Hausa NovelsYarima Suhail Hausa Novel

Yarima Suhail 11

Sponsored Links

page 1⃣1⃣ Yarima suhail bayan gimbiya sumayya ta fita dafe kansa yayi cike da jin haushin sumayya da take nema taraina masa wayau, watau ta ma san ya yi missing d’inta? to kenan ita batayi missing d’insaba tana nufin taimakonsa ma zatayi. tabbas yasan ya yi *BABBAN KUSKURE* da ya amince ya aureta domin ko kad’an batasan minene aureba tsaki yaja yace Allah yashirya sannan yakoma yakwanta yana mamakin halin sumayya. Sumayya a fusace takoma d’akinta cike da bak’in cikin wulak’ancin da Yarima yayi mata, ace kamarta daga ta je tataimaka masa shine yakoreta tana shiga bedroom tamurza key nan tafad’a saman gado tafara kuka. tun daga ranar aka koma ‘yar gidan jiya ba mai kula d’an uwansa kowa harkar gabansa yakeyi _______________ A 6angaren su zarah har yanzu babu abinda yasauya daga halaiyar ‘yan gidansu, malam bello yanzu islamiyya kawai suke samu suna had’uwa yauma bayan ta taso daga islamiyya tafiya take a nutse kanta sadde a k’asa daga bayanta taji ana mata sallama kamar ba zata amsaba sai kuma chan ta amsa batare da ta tsayaba mutumin cigaba yayi da binta yace dan Allah ‘yan mata kitsaya kisaurareni mana, Zarah ahankali tad’ago kai takalli mutumin da bazai gaza shekaru ashirin da biyarba, k’ara d’aure fuskarta tayi tace lafiya malam kaketa bina? Murmushi mutumin yayi yace ni dai sunana hamza ina zama chan waccan rumfar mai kayan miyar kullum ina ganin giftawarki idan kin dawo islamiyya kuma gaskiya ina sonki saisa natunkareki nafad’a miki domin insamu matsugunni a zuciyanki wlh ina sonki, ina k’aunarki ina begenki, wlh indai baki amshi tayin soyayya taba zan iya mutuwa. zarah baki tasaki tana kallonsa maganganunsa har sukaso subata dariya tadake tace ka gama? hamza yace eh nagama ina dai son inji daga gareki domin kema nasan nayi miki Zarah d’an murmushi tayi tace nagode sosai da tayinka ammah saidai kayi hak’uri domin ina da wanda nake…… katseta hamza yayi yace dakata malama ai daman abinda naji ma tsoro kenan saisa tun tuni nak’i tunkararki da maganar ammah wlh bakiyimin adalciba danma kin samu ance ana sonki wanene anguwarnan bai san halin gidankuba waye baisan ku ‘yan iska bane, dan ma kin samu antaimaka ance ana sonki. zarah murmushin takaici tayi sannan tace toh nagode kuma so ne bazan ta6a sonkaba, tana gama fad’in haka tawuce tabarsa tana jinsa yana ta yada mata bak’ak’en maganganu ammah tasharesa cikin ranta ko wani irin abune yatokare mata mak’oshi tabbas tasan abinda bawan Allahn nan yafad’a gaskiyane a game da gidansu, ahaka ta isa gida da tunani iri-iri cikin ranta. *BAYAN SATI ‘DAYA* Rauda yau kasancewar ta tashi da matsanancin ciwon kai da zazza6i kwance tawuni bata iya komai, da kaganta kasan tana jin jiki tuni ta fita hayyacinta saboda Amai da take yawan yi su mama sun tusata a gaba kowa tausayinta yakeji ganin irin wahalar da take sha kallonsu kawai zakayi kasan suna cikin matsanancin tashin hankali. zarah ko kuka kawai takeyi tana rik’e da hannun yayartata ko kad’an bata yarda tamatsa daga kusa da itaba domin ita tana da k’wallafar ‘yan uwanta. mama ce tahad’o mata ruwan bunu tare da indomie matsa mata sukayi sai taci, ba dan tasoba tadaure tamik’e dakyar tayi loma ukku shima dan taga hankalin dangin nata a tashe, kafin kace mi dagudu tamik’e tanufi toilet tadinga kwarara amai dasauri zarah tabita tarik’eta tana mata sannu har saida tagama, Aysha ce tad’ebo musu ruwa a buta nan zarah tataimaka mata tawanke jikinta sannan suka fito takoma takwanta. zarah kallon su mama tayi da sukayi jugum tace mama dan Allah kice ma yaya Rauda tatashi muje asibiti domin bai dace tazauna da ciwo ba. mama dogon numfashi taja tare da cewa hakane zarah nima abinda nake tunani kenan domin cikin d’an lokacin nan duk ta fita hayyacinta. Rauda dakyar tabud’e baki tace a’a ba zanje asibitiba kubarni a nan kawai in muturwace inyita a gida. zarah da Aysha fashewa sukayi da kuka ganin yarda ‘yar uwar tasu take jin jiki, mama tace A’a Rauda dole fa kitashi muje asibiti. Zarah tace mama ni zan rakata kice tatashi mutafi. mama tace ke mezaki iya idan kinje? Ni dai zan tafi da ita. Zarah tace dan Allah mama kibarni muje tare, mama ganin yadda zarah duk hankalinta yake a tashe dan ko abincin kirki bata samu taciba dan haka tace toh shikenan kushirya kutafi. Mama tataimaka ma Rauda tacanza kaya, Rauda cema Zarah tayi tad’auko handbag d’inta akwai kud’i a ciki dan kar a buk’aci wani abu. Aysha ce tafita tasamo musu adaidaita nan suka tafi General Hospital d’in garinsu. basusha wahala ba wajen ganin likita, ko da Rauda tashiga zarah zaune tayi tana jiran fitowarta, Rauda take zaune opposite d’in kujerar Doctor Xeey Xeey cike da kulawa doctor Xeey Xeey take mata tambayoyi ita kuma tana bata amsa nan Dr Xeey Xeey tarubuta mata taste tace taje tayi kuma tatabbatar yau ta kawo mata. Rauda Kar6a tayi tafito dasauri zarah tamik’e daga inda take zaune tana jiran fitowar ‘yar uwartata. tace Yaya Rauda sannu. Rauda dakyar tace Zarah taste ne tabani muje lab. zarah tace toh yaya Rauda. ko da sukaje lab aka d’ibi jininta sannan aka bata ‘yar roba tayi fitsari a ciki nan akace sujira nan da 30 minutes result zai fito. zama sukayi suna jira har minti talatin yacika aka basu nan Rauda taje takaima Dr xeey xeey sakamako. Dr xeey xeey tana dubawa murmushi tayi sannan tayi ‘yan rubuce-rubucenta bayan ta gama tad’ago kai takalli Rauda tace toh Alhmdllh ina tayaki murna domin kina d’auke da ciki tsawon wata biyu nasoma ace tare kukazo da mijinki. Rauda da tunda Dr ta ambaci ciki tarikece cikin d’aga murya tace doctor ciki? Dr xeey xeey tagyad’a mata kai tace of course dan haka za’a maida miki folder d’inki a ANC kidinga zuwa awo tunda har yakai kusan 2 months batare da anduba lafiyarsaba zaki dinga zuwa awo. Rauda zufa ce tafarayi dasauri taduk’e k’asa tare da fashewa da kuka. da mamaki Dr xeey xeey take kallonta tace menene abin kuka? kyautar da Allah yabakice bakyaso ko mi? Rauda cikin sheshek’ar kuka tace Dr dan girman Allah kitaimaka kiciremin cikin nan wlh bana sonsa. Dr xeey xeey fara’ar da take fuskarta tagushe cikin fad’a tace akan wane dalili zaki cire ciki idan ke bakyaso toh mijinkifa? ni gaskiya bana zubar da ciki. Rauda cike da tashin hankali tace Doctor yadda Allah yataimakeki nima kitaimaka min wlh bana son cikin nan idan nakoma da shi gida bansan da wane ido zan kalli iyayena ba. Doctor da tunda Rauda tafara maganar tazuba mata ido tana kallonta cike da 6acin rai tace idan na fahimceki kina nufin cikin nan na shegene baida uba ko? Rauda shuru tayi batace komai ba. ganin haka yasa Doctor tacigaba da cewa toh bari kiji ni bazan ta6a zubar miki da cikiba k’ara ma kiyi hak’uri kihaife abinki ammah kuma kin cuci abinda yake a cikinki domin kin samesa ba tahanyar da tadace ba, k’arama kiyi hak’uri kihaifesa domin kar zunubin yak’aru dan haka tashi kije nidai nabaki shawara haihuwar shi zai fiye miki. Rauda dakyar tamik’e jiki ba kwari tafito daga office d’in doctor. tana fita kallon zarah tayi nan hankalinta yak’ara tashi sai alokacin taji wata irin kunya tsaye tayi takasa k’arasawa wajen da zarah take tsaye. ganin haka yasa zarah tamik’e cikin sauri ta isa inda Rauda take cike da tashin hankali tace yaya Rauda lafiya naganki a haka me yake faruwane? Rauda hawaye suna zuba daga idonta dakyar tabud’e baki tace zarah ciki gareni. Zarah a firgice taja da baya cike da tashin hankali tace yaya Rauda ciki kuma? Rauda gyad’a mata kai tayi tare da mik’a mata takardar da doctor tabata, jikin zarah yana kyarma ta amsa taduba, aiko nan tafashe da kuka tace yaya Rauda meyasa kuka za6a ma kanku irin wannan rayuwar? meyasa kuka za6i son abun duniya kuka 6ata rayuwarku, kingani ko yanzu gashinan kiyi cikin shege cikin da ke kanki bakisan ubansaba kun d’auki alhakinsa idan kika haifesa me zaki ce masa? Rauda da take kuka dasauri tarik’o hannun zarah tace zarah wlh nima bansan ya zanyiba yau ne karo nafarko da nafara nadamar abinda nake aikatawa dan Allah kizo muje murok’i wata doctor d’in tacire min shi. zarah fizge hannunta tayi daga rik’on da Rauda tayi mata tana ja da baya tare da girgiza kai, cikin kuka tace yaya Rauda badani za”a had’a bakiba ayi kisan kai meyasa kikeso kikashe ran da baida alhakin kowa saima shi da yake da naku? kiji tsoron had’uwarki da ubangiji ga laifin zina ga na kisan kai, kituna tsayuwar ki gaban Allah ranar gobe k’igama, baki tsoron garin zubar da cikin kije kirasa ranki? Yaya Rauda wani irin nadamane taji ya zo mata nan tak’ara fashewa da wani sabon kukan tare da rik’o hannun zarah da itama take kuka tace zarah nafasa zubarwa wlh nayi nadamar abinda na aikata a yanzu kuma ba zan zubar da cikinba. zarah cike da jin dad’i tace nagode sosai Yaya Rauda da kika fahimceni. Yaya Rauda d’an tsagaitawa tayi da kukan da take tace saidai kuma inaso kiyimin taimako guda. zarah dasauri tace Yaya Rauda kifad’i abinda kikeso zanyi miki. Rauda tace inaso kafin muje gida kifara rakani wani waje zarah da mamaki take kallonta tace yaya Rauda ina zamuje? Rauda rik’o hannunta tayi tace muje kawai zarah. zarah batayi musuba tabi bayanta. mai adaidaita tatsaida musu tafad’i anguwar da za’a kaisu zarah dai shuru tayi tana mamakin inda zasuje. Rauda ce tadinga gwada ma mai napep hanya bayan sunzo anguwar, bakin gate d’in wani gida aka safkesu nan Rauda tabiyasa kud’insa sannan tayi Knockin d’in k’ofar maigadi ganin Rauda ce yasa yabud’e saboda daman ya saba ganinta nan suka shiga ciki, ita dai zarah binta kawai take cikin wani parlour suka shiga da sallamarsu ammah bakowa ciki Rauda kallon zarah tayi tace Zarah shigo muzauna, zarah girgiza kai tayi tace a’a yaya Rauda nan gidan wanene. Rauda ganin zarah duk ta rikice yasa tace kar kidamu bawani abu inaji suna ciki kizo kizauna. Zarah a tsorace tabi Rauda suka zauna nan Rauda tad’auko wayarta tayi kira itadai zarah kawai ji tayi ta ce gani cikin gidan ka sannan takashe wayar. zarah a tsorace tace yaya Rauda wai nan gidan wanene me zamuyi? Rauda har ta bud’e baki zatayi magana sai ga wani mutum ya fito daga cikin gidan, da kallo duk suka bisa fuskarsa d’auke da murmushi yazo yazauna d’aya daga cikin kujerun d’akin tare da washe baki yace baby daman kina tafe baki fad’amin ba? kallon zarah yayi da itama take kallonsa yace sannu ‘yanmata halan ke sister d’intace naga kuna kama? duk tambayoyin da yayi musu babu wanda yatanka mushi sai ma ido da suka zuba masa. Rauda fuskarta a d’aure tace Alh umar nazone infad’a maka ina d’auke da cikin wata biyu. nan fara’ar da take fuskarsa tagushe yace ciki kuma rauda? Rauda hawayene suka fara zuba daga idonta tace eh ciki. dariya yayi irin ta rainin wayau yace lallai Rauda toh garin yaya kika bari har ciki yashigeki? toh wai ma wanene yayi miki cikin? Rauda da mamaki take kallonsa tace Alh Umar in bakaiba wanene nake huld’a da shi? ai kaine uban d’an saisa nazo nafad’a maka. d’aure fuska Alhaji umar yayi tare da daka mata tsawa yace ke banason sakarci kingama zuwa kinbi ‘yan iska sannan kizo kice d’a nane, Rauda cikin kuka tace wlh d’ankane Alh umar a harzuk’e yamik’e tsaye yace toh bari kiji duk wanda yatsaya miki a garin nan bai isa yasa in amshi cikin kiba a matsayin d’ana kije dai kigano uban cikinki dan haka kutashi kufitar min daga gida. Zarah ranta ya 6aci sosai jin kalaman da Alh umar yake jifan yayarta dasu ga Yaya Rauda kuka kawai takeyi, cikin 6acin rai tamik’e tsaye tare da nunasa da yatsa tace kai malam kar karaina ma mutane wayau kana nufin k’arya akeyi maka ba cikin naka bane? ai ni wlh naga wautar yaya Rauda da ta iya ba jakki irinka kanta, ni ai ko a k’afa aka d’aura min kai sai na kwance. Alh umar ransa ya 6aci sosai cikin fushi yake ke karkinemi kigaya min magana wlh yanzu insa ad’aureki ni nace tabani kanta ba kwad’ayi yaja mataba? zarah cikin d’aga murya tace kai kar kasaki kak’ara d’agamin murya kuma idan bakasa and’aureniba toh ba’a haifekaba. Alh Umar a zuciye yad’aga hannu zai mari zarah cikin zafin nama zarah tagoce. yaya Rauda da take zaune tana mamakin yadda zarah take balbala fad’a tabbas tasan ankai zarah k’arshe domin zarah tana da hak’uri sosai, da sauri Rauda tamik’e tare da rik’o zarah tace zarah ki kyalesa tunda dai har ya k’aryata alhali kuma ya san gaskine toh yaje shi da Allah. Zarah fizge hannunta tayi tace yaya Rauda kikyaleni ya za’ayi mutum yana akan gaskiyarsa a tauye masa hak’i wlh dole yakar6i cikin nan. Alh umar dariya yayi yace ke yanzu har kina tunanin zan kar6a ko? toh muzuba agani wanene zai ci nasara. Rauda cikin kuka tace umar *LAIFI NANE* da na amince na mallaka maka kaina ammah inaso kasani ba zan d’auki matakiba saidai kaje kai da Allah domin shine kad’ai zai kwatarmin hak’k’ina kuma kai shedane kaine karabani da budulcina kayaudare kace zaka aureni, wlh a yanzu na tsaneka kaje kawai rik’o zarah tayi tace zarah wuce mutafi zarah har ta bud’e baki zatayi magana Rauda tadaka mata tsawa tace kiwuce nace miki! Zarah ba dan tasoba tabi bayan Rauda suka fita suka bar Alh umar a tsaye cike da takaicin bak’ak’en maganganun da suka yada masa. Ko da suka fita zarah kallon Rauda tayi cikin 6acin rai tace haba yaya Rauda ya za’ayi kina da gaskiyarki sannan kibari atauye miki hak’i. Rauda cikin kuka tace zarah ina kokwantone domin bansan ainahin cikin na waneneba. Zarah cikin tashin hankali tace ban fahimcekiba yaya Rauda. Rauda share hawayen fuskarta tayi sannan tace zarah ba zan 6oye mikiba wlh mutum biyune kawai nasan ina mallaka ma kaina. zarah tace yaya Rauda wannan wace irin rayuwace toh wanene gudan? Alh munir ne wlh bayan su bana huld’a da kowa. Zarah tace toh yaya Rauda me zai hana shima muje wajensa? Rauda jinjina kai kawai tayi nan suka samu mai adaidaita Rauda tafad’a masa anguwar da zai kaisu…….. _Comments_ *nd* _Share_ _Sis Nerja’art✍_ _*YARIMA SUHAIL*_ _*Written By~Sis Nerja’art*_ _*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_ *INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®* *[onward together]* *{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }* THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK *JUST GIVE US FOLLOW….✔* _Jinjina agareku sis Mugirat marubuciyar *KISHI KO HAUKA* da sis Ummie Adnan marubuciyar *HAUWA JIDDAT* gaskiya inajin dad’in novels d’inku basirarku da k’wazonku suna burgeni kunyi namijin k’ok’ari a wajen rubutunku Allah yak’ara basira da zak’in hannu acigaba da sambad’o mana, *KISHI KO HAUKA DA HAUWA JIDDAT* duk Wanda bai karantaba anbarsa a baya dan haka kugarzaya kukaranta, muje zuwa_ _~Gareka *DR ZAIN* ina jin dad’in novels d’inka Allah yak’ara basira da zak’in hannu, nagode sosai da kyautan pages d’in da nasamu, *’YAN GUDUN HIJIRAH* labari maicike da darussa duk wanda bai karantaba anbarsa a baya~_ _*Yau page d’in nakune Mummyn Afrah nd Meena Abbah Wlh ina ji daku irin sosai d’innan, jinjina agareku marubutan *NI DA MIJIN YAYATAH gaskiya kunyi namijin k’ok’ari a cikinsa Allah yak’a basira da zakin hannu I heart u all*_

Back to top button