Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 54

Sponsored Links

*Talented writers forum*

*54*

A hankali ya tura kofa tare da sallama idanunta na bisa screen din TV taki kallon inda yake bare ta amsa , kusa da ita yaje ya zauna qamshin turarensa ne ya daki hancinta har zuwa cikin brain nata hannayensa me laushin gaske ya dora bisa nata hannayen taji Wani irin shock ba shiri ta d’aga Ido suna kallon juna, numfashinta ne ya fara sarkewa a hankali tamkar zata shide dakyar ta samu ta fito dashi kirjinta na sama da kasa alamun bugun zuciyarta ya karu Yana kallonta Babu ko keftawa gaba d’aya abubuwan da ke aiki a jikinta sun tsaya cak! Yau me zata gani shin mafarki take ko kuwa meke Shirin faruwa ne irin haka, ganin irin shock da ta shigane yasa Ayman jawota gaba d’aya zuwa faffadan kirjinsa suna Jin bugun zuciyar juna sai a wannan lokacin ne ta samu kwarin guiwar turesa daga jikinta Amma ya Kara kankame ta nan Wani kuka yazo mata a hankali ta furta ” me kakeyi Yaya Ayman shin ka manta ni matar Wani ce meyasa zaka shigo min gida haka ” mamaki ne ya kamasa da alama batama San da waye aka daura auren ba , kuka take wasu hawaye masu dumi suka wanke mata fuska gaba d’aya ta b’ata masa jallabiya da eyeliner da kwallin da ta saka, kankame ta yayi Yana bubbuga bayanta kamar Kara tunzurata yake , a hankali yakai bakinsa saitin kunnenta ya furta “sshhhh… Is ok am your husband, ki kwantar da hankalinki bazan taba cutar dake ba I’ll always be with you”

“Husband..” kalamar na yawo a brain nata toh ta Yaya meya faru shin kodai Aman ya rasu ne ko yace ya fasa aurenta shine Ayman ya tausaya mata ya aureta, sai yanzu ta fara tuna kalaman da inna da Kuma anty Balqis suka fada mata da Kuma kalmar Ummeey da sukazo dazu, kalaman kawu Bakura ne ya dawo mata tiryan tiryan lallai wannan shine babban kalubale da zata fuskanta a rayuwa shin ta Yaya zata iya zaman aure da mutumin da Bata kaunarsa Kuma baya kaunarta Basu kaunar juna Babu komai tsakaninsu sai mutunci da ganin girman juna ya Allah… Kuka take har yanzu yaki sakinta tana manne a jikinsa taci kukan har ta gaji Bai sake ce mata komai ba saboda baisan me Kuma zai ce mata shi ba gwanin surutu bane bare ya Bata labari, lumshe Ido yake Yana Jin radadin kukan nata har cikin zuciyarsa amma meyasa Basu fada mata abunda ya faru ba tabbas baa kyauta mata ba, Wani tausayin ta ne ya lullubesa ya Kara kankameta tana sauke ajiyar zuciya a hankali yasa hannu Yana shafa kananun kitson dake kanta Yana shakar qamshin hair spray nata Yana Jin Wani kasala na sauko masa, shiru tayi a yayinda take sauke ajiyar zuciya a jere tayi lamo a jikinsa tanajin bugun zuciyarsa ta rasa meke mata dadi a wannan lokacin, a hankali ta d’aga manyan idanuwan nata suka fada cikin nasa taji Wani irin yanayi tayi saurin saukesu ta koma ta kwanta a jikin nasa ” tashi muje kici abinci” girgiza kai tayi alamar bazata ci ba , Bai saurareta ba ya d’agata kamar wata yarinya ta fashe da kuka tana Neman ya sauketa yaki kulata har ya karasa Ina kulolin abincin suke ya sauketa bisa kujera, kulolin ya Bude na safe Yana nan kadan ta taba ga Kuma Wanda aka kawo dazun, tuwo ne da miyan egusi da ganyen ugu sai qamshi ke tashi ya dauki leda d’aya ya juye a plate ya zuba Miya. Ya Duba Babu ruwan wanke hannu ya tashi ya shige bedroom nata inda Wani qamshi na musamman ke tashi , ya shiga toilet ya wanke hannu Yana fitowa ya hangota zaune bisa kafet cikin falon murmushi yayi yaje ya dauko plate din ya dawo inda take ya gutsura yakai saitin bakinta ta dauke Kai hawaye cike a idanunta, girgiza mata Kai yayi ya sake Mika mata ta kauda Kai gefe yakai lomar a Baki ya tauna miyar tayi dad’i sosai ya dauki tissue ya goge hannunsa ya tura plate din gefe ya dawo kusa da ita suna fuskantar juna har suna Jin hucin juna ” me kike so sanyin idaniya ta ”
Kauda fuska gefe tayi Yana murmushi ya jawo fuskar ya hada da tasa hancinsu na gugar juna ta kulle idanunta batayi aune ba taji lips nasa bisa nata nan ya fara kissing nata a hankali zuciyarta kamar zata fito fili wannan ne karo na farko a rayuwa da Wani yayi kissing nata, jikinta yayi laushi ta kasa tabuka komai ganin ya samu galaba akanta Yana ya jinginar da ita da kujera ya cigaba da kissing nata iya son ransa idanunta a rufe sai hawaye Wani ke bin Wani, sun share 10 minutes a haka kafin ya sake don Kansa Yana sauke numfashi this is the best moment of his life, tashi tayi a guje ta koma bedroom nata ta saka key ta kulle ta jingina da kofa tana Wani irin kuka me ban tausayi shikenan yanzu ta rasa Aman kenan har abada, meyasa Aman zai mata haka meyasa su inna zasu bari a daura mata aure ba tare da izininta ba, kuka tayi me isarta.

Ayman ya Maida abincin ya rufe ya koma d’akinsa ya canza kaya ganin Isha tayi yasa ya fita zuwa sallah bayan ya dawo ya fitar da abincin ya kira Fauzan yace a Kaiwa maigadi, ya koma d’akinsa ya Bude drawer Yana Neman spare key wannan yarinyar Allah yasa kar ta hallaka kanta bazai taba barinta ita d’aya ba, ya gano key din ya koma part nata har yanzu tana nan a jikin kofar yasa keys tana Jin motsi ta tashi tana zare ido sai ganinsa tayi ya shigo d’akin tana komawa da baya, ya Maida kofa ya rufe yace ” muje ki nemi abinda zaki ci don bazan yarda ki zauna da yunwa a gidana ba ” shiru tayi Bata kulasa ba ganin yayo kanta yasa tayi saurin cewa “sallah zanyi ”
“Ok..tashi kiyi ”
Babu musu ta shiga toilet ta wanke fuskarta tayi alwala ta fito Yana zaune Yana binta da kallo me ban sha’awa, kallo d’aya ta masa ta dauke Kai ta dauki hijabi ta tada kabbara Yana zaune har ta idar ta linke kayan ta Maidasu, ” good..tashi mu tafi Kinga Nima am hungry yau tun safe banci komai ba ”
Hararinsa tayi kasa kasa Yana murmushi yace ” Babu kyau hararin miji ” turo Baki tayi ta fice daga d’akin yabi bayanta Yana kallon yadda take juya jikinta ya lumshe Ido Yana Jin Wani farin ciki na ratsashi.
Bisa kujera ta zauna ya kalleta ya marairaice yace ” indomie fa zaki dafa mana am hungry please” Yana tsinkar mata da zuciya da irin wannan abubuwan da yake mata, Bata sake magana ba tayi hanyar kitchen ya tashi kamar jela ya biyota a haka ta Bude kayan abincin da aka kawo mata ta fitar da indomie, Yana tsaye ya nuna mata Wani drawer yace” ki Bude can ko akwai abinda zaki bukata ” batasan lokacin da ta murguda Baki ba tace ” Ina ruwana da kayan matarka ”
Wani murmushi yayi da ya Kara bayyana kyaunsa hajjo tayi saurin dauke Kai don ba karamin kyau yake dashi ba bugun zuciyarta ya tsananta har ta manta me take ta juya masa baya tana sauke numfashi a hankali, ya taka yazo ya rungumeta ta baya Yana magana kasa kasa ” are you jealous Qalbee..”
“Qalbee…! Sunan ya mata dadi tana nanatawa cikin zuciyarta, Kansa ya dora bisa kafadunta tayi Wani irin ajiyar zuciya Ayman Yana Neman zautar da ita Yana son jefata cikin Wani Hali,kamar yasan tunanin da take ya sake hada jikinsu Yana shafa beards nasa bisa wuyanta gaba d’aya ya saukar mata da kasala sai faman lumshe Ido take ya fuskanci Hakan ya sake juyo da ita ta gaba suna fuskantar juna ya saka bakinsa cikin nata ya sake aika mata Wani zazzafan kiss har tsayuwa na Neman gagararta , a hankali ya zare bakinsa Yana kallon idanunta da sukayi laushi Yana murmushi a yayinda yake shafa fuskarta da yatsun hannayensa masu sanyi da laushi
“Kiyi hakuri am sure ba ni kika so aure ba from day one amma haka Allah ya kaddara Ina son kiyi hakuri ki karbi wannan kaddara da hannu biyu I promise you never regret it, ki dafa mana indomie am hungry zan jiraki a living room dina”
daga haka ya juya ya fice, ta sauke numfashi me karfi har yanzu jikinta a mace yake haka ta dudduba abubuwan da zata bukata ta dora tukunya nan da nan ta gama girkin kitchen ya dau qamshi ta samu wani fancy plate ta juye ta dauki fork guda d’aya sai ruwa mara sanyi ta shirya a tray sannan ta wanke abubuwan da tayi amfani dasu ta kama hanyar zuwa part nasa,

Yana kallon TVC news yayi cross leg hankalinsa kwance ta karasa ta ajiye masa ya kalleta yace ” Babu sallama Qalbee nah ” Wani irin Yarr..taji a jikinta ta juya zata tafi yayi saurin tare gabanta “Ina Kuma zaki tafi, kinzo kenan ai ke da part naki Kuma sai da safe ko kin manta yau ke amarya ce ” gabanta ya Fadi Ras shin meyake nufi da wannan magana, gashi ya hanata samun lokacin tunani ya hanata sakewa,
jawota yayi suka zauna bisa kafet ya jawo plate din ya Bude nan da nan qamshi ya mamaye wajen ” Qalbee nah ba dai iya girki ba , u know ban tabajin Wanda ya iya dafa indomie ba kamar ki ” tabe baki tayi dama ashe haka yake magana, kamar yasan tunanin da take yace ” I can do anything for you zan Miki abunda ban taba yiwa kowane mahaluki ba a duniya” ya fara Bata a Baki taki karba ya shagwabe fuska Wanda shi Kansa baisan ya iya ba yace ” please Qalbee ki taimaka kici wallahi idan Baki ci ba bazan iya ci ba gara na kwana na yunwa ” lumshe Ido tayi ta rausayar da Kai gefe ya sake matsowa kusa da ita ” please don Allah ba don halina ba ” a hankali ta Bude bakin ya saka mata ta fara taunawa a hankali ya fara ci Yana Bata Yana ci har suka gama , murmushin Jin dadi yayi ” thank you Allah ya Miki albarka my wife” Bata amsa ba ya tashi da Kansa ya tattara ya Kai kitchen, tana zaune ta kasa tashi jikinta yayi la’asar ya gama kasheta da abubuwan da yake mata brain nata Bai samu damar yin tunani ba ya dawo ya sameta da sallama ya shigo ta amsa ciki ciki ya dawo kusa da ita ruwa ya zuba a cup ya Mika mata ta karba tasha, d’akinsa ya koma yayi brush ya dawo tana nan zaune murmushi yayi Yana Jin Wani farin ciki, tashi tayi ” Ina Kuma zakije ”
“Wanka zanyi ” ta furta cikin salon yanga tamkar Batason yin magana, jawota yayi ta fada jikinsa ya rada mata a kunne ” muje na Miki wankan ”
kukan shagwaba ta fara masa Yana tsokanarta cak ya d’aga ta yayi d’aki da ita Bai direta ba sai cikin bathroom nasa ya juya ya ja mata kofa Yana dariya.

Back to top button