Hausa NovelsYarima Suhail Hausa Novel

Yarima Suhail 38

Sponsored Links

PAGE* 3⃣8⃣

zinat dariya tashiga yi har sumayya tafara k’ulewa tace dallah malama idan kinsan dariya zakiyimin ai sai inkashe wayana daga na fad’a miki damuwata sai kitsareni da dariya.

zinat tsagaida dariyar tayi tace sorry my dear toh ai kece da laifi

Related Articles

sumayya tace ban fahimtaba me kike nufi?

zinat tace kefa ina fad’a miki kiyi baya-baya da mijinki domin su maza da sunga ana shige musu sai kiga sun 6ullo da sabon wulak’anci musamman ma wannan mijin naki, ammah da sunga anyi baya da su toh nan ne zakiga yadda zasu tattaleki.

hmm dear kenan kin mance har da hakan tajamin yarima yak’ara aure?

zinat tace ba dai hakan ba ko kin mance lokacin da kikayi baya da shi yadda yake zuwa yana tattalinki?
Dogon numfashi sumayya taja tace hakane yanzu nafahimta, shikenan dear koma dai mikenan sai munyi waya.

Ohk baby ammah please kikular min da kanki,
Dariya sumayya tayi tace ai kullum ina kular miki da kaina.
Aha dear fiye fa da yadda zaki kularma yarima.
Sumayya tace kema kinsan hakan, dariya sukayi sannan daga baya sukayi sallama.

Bayan sun gama wayar sumayya zagaye d’akin tashiga yi tana tunanin mafita dan ita sam shawarar da zinat tabata bata gansu da ita ba; sai chan daga baya tayi dariya tace yarinya da ni kike ja ayanzu zaki gane ainahin kalata.

Har wajen k’arfe goma Zarah shuru bataje part d’in yarima ba, kad’an kad’an ya duba lokaci duk ji yake ba dad’i rashin zuwanta har lokacin, tsintar kansa yayi da cewa kodai fushi take yi? ahankali yaja d’an guntun tsaki.

 

A chan 6angaren zarah ko da tagama shirinta kwanciyarta tayi part d’inta dan har a lokacin batada walwala duk yadda taso tayi bacci kasawa tayi juyi kawai take a saman gadon tana jin wani irin k’unci a ranta, ahaka har bacci yad’auketa.

Yarima ma haka yai ta juyi yana mamakin yadda duk yakasa cire damuwa akan rashin zuwan zarah cikin ransa yace ko dai fushi take da ni? Dasauri yabud’e idanuwansa tare da mik’ewa zaune yadafe kansa ahankali yace me hakan yake nufi da ni? Meyasa nadamu da wannan yarinyar? Chan 6angaren zuciyansa yace masa toh ko sonta kake?

Dasauri yarima yace No! It can’t be possible wlh! Mtsw wani irin haushin kansa ne yakamasa chan sai yaja dogon numfashi yace zan iya yarda dai nadamu da itane, to saboda me? Yatambayi kansa,
saboda tana nunamin kulawa,;,yaba kansa amsa,, chan kuma sai yayi murmushi tare da komawa yakwanta yamaida idanuwansa yalumshe yanajin wani iri a ransa, saida yakai kusan 1am sannan yasamu bacci yad’aukesa.

 

Dasafe ma haka yafita ammah zarah bata lek’osaba, ko da yaje hospital daurewa kawai yayi yaduba patients d’insa ammah duk motsi kad’an sai zarah ta fad’o masa a rai saidai kad’an-kad’an yayi ta jan tsaki.

 

Zarah ko breakfast bata samu tayiba dan jinta take wani iri sai wajen k’arfe ukku dataga yunwa tacita sosai ta fara gani bibiyu sannan tasa aka dafa mata indomie tad’anci kad’an,

Tun daga ranar bata k’ara shiga sabgar yarima ba haka take tursasa ma zuciyarta dan ganin ta danne sonsa da rashin ganinsa.

 

Ahaka kwana yadawo hannun sumayya sukasha kwanansu biyu ammah yarima har lokacin shi kansa ya rasa gane abinda yake damunsa, gashi yanason ko da sau d’ayane yasa Zarah a idonsa ammah girman kansa ya hana yaje inda take duk yadda tunaninta yafad’o masa a rai cikin sauri yake janyesa, dan ma yanzu sauk’in ba cika zama yayiba suna ta shirye-shiryen bikki.

 

Dangin ummi na masarautar agadaz sunzo da dama 6angare d’aya aka fitar musu daga cikin masarautar, ita kanta zarah da tagansu saida ta jinjina kai cikin ranta tace dole yarima da su rahma suyi kyau.

d’iyar yayar ummi ce safiya talik’e ma zarah saboda kusan kansu d’aya kullum tana 6angaren zarah ita take d’ebe ma zarah kewa kasancewar safiya akwai surutu, ahaka ranar girkin zarah yawuce ammah bata lek’a part d’in yarima ba.
Ita kanta sumayya tun lokacin da sukayi kaca-kaca da zarah rabon da zarah tasaka ta a idonta.

 

Ranar laraba aka gudanar da walimar bikkin rahma a cikin masarautar aka yanki fili akayi inda aka gayyato manyan malamai suka gabatar da wa’azi mai ratsa zuciya a chan tsakiyar fili naga an ajema amarya kujerar alfarma ta zauna alkyabba ce take sanye da ita tayi kyau sosai, daga 6angare guda kuma dangin amarya ne, sai d’ayan gefen dangin ango,
chan gefe nahango zarah da safiya zaune kusa da Aunty husna sunyi zugum suna sauraren wa’azi, nidai har nagama zagayena banga sumayya ba, bayan ank’are mutane sunci sunsha sannan aka watse.

 

ranar alhamis safiya part d’in zarah takwana tun da safe da suka tashi zarah tahad’a musu breakfast sukayi, nan suka zauna sukaita fira,

Bayan sallar la’asar suka shirya cikin anko d’insu na lace sunyi kyau sosai, musamman zarah d’inkin nata ya kar6eta, tana zaune gaban dressing mirror safiya tashigo, tsaye tayi tana kallon zarah, juyowa zarah tayi takalleta tasakar mata murmushi tace ya dai safiya?

Murmushi safiya tayi tace gaskiya kinyi kyau sosai Mrs prince (kasancewar sunan da take kiran zarah da shi kenan)
Kai safiya banason tsokana.

Wlh ba tsokana bane kema kinsan kina da kyau sosai,

Hmm safiya kenan ammah ai kinfini.

Safiya zaro ido tayi tace waceni? Wlh ban kamo ko k’afarkiba.

Harararta zarah tayi tace kedai kika sani da tsokanarki.

Hmm gimbiya kenan kema ai kinsan gaskiyane, yanzu dai kigama shirin gashi chan anfara d’aukar mutane ana tafiya da su wajen kamun, ko cikin motarki zamuje?

Zarah shuru tayi nad’an lokaci sannan tace anya zan yi driving d’innan? Kodai insa akaimu?

Haba kawai kijamu muje, ni nafiso muje a motarki.

Toh ai bansan wajen da za’ayiba.

Kar kidamu ni nasani sai muje.

Harararta zarah tayi tace keda ba garin kikeba ina kikasan wajen.

Dariya safiya tayi tace Allah dagaske, jiya munje mungano wajen, yanzu dai kiyi sauri kigama nasan anfara yanzu.

Zarah saka sark’a take tace ke banfa tambayi yarima ba.

Chab har ma sai kin tambayesa? Kizo kawai muje ai yasan hidima ake.

Mik’ewa zarah tayi tad’auki veil d’inta tayafa sannan tace bari inzo, bata jira Jin abinda safiya zatace ba tafita.

Ko da ta’isa part d’in yarima itama saida taji wani iri dan rabonta da d’akinsa kusan 5 day’s kenan, ganin baya parlour yasa tawuce bedroom nan ma baya nan.

Fitowa tayi takoma part d’inta wayarta tad’auka takirasa har tatsinke bai d’agaba, mamakine yakama zarah nan tak’ara dialing d’in number d’insa sai da takusan tsinkewa sannan yarima yad’aga lokacin yana gidansu shaheed.

Zarah naji ya d’auka bata bari yayi maganaba tace ina wuni?
Daga chan 6angaren yarima saida yalumshe idonsa jin muryar zarah, sai da yayi kusan 3 minutes sannan yace ina jinki.

Zarah ma wani sanyi taji aranta saida tazauna saman gado sannan tace am dan Allah inaso zanje wajen kamu,

Sai kindawo, yarima yafad’a tare da kashe wayarsa.

Zarah murmushi tayi tare da mik’ewa tsaye, had’a ido sukayi da safiya da take tsaye itama tana murmushi, dariya zarah tayi tace kekuma fa?

Itama safiya dariya tayi tace ina kallon yadda ake waya da habiby, harararta zarah tayi tace nidai wuce muje sarkin ‘yan sa ido,
Dariya safiya tayi tace gaskiya zanso inga soyayyarki da prince, na sansa da jin kai ku ma matansa yana yi muku? fad’amin sirrin.

Zarah d’aukar hand bag d’inta tayi da key d’in mota tawuce gaba, bayanta safiya tabi tana mata dariya har suka fita sukaje wajen motar zarah,

Zarah bud’e k’ofar tayi tashiga tazauna saida tayi addu’a sannan tatada motar abun yabata mamaki ganin yadda tatada motar batare da tsoron komai ba saboda wannan ne karo nafarko da tafita da mota dan tun lokacin da aka koya mata rabon da tashigeta, ahankali tajasu suna tafiya suna hira ammah duk hankalinta yana ga driving d’in da take ahaka har suka isa babban hall d’in da aka tanada.

Motocine duk inda kaduba gefe guda tasamu tayi parking sannan suka fito suka shiga daga chan gefe suka samu waje suka zauna daidai lokacin amarya da ango suka iso sunyi gwanin kyau, nan abokan amarya sukaje suka tarbosu aka kaisu har wajen da aka tanadar ma ango da amarya,

Daga gefen amarya sumayya ce zaune tayi kyau sosai itama sai yatsina take tana nuna isa, dan ma bawanda yadamu kowa hidimar gabansa yake,

Shaheed ne yaketa baza ido ammah baiga yarima ba ahankali yaduk’o yace ma rahma kinga yarima baizo ba ko? Bayan munyi da shi shiryawa zaije gida yayi.

Murmushi rahma tayi tace indai Bro ne zai aika wlh,
hmm barni da shi, wayarsa yad’auko yashiga kiran wayar yarima,
Yarima da yake shirin fitowa daga part d’insa ganin kiran Shaheed yasa yayi murmushi sannan yawuce yafita,

 

Lokacin da ya isa hall d’in abokan amaryane a fili suna ta kwasar rawansu shigowar yarima da abokinsa Dr khalil ne yasa gaba d’ayansu suka zuba masa ido, sanye yake cikin boyel milk colour wanda yasha d’inkin zamani ya yi masa kyau sosai kansa babu hula gashin kansa yasha gyara, nan MC yafara masa kirari
Daga chan gaba suka samu table d’in da ba mutane suka zauna, nan maza sukaita zuwa wajensa fuskar yarima a sake suke gaisawa.

 

Shaheed ne yayi ma MC magana nan mc yazo inda yarima yake cike da girmamawa yagaishesa sannan yace ranka yadad’e ga wajen da aka tanadar maka chan.

Yarima kallon saman high table yayi sannan yace no nan ma ya yi min, MC har yabud’e baki zaiyi magana nan yarima yad’aga masa hannu cikin sauri yawuce yabar wajen.

A chan nahango sumayya tunda yarima yashigo tafara washe baki dan duk a tunaninta wajenta yarima zaizo yazauna sai taga akasin haka ga ‘yan mata sai wucewa suke tagaban su yarima ko Allah yasa sutaya, sumayya da take kallon matan murmushin mugunta tayi tace yau duk wacce tanemi tataya mijina za’ayi bura’uba wajen nan.

A chan 6angaren zarah ma safiya hira take yi mata ammah hankalinta gaba d’aya yana wajen yarima tun lokacin da yashigo, ganin matan da suke bi tagabansa yasa tacika fam ji take kamar taje tashak’esu.

Shidai yarima tunda yazauna bayan sun gama gaisawa da mutane dannar wayarsa yake baisan wainar da ake toyawaba.

nan aka fara kiran babban abokin ango yashiga fili ammah yarima ko motsawa baiyiba ganin haka yasa shaheed yace ma MC akira muhammad abokinsa dan yasan babu wanda ya isa yasa yarima yin abunda baisa kansaba, a k’arshe dai saidai muhammad yakoma madadin yarima.

Bayan yashiga yayi rawa sannan aka ce kowa yafita yanzu filin yakoma na amarya da ango.

Shaheed rik’o hannun rahma yayi suka tashi suka safko daga high table suka shiga tsakiyar fili yana rik’e da ita suke d’an takawa ahankali, sumayya ce tamik’e taje tafara watsa musu kud’i nan abokansu ma suka take mata baya aka dinga watsi da kud’i.

Dr khalil yana murmushi yace ranka yadad’e kataso muje muyi ma aboki da k’anwa lik’i.
Ta6e baki yarima yayi yace ba zan iya shiga wajen chan ba saidai kai idan zakayi.

Haba yarima ammah dai da baka kyautaba, yarima bandir biyu na ‘yan 1000 yafiddo ya aje gaban dr khalil yace idan kai zakaje sai kawakilceni.

Zaro ido Dr khalil yayi yace ni kuma? A’a kai dai yafi dacewa kaje da kanta.

Banza yarima yayi masa yacigaba da dannar wayarsa,
Ganin haka yasa Dr khalil yamik’e yatafi dan yasan tunda dai har yarima yafurta a’a toh bawanda zaisashi yace eh, nan yashiga yi musu lik’i yace ma shaheed, yarima ne yawakiltashi yayi masu lik’e madadinsa.

Rahma da shaheed kallon juna sukayi sukai murmushi shaheed yace lallai yarima halinsa sai shi.

Safiya kallon zarah tayi tace Mrs prince muje muyi ma adda rahma lik’i,

A’a Safiya kije nidai ina nan,
Rik’o hannunta tayi tace haba Mrs prince dan Allah kitaso muje kinga ba dad’i.
Zarah ba dan tasoba tatashi suna rik’e da hannunsu suka nufi filin.

Kud’i suka ciro daga cikin jakunansu suka fara yi ma amarya da ango lik’e, zarah ji tayi ta bayanta ana zubo mata kud’i itama, dasauri tawaiwaya wani guy ne tagani fuskarsa d’auke da murmushi,

Harararsa zarah tayi tace dallah malam menene haka?
Fuskarsa d’auke da murmushi yace duk cikin sonkine baby kiban izini ingabatar miki da kaina,

Zarah Zaro ido tayi dasauri takai kallonta ga yarima da shima idanuwansa suna wajensu, ai yarima tunda yaga mutumin yana ma zarah lik’i wani irin abune yaji ya tokare masa zuciya wata irin harara yashiga wurga ma zarah,

Zarah saida ‘yan cikinta suka kad’a ganin hararar da yarima yayi mata, cikin sauri tafito daga wajen, mutumin ma binta yayi yana ta mata magana ita kanta batama san me yake cemata ba har takoma mazauninta tazauna.

Shima zama yayi gefenta yace haba baby wai menene haka wulak’ancifa baida dad’i daga na ce ina sonki sai ki6ata rai?

Zarah cike da tashin hankali tace dan girman Allah kakyaleni ni fa matar aurece,
Murmushi saurayin yayi yace nima mijin aurene.

Zarah kallon yarima tayi da yake kallonsu idanuwansa sun kad’a sunyi jawur, shima mutumin kallon inda take kallo yayi dan yaga duk ta ida daburcemasa ganin yarima yasa yayi murmushi yace baby kinsan prince ne?

 

Zarah mik’ewa tayi cikin d’aga murya tace malam na ce kafita harkata ni matar aurece!
Tana fad’in haka tawuce tanufi inda yarima yake zaune ya cika fam.

Kujerar da take kusa da shi taja tazauna rau-rau tayi da ido kamar zatayi kuka tace wlh bani nace yabi niba kuma nafad’a masa ni matar aurece.

Yarima ta6e baki yayi sannan yace wani abu kikaji na ce?
Girgiza kai zarah tayi.

Cikin nuna rashin damuwa yarima yacigaba da dannar wayarsa yana d’an murmushi, nan ko zuciyansa cike take da bak’in ciki,

Daidai lokacin Dr khalil yadawo yaja kujera yazauna, fuskarsa d’auke da murmushi yace amaryarmu watau kinzo kin tsare mijinki dan kar wata tayi miki k’wace ko?

Murmushi zarah tayi sannan tace ina wuni?

Lafiya lou amarya ai da nahangoki nad’auka irin ‘yan matan nan ne suka samu kar6uwa wajen yarima ashe amarya ce tazo takasa tatsare abinta, hakan da kikayi yayi kyau nabaki goyon baya dan na lura da ‘yan matan amarya sai rawar kai suke akansa sunaso suyi masa magana ammah ya yi mu k’warjini.

Murmushi kawai zarah tayi.

Yarima kallon Dr khalil yayi fuskarsa d’auke da murmushi yace Dr gaskiya ni nagaji kazo kawai muwuce.

Haba Dr tun yanzu zamu tafi?
Hmm bakaga time d’in sallah ya kusaba? Yarima na fad’in haka yamik’e tare da cewa idan ba zaka tafiba toh ni na tafi dan ko 1 minute ba zan k’araba anan, kallon zarah yayi yace kitashi mutafi.

Zarah ma kallonsa tayi tace da mota nazo, yarima mik’ama Dr khalil key d’in motarsa yayi yace gashi katafo da ita,

Kar6a Dr khalil yayi tare da mik’ewa yace nima ai bazan zaunaba.
Yarima kallon zarah yayi yace muje.

Zarah mik’ewa tayi tabi bayansa, wajen motarta suka nufa nan tamik’a masa key d’in.

Tunda suka fara tafiya kowa shuru yayi, yarima gudu kawai yake da motar, ahankali zarah tajuyo takallesa gani tayi ya wani had’e rai babu alamun fara’a a fuskarsa, janye idonta tayi daga kallonsa cikin ranta tace kai dai kasani.

Suna isa gida yana yin parking key d’in motar ya aje mata sannan yabud’e yafita batare da yayi mata magana ba, itama zarah bud’ewa tayi tafita tabi bayansa tana shiga direct part d’inta tawuce.

Saman cushin tazauna tare da jan numfashi tace Allah ya taimakeni da mutumin chan ya ja min bala’i wajen yarima, chan kuma cikin zuciyanta tace bayan basonki yakeba bai damu da ke ba to akan me zaiyi kishinki? Jinjina kai tayi k’wallah duk ta cika mata ido tace hakane kuma, wayarta tad’auka takira safiya nan tashaida mata da ta tafi gida.

Yarima ma zama yayi saman cushin d’in parlournsa yadafe kai hango zarah da wannan mutumin abokin shaheed yayi sai murmushi yake ma zarah, da k’arfi zuciyansa tabuga jingine kansa yayi tare da lumshe idonsa dan shima ya san yayi namijin k’ok’ari da bai d’au matakiba akansa kuma bayason zarah tad’auka ko ya fara damuwa da ita ne, bugu da k’ari a gaban idonsa aka aiwatar da komai babu ta yarda za’ayi yazargeta.
Ahankali yaja tsaki cikin ransa yace toh wai ma akan me zan damu? Gefe guda na zuciyansa yace dole kadamu tunda akwai aurenka abisa kanta.
Kiran sallar magrib ne yasa yamik’e yanufi toilet dan yad’auro alwallah.

wajen k’arfe tara zarah na shirin kwanciya safiya tashigo, kallonta zarah tayi tace kar dai kicemin yanzu kika dawo?
No tun d’azun muka dawo ina cikin gida wajensu mamina, kinsan wani abu?
Girgiza kai zarah tayi.
Wani guy ne yatambayeni wai dagaske kina da aure, inkuma baki da aure toh please inbasa number d’inki, bansan lokacin da nazaro idoba nace karufa min asiri kar kaja prince yasa arufeni, ai matarsa ce.

Shima guy d’in bakiga yadda yarikiceba wai wlh bai d’auka matar aure bace kuma matar prince ya ce dan Allah inbaki hak’uri wlh da ya sani da bazai miki maganaba, kuma ya ce zai samu prince yabasa hak’uri nace ai da kuwa hakan ya fi.

Murmushi zarah tayi tare da kwanciya tamaida idanuwanta tarufe cike da kewar yarima ammah ko bakomai ta d’anji sanyi a ranta da tasakashi a idonta, nan itama rahma takwanta.

Gimbiya sumayya kallon yarima tayi da yake kwance ita kuma tana gefensa tace yarima Allah ya taimaki ‘yan matan wajen nan da basuzo wajenkaba dan na lura da kallon da suka dinga yi maka wlh da sunzo da sai munyi bala’i.
Shine katafi ban saniba saidai nawaiga naga bakanan, kuma fa ko lik’i baka shigo kayi masuba.

Murmushi kawai yarima yayi tare da rungumota jikinsa, dasauri sumayya takallesa tace a gajiye fa nake yau, yarima kallonta yayi sannan yamaida idanuwansa yalumshe ganin haka yasa sumayya tagyara kwanciyarta ahaka bacci yayi awon gaba da su.

Ranar juma’a safiya jan zarah tayi sukaje part d’in ummi ammah zarah kasa sakin jiki tayi cikin dangin yarima daga uhm sai uhm-uhm daga k’arshema tattarawa tayi tadawo turakarsu.

Da dare duk inda zaka nufa a cikin masarautar shirin tafiya dinner akeyi, mutane duk sun saka material sunyi kyau.

sumayya tare da rahma sukaje shago akayi musu shiri suka fito gwanin kyau musamman ma amarya rahma.

Wajen 8:30pm zarah tagama shirinta cikin anko d’inta tufke gashin kanta tayi sannan tasaka head d’inta tayi gwanin kyau kallabin tayafa a kafad’arta sannan tazura takalminta tad’auki hand bag d’inta tana fitowa sukayi kici6is da safiya da wata ‘yar uwarta tsaye sukayi suna kallonta itama kallonsu tayi fuskarta d’auke da murmushi tace masha Allah ‘yan mata kunyi kyau sosai.
Haba Mrs yarima wlh bakiga yadda Kikayi kyau ba kamar kece amaryar.
Uhm zaki dai fara tsokanata ne da kika saba.
Safiya kallon ‘yar uwartata tayi tace dan Allah iman ya kika ga matar prince?
Murmushi iman tayi tace wlh tayi kyau sosai ji nake daman ma nice ita.

Ku dai kukasani da tsokanarku, tana fad’in haka tawuce tanufi part d’in yarima tabarsu nan suna ta binta da kallo.

Zarah tana shiga lokacin yarima yana zaune saman 3 seater yana kallo, ahankali tayi sallama, juyowa yarima yayi yakalleta saida gabansa yafad’i ganin wani irin kyau da tayi, Zarah ma tsura masa ido tayi sanye yake cikin dakakkiyar shaddarsa coffee colour ya yi mata wani irin kyau, sun dad’e suna kallon juna sannan yarima yajanye idonsa yamaida ga TV, zarah ajiyar zuciya tasafke sannan tace barka da hutawa.
yauwa yarima yace batare da ya kalletaba.
Ahankali tace dan Allah zan tafi wajen dinner d’in.
Juyowa yarima yayi yakalleta sannan yace bazaki jeba.
Marairaicewa zarah tayi tace dan Allah kabarni
Wani irin kallo yarima yayi mata sannan yace kije kihad’o min coffee.
Zarah aje jakkarta tayi tafita tana turo baki ko da takoma part d’inta kallon su safiya tayi da suke jiranta tace bari tayi sauri tahad’a ma yarima coffee.
Sukace toh, nan tayi sauri tashiga kitchen tad’aura.

Bayan tagama d’auka tayi tanufi part d’insa tana shiga mik’a masa tayi, sannan tace dan Allah toh intafi?
Yarima kallonta yayi tana ta turo baki sannan yace na fad’a miki bazakijeba, juyawa zarah tayi zatabar d’akin cike da jin haushi.
batare da ya kalletaba yace kisamu waje kizauna.
Kujerar da take opposite d’insa tazauna ta cika fam,
A hankali yakai cup d’in bakinsa yana sha.
Wayartace tafara ringing saida takalli yarima da yake kallonta sannan tayi picking tace safiya kutafi kawai bazan samu damar zuwaba, tana fad’in haka takashe wayarta,
Sun dad’e a zaune zarah duk ta k’ule ji take daman yabarta tatafi part d’inta ko baccine tayi.

Har wajen goma saura suna Zaune a haka, Kiran wayan shaheed ne yashigo a wayarsa murmushi yayi sannan yayi picking yace ya dai ango?

A chan 6angaren shaheed cike da k’ulewa yace dallah malam katafo kawani bar mutane suna ta jiranka.
Ta6e baki yarima yayi yace ai bance ajiraniba.
Kar dai kacemin bazaka zo ba? Cewar shaheed
Yarima yace ni ban fad’aba malam.
Toh mujiraka kenan?.
Uhm zan gani, yana fad’in haka yakashe wayarsa gaba d’aya gudun kar ak’ara kiransa.
Zarah da tunda yafara wayar kafesa tayi da ido har yagama ahankali tace toh saidai muzauna gidan tare.

Kallonta yarima yayi yace me kikace?
Dasauri tagirgiza kai tace ba magana nayiba.
Murmushi yarima yayi sannan yacigaba da shan coffee d’insa.

Zarah duba time tayi ganin har 11 ta kusa sannan tamaida kallonta ga yarima tace bacci nake ji inje inkwanta?
Yarima batare da ya kalletaba yace zaki iya shiga kikwanta.
Zarah turo baki tayi tace a nan?
Yarima komawa yayi yakwanta a saman kujerar tare da d’aukar remote yacanza channel.

 

 

_Comments_
*nd*
_Share_

 

 

 

_Sis Nerja’art✍_

_*YARIMA SUHAIL*_

 

_*Written By~Sis Nerja’art*_

 

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….*✔

_Wannan page d’in mallakinkine *Ummu Rahma* marubuciyar *’DAN GARGAJIYA* nagode sosai da kulawarki agareni Allah yabarmu tare_

 

Back to top button