Hausa NovelsYarima Suhail Hausa Novel

Yarima Suhail 70

Sponsored Links

PAGE* 7⃣0⃣

Yarima saida yai sallar asuba sannan yad’auko zarah suka dawo gida, staffs d’insa wad’anda sukayi night duty zuwa suka dinga yi suna tayasa murna,, a mota zarah da take rungume da babyn ido tazuba masa tana kallo cike da sha’awa, yarima da yake tuk’i juyowa yayi yakalleta yai murmushi har zaiyi magana sai kuma yafasa.

Lokacin da suka isa gida suna fitowa daga mota su dada da suke tsaye suka iso inda suke, sultana sadiya ce tafara kar6an babyn cikin jin dad’i tadubasa tai masa addu’a sannan tamik’a ma dada nan dada har da hawayenta tace suhail ashe da rabon zanga d’an cikinka, cikin jin kunya yarima yasosa kansa, zarah ko rufe fuskarta tayi da hijab d’inta saboda kunya, nan su memartaba ma suka amshesa cikin farin ciki sukayi ma yaron addu’a, sultana bilkisu ko d’an kallonsa tayi ta gefen ido saboda kunya, nan sultana sadiya takar6esa taja zarah suka wuce 6angarenta, room guda tasa aka bud’e ma zarah, jakkadiya tazo takar6i jaririn dan tayi masa wanka.

Related Articles

Dada aikawa tayi da mota aka d’auko mata wata hajiya tsohuwa da tayi ma husnah wankan jego lokacin da tayi haihuwar farko, koda tsohuwar tazo nan tayi ma zarah wankan jego.

Bayan sun fito tea mekauri aka had’a mata tasha kafin agama tuwo, sultana sadiya tayi-tayi zarah tashayar da babyn ammah tak’i wai ita kunya saida taga tana niyar kiran dada sannan takar6esa tana nok’e-nok’e cikin jin kunya tabashi yasha, daurewa tayi duk zafin da takeji cije le6e takeyi, nan sultana sadiya tatsareta saida taga ya k’oshi sannan takar6esa tace zarah takwanta tahuta, nan zarah tayi kwanciyarta dan rama baccinta.

Sultan bilkisu sosai taji dad’i da sultana sadiya tawuce da zarah part d’inta dan ta san halin d’an nata.

Yarima koda yakoma part d’insu nan kuyangi da bayi suka dinga tayasa murna akan k’aruwar da aka samu, saida yakira su mama yafad’a musu haihuwar sannan yaje yai wanka yakwanta ammah yakasa bacci saboda farin ciki, daga k’arshe mik’ewa yayi yajanyo alkyabbarsa yasaka yafito yanufi part d’in sultana sadiya, cikin sa’a yatarar da bakowa parlour Dan haka yawuce room d’in da zarah take yana tura k’ofan yaji ta bud’e cikin jin dad’i yashiga, hangota yayi saman gado ta baje tana ta kwasar baccinta, ahankali yamaida k’ofan yarufe sannan yawuce yaje yahau gadon yakwanta daga gefen zarah kallonta yake cike da tausayinta baccinta take a nutse, hannu yakai yana shafa fuskarta cikin so da k’aunarta ganin ta motsa yasa yajanye hannunsa nan yarungumota jikinsa ahaka shima yasamu bacci yad’aukesa.

 

Wajen k’arfe goma knocking d’in k’ofar da akene yatashesu daga baccin da suke, zarah cike da mamaki takalli yarima tace nashiga ukku yaushe kashigo nan? Murmushi yayi yace kina tunani zan iya yin nesa da ke?

6ata fuska tayi kamar zatayi kuka tace haihuwa fa nayi kuma nan ai ba 6angarenmu bane yanzu ya kakeso inyi idan aka shigo aka ganmu a tare?

Kedai baby tsiyata da ke kin faye tsoro toh menene dan anganmu.

Har ta bud’e baki zatayi magana nan aka k’ara knocking d’in k’ofar, nuni yarima yai mata alamun taje tabud’e.

Mik’ewa tayi tanufi k’ofan ahankali tabud’e tad’an lek’a kanta ganin sultana sadiya ce rik’e da baby daga bayanta wata kuyangata d’auke da tray nan wata irin kunya takamata dakyar ta iya matsawa tabata hanya.

Ganin yarima zaune saman gado yasa sultana sadiya tace suhail ba dai zuwa kayi ka hanata bacci ba?

Murmushi yayi yace a’a ummah ni ban hanata bacci ba yanzu ma tafarka,
Toh hakan ya yi, nan taba kuyangar dama ta aje tray d’in tafita.

Yarima kar6an babyn yayi daga hannunta.

Sultana sadiya kallon zarah tayi tace ga tuwo nan kizauna kici dada ta aiko miki da shi ta ce kicinyesa sannan ga pepper nan shima kar kirage komai har romon.

Ahankali zarah tace toh ummah ammah ai ban iya cinye duka.

Kedai yanzu safko kifara ci, mik’ewa zarah tayi taje tawanke bakinta sannan tadawo tazauna tabud’e tuwon ahankali takeci.

Kallon yarima tayi da yake wasa da babynsa tace kasafko muci.

Sai a lokacin yakalli tuwon yamitsa fuska yayi kamar Wanda yaga wani kashi yace menene wannan kuma?

Harararsa zarah tayi tace ba kasan tuwo bane.
Ta6e baki yayi yace ni irin wannan tuwon ya fi k’arfina aci lafiya.

Dariya sultana sadiya tayi tace daman wannan na masu jegone, yanzu dai yi sauri kici kiba yaron nan yasha dan yunwa yakeji.

Haka sultana sadiya tatsareta saida taci tuwon sosai taci pep d’in da aka kawo romon dukansa tashanye.

Bayan ta gama zuwa tayi tawanke hannunta tafito, nan sultana sadiya takalli yarima tace suhail gatanan katsareta taba yaron nan yasha dan yunwa yakeji.

Kallon zarah yayi da take turo baki sannan yace toh ummah.

Bayan sultana sadiya ta fita ahankali yace sweetmee kizo kizauna man.

Daga nesa dashi kad’an tazauna nan yamatso yad’aura mata babyn saman cinyarta.

babu yadda ta iya haka tadaure tashayar da shi, suhail saida yaga ya k’oshi sannan yad’aukesa yace baby kikwanta kihuta bari inkai ma ummah shi inkama gabana tun kan jama’a sufara zuwa.

Komawa tayi takwanta nan yabata peck a goshi sannan yafita a parlor yatarar da ummah nan yamik’a mata yaron sannan yaficce.

Kafin azuhur mutane dayawa sun taru gidan, sultana sadiya dakanta taje tahad’o ma zarah kayanta da na baby a chan part d’insu.

Su Rahama da sumayya sosai suka nuna farin cikinsu da suka ga babyn nan sukaita santinsa.

Yarima kud’i yaba Aunty Husna sosai taje tahad’a ma baby da mejego kaya na azo agani masu kyau da tsada.

Yarima yaso amaida masa matarsa part d’insu ammah sultana bilkisu tace kar yakuskura yatunkari sultana sadiya da maganar yabari tazauna chan har tagama wanka ba dan ya so ba kan dole ya hak’ura yabarta saidai kusan kullum yana manne da ita da babynsu, tun sultana sadiya tana fad’a har tagaji tadaina.
Ita kanta dada koda talura da yadda yake shige ma zarah fad’a tayi masa sosai ammah yashareta baifasa abinda yakeba.

Sosai su dada suke nuna ma zarah kulawa inda hajiya tsohuwa tazage tana gyara mejego sosai.

Su yaya rauda ko kusan kullum sai sunzo gidan hatta ita kanta amarya Aisha.

Tun ana saura kwana ukku suna ‘yan agadaz sukazo 6angare guda aka bud’e masu sosai masarautar tacika da bak’i.

Ranar suna yaro yaci suna Faruk Umar Faruk (Ameer Faruk) memartaba sosai yanuna farin cikinsa da karar da akayi masa shanuwa biyu da rago biyu yabada ayi hidimar suna, inda yaware shanu hud’u da garken tumaki sannan yakawo alkyabba yabada yace na takwaransa ne.

Su daddy da abbah ma ba’a barsu a bayaba dan filaye sukaba Ameer faruk sai cheque na mejego

Sultana sadiya da sultana bilkisu suma gudunmawa suka bada ta azo agani.
Dada kanta ba’a barta a bayaba kaya masu kyau da tsada tasa aka had’o ma mejegmejego da baby.

Shagali akayi sosai inda jama’a sukaci sukasha, zarah tasami kyautuka sosai a wajen ‘yan uwa da abokan arzik’i hatta abokan suhail da matansu ba’a barsu a bayaba suma sun bada tasu kyautar.

Jamila da Dr mu’az ma tun ana saura kwana biyu suna suka dura garin dasu akayi komai.

Yarima raguna hud’u da shanu ukku yayanka ranar sunan aka had’a da Wanda memartaba yabayar, a ranar anyi shagalin da ba”a ta6a kamarsaba a garin anci ansha har aka bari.

Da dare sultana sadiya ce sai su sumayya suke duba kayan da zarah tasamu dan turame da kayan baby kamar za”a bud’e shago, ga mak’udan kud’i, bayan sungama dubawa nan sukai mata sallama suka fita.

Ido tazuba ma kayan tana kallo turo k’ofan da akayine yasa tad’ago kai takallesa murmushin jin dad’i tayi dan rabonta da mijin nata tun d’azu da safe.

Takowa yayi ya iso inda take daga gefenta yazauna nan yakai hannu yad’auki Ameer da yake bacci sannan yace baby ya gidan da hidima?

Kwantar da kanta tayi a kafad’ansa cikin shagwa6a tace shine ko kalek’o kadubamu kabarmu da kewarka.

Murmushi yayi yace sweetmee taya zan shigo bayan gidan cike yake da mutane, kuma ga su dada sun sanya min ido, ke ni nagaji zuwa zakiyi mukoma part d’inmu kawai dan zanfi samun kwanciyar hankali in kina kusa da ni.

Mik’ewa zarah tayi tace ina zuwa nan taje tad’auko hand bag d’inta tafiddo kud’ad’en da tasamu tamik’a masa batare da ya kar6aba yace na menene?

Murmushi tayi tace wanda nasamu ne na suna kad’auka na mallaka maka, sannan ga kayan da muka samu nan ni da Ameer.

Murmushi shima yayi yace my sweet wannan hak’in kine ki aje wajenki kawai nagode, idan ban k’ara mikiba ai bazan kar6aba.

Turo baki tayi tace nidai a’a toh me zanyi dasu ni?
Janyota yayi jikinsa yace bakisan abinda zakiyi da su ba?

‘Daga masa kai tayi alamun eh.
Murmushi yayi yace toh kid’ibi wani abu kiba su baba sauran kuma sai kizuba a account d’inki inyaso daga baya sai kiyi tunanin abinda kikeso ayi miki.

Cike da gamsuwa da maganarsa ta jinjina kai.

Hannunsa yatura cikin rigarta tare da k’ara matsota jikinsa.

Zaro ido zarah tayi taturesa tace ban fa gama wanka ba.
Hmm toh wani abu nace zanyi miki? Na ma lura kamar dad’i kikeji da kikayi nesa da ni, ke nifa so nake kidawo hakanan.

Rungumesa tayi tare da marairaicewa tace wlh a’a kawai dai kunya nakeji kabari ingama wanka sai indawo nima ai nayi missing d’inka.

Janyeta yayi daga jikinsa yace nak’i wayon, in dagaskene kibini mukoma.

Dariya tayi tace wlh baza’ayi wannan abun kunyar da ni ba

Shuru yayi nan yasa hannunsa cikin aljihunsa yafiddo wani d’an k’aramin zoben azurfa mekyau da tsada yasa ma sultan a k’aramin hannunsa.

Zarah ma kallon hannun tayi tana murmushi tace yai kyau.

‘Dago kai yayi yakalleta yace dagaske?

Fari tai masa da ido, Kwantar da sultan yayi sannan shima yakwanta tare da safke ajiyar zuciya.

Kallonsa zarah take cikin tsoro tace please katashi kaje kakwanta dare yayi fa.

Janyota yayi jikinsa yarungume tare da yin light off, k’ara shigewa tayi jikinsa ahaka sukayi bacci.

Washe gari tun da asuba yatashi yakoma 6angarensu.

Zarah turamen tad’auka tad’ibar ma su dada, babu wadda bataba ba k’in kar6a sukayi, sukace a’a kije kid’inka kayanki hak’in kine.

Hajiya tsohuwa tad’ibar mawa, koda taba su sumayya suma k’in kar6a sukayi saida tanuna bataji dad’iba sannan suka kar6a sukayi mata godia.

Koda yaya rauda tazo nan tad’ibar mata nasu da na mama sannan tabata kud’i dayawa tace na su baba ne, nan taware wasu tace natane ita da aisha.
Sosai sukanuna farin cikinsu sukai mata godia.

 

Hata tacigaba da zama wajen sultana sadiya tana samun kulawa sosai daga kowane 6angare ga gyara da takesha wajen hajiya tsohuwa, Ameer yaro me farin jini da shiga rai kulawa yake samu sosai dan baima cika wuni wajen Zarah ba indai ka gansa ankawo mata toh yunwa ce takeji.

Shi kansa suhail saida ummi taimasa dagaske sannan yarage shige ma Zarah.

 

Ranar da tayi arba’in kitso da k’unshi tasha, sannan bayan sallar magrib aka maidata part d’inta, mamakine yakamata ganin ancanza mata kayan d’akinta komai sabo.

Bayan tayi sallar isha’i wanka tayi tashirya cikin wasu sleeping dress masu kyau, feshe jikinta tayi da turaruka masu k’amshi sosai.

Lokacin da tafito har an shirya ma Ameer dan haka tasa wata kuyangarta tad’aukesa suka nufi part d’in yarima.

Gani tayi shima komai ancanza masa sabo room d’insa ya burgeta sosai.
Kar6an Ameer tayi daga wajen kuyangar tasallameta, ahankali tatura k’ofan bedroom d’in tashiga kwance tahangosa saman gado yai pillow da hannuwansa.

Ganinta yasa yatashi zaune tare da mik’a mata hannu cikin sauri ta iso inda yake, mik’a masa Ameer tayi sannan tazauna gefensa, murmushi suka sakar ma juna yace baby dafatan kin dawo lafiya? Tun d’azun nake ta jiranki ammah shuru, hmm Nasan dai ba wani missing d’ina kikayi ba, ni kad’ai nayi missing d’inki.

Rungumesa tayi tace hearty wlh nima nayi missing d’inka tsayawa nayi ind’an kimtsa sannan inzo wajen rabin raina.

Wani irin kallo yai mata mai d’auke da sak’onni wanda yasa saida taji wani yar a jikinta, cikin sauri tasadda kanta k’asa.

Kallon Ameer yayi da yake baccinsa sannan yamik’e yaje yakwantar da shi yadawo nan yakwanta saman gadon.

Biyosa zarah tayi takwanta k’irjinsa tace hearty kayi hak’uri nima kasan kunyarsu ummah ne da nakeji ammah ai da tuni na gudo wajen mijina abun alfaharina dan nayi missing d’insa sosai.

Rungumeta yayi yana shafar bayanta yace baby aike bakya laifi duk abinda princess tayi daidaine dan ta cancanta tunda har tasace zuciyar suhail ai ba abinda yai saura, dole yahak’ura yabita yadda duk takeso.

K’ara shigewa tayi jikinsa tace hearty kaima ka sani da ace ana bud’e zuciya aga sirrin da yake cikinta da tuni na bud’e maka kaga abinda yake cikinta.

Janyo hannunsa tayi tad’aura saman k’irjinta tace duk wani bugu da zuciyata zatayi tare da sonka takeyinsa.

Tsura mata juna ido sukayi suna karance duk wani sirri da yake cikin ransu, zarah ce cikin sauri tazame jikinta tazauna saman gadon tana jin wani iri.
Inda yarima yamaida idanunsa yalumshe yana jin sonta yana fizgarsa, cikin sauri hannunsa har k’yarma yake nan yajanyota yarungume tare da had’e bakinsu waje guda yafara kissing d’inta, cikin dabara yarabata da duk kayan da suke jikinta nan yacigaba da sarrafata son ransa gabad’aya yafita hayyacinsa nan yaita mata sumbatu.

Zarah tausayin mijinta yakamata ganin yadda gabad’aya yarikice mata ita kanta ta san ya yi missing d’inta sosai.

Ta wahala sosai a hannunsa ya sa mata albarka ya fi ak’irga.

Bayan komai ya lafa yarima d’aukanta yayi sukaje sukayi wanka bayan sun gama d’aukota yayi yamaidota saman gado yakwantar da ita sannan shima yakwanta yarungumeta a jikinsa cike da shauk’in sonta, wata irin runguma yayi mata kamar zai maidata cikin ciki har saida zarah tayi ‘yar k’ara sannan yasafsafta rik’on,

Cikin dare koda Ameer yafarka saidai yarima ne yaje yad’aukosa daga cikin gadonsa dakyar yasamu zarah tatashi shima saida yataimaka mata sannan tabashi yasha.

Bayan ya k’oshi shi yaita riritashi inda zarah takoma baccinta har saida sultan yai bacci sannan yarima yakwanta.

Washe gari bayan sunyi breakfast zaune suke suna hira cikin nishad’i, mik’ewa yarima yayi tare da rik’o hannun zarah yace sweetmee taso muje kiga wani abu.

Mik’ewa tayi tabi bayansa koda suka shiga gaban dressing mirror yatsaya da ita sannan yatsaya a bayanta yace tarufe idanunta.

Koda tarufe sarka ce yasaka mata da zobe sannan yadamk’a mata keys a hannunta yace tabud’e.

Wuyanta tabi da kallo tana shafa sark’an da yasaka mata cikin jin dad’i sannan takalli keys d’in da suke hannunta juyowa tayi tafuskancesa tace hearty wannan sark’an kamar ta gold ce yanzu tawa ce?

Murmushi yayi tare da d’aga mata kai yace tabbas ta gold ce ga d’ankunnen nan, wannan keys d’in kuma d’aya na motar da nacanza miki ne d’ayan kuma na gidane na mallaka maki halak malak.

Zarah rasa me zatayi tai shin farin ciki ko me? Fashewa tayi da kuka tare da rungumesa tace nagode, nagode, nagode sosai hearty Allah yak’ara girma da d’aukaka Allah yarabaka da iyayenka lafiya, bansan me zanyi inbiyakaba dan Allah kafad’amin abinda zanyi wanda zaisa ko kad’anne kaji dad’i a ranka.

Rungumeta yayi yace kidaina yi min godia dear dan kin riga kin gama min komai dan akowane lokaci kina faranta min rai, saidai ince Allah yabaki masu yi miki kema, yanzu dai muje inbaki labari medad’i.

Haka yajata suka dawo parlour suka zauna nan sukacigaba da hira.

_______________

Kamar yadda yai ma Dr mu’az alk’awali hakan ko akayi dakansa yarubuta takardar neman masa transfer ya aika da ita, batare da 6ata lokaciba akayi requesting.

Gidan da zasu zauna ma shi yasiya masu nan mu’az yadawo hospital d’in yarima yacigaba da aiki.

Zumunci ake sosai tsakanin jamila da zarah.

A ranar da tayi arba’in ranar yad’auketa yakaita gidansu tayi wuni daga nan yawuce da ita gidan Aisha, saida yajera kwana ukku yana kaita gidajen ‘yan uwa day abokai.

 

 

_*A gurguje please*_

Sumayya da salim sosai kawai ake zubawa daga k’arshe dangin salim sukazo suka neman masa auren Sumayya ba a wani sa bikkin dayawaba, ahaka har akayi bikkin aka kaita agadas, sukaita zuba soyayyarsu me tsafta ga yaransu atare da su, sosai sumayya takejin yaran a ranta dan jinsu take kamar ita tahaifesu.

 

Yaya rauda ma Alh munir zuwa yayi yanemi gafara a bisa abinda ya aikata mata, dakyar yasamu yashawo kanta ta yafe mashi nan yanemi yafiyar iyayenta, daga baya yanuna yanaso ya aureta da ta nuna ba zata aminceba saida yanuna shi dagaske tsakani ga Allah yake sonta sannan ta amince sukayi aure.

 

_*BAYAN SHEKARA UKKU*_

Yarima kud’i sun zauna ya k’ara kyau da cika, sarauta ta k’aru.

Wani d’an yarone kyakkyawa wanda bazai gaza shekaru ukku ba naga ya shigo dagudu cikin maganarsa da bata ida k’warewaba yana kiran daddy daddy daddy dagudu yafad’a jikin suhail da yake kwance saman cinyar zarah
d’aukansa suhail yayi yad’aura saman jikinsa yace little prince wa yata6a min kai?

Cikin gwarancinsa yace daddy wajen meenal zaka kaini.

Shafa kansa yayi yace yanzu ko zan kaika.

Zarah da take saurarensu 6ata fuska tayi tace haba hearty kasa akaisa kawai ko yaje wajen hinde takaishi magana fa nakeson muyi ganin kana waya yasa najira kagama.

‘Dago kai yayi yakalleta yace sorry sweetmee me kikeso kice ina saurarenki, chocolate yamik’a ma Ameer nan yafara sha.
murmushi tayi sannan tace yauwa d’azun naji kana waya ka ce asa sunan su mama cikin wad’anda zasuje aikin hajji ka mance wanchan shekarar duk tare kabiya mana mukaje?

Murmushin shima yayi yace eh ina sane so nake sukoma, kema naso mukoma ammah hakan bazai yuwuba saidai muje umara tunda mefaruwa ta riga da ta faru.

Ido tazuba masa cikin rashin fahimtar maganarsa.

‘Daukan sultan yayi yamik’e yace bari inje inshirya inzo inkaisa gidan shaheed wajen meenal daga chan zan wuce fada tunda gabad’aya yanzu memartaba ya daina shiga sha’anin mulkin ya sakar min komai….yana fad’in haka yawuce yashige bedroom d’insa.

Zarah da kallo tabisa cike da son mijin nata sai kuma chan tamik’e tabisa bedroom d’in ganin sultan tayi zaune saman gadon yarima yana shan chocolate yana game da wayar yarima, inda yarima yake cire kayansa zai shiga wanka, takawa tayi ta isa inda yariman yake nan tashiga tayasa fuskarta d’auke da murmushi, rungumeta yayi jikinsa yace sweetmee wannan murmushin fa?

Kwantar da kanta tayi saman k’irjinshi tace hearty baka bari muka ida magana ba zaka fita.

Shima k’ara rungumeta yayi yace kijirani da nadawo zamuyi magana kinsan a yanzu haka nasan waziri yana chan yana jirana dan shima so yake ya aje mulkin yadamk’a ma shaheed.

Cikin wata irin murya tace toh shikenan hearty muje intayaka yin wankan.

Nan suka shige toilet sukabar Ameer zaune yana shan chocolate yana game.

A tare suka fito kowa d’aure da towel suna dariya nan suka shirya, ido tazuba ma suhail lokacin da yake sa alkyabba, juyowar da zaiyi nan suka had’a ido murmushi yasakar mata yace sweetmee wannan kallo haka ai sai kija infasa fita.

Fari tayi mashi da ido sannan tace duk cikin sonkane hearty, rungumota yayi tare da had’a goshinsu waje guda suna aika ma junansu wani sihirtaccen kallo,
muryar Ameer sukaji ya ce daddy kazo kakaini wajen meenal,

Janye zarah yayi daga jikinsa yarik’e hannun Ameer sannan yace baby bari muje sai mundawo.

Duk’awa tayi tace Ameer so kake daddy yatafi yabar mummynka ko?
Girgiza kai yayi cikin maganarsa yace a’a mum kibari inmuka yi wasa da meenal zanzo inkaiki wajen granny sultana.

Shafa kansa tayi tare da bashi peck a goshi tace toh shikenan my boy ina jiranka.
Shima peck d’in yabata a kumatu sannan tad’ago takalli yarima tace please hearty kar ka dad’e.

Kar kidamu baby zan dawo dawuri, hannu tasa tarufe ma Ameer ido sannan tayi ma yarima kiss a baki.

Murmushi suka sakar ma juna tace adawo lafiya my heartbeat.
Allah yasa baby nan tad’aga masu hannu har suka fita.

Take masa baya guards d’insa sukayi nan yasa Ameer a mota yace akaishi gidan shaheed sannan yawuce yagaishe da su memartaba da yake fama da ciwon k’afa bayan sungaisa yaje yagaishe da su ummi da sultana sadiya daga chan yawuce fada.

 

Wajen k’arfe takwas koda yadawo yatarar da zarah har tayi bacci nan yai shirin baccinsa sannan yahau gadon kallon zarah yayi da tabaje tana ta kwasar bacci ahankali yad’age rigarta yakai hannu yana shafa cikinta daga k’arshe yad’aura kansa saman cikin.

Jin abu samanta yasa tafarka daga baccin da bata dad’e da fara yinsaba, kallon yarima tayi tashafa kansa sannan tace hearty me kakeyi nan?

Murmushi yayi batare da ya d’ago kansaba yace ina gaisawa da baby na ne.

Zaro ido tayi tace wane irin baby?
Sai a lokacin yad’ago yakalleta yace Wanda yake manne a cikinki.
Karufan asiri ni banda komai.

Murmushi yayi yace taya kike tunani zan k’ara bari kisamu ciki batare da nagane ba, wanchan karen ma dande ban maida kaiba ammah ai naga alamomi kawai jin kai ne yahana intabbatar da hakan.

Ajiyar zuciya tasafke tace toh taya akayi kagane ina da ciki bayan ni kaina bansan da shi ba.

Rungumota yayi jikinsa yace baby ko kin mance ni doctor ne? Insha Allahu nan da wata shidda zaki haifo min wani babyn.

Zaro ido tayi tace nashiga ukku yanzu har ina da ciki wata ukku batare da na saniba?

Jan hancinta yayi yace toh kidai shirya ni d’in kinsan ba ma wasa bane.

Marairaicewa tayi tace toh ammah duka fa Ameer shekararsa ukku.

Toh ai ya ma kwana biyu ai na gama wasa duk bayan shekara biyu zaki dinga haihuwa Insha Allahu k’ara ma kishirya dan mijin nan naki yana da son yara, wlh zarah indai kece bazan damuba dan inaso inga kin haifar min yara kodan susamu irin tarbiyanki, dan halayyarki ce ta kirki tacanza min rayuwa, tabbas na yarda kud’i basu bane rayuwa, rayuwa medad’i itace aginata akan ilimi na addinin musulunci, duk kud’in mutum indai baida ilimi toh bai cika mutum ba yana da tauwaya a rayuwarsa, a kodayaushe ina k’ara gode ma Allah da yamallaka min ke a matsin matata tagari wlh wani lokacin har ji nake kamar ba zan iya rayuwaba in babu ke, zarah kece komai nawa, ina fata zaki cigaba da haifamin yara masu irin tarbiya da hak’urinki wad’anda duniya zatayi alfahari da su.

Rungumesa tayi kamar zata maidasa cikin ciki hawaye suna fita daga idanunta tace nagode sosai mijina Allah yabarmu tare, duk abinda kakeso toh nima shi nakeso dan ka riga ka zama ni nima nazama kai fatana Allah yabarmu tare har k’arshen rayuwarmu, ka gama min komai a rayuwata kaine silar dawowar duk wani farin ciki nawa, a kodayaushe bakina cikin yi maka addu’a nake dan addu’a ce kawai zanyi maka inbiyaka abubuwan da kakemin, kaduba kaga gidan da su mama suke zaune yanzu babba ne sosai kuma kai kamallaka masu, sannan duk wata sai ansafke masu kayan abinci, hatta su yaya rauda baka barsuba kullum cikin kyautata masu kake sannan…….cikin sauri yarima yasa hannu yarufe mata baki yace baby ya isa haka duk abinda nayi ma su abba cancantace tasa haka ko da ace bana aurenki zan iya yi masu fiye da haka, kukan ya isa haka dear indai ba so kike nima inyiba, cikin sauri tagirgiza kai tace a’a kar kayi,,,harshensa yasa yashiga lashe mata hawayen fuskarta bayan ya gama nan yashiga yi mata rad’a a kunne chan sai suka saka dariya gabad’ayansu, turesa zarah tashiga yi tace nak’i wayon naka ni kak’yaleni.

Rik’o hannunta yayi yace please dear kitaimaka min.
Tallabo kansa tayi tatura bakinta cikin nasa nan suka shiga kissing d’in juna kowa yana nuna ma d’an uwansa k’warewarsa cikin salon so daga k’arshe yarima suhail yajanyo blanket yarufesu.

 

_Laifin dad’i k’arewa_

_*Alhamdulillah* anan muka kawo k’arshen wannan novel mesuna *YARIMA SUHAIL* abinda muka fad’a daidai Allah yabamu ladar kurakuren da suke ciki Allah yayafe mana_

_Fatan alkhairi agareku dukkan masoyana naji dad’i kuma nagode ma Allah akan yadda wannan novel d’in yasamu kar6uwa sosai a wajenku_

_Duk wani wanda nata6a 6atamawa ina fata zai yafemin domin duk d’an Adam ajizine tsakanin harshe da hak’ori ma ana sa6awa balle tsakanin mutane, Allah yayafe mana gabad’ayanmu al’ummar musulmai_

_Daga k’arshe ina taya dukkan d’aukacin al’ummar musulmi murna akan wannan wata mai albarka da zamu shiga, ina fata Allah yabamu ikon shiga watan ramadan lafiya sannan yabamu ikon azumtarsa, ya ubangiji kasa muna daga cikin bayinka wad’anda zaka ‘yantar a cikin wannan watan me albarka_

_Sis Nerja’art takuce a duk inda kuka kasance masoya,_

 

_Comment_
*Nd*
_Share_

 

 

_Sis Nerja’art✍_

Back to top button