Hausa NovelsYarima Suhail Hausa Novel

Yarima Suhail 21

Sponsored Links

PAGE* 2⃣1⃣

Da daddare sultana bilkisu takira zarah bayan sun gaisa nan take fad’amata zuwan da yarima zaiyi gobe,

zarah saida gabanta yafad’i ammah tadake tace ummi Allah yakaimu.

Related Articles

A ranar kasa baccin kirki tayi, tunani da fargaba duk suka cikata.

 

wanshe kare shaheed shiryawa yayi yanufi gidan yarima, lokacin da yaje part d’in yarima nan guards d’insa suka gaishesa sannan d’aya yashiga yasanar da yarima zuwan shahid nan yarima yabada izini abarsa yashigo.

ko da shahid yashiga parlourn tsaye yayi bakin k’ofa yana kallon yarima da yake kwance saman 3 seater cike da mamaki yace haba yarima kaifa kacemin after la’asar zamuje ammah jibeka baka shiryaba.

yarima batare da ya d’ago kai ya kallesaba cike da rashin damuwa yace ina kenan?

cike da jin haushi shshid yace au kana nufin ka mance inda zamuje? yanzu saboda Allah amaryartaka ce kamance da ita ko me?

ta6e baki yarima yayi saboda shi shaf ya ma mance da maganar zuwan da zasuyi wajen zarah.

shahid jinjina kai yayi yace lallai yarima ka cika d’an wulak’anci.

harara yarima yawurga masa yace toh ina ruwanka ai sai kazauna kajirani inshirya,

dariya shahid yayi yace ba fa ruwana ranka yadad’e yanzu dai kaje kashirya kafito muje dan Allah kar kadad’e.

ko kallonsa yarima baiyiba yashige bedroom d’insa.

tashi shahid yayi yakunna kallo sannan yabud’e freezer yad’auko maltina yazauna yana sha yace kafin wannan d’an rainin hankalin yafito.

bayan minti ashirin yarima suhail ne yafito sanye cikin dakakkiyar shaddarsa blue wadda tasha aiki, kansa sanye da hula kalar shaddar, kamshin turarensane ya ankarar da shahid daga kallon da yake dasauri yajuya yazuba masa ido yana kallonsa yace kai yarima wannan kyau haka saikace yau zaka angwance? gaskiya kayi kyau sosai natabbata ita kanta amaryar bazata ganekaba kar fa karikita d’iyar mutane,

yarima suhail wayoyinsa yad’auka batare da yace ma shahid komai ba yawuce zai fita,

dasauri shahid yamik’e yabi bayansa, ko da suka fita nan guards d’insa suka take masu baya, wajen da aka tanadar musu motocin da zasu fita da su suka nufa tun kan su ida isa naga anbud’e musu bayan wata dank’areriyar mota bak’a da take tsakiyan sauran motocin, saida suka shiga aka maida aka rufe sannan cikin sauri guards d’in sukaje suka shiga sauran motocin.

 

A chan 6angaren zarah Aunty kubra sata tayi tashirya, sosai tayi kwalliya had’ewa tayi cikin material Black colour mai ratsin marron nan tamurza d”aurin kallabinta tare da yafa veil marron, takalmanta da jakkarta ma duk maroon colour ne.

ba ita kantaba hatta su Aunty kubra sun yaba ma kyaun da zarah tayi, 6arin turaruka akayi mata sosai a jikinta.

 

ko da su yarima suka iso mai gadi hangame musu gate yayi motocinsu a jere suka shigo; dasauri guards d’insa suka fito daga cikin motocin da suke sukazo suka bud’ema su yarima murfin mota, ahankali yasafko k’afarsa sannan daga baya ya ida fitowa daga cikin motar, cike da tafiyarsa ta k’asaita yake takonsa shaheed yana gefensa nan wasu daga cikin guards d’insa suka take masu baya har part d’in mummy sa’adatu, daga wajen parlour guards d’in suka tsaya inda yarima suhail da shaheed suka shiga ciki da sallamarsu lokacin mummy sa’adatu tana shirin tafito taje ta tarosu,

ganinsu yasa tayi murmushi tare da cewa marabanku da zuwa, yarima murmushi kawai yayi shaheed ne yace yauwa mummy sa’adatu shidai shaheed kansa a d’aure yake har suka zauna domin yayi tunanin d’iyar mummy sa’adatu ce yarima zai aura, shidai yarima daman ummi ta fad’amasa zarah tana nan gidan hajiya sa’adatu kuma ta ce yabiya gidansu zarah yagaishe da iyayenta saisa baikawo komai a ransaba.

bayan sun zauna nan suka gaisheta cike da girmamawa, ta amsa cike da kulawa tare da tambayarsu mutanen gida sukace kowa yana lafiya, nan da nan aka cika musu gabansu da kayan tand’e-tand’e da shaye-shaye, mik’ewa hajiya sa’adatu tayi tare da cewa son kugama cin abinci sai inkira muku ita.

shaheed ne yatsiya musu ruwan inibi yamik’a ma yarima sannan yace mummy wlh a k’oshe muke abincin bazai shigaba.

murmushi mummy sa’adatu tayi tace ku daman ina rik’e da ku bakwacin abincin ginnan, kokuma ma ai bazuwa kukeba duka wannan zuwanku na ukkune shima duk ta dalilin umminku, bakwason zumunci ko?

yarima suhail murmushi yayi yace insha Allahu zamu gyara, tace kullum wak’ar kenan bari inje inkira muku ita toh tunda kunk’i cin abinci.

ko da hajiya sa’adatu tafita shaheed apple yad’auka yana ci tare da kallon yarima da yake rik’e da cup d’in ruwan inibi yace kasha mana,

yarima batare da yayi maganaba ya aje cup d’in tare da jawo wayarsa yana operated d’inta, shaheed murmushi yayi tare da ci gaba da cin Apple d’insa.

Hajiya sa’adatu lokacin da tashiga part d’in da su zarah suke tun daga bakin k’ofa tafara washe baki tana kai daughter wannan irin kyau haka?

zarah dai murmushi kawai tayi tare da sunkuyar da kanta domin gabanta fad’uwa kawai yake,

Hajiya sa’adatu tace yauwa toh yanzu kitashi kije parlour na suna chan suna jiranki.

kallon Hajiya kubra zarah tayi, Hajiya kubra tace kitashi mana.

idanuwanta nan suka ciko da k’wallah, Hajiya kubra tace a’a zarah dan Allah kar kiyi kuka ki6ata kwalliyarki.

zarah murmushi tayi tace Toh Aunty kubra, nan kuyangin da ummi ta aiko mata da su suka take mata baya tafiya take cikin takunta mai aji hango motocin su yarima da tayi da sauran guards d’insa saida gabanta yasake fad’uwa duk tsoro da fargaba suka cikata har ta isa parlour nan guards d’in da suke tsaye wajen k’ofar suka gaisheta ahankali tabud’e labulen dakin tashiga inda tabar kuyangin tsaye waje.

cikin ‘yar siririyar muryatarta tayi sallama, shaheed ne ya amsa mata tare da d’ago kai yakalleta zaro ido yayi yace wow masha Allah matarmu bismillah mana.

ahankali zarah tatako tazauna saman kujerar da take opposite d’insu cike da nutsuwa tagaishesu, shahid ne kawai ya amsa mata domin yarima har lokacin bai d’ago ya kalli inda takeba barema asa ran zaiyi magana.

Shaheed kallonta yayi yace amaryarmu gaskiya kin had’u, dafatan mun sameki lfy? , murmushi zarah tayi tace lafiya lou ya gida?

shahid yace kowa yana lafiya, sannan yamaida kallonsa ga yarima da yake zaune kamar baisan abinda akeyiba, murmushi shahid yayi yace ranka yadad’e kayi shuru bakace komai ba,

Zarah ahankali tad’ago kai takalli mutumin da tunda tashigo baiyi maganaba dannar wayarsa kawai yakeyi saida gabanta yafad’i, batare da yad’ago kai ya kalletaba yace akawai event d’in da zakiyi ne?

shuru zarah tayi tana kallonsa, ahankali yarima yad’ago kai yakalleta nan suka had’a ido, dasauri yajanye idonsa daga kallonta yace kamar nawa kike buk’ata inbaki?

zarah dakyar tabud’e baki tace bana buk’atar ko naira, ta6e baki yarima yayi, ganin haka yasa shahid yace a’a amarya kar kice haka kifad’i yadda kike buk’ata nagama kamar kunyata kukeji kowa yakasa magana bari inbaku waje kuyi magana.

Yarima yace no nima ai tafiya zanyi yanzu, harararsa shaheed yayi yace toh ai sai kugaisa dan naga ko gaisawa bakuyi ba kar ace ni nahana nabarku lafiya, yana gama fad’in haka yaficce yabar musu d’akin,

nan d’akin yad’auki shuru ba’ajin motsin komai zarah wasa kawai take da yatsun hannunta, jin baida niyar yin magana yasa tad’ago kai takalli yarima dayake ta dannar wayarsa kamar baisan da zaman mutum ba a wajen, zarah wani k’ululune taji ya tsaya mata a mak’oshi, janye idonta tayi ga kallonsa mamakinsane yacikata cikin ranta tace mutumin nan ko dai kurma ne? chan wata xuciyantace toh kuma ai yanzu taji ya yi ma d’an uwan nasa magana, chan da tagaji da shurun ahankali tace ina wuni?

shuru yarima yayi bai amsaba jin shurun da yayi yasa tad’auka baijitaba nan tak’ara d’ago kai takallesa har lokacin dannar wayarsa yake, sai a lokacin ya amsa mata cikin muryarsa mai dad’i, zarah mamakine yakamata domin bata d’auka miskilancin nasa yakai hakaba, ahankali tace lallai wannan mutumin d’an wulak’ancine, jiyo muryasa tayi yace magana kikayi?

cike da k’ulewa tace ni bance komaiba,

d’ago kai yarima yayi yakalleta kallo d’aya yayi mata yad’auke kai tare da mik’ewa tsaye, takawa yayi yaje inda take ya aje mata cheque a gefenta sannan yace gashinan idan basu ishekiba sai kiyi magana.

zarah ida k’ulewa tayi ganin baima jin zai iya bata saima ajemata yayi, cike da jin haushi tace kabarsu kawai ba abinda zanyi da su.

yarima kallonta yayi cikin rashin damuwa yace indai nafitar da kud’i bana maidasu idan basu ishekiba zaki iya yin magana, yana gama fad’in haka yawuce yafita yabar d’akin,

tsaki zarah taja tare da mik’ewa tabi bayansa domin suyi sallama da shaheed, ganinta yasa shaheed yatafo wajenta yana murmushi yace amaryarmu yanzu nake shirin zuwa muyi sallama.

Murmushi itama tayi tace nima cewa nayi bari nazo muyi sallama, yarima gaba yayi aka bud’e masa mota yashiga saida suka iso wajen motar sannan zarah tayi musu sallama takoma ciki tana mamakin halin yarima, cikin ranta tace ashe akwai babban aiki a gabana.

 

ko da su yarima suka kama hanya shahid kallon yarima yayi yana murmushi yace gaskiya yarima ka iya za6en mata kaga yadda kukahad’e kukai matching? yarima batare da ya kallesaba yace bawani dacewa ai wlh kai yakamata ma ace anma dole ka yi aure, dariya shahid yayi yace nima fa abin yana damuna ganin har kana shirin yin na biyu ammah ni ko d’aya banda ita, yamitsa fuska yarima yayi yace nima ba ason raina nayi aure yanzuba dan banma shirya yinsaba by my age, kaduba kaga duka yanzu fa 28yrs ammah mata har biyu tsaki yarima yaja cike da takaici yace ina ma amfanin hakan.

dariya shaheed yayi yace ai abun jin dad’ine hakan kuma matsayinka ya kai hakam, nima insha Allahu kwanannan zan faso zan baku mamaki,

ta6e baki yarima yayi yace wajen surutunka kayo yarinya ko?

shahid gyara zamansa yayi tare da cewa haba dai kabari zakasan ko wacece nan gaba jira nake agama wannan hidimar auren naka nima in6ullo kai dan bama zanso asa sama da wata d’ayaba,

yarima suhail jingine kansa yayi da sit din da yake zaune tare da lumshe idonsa,

ganin haka yasa shahid yaja bakinsa yayi shuru dan yasan maganarce ta ishi yarima.

tunda suka kama hanya basu zarce ko inaba sai gidansu zarah saboda tun dare sultana bilkisu ta kira iyayen zarah ta shaida musu yarima yana nan zuwa zai gaishesu, dan haka tun da safe suka dinga hidindimu kaji shidda baba yasiyo akayi pepper da ukku aka soya ukku, had’add’ar wainar shinkafa su mama sukayi da miyar ganye sannan suka had’a kunun aya wanda yasha madara, bayan sun gama duk suka shirya suna jiran zuwan yarima dan su Aysha sun k’osa sosai suga mijin zarah.

 

A gaban gidansu zarah sukayi parking d’in motocin dasauri guards d’in sukafito daga motocin da suke ciki sukazo suka bud’ema su yarima k’ofa tare da cewa ranka yadad’e nan ne,

yarima batare da yafitoba yadinga k’arema gidan kallo cike da mamaki, shima shahid mamakine yacikasa ganin gidan da yarima yanemi aure.

malam musa da yake zaune cikin gida jin k’arar mota yasa yakalli su mama yace ina tunanin sun iso bari inje induba,
cike da jin dad’i Aysha tace yauwa Allah yasa sune.

malam musa ko da yafito yaga jerun motoci cike da fara’a yanufo wajen, ganinsa yasa yarima yafito daga motar, nan guards d’insa suka shiga gaishe da malam musa.

malam musa hannu ya mik’a ma su yarima suka gaisa yace maimakon kushigo sai kukayi tsaye? shaheed ne yace daman yaro muke nema mu aikasa yayi mana sallama da kai,
malam musa yace ayyah Allah sarki toh bismillanku.

batare da sunyi musu ba sukabi malam musa suka shiga har cikin soron gidan, saman tabarma suka zauna.

cike da girmamawa suka gaishe da malam musa ya amsa musu tare da tambayarsu mutanen gida, shaheed ne yace suna lafiya lou, sunce agaisheku

malam musa yace muna amsawa sannan yakalli yarima da tunda yagansa yagane shine mijin da zarah zata aura, malam musa yace ya su mahaifiyartaka?

murmushi yarima yayi kansa yana sadde a k’asa yace lafiya lau suke.

malam musa yace toh masha Allah, mik’ewa yayi yace ina zuwa nan yashiga gida.

bai dad’e da shigaba yafito tare da su Rauda da suke d’auke da kuloli da sallamarsu suka shigo, su yarima suka amsa musu gabansu suka aje kulolin, tare da gaishesu cike da sakin fuska su yarima suka amsa, malam musane da yake tsaye yanuna rauda yace wannan itace yayar amarya, kallonta yarima yayi yana murmushi yace sannu yayarmu.

itama rauda murmushin tayi tace yauwa k’anena.

Aysha ce tayi karaf tace nikuma nice k’anwar Aunty zarah kuma autarsu.

gaba d’ayansu dariya sukasa mata banda yarima da yayi murmushi kawai, shahid yace tun ba’a tambayekiba?

yarima suhail yace ina ruwanka ai ni tafad’a mawa ko k’anwata?

‘yar dariya Aysha tayi tace eh yayana, ammah ai kaine angon namu ba wannan ba (tanuna shaheed)

shaheed yace nine mana.

Aysha tace chab gaskiya wannan nafiso yakasance mijin yayata.

murmushi yarima yayi yace saboda me?

Aysha tace saboda kunfi dacewa da ita,
yaya rauda tace zanci gidanku Aysha banason rashin kunya.

shaheed yace a’a babbar yaya kibarta kawai tunda tace bamu daceba sai inhak’ura inbar masa.

Aysha tace A’a ni ba haka nake nufiba kaima ka dace da yayata sosai.

shaheed kallon yarima yayi yana murmushi yace toh ka dai ji abinda tace kaje nabarmaka ita.

shima yarima murmushi yayi yace k’yalesa my sis ai nine angon ba Shiba tsokanarki kawai yakeyi.

cike da jin dad’i Aysha tace yeahhh wlh naji dad’i, murmushi kawai suhail yayi batare da yace komai ba.

daidai lokacin abbah yafito daga cikin gida d’auke da swan water yace kutashi kubasu waje suci abinci mana.

atare suka mik’e suka shige gida, abbah ajiye ruwan yayi yace dan Allah kuci abinci.

shaheed ne yace Alhmdllh abbah wlh a k’oshe muke.

abbah yace gaskiya ba zanji dad’in hakan ba nasan kunfi k’arfin abincinmu ammah ko yayane kusanya albarka.

yarima ne yakalli abbah yana murmushi yace kar kadamu abbah zamu ci.

abbah yace yauwa gaskiya naji dad’i bari inshiga ciki kafin kugama.

Bayan abbah yashiga gida shaheed ne yabud’e kulolin cike da jin dad’i yace yarima ur best food ne fa,

yarima batare da yakalli abincinba yayi murmisho, shaheed ne yayi serving d’insu ya aje ma yarima nasa a gabansa.

yarima waina biyu yaci tayi masa dad’i sosai saida ya jinjina ma k’ok’arin da iyayen zarah sukayi wajen tarbarsu, kunun ayan dai saida yashanye 1 cup kasancewar yana sonsa sosai, shidai shaheed loda ma cikinsa kawai yake yana santi har yaso yaba yarima haushi.

 

bayan sun gama abbah yadawo nan yazauna suna d’an ta6a hira kad’an-kad’an sannan yashirga da su cikin gida suka gaishe da mama cike da girmamawa, da zasu fito yarima dubu d’ari yamik’a ma Aysha yace sunyi hidimar bikki, da fari k’in kar6a tayi dan baba yahana saida yarima yace shifa ba dan wani abu yabataba kawai saboda tayi kwalliyar bikkin yayarta da za’ayi a matsayinta na auta, dariya sukayi sannan sukayi masu rakiya har wajen mota suna godia, cike da jin dad’i domin suna ganin zarah tayi sa’ar miji mutumin kirki.

A cikin mota shaheed kallon yarima yayi yace gaskiya mutanen nan suna da mutunci sosai daman daga ganin zarah kaga mutuniyar kirki ashe wajen iyayenta tagada.

yarima a tak’aice yace danginta suna da kirki sosai.

shahid Jin maganar da yarima yayi yasa yayi murmushi yace Allah yabarmin kai yarimana.

 

kud’in da yarima yaba zarah nan tabarsu inda ya aje mata saida hajiya sa’adatu tashiga tagani sannan takaima zarah,

zarah ganin cheque din 300,000 saida ta tsorata tace nashiga ukku ina zan kai wad’annan mak’udan kud’in, daga k’arshe yanke shawara tayi tace kawai iyayenta zataba idan takoma gida.

 

Agurguje ana sauran kwana ukku bikki sultana bilkisu ta aika da mota aka d’auki zarah aka maidata gida, kasancewar tun ana saura kwana hud’u hajiya kubra takoma gidanta.

mummy sa’adatu taso abarmata zarah har sai ranar bikki ammah sultana bilkisu tace a’a abarta takoma wajen iyayenta tunda suma suna buk’atarta a kusa.

ko da aka maida zarah gida ‘yan gidansu basu ganetaba mama ce kawai taganeta itama dariyar zarah tagane.

murna sukayi sosai da ganinta mamaki yacikasu ganin yadda takoma kamar ba itaba dan komai nata ya canza dan Aysha ma cewa tayi an canza mata yaya anbata ‘yar gayu.

 

zarah kud’in da yarima yabatane taba abbah tace ayi gyaran gida, da fari k’in kar6a abbah yayi yace taje tayi hidimar bikki sauran kud’in neman aurantama suna nan zai d’auko mata, zarah tace a’a ta bar musu

abbah yace ai hak’intane, zarah saida tasa ma su abbah kuka sannan suka kar6i 300,000 d’in yace sauran kuma natane,

Aysha da ta zauna labarin yarima kawai takeba zarah irin kirkinsa da rashin girman kansa, ita dai zarah saidai tayi murmushi cikin ranta tace ku dai kukaga haka ammah inba ji da kai ba me ya aje…

 

 

_Comments_
*nd*
_Share_

 

 

_Sis Nerja’art✍_

_*YARIMA SUHAIL*_

 

_*Written By~Sis Nerja’art*_

 

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….*✔

 

 

Back to top button