Hausa NovelsIkraam Hausa Novel

Ikraam 66

Sponsored Links

~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 66….. Ikram ta bude ido da
sauri jin muryar Aliyu, sae ta fashe da kuka ta sakko kasa ita
ma ta durkusa gabansa, tana kallonsa tace “yayana ance min
kai ne mijina, amma ban ganka ba sai yaya Khaleel” kasa daga
kai ya kalleta Aliyu yyi, hawaye kawae yake, Mami ta dafa sa ta
dago kansa tana kallonsa cike da tausayi tace “kar ka kuma
cewa hka son, kai ma kasan i luv yhu more den abinda na
haifa, its nt my fault Aliyu, mum dinka ce tasa nayi hkn, but ka
kwantar da hankalinka in’sha Allahu xaka auri Ikram, don ynxu
ba aure tayi ba, at anytime xan karbi takardarta hannun
Khaleel, dan he is nt meant 4 her, nd she’s meant 4 only yhu
son,” Khaleel ya ajiye kofin hannunsa ya kauda kansa yana
murmushi, kasa ce mata komai Aliyu yyi har lkcn kansa na
kasa, Mami ta mike a sanyaye ta haura sama, Aliyu ya dago da
kyar yana kallon Ikram, Ikram ta matso kusa da shi tana goge
masa hawayen fuskarsa tace “ka daina kuka kaji yayana, ni ina
sonka wllh” a sanyaye yake gyada mata kai, ta rungumesa ta
fashe da kuka, ya rumtse ido duk da yasan bae kamata ba
amma ya kasa cireta daga jikinsa, a hankali yaji tana cewa
“yayana ka manta promise din da nayi maka baxan aura kowa
sae kai ba” dagowa yyi yana kallonta, ya sakar mata murmushi
yana kallon cikin idonta yace “na tuna kanwata” ita ma tayi
murmushin tace “to har ynxu ni banyi aure ba, kai kadae xan
aura ka ji” ya gyada mata kai a sanyaye, a hankali yace “to kiyi
min promise cewar baxa ki bari kowa ya taba min jikin ki ba
Ikram” ta xaro ido tace “to dama ae baxan bar kowa ya taba ni
ba yayana sae kai” yyi murmushi yace “to ngdd kanwata, Allah
yasa ki rike min promise dina kanwata” tace “wllh xan rike
yayana” mikewa Khaleel yyi yana murmushi ya nufi stairs ya
haura sama, Aliyu ya bisa da kallo snn ya Mike da kyar ba tare
da ya kalli Ikram ba yace “na tafi kanwata” binsa tayi da kallo
har ya isa bakin kofa snn tace “to ina xaka yayana” ba tare da
Aliyu ya juyo ba yace “gidan xani” ya bude kofar ya fice ransa a
dagule. Karfe takwas na dare Mami tace ma Khaleel ya dauki
Ikram su tafi can gida Dad na son ganinsu, bayan ya gama
shiryawa ya shigo dakin Mami yi mata sallama, mami tace “kar
ka sake ka gaya ma dad dinka deal dinmu, ko me xae ce maka
kaji kawae ka tashi, snn da seeyama xaku je can gidan” yace
“to Mami” Mami ta juya tana kallon Ikram dake kallo tace
“tashi ku je dota” Ikram ta bata fuska tace “ina xa mu Mami”
Mami tace “can gidansu Momy xaku je, ku dauko seeyama”
Ikram tace “amma ae gidan nn xamu dawo ko” Mami ta gyada
mata kai, snn ta mike ta sa Hijab dinta ta fita, Khaleel ya dauki
jakar uniform dinta da wasu kayanta da Mami ta shirya mata
xae fita Mami tace “kar ka bar min yara su makara xasu
makaranta gobe, da asuba jummai xata kawo maku breakfst,
idan abubuwa suka dawo min nml, xata koma can ita ma
jumman” yace “to sae da safe Mami, but sch bag dinta fa”
Mami tace “jummai xata kawo gobe” ya juya ya fita daga
dakin, bakin mota ya tar da Ikram, ya bude mota ya shiga ita
ma ta bude ta shiga suka bar gidan, har suka isa gidansu Aliyu
bae ce mata ba bata ce masa ba, yana gama parkin ta bude
mota ta fice tayi cikin gidan, fitowa yyi ya bi bayanta, basu
wani dde ba a gidan, Daddy yyi masu nasiha ssae ita dae
Ikram bata ma san me yake cewa ba don hankalinta gaba
daya na gun kallon da take, Khaleel ya mike ya nufi sama
bayan Dady ya sallamesu ya shiga dakin Momy ya fadi mata
sakon Mami na cewa ta basu seeyama, Momy tace “tab,
seeyama ma bata nn wllh, tana can gidan kanwata kuma
karatun fa” yace “ae daga can xata dinga xuwa” Momy tace “to
sae ta dawo” tare suka fito da momy xata rakasu, suka hadu
da Hajiya a corridor, Hajiya na yar murmushi tace “A’a ango ne
a gidan namu yau, sannu ango ina Amaryar taka” dariya ta
basa, ya dae yi murmushi ya gaisheta yyi gaba, Momy tayi
tsaki ta sauka ita ma, har bakin mota ta rakosu snn suka bar
gidan, sha daya saura suka isa gida, ya juya yana kallon Ikram
yaga bacci take, bude motar yyi ya fito snn ya xagayo ta inda
take ya bude motar yana kallonta, bakinta ya dan buge, ta
farka a dan tsorace ta fito da sauri daga motar tana hararansa
tace “meyasa xaka taba ni” tsaki tayi ta shiga kalle kallen inda
suke, ta bata fuska xata yi kuka tace “meyasa ka kawo ni gidan
nn kuma, ni wllh ka mayar dani gidan Mamina” rufe motar yyi,
ya nufi hanyar shiga gidan, ta bisa da gudu tana kuka, suka
shiga falon ya kunna wuta snn ya haura sama tana biye da shi
a baya tana kiran Mami, yana shiga daki ya shiga bathroom ya
canxa kayan jikinsa xuwa na bacci snn ya fito yyi kwanciyarsa
don yyi wanka a gida, ta tsaya daga bakin kofa tana rera kuka
tana kallonsa, kashe wutan dakin da yyi yasa tayi gunsa da
gudu tana cewa “ni ka kunna min wuta in dinga ganin haske”
fixgota yyi kmr jiya ta fado jikinsa, ya rungumeta, a hankali
yace “shiiii” shiru tayi kmr jiya yana jin bugun xuciyarta, gashin
kanta ya shiga gyarawa a hankali yaji ta xamo daga jikinsa
bayan kmr minti biyar ta juya masa baya, ya juya yana kallonta.
Like · 5 · Reply · R

Back to top button