Ikraam 80
Ikhram~ By Khaleesat Haiydar 80…… Ikram ce xaune ita kadae dakin Jummai ta hade kai da gwiwa tana rera kuka a hankali, wani mugun tsanar Khaleel take ji kawae a ranta lkcn, ko ganinsa bata son yi, ba karamin fada Mami tayi mata daxu ba, don wnn karan ba Jummai ta sa ba, cire kunya tayi ta mata da kanta, Jummai ma ta kara mata nata a kai, karfe goma saura Jummai ta shigo dakin, ta bude baki tana kallonta tace “lah ha ilah, Ikram kuka kike har ynxu” Ikram ta dago kanta da sauri tana goge fuskarta, Jumma ta dagota tace “haba ikram din Mami, to kiyi hkuri kin ji, maxa ki wanke fuskarki ki je Mami na kiranki” ba musu ta shiga bayi ta wanke fuskarta ta fito, snn ta fita xuwa dakin Mami, Mami na shan fruitsalad, tace “kin ci abincin?” Ikram ta gyada mata kai kanta a kasa duk da bata ci ba, Mami tace “to wuce kije kiyi wanka” ba musu ta nufi bathroom bayan ta dauki towel, tana fitowa tayi shafe shafenta gaban madubin Mami snn ta dauki yar vest fari tasa, ta daura xaninta ta nufi gadon Mami ta kwanta don nn xasu kwana ranar, karfe goma da rabi Khaleel ya shigo dakin, ya gaida Maminsa snn ya fita xuwa dakinsa, sha daya dae dae Mami dake kan computer ta juya tana kallon Ikram tace “a nn xaki kwanan min?” Ikram tayi shiru bata ce komai ba, can ta mike a hankali ta dauki hijab dinta tace “sae da safe Mami” snn ta fita daga dakin, yana xaune yana shan tea ta shigo dakin, ko kallonsa bata yi ba fuskarta a tamke tayi kwanciyarta ta juya masa baya. Washegari sunday da daddare suka koma gidansu bayan Mami tayi mata nasiha ssae, jummai ta dora da nata, sae da tayi kwana uku bata kulasa ba as usual, snn don kanta ta sakko ta fara masa mgnr, amma duk abinda Mami suka gaya mata a bnxa don bata yi aiki da su ba, kememe ta nuna masa ita baxata amince da shi ba don ba shi take so ba, tun daga ranar da ta gaya masa hka bae sake bi ta kanta ba a kan batun, sae dae bae canxa mata ba suna xamansu lfya kmr wasu masoya, idan yaji baxae iya ba sae dae ya dau Axuminsa kawae, in ko al’adarta ya tashi har gado ana basu a asibiti sbda ynda take wahala, amma hkn bae sa Ikram ta saduda ba, ta gwammace tayi ta wahala kmr xata mutu, har bayani likita tayi mata a asibitin da suke xuwa, a kan abinda xae sa ta samu saukin ciwon cikin nata da ta fahimce tana da aure, amma Ikram taki saurarta, sae da suka dawo gida take ce ma Khaleel, nxt tym idan cikina ya fara ciwo wani asibiti xa mu canxa matar nn ta sa min ido, yyi murmushi yace to.