Matar So 25
Page….25
Sauka yayi daga gadon jiri na ɗibanshi ya ɗauki hijab ya saka min, kallon yanda na makale a jikinshi naki rabuwa dashi yasa shi kara rungumana, wayata ya amsa ya kira Aman rahilah ce ta ɗauka ya ce.
“Kicewa Aman yazo yanzun.”
Toh tace.
Takira Aman da yake bangare hindu, ta faɗa mishi da sauri ya nufi asibiti koda ya isa ganin yanda nake kuka gashi na makale mai nasara, sai abin ya bashi mamaki yace.
“Man lafiya?”
Dakyar mai nasara yayi mishi bayani. Hmmm tashin balagan tsintsiye fita Aman yayi yaje gurin babba likintan yayi mishi bayani abinda dr Femi, kuma yau zaisa a rufe asibiti.
Kafin seven na safe manya da kananu na asibitin sun taru ana meeting, dakyar aka shawo kan Aman dan Mai nasara yace sai kotuce za rabasu da dr Femi.
Su kuma asibitin suna ɓoye maganar ne dan kar siyasa tashiga a rufe musu asibiti musaman da suka san Waye Mai nasara.
Abinda sai da aka haɗa da Mahaifin Aman sannan suka hakura, har lokaci ina jikinshi dan gani yake ko ya-ya ya kyale ni wani zai kaimu hari.
Karshe dakatar da Dr Femi akayi na wata shida da hanashi albashin watanin.
Can gurin 8 aka kawo mana kunun tsamiya, da soyayyen dankalin turawa sai farfesun zabuwa ina jin kamshi na dira a jikinshi dan kamshin girkin Mama Amarya ce, gaida ya Kabir nayi wanda yazo ganin gida dan aikinshi a abuja ne, hira sukayi da mai nasara da Aman bayan tafiyar Ya kabir, Mai nasara ya wani tsuke fuska, yana hararana kuma abinci nake zuba mishi fa,
“Kee dawo nan.”
Ya buga min tsawa, sake abincin nayi na koma jikinshi na lafe, har da kifa kaina a kirjinshi suka cigaba da hiransu.
Abincin da banci bakenan shima kuma bai ci ba, nayi barci har Aman ya tafi bai tashe ni ba.
Sai kallon fuskana yake yana shafawa a hankali.
A cikin kwanaki huɗu da mukayi a cikin asibitin, naga kayan takaici dan tsakani da Allah mai nasara ya hanani walwala a gaban mutane. Wani shegen kishi ya tsiro mara ma’ana.
Ranar na rakasu Mama Amarya da suka zo gaishi, na jiyo zan koma cikin asibitin sai ji nayi ance.
“Maryam Omer Hayat.”
Juyawa nayi naga Uncle Mustapha na makarantarmu, cikn sakin fuska na gaidashi nace.
“Uncle waye kazo dubawa.”
“Mata ta ce tahaihu shine na kawo musu abinci.”
“Ayya muje naga matartaka.”
Haka muka tafi har inda aka kwantar da matar ina zuwa naga babyn naɗe a showel pink ɗauka babyn yayi ya mika min, na kalle matan na gaisheta ina murmushi nace.
“Masha Allah barkallah.”
Addu’ar da akewa jarirai nayi mata sannan nace.
“Uncle babyn da Mamienta take kama fa bada kai ba.”
Dariya yayi sannan yace.
“Allah ko?ke waye kika kawo asibiti?”
Mikawa matar babyn nayi cikin kunya nace.
“Mijina ne ba lafiya, amma ina ganin anjima zamu sami sallama,”
Sake kallon pink lips ɗin babyn nayi,
“Ayya Allah ya bashi lafiya, zan bi ki nagaida shi.” yace min,
Sallama nayi musu sannan muka fita har ɗakin da mai nasara yake, cikin mutunci suka gaisa da uncle yayi mishi ya jiki, a fakaice kuwa hararata yake da wutsiyar idanunshi, har uncle ya fita na mishi rakiya waje tare da godiya yace.
“Dama Yunus marafa ne mijinki, Ah na tayaki murna dan mutumin kirkine.”
Gyaɗa kai nayi tare da godiya, sannan ya tafi ina shiga ɗakin yace min.
“Koma inda kika fito.”
Kallonshi nayi cikin rashin fahimta nace.
“Kamar ya?”
Na tambaye shi.
Banza yayi dani, dan yaga zan rena mishi hankali.
Shiru nayi na nemi guri na zauna, amma ranshi na kara ɓaci.
Yo ni wallahi ban fahimci haushi yake jiba sai daya sake min magana a hasale.
“Tashi ki koma gurin sabon saurayin da kika yo, wato ni zaki mai da ɗan iska shine har da gayyato min kato kaina, hmm Allah ya bani lafiya zamu haɗu a gaban Ummanki.”
Sororo nayi sannan na taɓe bakina na ɗaga kafaɗata nace.
“Wannan damuwarka, ban taso naga ana abu mara kyau a gidanmu ba balle afara a kaina, daga malaminmu yazo gaisheka sai ka nemi jifata da wasu maganarka marasa daɗi,su matanka da suke fita kusan tsirara baka taɓa ihu akansu ba sai ni da nake sanye da hijab da nik’af toh ba damuwa bari naje gurin sahibin ruhin na……”
Bansan wani irin tsalle yayi ba, sai jinshi nayi a kusadani yana huci. Dama kunsan wakiliyar tsoroce jikina ne ya ɗauki rawa.
Zare hijab ɗin yayi cikin wani mahaukacin kishi ya haɗi da bango ya shiga kokarin, ladabtar dani ta hanyar ya mutsa min jiki da zaffafan sakonshi.
Dake ina jin haushi sam banji komi ba sai dai shi da ya gama shirmenshi ya kyale ni, a gurin.
A ranar ya nemi sallama, muka nufi gida tun a hanya na ajiye ɓacin raina na shiga hankalina.
Koda muka isa gidan, ko ina ba daɗin shiga dan ma Ahmad yana sauke mu ya juya, murmushi nayi ganin falon har zai wucce nace mishi.
“Yau zaka ga amfanina.”
Na haye sama, wanka nayi na sauya kaya dama nakan zo gida ɗaukar kayana, ko wani abu.
Gyara ɗakina da falona nayi na sauko kasa na gyara kitchen, na ɗaura taliya jallop da irish, sai bushashen kifi na haɗa zoɓo nasaka gwaiba da Qcumbe, gabaki ɗaya gidan ya ɗauki kamshi da turarena da girkina,
Saka zoɓo nayi a firij nasaka hijab ɗina, na fita waje gurin drvn gidan na bashi dubu ɗaya nace.
“Don Allah malam, yahya ko zaka sayo min bevi mix da tiara, na dukka kace su haɗa maka kaloli daban daban.”
Karɓa yayi cikin mutuntawa ya fita, bai ɗauki mota basai nacewa Mai gadin ya kirashi na bashi kuɗin mashi yana lekawa ya dawo yace.
“Hajiya har ya tafi.”
gyaɗa kai nayi na juya, sai akan idanunshi wallahi sai da gaba ya tsinke, Fareeda na tsaye a gurin, nazo na wucce bin bayana suka ina shiga falo yace.
“Maryam wallahi kina kure ni fa, zan miki shegen duka.”
“Toh kayi hakuri bazan kuma ba.” nace tare da wuccewa kitchen ɗina, kumfa naga yana fitowa a cikin tukunyar girkina buɗewar da,zanyi kamshi morning fresh ya dake ni. Lumshe idanuna nayi na sauke girkin na kashe gas ɗin, ajiye abincin nayi yayi sanyi sannan na juye a leda, nasaka a kwndon shara.
Wanke tukunyar nayi na ɗauki wata yar karama na dafa indomie da kifin dan raina naso na juye a filet na zauna jiran tiara na kaman ance na ɗauko zoɓon na duba shi kuma gishiri aka zuba min, wankewa nayi na zubar na fito kan dinner table na zauna ina cin indomie dan rashin kunya sai ga Sameer yazo wai “kee ki bani abincin da kike ci.”
Murmushi nayi na ɓoye bacin raina nace.
“Kaje kitchen ka ɗauko fork kozo muci.”
Dariya yayi sannan yace.
“Ashe kina da kirki ai Mommyna da Mufeeda suka zuba miki morninig fresh da gishiri a cikin a bincinki.”
Juya idanuna nayi irin ba damuwar nan zomuci.
Kallon Uwarshi nayi wacce ta buga mishi tsawa sai da Uban yafito dake tarbiyan da suka aza yaron akai knn yace.
“Mommy ai ba karya bane morning fresh kuka zubawa bakuwar Dddy a cikin abincinta, har da drink ɗinta kuka sak…”
“Sameee.”
Kallonta Mai nasara yayi cike mamaki, yace.
“Ki biyo ni ɗakina.”
Ba musu ta bishi, ban san mi ya faru ba sai dai yanda na gan take tafiya yasani shiga ruɗu. Mi yayi mata take tafiya kamar Yar kaciya.
A ɗakinshi kuwa da ya kirata girma da arziki ya fara mata magana aikuwa ta shiga mishi ɗanye kai shine ya murɗa ya biya bukatarshi tare da doka mata gargaɗi, da kuma horon fita ko ina sai bayan sati biyu.
Ina zansan wainar da suke toyawa ba, sai dai sun fito min ta inda ban tsamanta ba, dan har takai Mufeeda takan iya kallon idanuna na tace min karuwa,
Ranar a gabansu Fareeda ta faɗa min.
“Karuwa kawai wacce take kazamta da Daddy ko an ce miki banga kina saka bakinki na nash….”
Faɗuwar abu muka ji a bayanmu ashe ya shigo gidan, wayarshi tana cikin vibrater zai ɗauka yaji abinda yarshi take faɗa sai da wayar ta tarwatse gida biyu, kaman zaki haka yayo kan Yarinyar ya shiga kwallo da ita tare da fincikar wayar kayan kallo ya shiga zabga mata inda yake shiga bana yanke fita ba, shegu munafukai guduwa sukayi, tun yarinyar na kiran Mommy kozo daddy zai kashe har tayi shiru bai fasa, haka uwar yarinyar tazo ya haɗa da ita da gudu tabar gurin.
Bayanshi naje na runguma tare da kwantar da kaina nace.
“Mai hakuri yana tare da Allah, duka ko zagi bashine tafarkin shiriya ba, addu’a da kai wa Ubangiji kuka shine jigon shirya, sai tarbiya tasamu yanda ake bukata.”
Tsit ya tsayar da dukan tare da juyawa ya kamo hannuna ya kalle ni, cikin wani irin murya ya buɗi baki zai magana amma ya kasa, ɗakinshi na mai dashi na zaunar dashi, ruwa na ɗibo mishi na bashi yasha. Sannan na xauna ɗaura kanshi yayi akan cinyata jin ɗumin ruwa yasani shafa inda nake ji a she kwalla yake zubdawa.
Shafa kanshi na shiga yi, har naji yana sauke ajiyar zuciya, zuwa wani lokaci naji shiru kwantar da kanshi nayi a pillow na fita waje, babu wanda yayi yunkurin zuwa gurin yarinyar wacce ta suma, ruwa na ɗauki na watsa mata, ta fasa kara tare da ɗaga hannayeta, mikar da ita nayi na kaita ɗakina na haɗa mata ruwan wanka tana dawowa hankalinta taga nice..
“Muguwa azzaluma, karuwa na faɗa miki na kuma faɗa miki naga lokacin da Daddy yake taɓa nononki mayya….”
Bansan ya fito yabiyo ni ba, sai ganinshi nayi a tsakiyarmu, sabon kuka ne ya kamata, ya riko hannunta wanda tsabar rikon sai da tasake fitsari ya kaita ɗakin Uwarta ya cillata kan balkisun da suke Waya da Mama kilishi tana faɗa mata, abinda Yunus yake musu tunda na dawo gidan,
Tsabar karfin cillata da yayi sai da ta bugu da center table take goshinta ya ɓalle da jini Balkisu tace.
“Mama kinga ya kashe min, dan bai san darajarta ba.”
Zama nayi ci kuka a ranar toh idan banyi sirri da mijina ba dawaye zanyi wato har yarinyar ta gano irin abinda yake min ysr shekara goma fa, na shiga uku nace.
Shigowa yayi na goge kwallata zama yayi kusadani, yana shafa bayana, ganin balkisu mukayi ta cilla mishi wayarta ɗauka yayi yaji Muryan Hajiya tace.
“Gobe ka haɗosu kuzo zaria.”.
“Toh hajiyata”
Ya kashe wayar, kunnena ya laluba yace.
“Kina son mukoma gurin mazaje mu hau doki.”
Juyawa nayi ina mamakin yanda yake boye damuwarshi murmushi nayu tare da jan hannunshi na naɗe cikina dasu na kwantar da kaina kirjinshi ina dariya kwalla na sauka, jin bugun zuciyarshi har yana ratsani, gyara rikon yayi tare da sauke a jiyar zuciya, kwalla ke sauka a idanunshi zuwa ka faɗata, ina ji kuma ina gani, bazan iya hanashi ba, sabida wannan itace hanyar da zai rage damuwarshi, ta zubda kwallar kwanciya mukayi.
Yanayin ya tafi da halin da muke ciki kuma na fahimci wani abu guda shine, yunus nada matukae fusata da zafin zuciya, amma kuma mutum ne mai iya shanye zafin da kona, juyawa nayi na kalleshi ina goga hancina kan nashi, nace.
“Daddy”
“Shiiiiiii! Am ok.”
Gyara kwanciyana nayi ina wasa da gargasar fuskarshi, ina kuma karewa farar fuskarshi da tayi ja, a yau a hankali na tsotsi bakinshi, na kalleshi har lokacin idanunshi rufe, sake yu nayi bai buɗe ba, sai da nayi mai karfi ya buɗe shanyayyun idanunshi wnda suka kara rinewa, rike kaina yayi yana bina yanda nake mishi a hankali na shiga gwada mishi irin abinda yake min, buɗe idanunshi yayi yace.
“Maryam bari haka ya isa am not in mood.”
Janye jikina nayi na juya mishi baya, tare da fashewa da kuka, yayi yana sauraron kukan nawa, wanda yake kokarin fasa mashi dodon kunne, janyo ni jikinshi yayi ya juyani yana share min kwalla, dakyar ya iya buɗan bakinshi yace.
“Miye abin kuka kuma, kinsan bani da lafiya, ga yawan tension ga jigilar aiki ga damuwar iyali maryam da wanne dan ji, gaki kina min kallon mara adalci suma wayancan suna min kallon haka, yakuke son nayi ne? Ko so kuke kuga na faɗi hawan jini ya likani da kasa ko, yanzun kiga abinda mufe…”
Rufe mishi bakinshi nayi da yatsar hannuna, ina kallon cikin idanunshi, nace.
“Tun fil’azal kaine ka lalata gidanka da hannunka, Daddy baka ɗauki mace da kima ba, bata da wata daraja a gurinka kasan sabida mi yasa haka?”
Girgiza min kai yayi cikin sanyi jiki.
“Sabida dukkanmu babu wacce ka gani kake so, duk lika maka mu akayi babu wacce ka bugi jiki ka nime aurenta dan kana sonta sai dai Hajiya susaka ka cire kuɗi su haɗa maka komi kai dai tsakaninka da mace ku haɗu bayan aure ko ba haka bane? Idan ta sami ciki magana ya kare dan zata haifa maka yara, daga nan ta haihu dama bata ita kake ba ta ɗanka ne kuma ta sauke magana ya kare, zaga zuba mata kuɗi tayi rayuwar freedom ko ba haka kace ba? Daddy knn, ka ɗauki yahudu da nasara ka lika a rayuwarka ka ɗauko *Al’adun wasu* (Aunty Batul Mamman) ka ɗaurawa rayuwarka san baka yarda da komi ba sai Rayuwar bature babu addini a ginin gidanka, wanda ya dace ka tsawatarwa basu kakewa ba sai wanda kasan ko kara kasaka bazasu gifta ba kayi nazari da kyau babu amfanin aro abu a wani yaren da ba addini ba, dan ni Musulinci shine Yarena Addina.”
Zame jikina nayi dan ganin kamar yayi barci, murmushi nayi me ciwo duk surutun da nake mutumin nan ashe barci yake ma abinshi. Fita nayi na sauka kasa, na fara girka abinda zamu ci, ina cikin girkin naji an finciko ni juyawa nayi takuwa sa hannunta ta kife ni da marin a kiɗime na riƙe fuskana zata kara min na rike hannunta, cikin kuka nace.
“Wallahi sabida huda zan kyaleki amma badan haka ba, da sai na rama akan mi, kina jin ciwon dukan da yayi mata kika gaza tsayawa ki kwaceta ba, kika gudu idan da ke uwar gaskiya ce tsayaqa zakiyi dan karɓan rayuwar Y’arki amma kika gudu kin haife Yara amma baki san miye suke ba, Yar shekara goma amma tasan mi ubanta yake aikatawa kin bar Yarinya tsakanin kishiyoyi tana kara kaina, wallahi Allah bazai barki ba kuma kika kuma kara taɓa ni zan miki hauka, babu abinda ya dame ni miji kike aure nima shi nake aure baki da hujjar taɓa lafiyata.”
Wurga hannunta nayi na cigaba da aikina, sororo sukayi suna kallona wato basu yi tsamanin zan kwaci kaina ba, gashi sun zugota so suke ta kamani da duka wato ga jakarsu.
Yana zaune a kan kujeran Dinner table yana jinmu, juyawa sukayi duk sai da suka razana tsabar tsoro da firgici, wato a duk lokacin da suka shirya min kata’i sai Allah ya turo min shi. Idan mutum yaga tagumin da yayi sai cikinshi yayi ciwo sabida dariya, lumshe idanunshi yayi ya zauna ya buga tagumi, fuska a sake kamar bai ji komi ba haka suka fito kamar munafukai kowacce ta ja tsintsiyar kafarta zuwa ɗakinta,
Suna fita na fashe da kuka, sosai dan sai da na rufe kofar kitchen ɗin na zauna a kujerana ɗan tsuguno, na sunkuyar da kaina kasa ina kuka, tashi yayi ya shigo yazo bakin kofar kitchen ɗin ya murɗa hannun kofar ya leko da kanshi, yana kallon yanda nake yanda na cusa hannuna cikin gashin kaina, wnda ɗan kwalin ya warware.
Shigowa yayi ya jingina da kofar yana kallon yanda nake kukan, takowa yayi har gabana ya durkusa ya jima sosai kafin ya ɗago kaina, juya fuskana yayi yaga yanda yatsun balkisu ya kwanta a kuncina sai yaji ranshi ya soma ɓaci, mikewa yayi ya juya yabar kitchen ɗin ba tare da tace min kala ba.
A hankali na mike nima na wanke fuskana na karasa chinese fried rice, da qcumbe juice sai peppe fishi, na juye su na, jera a ture na wucce dasu sama, na baza a falona.
Na tashi na rufo kofar na faɗa ban ɗaki nayi wanka, sosai nazo nasaka riga da skirt na roba, wannan atamfar roban nan, dai na 1500, yaji ɗinki sosai dan sai ka kure mishi kallo zaka fahimci robane( Toh ynz wata sai tace akan mi matar mai nasara zata ɗaura wuta sallau, ku duba gidan da Maryam tafito kuma ma yanzun matan masu kuɗin ɗaura roba suke balle mu talakawa musu ɗauƙar rayuwa high class)
Zama nayi na ɗaura ɗan kwalin kamar yanda zahra buhari take ya zauna min sosai(Not ɗaurin zahra buhari ba sabon trender bane sunan ɗaurin dacan Maryam Babangida, muna yara dashi Dear Mama take kahe mana Babanmu yasin kuwa Allah ya mata Rahama yasan can yafi mata nan kyawawan da alkhairin da abinda ta bari muzame mata, haske akabarinta, Amin Ya Allah)
Kwali na ɗauka na murza a idanuna wanda suka jeme da kuka, sannan na shafa hoda sleek a fuskana, zubawa madubin ido nayi, jin ana buga min kofa yasani mikewa dakyar nafito, buɗe kofar nayi ina kallonshi sanye da dark brown kaftani trouse da farar janfa kana hango black singlet ɗinshi ya zura hannun da ya buga kofae a aljuhun wando ɗaya hannun yana shafa kanshi, tsayawa nayi ina kallonshi daga sama har kasa, kamshin dior na shaka turarenshi bansan lokacin dana lumshe idanuna ba, sai da ya gyara murya yana wani munafikin murmushi, tare da kashe min ido ɗaya.
“Zaki bani hanyane ko zaki tsaya kallon Daddyn kawarki.”
Buɗe mishi kofa nayi ya shigo falon, nima nabiyo bayanshi na zauna akan kujera dake kallon nashi, kallon abincin yayi ya kalle ni, na fahimci abinda yake nufi dan haka na mike tsam nayi serving ɗinshi, zan miki ya riko hannuna yace.
“Zauna muci.”
Kallonshi nayi ina jin zafinshi da haushinsa kasa nayi da kaina nace.
“Na koshi.”
Tura min abincin yayi zai mike, da sauri nace.
“Kayi hakuri zanci.”
Saka spoon ɗin nayi hannuna na rawa na ɗibo zan kai bakina ya riko spoon ɗin zuwa bakinshi, haka nasake ya kuma juye abincin bakinshi take na fahimci abinda yake nufi ina ɗiba zan kai bakinshi, falauu Aneesah ta shigo babu sallama.
Bai ɗago ba kuma bai fasa karɓan abincin ba, sai da tazo tasa hannunta ta ɗauki kular, ya ture hannuna ya kama hannunta, ya amshi abinci. Naga tashin hankali a duniya ban taɓa sani mutum mai shiru da rashin magana wutane ba sai a lokacin yana ajiye kular ya mike da hannunta wallahi sai danaji karan kashin hannun, zuɓewa tayi sumamiya take na fasa ihu nayi baya jikina na wani irin rawa, babu tausayi babu komi yajata, har tsakar falon da kowa yayi cirko cirko, ya wurgata ya shigo falona ina ganinshi na fara ja da baya, jikina na rawa.
“Zoki karasa bani abincin ban koshi ba.”
Ya faɗa kamar bashi ba, girgiza kai nayi nace.
“Bazan iya kaci kawai.”
Mikewa nayi yayi, nayi bayi tsabar na razana dashi saura kiris nayi karo da show glass ɗina na turaruka, yayi maza ya rikoni ajiyar zuciya na sauke tare da tafiya baya zan zuɓe, na tsorata sosai dan ko dukar da yayi min bai sani jin tsoronshi ba kamar karya hannun Aneesah kamar ba Y’ar uwarshi ba.
Dauka na yayi ya kwantar dani akan kujera ya tashi, ya ɗauko ruwa akaramin firij ɗin falona ya buɗe ya watsa min, firgit nayi na mike naja da baya zan hantsila, ya rikoni sosai, yace.
“Ki fahimci abu ɗaya, ni bana komi sai da dalili baki min komi ba akan mi zan taɓaki, kuma nayi alkawarin bazan taɓa barin wata taci mutuncina a gaban kowa…”
“Mi yasa zuciyarka bata iya sarrafa fushinta?”
“Sabida ni mutum ne kamar kowa, bana son ka taɓa ni indai ina kiyayye maka.”
Kuka nasaka tare da maida kaina nayi ina kuka, ya zuba min ido.
“Gaskiya ina jin tsoronka.”.
“Ba damuwa tunda ni bana tsoronki kawai ki bar kukan ya isa haka ki shirya mufita.”
Kamar zance bazani ba sai nayi shiru, abincin da bamu karasa bakenan, ya fita nima na tashi na shige ɗakina na sako hijab ɗina, na fito, duk suna tsaye sunkuyar da kaina nayi sabida karfin kallon da suke min, na sauka da sauri ina jin mufida tana cewa.
“Mayya karuwa, me bin maza kawai.”
Uku uku na haɗa step ɗin na sauka, kallona yayi tare da guntun murmushi, nima na maida mishi na wucce ganin yayi gaba,
Shiru nayi ina nazarin, gidan Yunus da abubuwan cikinsa, bashine matsalata ba a yanzun matanshi ne matsala, dan bana ta mufida.
Yawo mukayi a garin kaduna, har gurin cin abinci ice cream da su snack, kan da chocolet munyi kayanshi kallona yayi, yace.
“Ko xaki gaidai da ummankine.”
Zaro ido nayi cike da murna har na manta ɓacin ran da nake fama dashi nace.
“Don Allah da gaske, kace wallahi”
Girgiza kai yayi, yana kallon hanya rike hannunshi nayi ina wani blush da fuskana.
Jan hancina yayi, na zaro ido nace.
“Karka cire min hancin.”
Hanyar unguwarmu ya nufa sai yayi parking ya kalle ni yace.
“Haka zamuje musu hannu rabbana.”
Ina hango gida, yana shirin min bukulu raurau nayi da ido ina niman kwallar da zan sauke mishi, dungureni yayi yace.
“Magulmaciya ba hanaki zuwa zanyi ba, kawai ba daɗi muje musu haka mu koma idam muka dawo daga zaria sai na kaiki ki wuni ko?”
Sunkuyar da kaina nayi tare da gyaɗa mishi. Jan motar yayi muka koma gidan mun sami Mahaifiyar Aneesah da kannenta sun zo, da me ɗori, sai ihu take.
Taɓe baki yayi yace.
“Umma alti ina wuni.”
Yanda ta tsare gida irin bana son tsurku.
“Yanzun Yunus gigin auren budurwa ce tasaka karya hannun Yar uwarka.” ta wurga mishi tambayar.
Juyawa yayi ya kalleni ganin inata gaishesu basu amsa ba sai kallon banxa suke min.
Gyara muryanshi yayi ya kalle step ya sake kallona, kafin ya buɗe bakinshi na kama hanya. Ciki da mamaki suke kallona, har Mahaifiyar Aneesah zama yayi, akan ɗaya daga cikin kujerun falon yayi crossing leg, yayinda ya zuba hannuwanshi sama kujeran.
Ya lumshe idanunshi bayan ya ɗaura kanshi saman kujeran, yace.
“Malam mi gyara baka gama bane? Kuma ya,zaka shigo min gida kai tsaye idan nasaka aka kamaka waye da gaskiya.”
Mutumin bai iya bada amsa ba ya haɗa shirginshi yayi waje.
Yana jin fitar mutumin ya ɗago kanshi kallon Munira da Juwairiya yayi, irin kallon kuma ku bani guri.
Tura baki sukayi tare da tambayar Aneesah ɗakinta, faɗa musu tayi suka hauro sama gyara zama yayi ya saka hannunshi akan fuskarshi yace.
“Umma alti!!!” har sau uku, cike da mamaki take kallonshi, murmushin takaici yayi ya mike ya tafi ɗakinshi ya kunna wayar Aneesah da ya kwace ya buɗe mata abubuwan da ta ɗauka namu, sannan ya kunna systerm ɗinta ya nuna mata,
Sannan ya kashe yana murmushi wanda zaka san *Da ciwo a rayuwarshi* mikewa Ummaalti tayi ta kwalawa Munira da Jawairiya kira, da sauri suka sauko fita tayi har takai bakin kofa tace.
“Kayi kokari mada iya hannun ka karya, banyi tsamanin saki baxai biyo bayan laifin ba, duk abinds ka yanke dai daine.”
Tana gama faɗar haka tayi waje cike da kunya da ɗan danasanin, zuwanta da maganar da tayi mishi.
Ina zaune ya shigo har lokacin fushi nake dashi dan yaki kaini gurin Ummana, amma a haka alewar tsinke ne a bakina, yana shigowa na kauda kaina, tare da zare alawar lasa, sannan na maida bakin, sake cirewa nayi na lasa cike da jin daɗi, amma zuciyata ba daɗi sam, ɗaukar ledojin yayi ya fita dasu, ya kaiwa kowacce ɗakinta, a wulakance suka kalleshi.
Koda ya dawo ya mika min nawa na amsa nace.
“Allah ya kara buɗe.”
*Allah ya haɗamu gobe a zaria dan mai nasara ya zama abin tsoro*
[8/25, 3:00 PM] Real Mai Dambu:
*MATAR SO*
*MAI_DAMBU*
*Wattpad:Mai_Dambu.*
*HAZAKA WRITER’S ASSO*
(HWA)
Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai….
Sadaukarwa Ga Yan grp ɗin Matar So….
Dedicater To Hafsat Abubakar
_Wannan buk ɗin hakk’in masu shine idan kinsan baki saya ba karki karanta, mai fitarwa kuma ki duba girman Alkawarin da kika ɗauka na cewa bazaki fitar ba, tunda nace idan kinsan zaki saya ki fitar na Yafe ba sai kin saya ba_