Hausa NovelsMatar So Hausa Novel

Matar So 26

Sponsored Links

Kallonshi nayi ina jin zafinshi da haushinsa kasa nayi da kaina nace.
“Na koshi.”
Tura min abincin yayi zai mike, da sauri nace.
“Kayi hakuri zanci.”
Saka spoon ɗin nayi hannuna na rawa na ɗibo zan kai bakina ya riko spoon ɗin zuwa bakinshi, haka nasake ya kuma juye abincin bakinshi take na fahimci abinda yake nufi ina ɗiba zan kai bakinshi, falauu Aneesah ta shigo babu sallama.
Bai ɗago ba kuma bai fasa karɓan abincin ba, sai da tazo tasa hannunta ta ɗauki kular, ya ture hannuna ya kama hannunta, ya amshi abinci. Naga tashin hankali a duniya ban taɓa sani mutum mai shiru da rashin magana wutane ba sai a lokacin yana ajiye kular ya mike da hannunta wallahi sai danaji karan kashin hannun,  zuɓewa tayi sumamiya take na fasa ihu nayi baya jikina na wani irin rawa, babu tausayi babu komi yajata, har tsakar falon da kowa yayi cirko cirko, ya wurgata ya shigo falona ina ganinshi na fara ja da baya, jikina na rawa.
“Zoki karasa bani abincin ban koshi ba.”

Ya faɗa kamar bashi ba, girgiza kai nayi nace.
“Bazan iya kaci kawai.”

Mikewa nayi yayi, nayi bayi tsabar na razana dashi saura kiris nayi karo da show glass ɗina na turaruka, yayi maza ya rikoni ajiyar zuciya na sauke tare da tafiya baya zan zuɓe, na tsorata sosai dan ko dukar da yayi min bai sani jin tsoronshi ba kamar karya hannun Aneesah kamar ba Y’ar uwarshi ba.
Dauka na yayi ya kwantar dani akan kujera ya tashi, ya ɗauko ruwa akaramin firij ɗin falona ya buɗe ya watsa min, firgit nayi na mike naja da baya zan hantsila, ya rikoni sosai, yace.
“Ki fahimci abu ɗaya, ni bana komi sai da dalili baki min komi ba akan mi zan taɓaki, kuma nayi alkawarin bazan taɓa barin wata taci mutuncina a gaban kowa…”
“Mi yasa zuciyarka bata iya sarrafa fushinta?”
“Sabida ni mutum ne kamar kowa, bana son ka taɓa ni indai ina kiyayye maka.”
Kuka nasaka tare da maida kaina nayi ina kuka, ya zuba min ido.
“Gaskiya ina jin tsoronka.”.
“Ba damuwa tunda ni bana tsoronki kawai ki bar kukan ya isa haka ki shirya mufita.”

Kamar zance bazani ba sai nayi shiru, abincin da bamu karasa bakenan, ya fita nima na tashi na shige ɗakina na sako hijab ɗina, na fito, duk suna tsaye sunkuyar da kaina nayi sabida karfin kallon da suke min, na sauka da sauri ina jin mufida tana cewa.
“Mayya karuwa, me bin maza kawai.”
Uku uku na haɗa step ɗin na sauka, kallona yayi tare da guntun murmushi, nima na maida mishi na wucce ganin yayi gaba,

Shiru nayi ina nazarin, gidan Yunus da abubuwan cikinsa, bashine matsalata ba a yanzun matanshi ne matsala, dan bana ta mufida.

Yawo mukayi a garin kaduna, har gurin cin abinci ice cream da su snack, kan da chocolet munyi kayanshi kallona yayi, yace.
“Ko xaki gaidai da ummankine.”
Zaro ido nayi cike da murna har na manta ɓacin ran da nake fama dashi nace.
“Don Allah da gaske, kace wallahi”

Girgiza kai yayi, yana kallon hanya rike hannunshi nayi ina wani blush da fuskana.
Jan hancina yayi, na zaro ido nace.
“Karka cire min hancin.”
Hanyar unguwarmu ya nufa sai yayi parking ya kalle ni yace.
“Haka zamuje musu hannu rabbana.”
Ina hango gida, yana shirin min bukulu raurau nayi da ido ina niman kwallar da zan sauke mishi, dungureni yayi yace.
“Magulmaciya ba hanaki zuwa zanyi ba, kawai ba daɗi muje musu haka mu koma idam muka dawo daga zaria sai na kaiki ki wuni ko?”

Sunkuyar da kaina nayi tare da gyaɗa mishi. Jan motar yayi muka koma gidan mun sami Mahaifiyar Aneesah da kannenta sun zo, da me ɗori, sai ihu take.
Taɓe baki yayi yace.
“Umma alti ina wuni.”

Yanda ta tsare gida irin bana son tsurku.

“Yanzun Yunus gigin auren budurwa ce tasaka karya hannun Yar uwarka.” ta wurga mishi tambayar.

Juyawa yayi ya kalleni ganin inata gaishesu basu amsa ba sai kallon banxa suke min.
Gyara muryanshi yayi ya kalle step ya sake kallona, kafin ya buɗe bakinshi na kama hanya. Ciki da mamaki suke kallona, har Mahaifiyar Aneesah zama yayi, akan ɗaya daga cikin kujerun falon yayi crossing leg, yayinda ya zuba hannuwanshi sama kujeran.
Ya lumshe idanunshi bayan ya ɗaura kanshi saman kujeran, yace.
“Malam mi gyara baka gama bane? Kuma ya,zaka shigo min gida kai tsaye idan nasaka aka kamaka waye da gaskiya.”

Mutumin bai iya bada amsa ba ya haɗa shirginshi yayi waje.

Yana jin fitar mutumin ya ɗago kanshi kallon Munira da Juwairiya yayi, irin kallon kuma ku bani guri.

Tura baki sukayi tare da tambayar Aneesah ɗakinta, faɗa musu tayi suka hauro sama gyara zama yayi ya saka hannunshi akan fuskarshi yace.
“Umma alti!!!” har sau uku, cike da mamaki take kallonshi, murmushin  takaici yayi ya mike ya tafi ɗakinshi ya kunna wayar Aneesah da ya kwace ya buɗe mata abubuwan da ta ɗauka namu, sannan ya kunna systerm ɗinta ya nuna mata,

Sannan ya kashe yana murmushi wanda zaka san *Da ciwo a rayuwarshi*  mikewa Ummaalti tayi ta kwalawa Munira da Jawairiya kira, da sauri suka sauko fita tayi har takai bakin kofa tace.
“Kayi kokari mada iya hannun ka karya, banyi tsamanin saki baxai biyo bayan laifin ba, duk abinds ka yanke dai daine.”

Tana gama faɗar haka tayi waje cike da kunya da ɗan danasanin, zuwanta da maganar da tayi mishi.

Ina zaune ya shigo har lokacin fushi nake dashi dan yaki kaini gurin Ummana, amma a haka alewar tsinke ne a bakina, yana shigowa na kauda kaina, tare da zare alawar lasa, sannan na maida bakin, sake cirewa nayi na lasa cike da jin daɗi, amma zuciyata ba daɗi sam, ɗaukar ledojin yayi ya fita dasu, ya kaiwa kowacce ɗakinta, a wulakance suka kalleshi.

Koda ya dawo ya mika min nawa na amsa nace.
“Allah ya kara buɗe.”

*Allah ya haɗamu gobe a zaria dan mai nasara ya zama abin tsoro*
[8/25, 3:00 PM] Real Mai Dambu:
*MATAR SO*

*MAI_DAMBU*
*Wattpad:Mai_Dambu.*
*HAZAKA WRITER’S ASSO*
(HWA)

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai….

Sadaukarwa Ga Yan grp ɗin Matar So….
Dedicater To Hafsat Abubakar

_Wannan buk ɗin hakk’in masu shine idan kinsan baki saya ba karki karanta, mai fitarwa kuma ki duba girman Alkawarin da kika ɗauka na cewa bazaki fitar ba, tunda nace idan kinsan zaki saya ki fitar na Yafe ba sai kin saya ba_

Back to top button