Matar So 13
Page…13*
” Zan zame maka haske rayuwa, koda bazaka soni ba bazan barka kayi maraicin so ba”
“Mhhh Mr nd Mrs Mandara gashi kuje gida ku cigaba da amayar da kaunarku.” mika musu takarda yayi, yana murmushi.
Juyawa Aman yayi yace.
“Zuwa anjima zaka ji sakona.”
Yana gama faɗar haka ya sunkuci matarshi yayi waje da ita, zuciyarshii fessss gani yake kamar yana barinta tayi motsi babynshi ne zata faɗo.
Haka sukayita ratsa mutane har suka fito gurin motarshi, ajiyeta yayi a saman motar ya ajiye ta sannan ya buɗe motar, dawowa yayi ta ɗauketa yasakata a gaban motar, ya zaga gurinshi ya xauna.
A hankali yake jan motar dan kar wani abu ya samita, suna tafiya taga mi yalo tace tana so ya saya mata na dubu, ɗaya akaje gurin mi kosai ya saya mata, kafin su koma gida ya cika motarshi da ledoji (sabi sabi)
*****
“Mmmm! Wai dama ko zaki faɗa inda ya dace a saka yarinyar can ne,” yanda yayi maganar ce yaso bawa Mama kilishi dariya, tace.
“Banda abinka toh ka haɗasu gida ɗaya mana.”
D’ago kanshi yayi kaman wanda kunama ta harbe shi, girgiza kai yayi cikin rashin jin daɗi yace.
“Mama da wani, ido zan kalle sauran matana nace musu ga yarinyar da na auro musu a matsayin kishiyarsu, tunda ina da gida a g.r.a kusada gidan Ahmad zan kaita can.”
Cike da mamaki ta sake baki tana kallonshi, gyaɗa kanta tayi cikin nutsuwa tace.
“Hmm duk yanda yayi maka,”
Tsab ta lura auren ne baya so, kuma bazai ce haka ba shine ya ɓuge da ware wani gidan dan ajaye amarya can,
Mikewa yayi ya fita, ita kuma taje tasami Hajiyarsu da maganar shiru tayi cike da takaici tace.
“Auren ne baya so kuma zanga yanda za’ayi idan aka ɗaura sai ya sunce, barni da mutumin banza kawai.” Sababi tayi tayi kamar zata cire bakinta,
Hakuri Mama ta bata, dan tasan hajiya akwai faɗa,
****
Bayan sati biyu mun fito daga jarabawarmu ta karshe wanda ya ɗaukemu wata ɗaya, hotuna mukayi da kawaye nan muka mika musu ankon bikinmu, wasu suna ta murna wasu mamaki kaman yanda nayi a mkrntrmu haka Rahimah tayi itama, saura neco shi kuma daga gidajenmu zamu tafi.
Da wuri muka isa gida, rahilah muka samu da Umma da wasu daga cikin yayunmu gaidasu mukayi muma muka rama abinda tayi mana, ko kallon inda take bamuyi ba, abinka da mai juna biyu take idanunta suka kawo ruwa, kafin kace mi ta sake kuka, sororo Umma sukayi cike da mamakinmu taɓe bakin Rahimah tayi cike da jin daɗi tace.
“Maryam Sajida muma mun rama, haka kawai yarinya mu rabu dake lafiya, ki dawo ki tsiro mana da rashin mutunci wai daga miki magana kika sake mana kuka irin ga mayun nan.”
Dariya nasaka nace.
“Eh bata fita a sahunmu ba mi muka sani ita kuwa tasan komi, shi yasa zata mana haka.”
Mu biyunmu muke hiranmu muna dariya har yana fitowa tsakar gidan, aikuwa tasake kara karfin kukanta.
Haushine ya kama Umma ta biyo mu ɗakin cikin masifa, tace.
“Kun bani kunya, wallahi mi tayi muku haka da zaku ɓata mata rai, Allah idan kuka bari raina ya ɓaci zan baku mamaki, marasa kirki kawai.”
Fitowa mukayi, tana zaune takifa kanta da cinyarta tana kuka duk sai muka ji mun munzanta, tsabar rashin adalci mun gaza fahimtar Yar uwanmu mika mata fura da nono Umma tayi tana karɓa karnin nonon yasata fara amai, duk sai muka ruɗe bandasu Umma zuwa nayi na tsuguna a gabanta, ina riketa idanuna cike da kwalla nace.
“Sannu Hilah, mun saki amai ko.”
Ruwa Rahimah tayi na mika mata ta wanke bakinta sannan muka ɗagata,zuwa ɗakinmu ta cire kayanta kauda kai mukayi sabida kunya dariya tayi tace.
“Bazaku ga yanda babynku yasani kara zama super mama ba, ga kuma hot milk da nake samu akai akai, daga Yaren novel.”
Ai da sauri ku nime fita tace.
“Allah ku zo kubani riga, munafukai ai labarin dare nan na jiranku, Allah yara sai kunsha Anacondo na ratse da Allah zakuyi bayani da zabarmanci.”
Doguwar riga muka wurgo mata da gudu muka fita muna dariya, ganin haka Umma tace.
“Munafukai, wai mu zasu mannawa hauka.”
Komawa ɗakin mukayi tana lafe akan fado kallonmu tayi tace.
“Don Allah wayata da bag ɗina yana ɗakin umma, ina son kiran baby love ne.”
Rahimah ce tafita ni kuma na nemi guri na zauna, dama yaya lafiyar kura balle kuma tayi hauka, Rahimah na shigowa ta amshi wayarta kiran Iphone, a hankali take duba wayar har ta ɗauko nomber shi.
“Hello! Baby i miss u.”
Ta faɗa da wni narkakken murya, haɗi da lumshe idanunta.
“Hmm My cutie, ko nazo ne kiji ɗumina.”
“Hhh yi zamanka but i miss u badly,l.”
“Don Allah ki daina zautar dani mana.”
Wani fitinanen nishi tayi tare da cewa.
“Ai g…a..s..k…i..y..a n..a faɗa.”
Yanda take jan maganar sai ya baka mamaki.
“Ohhh My Allah don Allah nazone, kin ɗaga min hankali.”
“Hmm kawai kabarshi dan nasan yanzun kana gurin aiki.”
“A’a don Allah My Cutie cire min kayanki na ganki keda Babyna.”
“Ok rike wayar ko kuma ka kirani.”
Katse kiran tayi tace.
“Allah fita zakuyi dan hira zanyi da mijina, ɗazun suka bar garin nan sun nufi abuja, kuma nayi miss ɗinshi.”
K’in fita mukayi, dake mun shahara da gulma.
Ban ɗaki tashiga ta kwara ruwa akanta tafito duk gashin kanta ya jike, dan tacire rigar ɗaura zani tayi ta zauna a saman gadon ta warware zanin ta kurawa wayarta ido can kuwa sai ga kiranshi take ta shi ga ɓalle bra ɗinta mun ɗauka da wasa take sai da muka ga da gaske zigidir tayi, suka cigaba da hiransu taɓa tuni muka rufe ɗakin muka barta ita ɗaya, kaiii Rahilah ta lalace haka sukayita misayar kalamai masu nayi da tada hankali. Duk suka rikita kansu, kaman da wasa yace.
“Ganin nan zuwa.”
Kashe kiran tayi itama ta ɗauki rigarta tasaka, sannan ta kwanta.
***** karfe biyu da rabi sai gashi yazo tana kwance, cike da kewarshi ana ce mata yazo ta zura hijb mi hannu babu kaya a jikinta, tsabar jaraba idanunta sunyi kananu tace.
“Umma munyi baki, yazo ɗaukana.”
Dake dukda su Mama a tsakar gidan babu wanda ya kawo komi, sai ma fatan ta isa gida lafiya, dan ma sunga tana saurine umma taso bata wasu addu’o’i amma hana ta sunguci jakarta sai gurin mijinta,
Tun a kofar gidanmu aka fara tabargaza har suka isa gidansu Hindu na tsaye da hafsa suka shigo, bin motar sukayi da ido, ganinsu yasa hindu tace.
“Karuwa, an fara nuna haline.”
Dariyar karfin hali Rahilah tayi sannan ta ɗan gafe kafarta cikin niman rigima, tace.
“My Man nifa bazan iya tafiya da kafata ba.”
Kafin ya amsa Hindu tace.
“Irin gidan boka, ba dole ba an wanke an bashi yasha yar iska mara kunya.”
Dariya Rahilah tasake yi ta leko tace.
“Ai idan na wanke na bashi ya sha bam cika cikakkiyar yar gidan boka ba, da kanshi zaisha abukace zai lashe kayanshi muje kasha karka bar ko ɗigo, idan mace ta yarda dakanta gobe ta kwace mijinta a hannun Yar iska karuwa ni kuma zan bar mata mijinta har abada idan ta kasa kuwa nayi gaba dashi.”
Sunkutar ta yayi suka shige side ɗinta, hindu na ihu da cewa..
“Wallahi sai nayi ajalinki sai naga karshenku keda shi, munafiki da munafukar uwarshi duk sai naci kutum.”
Ranshine ya ɓaci zai fita rahilah ta dawo dashi, inda ta zare hijab ɗinta daga nan suka manta da hindu mahaukaciya.
****
“Zanga inda Mai nasara zai sake tusa wata mace dan gidan nan na zaman mata uku,”” Inji Farida.
“Kutt aure zai kara lallai mutuminn nan bai da kirki ko shine kuɗin da ya turo mana, lallai kuwa a ina ya tsinto matar.”
Inji Aneesah,
“Ina sani kuma,”
Suna tsaka da masifarsu Huda tafito sanye da legies ta ɗaura top akan yar rigar jikinta hannunta rike da goran dudu, dariya tayi dan tana jin hiransu tace.
“Allah yasa matar da zai aura, ta kawo karshen matsalarshi dan na lura baku da lokacin Daddy ni haja yayi min dadi fa.”
Rufa mata sukayi da magana cikin tsokana tace.
“Insha Allah sai kun zama yankallo kuna ganinshi zai auro min new mom danku baku da wani anfani.”
Tana gama fadar haka tayi komawarta ciki, duk wannan hayaniyar yana kallonsu dan shigowarshi kenan.
Mufida da take ɗakin karatu tafito ganinshi yasa ta tawo da sauri tace.
“Daddy wai aure zakayi.”
“Eh” ya bata ansa, a takaice.
“Wallahi ni bana sonta daga ganinta zata ɗauke mana kaine a ina zaka sakata.”
“A gidana na g.r.a.”
“Daddyyyyyy a wanan mansion ɗin zaka ajiyeta ita kaɗai bama damu ba, sabida baka sonmu wallahi na tsaneta kuma idan tazo dole tabar mana kai, i with not let her to take u away for us i hater her.”
Tana gama faɗar haka ta juta tabar gurinshi, dafe goshinsa yayi ya bar falon,
Wasa gaske matan mai nasara suka shiga zuga Mufida, da ta buɗewa Ubanta wuta, dan kar ya aure.
Tun abin bai damunshi har yakai, kanshi yayi masifar zafi tun ba’a a fara komi ba, Sun taso shi a gaba da fitina, sai da ya kare ranar ya fito musu namijin duniyarshi.
“Daddy ka fasa kawo wancan banza da kake son aurowa.”
Dake haka suka zugota ta faɗa mishi. Takaici da bakin ciki suka sashi, zare wayar chaji ya shiga tsula mata,ba kakkautawa sai da uwarta tazo da kanta ta kwaci yarta, tana mi kallon cikin idanunshi ita kanta sai da ta razana amma dan karfin hali tace.
“Dan zakayi aure sai akace ka kashe min Y’a.”
Dago hargitsatsun idanunshi yayi ya kafa mata, dole yasa tayi baya, tsawon shekara goma sha biyar bata taɓa ganin fusatarshi sama da yau ba, fita tayi tabar mishi falon da Mufida, tun kafin su isa side din uwar tace.
“Ni ki sake ni, wallahi sai nasashi ya mata dukan da yayi min, kuma dole yakaimu can ɗin inda zai sakata.”
Sosai Al’amarin Mufida yabawa balkisu haushi ta kifa mata mari ita ma, sannan ta tureta a gurin,
……..
“Hakuri shine mafita hindu matukar kika ce zakiyi faɗa karshe idan giyar amarci ya kwaso shi ya sakeki kinga ai kin faɗi ba nauyi.”
Shiru Hindu tayi tace.
“Hmmm yarinya karama ta haukata shi ya wucce.”
Haka suka rabu da Hafsa zuciyarsu ba daɗi dan itama ɓoye nata take amma ba wai tana cikin jin daɗi bane.
****
A ɓangarenmu anata hidima, ba kama hannun yaro.
Ina kwance idanuna a rufe, sai ganin Yar budurwa nayi a kaina tashi nayi na zauna nace.
“Sannu da zuwa.”
“Yawwa. Aunty Mom.”
Sam sai naji sunan yayi min girma, murmushi tayi sannan tace.
“Baki ganeni ba ko? Nida Daddy muka zo, yana waje munzo da tela ne ki zaɓi style ɗin da kike so.”
Duk sai na diririce na shiga ruɗu nace.
“Toh bari na kawo miki ruwa mana”
Fuskarta ɗauke da murmushi tace.
“Barshi kawai, muje.”
Fita nayi na ɗiba mata ruwa na kai mata, kurɓa ɗaya tayi ta ajiye tace.
“Muje ko.”
Fitowa nayi na kalli Umma nace.
“Hmm dama yazo ne, yace wai.”
“Toh uwar shiririta mi muka ce miki bismillah kuje.” Inji Mams knn,
Fitar da nikk’af ɗina nayi na ɗaura akan fuskana, zarewa Yarinyar tayi cike da mamaki tace.
“Lallai gurin Daddyn nawa zaki da nikk’af ai wannan abin an daina show ɗinshi, muje haka kuma baki tambayi sunana ba, kinga ni dake na damu sai da nace ya kawoni gurinki.”
“Kiyi hakuri hmm bansa ba fita haka ba.”
“Toh yayi…..”
Kuyi hkr Daga yau zuwa friday zakuna hakuri dani….
[8/25, 2:59 PM] Real Mai Dambu:
*MATAR SO*
*MAI_DAMBU*
*Wattpad:Mai_Dambu.*
*HAZAKA WRITER’S ASSO*
(HWA)
Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai….
Dedicater To Hafsat Abubakar
_Wannan buk ɗin hakk’in masu shine idan kinsan baki saya ba karki karanta, mai fitarwa kuma ki duba girman Alkawarin da kika ɗauka na cewa bazaki fitar ba, tunda nace idan kinsan zaki saya ki fitar na Yafe ba sai kin saya ba_
*BOOK 1*