zancen komai ki yafe mana bisa son zuciya da mukayi duk da cewa Yana cikin kaddarar rayuwarki ne Amma kiyi hakuri” nan ya Muhammad ya nemi yafiya akan cewa laifinsa ne haka suka dora da hira maimartaba Yana Jan hajjo da wasa ita kuwa kunya ya hanata sakewa.
Daga wajen sarki suka zagaya bangaren matan baban nata suka gaisa da kowa daga karshe suka koma part din yakumbo, tsohon d’akin inna lokacin da take budurwa a nan suka sauka aka shirya musu abinci na alfarma da kayan motsa Baki, wanka hajjo ta fara kan ta fito taci abinci ta kwanta nan da nan bacci ya dauke ta.
Satinsu biyu a Maiduguri sun zagaya dangin inna kaf daga karshe suka fara Shirin komawa saboda ana neman Yaya Yusuf a Abuja, a wannan lokacin ne hajjo ta shirya zuwa yola domin haduwa da babanta Wanda kullum sai sunyi waya fiye da sau 4 a Rana. Inna ta shirya zasu wuce Abuja tare da Abba hajjo kuwa yola zata wuce a nan suka rabu Hajjo ta rigasu tafiya, sun kwashi tsaraba ba kadan ba kayan qamshi iri iri inna ta sake Siyan wasu kayan aikin da zata hada ta zuba a shagonta, anty Balqis ta koma akan zasu Hadu a Abuja haka inna ta shirya tana Mai kewar yakumbo sukayi sallama akan idan azumi ya gabato yakumbo zata Kai musu ziyara.

Hajjo ta sauka yola da yamma Kai tsaye gidan yayan baban nata driver ya sauketa a can dougirei dama shine Dan Boko a dangin Kuma Yana da arziki sosai, ta samu kyakkyawar tarba wajen anty faty mace me kirki da karamci ta karbeta da fara’a tamkar sunsan juna, Baba na hanya daga Abuja ya taso ya kasa jiran su koma Yana son ganin tilon y’ar tasa. Sai wajen 9pm Baba ya shigo gidan hajjo har ta fara bacci aka tasheta cike da murna ta fito ta samesa a falo suna kallon juna tana murmusawa ta karasa kusa dashi tare da rike hannunsa ” Baba nah yau kaine a gabana ”
“Nice mama nah haka kika girma, ashe mun kusa Shan biki ” murmushi tayi cikin jin kunya suka gaisa tana tambayarsa ya hanya, an kawo masa abinci yace sai yayi sallah, haka suka Dade suna hira Yana tambayar lafiyar inna , nan tausayinsa ya kama hajjo tayi shiru yace ” na matukar Taya Yusuf murnar samun Amina a matsayin matarsa, Amina tayi a rayuwa macece me rufin asiri ga hakuri ga saukin Kai ga ladabi da biyayya Kai Allah dai ya Bata ladan abubuwan da ta mini a rayuwa” take fuskarsa ya canza hajjo tace ” kayi hakuri Baba Allah zai baka wata ”
“Hmmm nasan bazan Kara samun me irin halayenta ba ” haka suka cigaba da hira sai wajen 11pm hajjo ta masa sai da safe ta koma d’akinta shi kuwa murna yake duk da cewa Amina tayi masa nisa Amma tunda Basu Hana Hajjo zuwa ganinsa ba da sauki, da safe tare suka karya da mahaifin nata tana Jin Wani farin ciki duk da cewa tana kewar inna saboda wannan shine karo na farko da tayi Nisa da innar tata.

Kwana biyar sukayi a yola daga nan akayi booking flight ticket Hajjo zata koma Abuja Baba kuwa zai wuce kojoli wajen iyayensa nan sukayi bankwana akan zasu Hadu a Abuja, jirgin 7:00am ta shiga donhaka after 8 tana cikin Nnamdi Azikiwe international airport Abuja dama driver na jiranta Kai tsaye suka wuce gida. Maman Nana Basu dawo ba gidan ya rage daga inna sai sabuwar Mai aikin da ta taho da ita tun daga Maiduguri wata baiwa ce daga gidansu Mai suna Hafsatu suna ce da ita Hafsi , haka rayuwa ta cigaba har akayi resuming school sun koma haka Kuma soyayyarta da Aman sai abunda ya karu saboda yanzu har cikin falo yake zuwa susha hirarsu irin ta masoya ya gama magana da Dad akan next week za’a turo , inna ta fadawa ya Yusuf ya kira Baba nan Baba ya nuna cewa a gidan Yaya Yusuf za’azo Neman auren zai kira Wani yayansa Dake Kano yazo su Hadu a gidan ya Yusuf din a nan za’ayi maganan auren.
Kamar yadda suka tsara Hakan ta kasance Bappa Sama’ila shine yayan Baban Hajjo da ya taso daga Kano yazo gidan ya Yusuf ya samu kyakkyawar tarba da masauki washegari Abba ya kira Wani amininsa a nan Dad yazo da Yan uwansa biyu da abokansa biyu sukazo Neman auren Aman da Hajjo, ana suka zauna sunyi hira sosai kafin aka gabatar da abunda ya dace ya Yusuf yace duk abunda Ake ciki zai tuntubesu daga karshe aka hada musu kayan makulashe kamar yadda al’adar Adamawa ya tanada da Kuma na Yan Borno sukayi sallama cikin girma . Bayan kwana biyu Bappa Sama’ila ya koma Kano , ya Yusuf ya nemi Baba yazo gida su tattauna Amma Baba Yana ta kaucewa har ya ganosa wato bayason zuwa gidan ne, Hajjo na zaune da Ummeey cikin mota sun fito lectures kenan zasu koma gida Ummeey ta kalleta tace ” uhmm su love birds buri ya cika , toh yaushe zamu Sha bikin ” murmushi tayi tare da rausayar da Kai ” toh ai Kya bari a saka rana koh hajiya”
“Allah ya nuna mana ai dole yau na watsa ku media ” ” don Allah karki saka bana son wata ta hango min my heart kinsan Yan mata da son kyawawa ” dariya Ummeey take harda kwalla tace ” ashe haka kike da kishi lallai, wallahi Baki Isa ki hanani sakawa a status ba ko da bansaka a Instagram ba ” tabe baki Hajjo tayi ” ni kija mota mu tafi yunwa nake ji ” ” a Cici matar Aman ” dariya suke nan ta tada motar suka dau hanyar gida.

Da dare Ummeey na gida taga call din anty zee ta d’aga ” mom Fahad ” ke banson iskanci so nake ki min bayani akan y’ar iskar da kika saka pix nasu da mijina ” ita harga Allah ta manta da anty zee na da contact nata, shiru tayi ta kasa magana ” ke ba magana nake Miki ba, kinsanta ne ?”
” Umm..ehh anty kawai ”
“Ummeey zanci ubanki wallahi ki fadamin wacece yarinyar ” kawata ce ” keee…buro Uba, wato dake za’a hada Baki a kasheni Ummeey, innalillahi…yau naga abin mamaki kanwata uwa d’aya Uba d’aya Anya Ummeey Anya…” Kashe wayar Ummeey tayi tana rike Kai ta bani yau ta shiga babban matsala tasan Halin anty zee sai ta hadata da mom nasu, kwanciya tayi tana tunani kala kala lallai ta shiga tsaka Mai wuya Babu me fiddata sai Allah.

Zee tana kashe wayar ta kira mom nasu Bata d’aga ba sai zagaya d’akin take kawar Ummeey kawar Ummeey! toh wacece nan ta sake Bude pix din tana zooming dama tayi saving nan ta tuna fuskar tabbas itace suka taba zuwa da Ummeey toh kodai a ranar Aman ya fara ganinta, lallai dole ta dauki mataki don bazata taba bari ya kawo mata wannan kyakkyawar a cikin gida bah, tun yanzu ya fara mata tijara bare idan akayi auren gashi har yanzu Basu Wani jituwa Kuma juya Ammi ta fada mata cewa manya sun shiga lamarin ana jiran amsa daga gidansu yarinyar ya zama dole ta sake komawa ta girgiza su tunda warning din farkon Bai shigesu ba da wannan shawarar ta samu salama Sam bazata musu da sauki ba.

Back to top button