Hausa NovelsYar Zaman Wanka Hausa Novel

Yar Zaman Wanka 17

Sponsored Links

Aikuwa dai sai na shashshafa gidan nan da hannu na, a saka a baka ai ya fi a rataya, ko da a ce baka da rabon zama a cikin waɗan nan gidajen a duniya to kafin mu je aljanna mu samu rabonmu gwara dai na taɓa in ji, ai da hanau gwara mannau” Cewar Inna tana dosar wajen, hannunta ta kai jikin ginin ta shafa shi da hannu biyu kamar wacca ta samu ka’aba har da jingina fuskarta a jiki ta goga fuskarma a jiki hagu da dama.

“Na taɓa ka da alkairi gidan ƴan gayu” Tana ƙara shafawa. Haka ta rinƙa bin wurin tana ganin ginin tana gyaɗa kai alamar mamaki.

“Oh ni ƴasu mutane masu kuɗin nan ko a ina suke samun kuɗaɗe haka su yi ta baje hajarsu a duniya son ransu, ko kuwa rijiyar haƙo kuɗin garesu irin wannan gida, to mu da bamu dashi haƙuri ya ganmu, dan ma dai da daɗi saboda Malam ya faɗa mana cewa ko a lahira sai talaka ya riga me dukiya shiga aljanna, yo kai da baka da kuɗi ina ka ga tarin tambayoyin da za ka amsa dangane da ina ka samo kuɗi kaza, ta wace hanya ka kashe su” Ta faɗa tana kama haɓa har lokacin kaɗa kai take kamar ƙadangaruwa. Leƙa cikin get ɗin ta ɗan yi daga inda take tsaye ta yi dogon wuya tana so ta ga ko za ta hango me gadi, amma babu abin da take hangowa sai tarin fulawoyi masu matsanancin kyau.

“Ni Azumi da a ce zan samu shiga cikin nan ɗin ma ba tare da na zauna na yi rayuwa a ciki ba, da wallahi tallahi iya hakan ma na godewa Allah kuma na ji daɗi, yo in ban shiga na gani ba na kashe ƙwarƙwatar ido na ba me aka yi da maza, kawai shiga zan yi komai ta fanjama fanjam” Ta ce tana takawa a hankali cikin sanɗa ta durfafi get ɗin, tana shiga sai ta ga ashe ma babu abin da ta gani a waje motoci ne gasu nan wasu a lulluɓe wasu a buɗe.

“Ikon Allah na kwance ya faɗi wato dai a duniya ma akwai aljannar duniya, lallai masu gidan nan kun huta amma duk da haka ba za mu shiga sahun ƴan Allah baku mu samu ba” Ta faɗa tana leƙa cikin wata mota tare da shafawa.

“Tabbas idan na koma garinmu duk mai son in bashi labarin gidan nan sai ya biya ko da kuwa Malam ne, Tasalla kwa ko a da kuɗinta bata da rabo dan ba zan bata labarin nan ba” Ta faɗa tana ɗaga kai sama tana ƙarewa benen kallo ga wasu hazbiya a saman suna ta waricinsu. Haka ta rinƙa kutsa kai cikin farfajiyar gidan tana ta kallo abinta.

“Ni ai yau ta waru wallahi yawon buɗar ido dai da wasu ke biyan kuɗi suna hawa jirgi su tafi ƙasashen waje, to ni ga nawa yawon buɗar idon a nan babu ko sisina bare taro, yo da na san akwai gidaje masu kyau kamar wannan a kusa da gidan Halima ai nan da gidan Halima babu nisa da nan zan ke tahowa in na gaji da zaman gidan, da dai in ke zama da wannan Imiranan me baƙar zuciyar tsiya ga mugunta ai gwara in zo nan in wanke dauɗar idona” Ta faɗa tana bin bayan gidan daga can ciki.

“Anya kuwa Azumi kya ke fitowa kina barin Imirana daga shi sai Halima a cikin gidan, bakya ganin wani abu zai faru” Wani ɓangare na zuciyarta ya tambayeta.

“Kuma fa da hakan ne wallahi, kar in je in fito yawon buɗar ido shi kuma ya je ya buɗe ƴar mutane a gida ya je ya rugurgujeta son ransa ya farke mata ɗinki a shiga uku” Ta faɗa a fili tana saurin juyowa dan ji ta yi ma kallon ya fita daga kan ta duk da akwai Ashrof a gidan kuma ƴan barka na zuwa amma sai take ganin Imran zai iya aikin Ashrof wani wuri dan ya cimma burinsa.

“Dole in yi maza ma in koma gidan dan yanzu komai ma zai iya faruwa amma in ina kusa dolensa ya ɗauki dangana ko ba ya so” Ta faɗa lokacin ta dawo hanyar fita, tana shirin ficewa ta hango wani wuri na shaƙatawa an jera faraen kujeru ga falawoyi kewaye da wurin.

sakin baki ta yi ya layar me tafiya tana dosar wurin a ranta tana cewa.

“Ai kuwa yau sai na ɗosana ɗuwaiwukana a kan kujerun nan” Haka ta ƙarasa wajen ta zauna a kan kujerar har da ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana jin una ma nan gidan Malam ne da kuwa kakarsu ta daɗe da yanke saƙa.

Daga can wajen gidan wata mota ce ta faka a ɗan nesa da gidan, wasu maza matasa majiya ƙarfi suka fito su biyu, suka bar wanda ke tuƙawa a ciki.

“Kar fa ku yarda wani ya gan ku, ku bi a sannu, kun ga dai yanzu da sauran haske a gari magriba bata kai ga yi ba, dan dai ma unguwar masu hannu da shuni ce kowa yana cikin gidansa tun da shi me gidan ba ya ƙasar shi da matarsa, kuma Oga ya sanya an zo an ɗauke me gadin to ku tabbatar kun ɗakko tsohuwar nan kar ku bari a samu matsala, daga it sai ƴan aiki a cikin gidan, wallahi kar ku bari a samu matsala dan Oga ya ce ba ƙaramin kuɗi za a karɓa ba idan muka kawo masa tsohuwar nan domin Alhajin zai iya bayar da ko ma nawa ne idan ya ji an kama mahaifiyarsa dole ya bada kuɗin fansa idan ya ji za a aikata barzahu in bai bada kuɗi mai tsoka ba” Cewar wanda ke mazaunin direba cikin muryar dabanci

“An gama za mu yi duk yadda za mu yi mu kawo ta” Suka faɗa tare da juyawa suka nufi gidan, ta baya suka zagaya suka fara leƙen gidan daga wasu ƴan ƙofofi da aka yiwa gidan kwalliya da shi suna so su samo yadda za su shiga, duk da ba me gadi dan Ogansu ya sa an kama shi dan ma kar su zo ɗaukan tsohuwar su tafi ya kira me gidan ya faɗa masa, a kira ƴan sanda a sanar da su amma in suka ɗauketa kafin a gano hakan sun sanar masa sun kuma gargaɗeshi a kan kar ya sanarwa ƴan sandan. Hango Inna suka yi zaune kan kujera a wajen shaƙatawa ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya.

“Baaba ai ka ga tsohuwar ma a araha tana zaune ba sai mun sha wahala ba wajen shiga can cikin gidan”

“Wallahi kuwa ai kawai mu gewaya mu shiga gidan” Ɗaya ya faɗa, haka suka gewayo dan zuwa su shiga ta get ɗin gidan.

Inna da ke zaune ta ɗakko alkakinta ta gutsura ta mayar a ranta ta ce.

“Kin ga Azumi tashi ki tafi, kar masu gidan su fito ki shiga uku dan ba makawa sai yadda hali ya yi” Ta faɗa tana tasowa dan ta tafi.

“Kai dakata mu laɓe gata nan ma za ta fito daga gidan, tsuntsu daga sama gashashshe” Cewar ɗaya yana janyo rigar ɗaya suka dawo suka laɓe.

Inna da ke tafiya hankali kwance tana ƴar waƙarta
“Duniya ba wurin zama ba, da ka cuta ƙwara a cuceka, yau taka gobe ta ɗan…

Raf ɗin da aka yi da Inna da bata ma lura da samarin ba shi ya dakatar da ita daga ƴar waƙarta, bakinta suka danƙe da hannunsu suna waige-waige irin n marararsa gaskiya, cikin azama suka rinƙa ƙoƙarin kai Inna inda motarsu take, amma Inna sai turjewa take tana neman gagararsu. Idanun nan nata kwa ya fito ƙulu-ƙulu sai son tofa albarkacin bakinta take amma riƙon da bakinta ya sha ba na wasa bane.

“Kai Baaba wannan tsohuwa da shegen ƙarfi take, ka ga yadda take neman gagararmu” Cewar ɗayan yana huci kamar wanda yake kokawa da doki.

 

Back to top button