Matar So 2
Free Page..
*BOOK ONE…Page…02*
Hannunshi rik’e da k’ugunshi sai sinturi yake yana duba agogonshi, tare da kallon kofar get ɗinshi zuciyarshi na kona komawa yayi ya jingina da motar idanunshi nakan get ɗin, karan mota yaji ajiyar zuciya ya sauke sannan yakara kallon, agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunshi jingina kanshi yayi da jikin motar. Ya lumshe idanunshi zuciyarshi kamar ta ɗirko, me gadin gidan ya buɗe mata kofa a hankali ta zuro kafarta cikin nutsuwa take taku, karan takalminta yake ji kamar ana kwala mishi guduma,
Bata lura dashi ba sai da ta iso tsakiyar gidan a tsorace tace.
“My Toys luv.”
K’in buɗe runannun idanunshi yayi dan sunyi wani irin ja, wanda har maikon kwalla suke takowa tayi gabanshi tare da niman taɓa shi, cikin sanyi murya yaja da baya. Sannan yace.
“Ko zaki iya buɗe min…”
Da sauri ta nufi kofar shiga gidan, tunda ta buɗe yazo ya shige ciki, rufa mishi baya tayi har ɗakinshi tana zuwa ta fara wurgi da takalminta, sannan ta rigashi shigewa ban ɗaki dan akwai inner wear ɗinshi da yabar ta wanke mishi , amma bata samu damar wankewa ba. Yana saka kafa yabar garin itama ta zari gyalenta tabar gidan.
Gajiya yayi da zama ya juya yakalle bedsheet ɗin gadon take zuciyarshi tafara tafasa, mikewa yayi ya wucce ɗaya ɗakin acan yayi wanka, sannan ya kwanta a ɗakin.
****
Kallonmu Rahila tayi cike da takaici, sannan ta mike tazo tsakiyar mu da Rahima, tace.
“Kinsan anyi waje dani, a grp ɗin zubar gadi.”
Dariya muka saka mata sannan Rahima tace.
“Wai ke! Miye matsalar ki da shiga abinda bai dameki bane?”
Mikewa tayi ta shiga ɓalle rigarta, duk muna kallonta juya mana baya tayi bayan ta rike kugunta, a nutse tace.
“Wai shin bankaci mace bane? Ko ban isa ɗaukar wasu abubuwan bane?”
Juyowa tayi tana kare kirjinta, da sauri muka juyar da kanmu dariya tayi ta ɗauki rigarta tasaka.
” Kansacewarki cikakkiya ba zai hana ki iya samun matsala da mijinki ba koda abokiyar, zamanki ba kawai fatarmu mazaje na gari sai Rahila yaushe kika koma haka ne? Ni har tsoronki nake dan naga Idanunki sun buɗe.”
“Hmm! Maryam Sajida tambayeta dai yarinyar nan so take a kone tun bata tafasa ba” Inji Rahima.
Dariya tasaka mana har da tafa hannunta tace.
“Woww! Kenifa ban ɓaci ba.”
Haɗe baki mukayi dukkamu muka ce.
“Ai bamu ce kin ɓaci ba.”
Gyara rike wayarta tayi cikin nutsuwa tace.
“Ina karance karance kuma kunsan da haka, amma duk buk ɗin da nakaranta ina ɗaukar abun ɗauka na ajiye na banza, ina karanta buk na soyayya sosai amma kusan mi?”
Girgiza kai muka tare da ce mata.
“Sai kin faɗa.”
“Ban taɓa yunkurin karanta buk ɗin da zai tada min feelings ba, asalima idan akwai romance a cikin page tsallakawa nake, kusan sabida me nake haka.”
Kamar wasu dolaye muka sake kad’a mata kanmu.
Dariya muka bata tayi sosai sannan tace.
“Sabida bana son na rage karfin feelings ɗina tun a waje….”
Bata karasa bayaninta ba muka ja bargonmu, muka rufe kanmu dariya tasaka mana tace.
“Hegu munahuka, daga jin ina magana kunja kun rufe kanku wai ma kunsan ma’anar ayaba a yaren noɓel.”
Janye bargonmu muka, cike da son jin kwaf amma girman abinda zata ce yasa muna tsoron fitowar shi daga bakinta.
Haurowa katifarmu tayi, ta zauna a tsakiyarmu tace.
“Ma’anarshi, abin fitsarin Baby Khalif…”
Dira nayi daga dagon na wahe gadonta nace.
“Kiwa darajan Allah ki barmu muyi barci,”
“Eh nifa wayar muku dakai nake.”
“Ina wayar dakai anan, zaki lalata mana rayuwa don Allah Rahila jeki kwanta ubangiji ya kawo miki shiriya a cikin barcinki.”
Rahima na gama faɗar haka ta juya mata baya, ita kuwa mi zatayi mana banda dariya har da rike cikinta.
Dukka dukka shekarunmu basu wucce sha bakwai ba, da watannin amma rahila tasan iya karance karance, gyara kwanciyana, ina nazartan maganarta baki ɗaya bansan iya lokacin da na ɗauka ba, har barci yayi gaba dani.
…….. Buga mana kofa Mama Amarya tayi dakyar na buɗe idanuna, wanda suke cike da barci mika nayi tare da salati nace.
“Yau fa asabar ne! Ai sai abarmu mu huta.”
Kallona Rahima tayi bayan tashigo ɗakin nace.
“A ina kika kwana.?”
“Hmmm! Ai Allah ya takaita mana ne, jiya Asthmar Mama Amarya ya tashi ina kwance bayan kunyi baci sai ga, bakona yazo shine na tashi nashiga banɗakinmu naga baruwa, sai na ɗauki Pad da kuma pant ɗina na shige gurinta nasamu tana ta fama, gashi inhelarta ya kare, sai danaje na bugawa Malam kofa dan yana ajiye dasu, muna zuwa har idanunta sun fara hawa sama, kaii Allah ya isa mana tsakaninmu da Aunty Gausiya dan itace sanadin tada asthmar Mamanmu.”
Fita mukayi nida Rahila, har muna ture juna, muka samu tana sallah, a ɗ’akin mukayi sallar muna idarwa muka zuɓe a jikinta tare da sake kuka, rungumeta mukayi sai kuka muke, kamar wani abu zai sameta.
Shafa kanmu tayi, cikin nutsuwa tace.
“Ya isa haka! Yan ukuna bagani nan a raye ba. Toh ya isa haka ba kuka zakuyi addu’a zaku tayi min Allah ya kara min lafiya.”
Kallonta Rahila tayi cikin kuka, sannan tace.
“Wato da Rahima, bata shigo ba dashi knn sai dai musa mi mugun sako, Don Allah Mama ki daina saka damuwa a ranki.”
Shafa kanmu tayi cikin jin daɗi tace.
“Toh nadaina.”
“Toh karya mana ita zakuyi, Auta da yan biyu.”
Mikewa mukayi, muna dariya dan Babban Yayan Hayat na ya shigo rike da basket, zama yayi cikin nutsuwa. Mikewa nayi na amshi basket ɗin na kai kusada ita, gaisheshi mukayi ya amsa, yana murmushi yace.
“Mama ashe abinda ya faru knn? Amma ai an gaya miki ki rage iza damuwa cikin ranki, banda kwanarki na gaba Allah ya kawo Rahima ai da bamu kai labari ba, don Allah ki cire al’amarin Gausiya, a ranki ko muma Yaranki zamu sami nutsuwa.”
“Yayansu! Ai ba wai narike damuwarta bane kawai ciwone ya tashi min, amma zan kiyayye gaba.”
Lekowa Umma tayi tana kallonmu yanda mukayi rashe rashe, a cinyar Mama.
“Mmm! Zaman jiranku zanyi ne? Ko kun manta kuna da mkrantane. Ga wanke wanke can.”
Da sauri muka mike, zuwa waje aikinmu kowa ya kama, dan munsan da aikin.
Nike wanke wanke da shirya kayan karyawa, Rahila sharan ɗakunan Iyayenmu da wanke ban ɗakinsu da kuma namu, Rahima kuwa da ita ake girki, shima juya abin ake, turn by turn.
Karfe bakwai da arba’in muka gama kome, sai wanka muka shiga ni na tafi ɗakin Mama Amarya, Rahila ɗakinmu rahima ɗakin Umma, dan a kowani ɗakin muna ajiye kayanmu, cikin sauri muka fito dan karyawa Umma da Mama suna ɗaki.
Shigowar Malam yasa muka juya gareshi cikin nutsuwa muka ce.
“Barka da Safiya, Malam ya mi jiki ya zafi.”
Murmushi yayi cikin dattako ya zauna a kusadamu ya amshi cokalin hannun Rahima yace.
“Kice da hannu kamar Yan uwanki, yafi albarka.”
Kaman zatayi kuka tasaka hannunta, a cikin jollof ɗin taliya da dankalin turawa ta fara ci, kunshe dariyarmu mukayi dan tana da matukar tsaginagini( kyama ko kyankyami) amai ta fara niman yi muka ɗaga kwanonmu da saurinta taje gurin wanke wanke, tana amai.
Lekowa Umma tayi cikin ta ɗaga labule, tace.
“Amma ai kinsan baki cin abinci da hannu matukar ba tsarki kike ba.”
Kunyar malam yasa na tsame hannuna na ɗauki tea na shige ɗakinta, Rahila kuwa ko a jikinta sai ma murmushin da take dokawa mun bar mata abinci.
Cikin harshen zabarmanci Umma ke ɗaya mishi aiga abinda yasata amai, dariya yayi cikin hausa yace.
“Kinga kuwa nine na kwace mata cokalinta.”
Wanke gurinda ta ɓata tayi, sannan ta ɗauki tea ɗinta ta shigo ɗakinmu,
….. Takwas muka shirya tsaf muka fito, kallonmu Umma tayi muna sanye da unifoam, ruwan toka sai nikk’af da muka rufe idanunmu da shi.
Mika min hand out Umma tayi tace min.
“Yau bazan shigo ba, ki duba idan hajiya Falmata tazo ki bata sai kuma yan ajina ki kara musu, karatu inda suka tsaya.”
D’aga nikk’af ɗin nayi ina kallon Umma nayi idanuna cike da kwalla, bakina na rawa nace.
“Umma ni..”
“Ke nace, kishiga ajina ki musu kari.”
Kamar kazar da kwai ya fashe mata haka nafito, daga ɗakinta sallama muka musu….
**** Tsit kake ji banda Mai Nasara da tafita zuwa masalaci babu alamun akwai mutane a gidan, shima da ya dawo ɗakinshi ya wucce, me girkin gidan ya gaishe shi cikin girmamawa yace.
“Sir mi za’a girka,”
“Anything.”
Ya bashi amsa a takaice, sannan ya shige.
Shiru mi girkin, yayi cike da damuwa yasan yau kam sai yayi girki sama da kala goma dan kowacce mata sai ta tsiro da abinda zata ci,
Shigewa ciki yayi ya fara aiki, shigowar Aneesa, a gurguje tace.
“Mr Johson a haɗa min, abinci cikin gaggawa ina da meeting yau.”
“Ok Mah.”
Cikin sauri ya haɗa mata, makaroni da kayan ciki, wanda yasha curry da tymer, juye mata yayi ya kai gurin cin abinci,
Ya dawo ya cigaba da aikinshi.
A gurguje ta fito zata karya lokacin Mai Nasara shima ya fito, wave ɗinshi tayi da hannun sannan ta fara cin abinci wanda ta ɗiba a cikin ɗan karamin bowl,ruwan khal ta ɗiga a abincin sannan ta fara ci,
Ko cokali biyar batayi ba, ta mike gurinshi tazo tana goge bakinta da tissue ta ɗan rungume shi, sama sama tace.
“Barka da safiya, Mai nasara ina da meeting sai four zan shigo gida da fatan babu matsala.”
( Don Allah kuji wata rayuwa tana tambayarshi bayi da matsala)
Riketa yayi ya daidaita tsayuwarsu, sannan yasaka bakinshi a kunnenta yace.
“Ina da matsala, i need U.”
Agogon hannunta ta kalla da sauri ta raba tsakaninsu tana yake tace.
“My Dear, ina da meeting ne fa kayi hakuri na dawo sai nasan abin…”
“Jeki Allah yabada sa’a.”
Sake bashi wani kiss tayi ta juya da sauri tana cewa.
“Bye baby.”
(Ni a tunanina gatse yayi mata, amma dake sakarya ce ko a jikinta)
D’akin balkisu ya nufa, tana cikin uwar ɗaka, har can yabita tana kwance tunda ta idar da sallar asuba, ta koma ta kwanta, baiyi wata wata ba, ya haye gadon ya cire rigar jikinsa ya kwanta tare da janyota jikinshi.
Shiru tayi taki kulashi, haka yayita kiɗanshi da rawanshi ko tari batayi ba, kamar zai saka kuka ya kalleta yace.
“Laifin mi nayi mukune haka? Da kuke azabtar dani akan abinda Allah ya haltamin shiknn bazan sake zuwa, tunda na fahimci zina kuke son na fara.”
Mikewa yayi, ya sanya kayanshi ya bar ɗakinta, taɓe baki tayi ta tattara bargon ta shige banɗaki tayi wanka sannan tafito tana karamin tsaki, ita sam bata da lokacin……….
“`Abin dariya ko? Wasu matan sai addu’a“`
[8/25, 2:59 PM] Real Mai Dambu:
*MATAR SO*
*MAI_DAMBU*
*Wattpad:Mai_Dambu.*
*HAZAKA WRITER’S ASSO*
(HWA)
Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai….
Dedicater To Hafsat Abubakar
*Toh makaranta nan na kawo muku karshen free page ina da sauki kuma ina da zafi bazan cutar da kai ba kuma karkayi yunkurin cutar dani, Don Allah idan kinsan zaki saya ki fitar min Wallahi na yafe miki basai kin saya ba idan duniya da gaskiya ku duba girman Buk ɗin da Ciwo A rayuwata karku cutar dani, tunda nayi muku adalci duk wanda ya shiga hakkina Akwai Allah*
*Ga musu saya ga number acct ɗina Gtbank:0472282105 sai phone number:08130269641 na idan ka tura kuɗin sai kayi min screen short kuɗin Book 300# sannan zaku iya turo rechg card na MTN Nagode Allah yasa Mudace*