Banana Island Hausa NovelHausa Novels

Banana Island 25

Sponsored Links

Asabar , Nigeria.
Kwanci Tashi asaran kwana yau gashi Su Lili da Iftihal ana bikin yayesu, kowa ka gansa yina cikin farinciki saye da graduation gown ɗinsa‍ Iyaye da dangin kowa sun zazzo ,manyan mutane sun cika harabar makarantar ,amma banda iyayen Ifty ba wani mutum ɗaya nata da yazo ,but she’s still happy Tunda zata koma wajen everlasting mother dinta ,cikin aminci ,dama bata tsammaci zuwan wani nata ba,tunda suɗin ƴan jeji ne.,tana tareda familyn Lili sunata hotuna ,har 10.30am

Daga nan aka natsu a ƙatoton ɗakin taron makarantar mai kama da katoton theatre

Bayan shugabar makaranta da sauran masu manyan muƙamai daga professoshin makarantar sun tashi sunyi jawabinsu,sannan aka bar speaker ɗin makarantar on the stage Wanda shine zai fara kiran manyan baƙi na musamman .

“…and also a very benefit to our university with Mr. Adnan….jeeeeehh” Kalmomin speaker ɗin da ya shiga cikin kunnen Ifty kenan daidai sanda take shigowa ɗakin taron a makare.

take wajen ya rikice da tafi da sowa ,kowa ya ƙosa yaga young billionier ɗin da duniya take labarinsa

Adnan dake zaune a wajen manyan baƙi na musamman ƙafarsa harɗe ɗaya kan ɗaya jin an kira sunanshi yasa ya mike yina gyara zaman kwat ɗin sa ,ya haye kan stage ɗin masu tsaron lafiyarsa suna take masa baya.

Ranƙwafawa speaker ɗin yayi cikin girmamawa ya miƙa masa abun magana ɗin ,a dake ya amsa gami da cewa “Thank You”

Ifty da tayi mutuwar tsaye haɗiye miyau tayi da kyar ,daidai sanda Lili ta fizgo hannunta ,suka wuce inda aka tanadar don su daliban da ake yayewa.

Da haɗaɗɗen turancinsa ya fara jawabi a takaice
“Congratulations potential journaliste ,I my self deeply want to solicit you….”

Su Sumayya zakari ne suka haɗe kai wajen magana i junansu “Gaskiya gayen nan is hott…haɗaɗɗene!”

“Kudai Allah ya baku aiki kowa kuka gani sai kun tanka,ynz dai lokaci yayi da zaku tsaida miji kuyi aure”
Cikin bala’i sumayya ta kalli ifty

“Jini da wannan halan baƙin ciki kike mana ,ke an riga an kulle dake daga ciki ba sauran flexing life ,ko da yake auran kwadayi akayi gayinan auren ya kwai ya babu…”

Tuntsirewa da dariya Faty tayi “Ke ma dai zakari da wautanki ke kin yarda anyi auren? An dai buga barikin na wucin gadi ,wani mai kudine zai aura wannan baƙar halittar? Gashidai yayi using dinta yai damping banza ….kullum muku ² ana aiki a munafurce irin wai ga masu addinin nan .
Hmm ,yanzu dai matsayin mu daya bakida budurcin bandashi …gwara mu international ƴan iska ne da mun fita akwai identity za’a tare mu mu samu kuɗi. ..itakuwa bad belly ya kasheta haka zatayi ta zama”

Idon ifty tuni ya kawo ƙwalla tana kallonsa tana ganin duk shi ya ja mata wannan tozarcin ashe kallon karuwa ma ake mata?

Basu Ankara ba ,sukaji an fara kiran sunayen zakarun ɗalibai yina Basu certificate da award.

Mutane biyu aka kira aka fara shelan kiran sunan Iftihal_khair matsayinta Na gwarzuwan shekara wacce tafi kowa ƙoƙari .

Jiri na ɗibanta ta miƙe ,jikinta a sanyaye take takawa har ta isa gaban malaman ,su kuma suka turata wajen Adnan Wanda shine zai bata award ɗin.

Kautar da kanta gefe tayi,ta mika masa hannu da nufin ta amsa award ɗinta ta wuce ,zaraf ya kama hannunta ya riƙe tafin hannunta cikin tafin hannunsa ,A tsorace ta waigo ta kafesa da ido shi da alama ma ya manta abunda yayi ba daidai bane

Lalubo ƙwarar idonta yayi ya haɗe cikin nasa “Congratulation”

Turo baki tayi tana kiciniya da hannunta “To nagode ka cikani in wuce”

Ƙasa ƙasa yake mata magana kamar munafuki Camera man kuwa sai haskasu yake da hasken
“Jibi yanda kikasa hulan nan ana kalle mun gashin kanki,kefa matar aurene …matso in gyara maki”

“stopp now” ta faɗa tana waige ²,taga yina yunƙoron taɓa mata kai

“Kin manta dani? Kin daina ji dani?…me nayi maki?” ƙwalƙwal tayi da ido Jin an kira ɗalibi na gaba shikuma yaƙi cikata

Gaba daya annurin fuskarsa sauyawa yayi zuwa damuwa kamar zai mata kuka “Mrs miee kiyi magana”

“Dama …dama ina tunanin…”
“Nayi kewarki da yawa Plz ki bari mu haɗu yau ,na rantse sabd ke nazo wajen nan”

“No ita strictly on invitation Kuma ban gayyaceka ba so tsakaninka da management” ta janye hannunta da sauri ta barshi tsaye da award ɗinta Bata amsa ba ,riƙe award ɗin yayi sororo yabi bayanta da kallo kamar wani sakarai ,yinajin wani matsanancin sonta yina taso masa .

Bai ankara ba saida ɗaliba na gaba tayi masa magana ,ta gaji da tsayuwa bai kulata ba hankalinsa nacan wajen ifty da tayi tafiyarta .

Ɗan wayancewa yayi ya ajiye award ɗinta a gefe ,ya amsa na yarinyar a ƙagauce ya mika mata gamida cewa Congratulations baison ma hada ido da ita . Yarinyar na wucewa shima ya ɗaga ma speaker ɗin hannu alamun ya gaji ɗin nan ,an kira wani ya cigaba……

Ta bangaren student kuwa ifty da Adnan sun barsu da tsegumi saida lili abu ya isheta taji ana ta surutu tace mijinta ne fa ,yazo musamman ma saboda itane meye haka?”

“Mtseww na banza ! To in mijinta ne sai sun fito sun nuna ma duniya kamar akansu aka fara aure banza baƙa…” Hafsat tace cikin hassada

Sumayya ko zabura tayi “Au shiyasa saboda baƙar kishi daga mun yaveshi tahau mu da jaraba ,to munga ƙaruna indai kudine zai saki ɗagawa ƙarshe ma Allah nitsar dashi yayi dashi da tsiyarsa a cikin ƙasa ,don arzikin da ba’a tarashi ta hanyar Allah ba aikin banza ne”

Faty dake neman gindin zama wayancewa tayi “Kai sumayya banda kishi”

“Wa zanyiwa kishi wancan abun ?? Asaraaa…mtseww”

Adnan gudunmuwar maƙudan kuɗaɗe ya bada a rabawa fresh graduates ɗin sannan yaba zaƙwaƙuran ɗalibai kyautar motoci sabbin yayi.

Ai yina miƙewa zai fita daga ɗakin taron kikaga duk mutane sun bishi bayansa ɗuuuuuuu!
An tafi yin masa Rakiya . Har zai shiga jirginsa yasa a kirawo masa Lili .

 

Oum Aphnan
09065990265️ _*BANANA ISLAND*_
_(Billionaire’s paradise)_

Book 3
Page *U*

Na…
Oum Aphnan ✍

Back to top button