Hausa NovelsYarima Suhail Hausa Novel

Yarima Suhail 7

Sponsored Links

page 7⃣

yarima sai dare sannan yabaro turakar su ummi yakoma part d’insu, saida yayi wanka yashirya sannan yafito dining yad’anci abinci bayan ya gama kallo yakunna yana yi, bud’e k’ofar akayi aka shigo bai ko d’ago kai ba domin ya san gimbiya ce.

gimbiya sumayya ganin bai kalletaba yasa tatako tazauna gefensa cike da isa tace daman nazo infad’a maka jibine fa zan tafi kuma kasan ba zan iya tafiya mai tsayi a motaba dan haka sai kabada kud’i ayomin Visa,

wani mugun kallo da yarima yawurga mata saida hantar cikinta takad’a, batare da ya janye idonsa a garetaba yace ni na’aikeki?

Gimbiya sumayya itama kallonsa take tace toh naga kai yafi dacewa da kasa ayankar min ticket tunda k’ark’ashinka nake.

yarima shuru yayi kamar ba zaice wani abuba sai chan kuma yace ke ban ta6a sanin bakida hankaliba sai yanzu baizama dole inyi miki hakanba kuma bana tunanin akwai Wanda ya isa yasani dole, dan haka tashi kifitar min daga d’aki tun kan in6ata miki rai.

gimbiya sumayya mik’ewa tayi saida takai bakin k’ofa sannan tajuyo takalli yarima suhail tace koma dai me kenan katabbatar zuwa gobe ka yimin abinda nakeso inkuma bahakaba zan fad’ama dada, tana gama fad’in haka taficce daga d”akin.

yarima suhail takaicine da bak’in ciki suka taru sukayi masa yawa tsaki yaja kawai ak’arshe ma yakashe kallon yatashi yashige bedroom d’insa cike da 6acin rai yakwanta, yanajin wani iri a zuciya ji yake an cucesa da aka za6a masa gimbiya sumayya a matsayin matarsa domin kwatakwata halinta baiyi masaba.
ak’arshe wayarsa yajawo yakira d’aya daga cikin yaransa yace zuwa gobe a tabbatar anyi ma sumayya Visa.

Wanshe kare wajen k’arfe sha biyu da yarima yagama shirinsa fitowa yayi yanufi d’akin gimbiya sumayya inda yataddata a lokacin tafito daga wanka, a wulak’ance yakalleta sannan yawurga mata ticket yace ba dan halinki nasa akayi mikiba dan ganin damanane.

harararsa gimbiya tayi tace eh ahaka d’in dai saida nayi magana, yarima suhail murmushin mugunta yayi sannan yataka inda sumayya take, dak’arfi yajawota tafad’o jikinsa har saida tad’anyi ‘yar k’ara sannan yace sumayya inaso kisani darajar iyayena kawai kikeci da badan hakaba wlh da sai kin gane kuskurenki.

gimbiya sumayya tace suhail kadad’e baka nuna min kuskurenaba kuma yadda kake tak’ama da sarautarnan nima ai jinintane, bamuda banbanci ni da kai, kuma idan ka cika d’an halak kata6ani kagani, kuma bari kaji jikina kagama samunsa tunda har kata6amin fuskata jiya yanzu daidai nake da kai.

yarima suhail d’auke ta yayi da mari yak’ara mata wani tare da wurgata saman gado yace banyi niyar kwanciya da ke ba ammah yau zan nuna miki na ciki d’an halakne ni, saman gadon yabita tare da fizge towel d’in da yake jikinta nan suka shiga kokawa ak’arshe yarima suhail yasakarmata nauyinsa.

mugunta yasa mata yadirjeta son ransa, gimbiya sumayya kuka kawai take, yarima saida yagaji dan kansa sannan yabarta,

kayansa yad’auka yasanya bai ko k’ara kallon inda sumayya take kwanceba tana ta ja masa Allah ya isa, fita yayi daga d’akin yakoma part d’insa yayi wanka yashirya sannan yaje fada yagaishe da sarki daga nan yafita yabar gidan.

Tun daga lokacin basu k’ara had’a hanya da gimbiya sumayya ba baima san lokacin da tatafiba sai wajen dada yakeji,

hatta umman sumayya yanzu ko ya gaisheta bata amsawa dan haka shima yadaina gaisheta, ko da ace tana tare da abban sumayya toh abbah kawai yake gaishewa tsakaninsa da ita saidai tahararesa shikuma yanuna ko inkula.

__________________

awata anguwa mai suna yamza wata yarinyace take tafita a nutse kanta a k’asa yarinyar ba zata gasa shekara ashirinba wani gidane tashiga gidan da kagansa kasan bamasu hali bane saidai rufin asiri, da sallamarta tashiga, wata matace da nahango zaune tana wanke-wanke ciki-ciki ta amsa mata sallamar

cike da ladabi zarah tak’arasa inda matar take tare da tsugunnawa tace mama sannu da gida.

harara matar tawurgamata tace ke shine bakiyi min wanke-wankeba kika kama hanya kika fita daga gidan ko?

zarah cike da nutsuwa tace mama dan Allah kiyi hak’uri wlh ganinayi na makara islamiyya shiyasa.

rik’e baki mama tayi tace eh islamiyya fad’amin nida banyi islamiyarba, ke ga ustaziya ko? to wlh inbaki canza haliba haka zakizo kik’are cikin gida, kiduba kiga ‘yan uwanki kullum sai sun fita sun samo mana ‘yan kud’in da zamuyi hidima ammah ke kina nan jibge a cikin gida saidai aciyar dake ashayar da ke iyakarki kashi, toh wlh indai bakiyi dagaskeba sai kin rasa mashinshini domin wannan girman kan naki babu inda zai kaiki.

zarah shuru tayi batace komai ba domin idan da sabo ta saba da halin iyayen nata,

tsawa mama tadakamata tace watau ga mahaukaciya ina magana shine kikayi shuru kika kyaleni watakau ga mahaukaciya tana magana.

zarah cikin nutsuwa tace Allah yabaki hak’uri mama kawo wanke-wanken in k’arasa miki.

ummah d’auraye hannunta tayi tamik’e tace ai ko bakiceba daman ke zaki idashi tunda baki aikin komai sai karatu saikace alhuda-huda.

mama tana tashi zarah tacire hijab d’inta tarataye saman igiya sannan tazauna tacigaba da wanke-wanken.

tana cikin yi saiga yayarta tashigo babu ko sallama kallonta zarah tayi cike da takaicin ganin irin shigar da take jikinta kayan sun matseta gyalen da tayafa ko dashi k’ara babu, d’auke kanta tayi daga kallonta tacigaba da wanke-wanke tana addu’a cikin zuciyarta Allah yashirya su sugane gaskiya.

muryar yaya rauda ce tajiyo tana cewa zarah ina mamanmu take? batare da takalletaba tace tana cikin d’aki.

Rauda kira tashiga kwala ma mama daga inda take tsaye, mama datake d’aka dasauri tafito kallabinta a hannu tana washe baki tace a’ah ‘yar albarka har kin dawo?

Rauda yamutsa fuska tayi tace eh ga wannan ledar da take hannunta tamik’a mata, ummah cike da farin ciki ta amsa tana cewa me muka samu yau?

malam yusuf ne yashigo gidan yana cewa a’a ‘yar baba ai naga lokacin da aka safkeki kinga har da ‘yan canji mutumin yabani gaskiya yana da kirki.

Rauda yamutse fuskarta tayi tace ammah ai abba nace kadaina tambayarsu kud’i inkana tambayarsu ai sai kaja surainani ,

abba yace ‘yar baba bafa tambayarsu nakeba sune suke bani kuma kinga babu kyau maida hannun kyauta baya ko ba haka bane Zainabu?
mama tace hakane malam, yanzu dai mik’o wani abu nan dan musamu daren nan muci mai d’an dad’i-dad’i.

abba yace toh naji yanzu dai menene cikin ledarnan?

mama duba ledar tayi tare da washe baki tace ashe kazace yau shagali zamuyi kenan.

Abba ma washe baki yayi yace gaskiya naji dad’i daman wannan bakin nawa yakwana biyu bai ci namaba, ammah dai ‘yar baba Allah yaimiki albarka,

mama tace toh yanzu dai kakawo asiyo kayan miya muyi d’an pepper chicken,
abbah dubu d’aya yamik’a mata yace gashi sai akasiyo har da buredi wanda zamu d’an dangwala romon ai haka zaifi ko?

mama tace eh malam, ai saima autarka tadawo muga ita mi zata kawo mana, ai ni yau naga amfanin haihuwar ‘ya’ya mata daman malam ai nafad’a maka ‘ya’ya mata dad’i garesu,
malam yace hakane sannan yakai dubansa ga zarah da take tsugunne tana ta wanke-wanke, yamutsa fuska yayi yace Asma’u wlh d’iyar chan duk cikin ‘ya’yana ita kad’aice batada k’ashin arzik’i wani ma lokacin ji nake anya jininace?

ummah tayi karaf tace a’ah malam wannan cin mutuncin da me yayi kama idan ba d’iyarka bace toh wanene ubanta? ko akwai wani mijin da na aura bayanka? ko kuma kana nufin ina bin mazan banza.

malam yace a”a zainabu nidai ina nufin kwata-kwata bata d’auko halinaba, kiduba kiga ko farin jinin samarin nan ita batadashi,

ummah tace ah toh yanzu naji bayani, ai malam kakalli wannan munafukar kawai bak’in ciki kawai take yi mana dan kar muci moriyarta kasan yanzu sai kahaifi d’a baka haifi halinsaba, wlh akwai samarin wulak’antasu kawai take tana korarsu sai wannan matsiyacin malamin nata da ta lik’e mawa me na k’asa yaci bare yaba nasama.

malam yace oh ni wlh daman nayi zaton haka ni wlh wannan sakaryar d’iyar bansan yaushe zata waye kamar ‘yan uwantaba, Allah dai yashiryata.

mama tace Ameen dai

malam yace yanzu dai dafa mana kazar a d’ansa kayan yaji nasan zatafi dad’i haka bari ind’an fita.

ummah tace toh malam adawo lafiya.

zarah dai zaune take tana wanke-wankenta duk firar da iyayenta sukeyi akan kunnenta hawayene yacika mata ido tana jin wani abu ya tokare mata mak’oshi saboda takaicin halin iyayenta, cikin ranta addu’a take Allah yashirya mata iyayenta da ‘yan uwanta sugane gaskiya.

bayan ta gama alwallah tad’aura sannan tad’auki hijab d’inta tashige d’akinsu, lokacin yaya rauda tana shafa da alamu daga wanka tafito.

zarah shimfid’a darduma tayi tad’auko alk’ur’aninta tana karantawa har aka tada sallar magrib sannan tatashi tayi sallah

ido tazuba ma rauda tana kallon yadda take sallah cikin sauri babu alamun nutsuwa atare da sallartata

ko da rauda tagama sallar zarah kallonta tayi cike da nutsuwa tace yaya rauda ya kamata idan kina sallah kidinga nutsuwa domin duk abinda zakije nema yana a hannun wanda kike gabansa a yanzu.

harararta Rauda tayi tace toh malama yimin wa’azi tunda kinfini sani, kinsan Allah zarah idan baki fita daga hancinaba sai na 6a66allaki a cikin gidan nan
kuma da kike maganar sallah ai Allah da zuciyar mutum yake amfani, kuma idan ke kike raba ladar toh dan girman Allah kihanani ‘yar bak’in ciki kawai.
tana gama fad’in haka tatashi fuuuu taficce tabar d’akin tana ta mita…….

_Comments_
*nd*
_Share_

_Sis Nerja’art✍_

_*YARIMA SUHAIL*_

_*Written By~Sis Nerja’art*_

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….*✔

Back to top button