Hausa NovelsKurkukun Kaddara Book 2 Hausa Novel

Kurkukun Kaddara Book 2 Page 4

Sponsored Links

_~*BossLadiesWriters*~_

_*KURKUKUN ƘADDARA*_

 

_The Prisoners E4_

*Daga alƙalamin Hafsat Bature*

~Middle step~

 

_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty._

wani sabon kukan ne ta kuma fashewa dashi ga matsanancin ciwon kai da ya takura mata, saboda tsabar kuka shatun jijiyoyin wuyanta sun fito ruɗu ruɗu kamar zasu fasa fatarta, hatta saman fore head ɗinta jijiyoyin ne….

A 6angaren su Haris kuwa da ke a cikin ɗaki, tun suna kuka har sun fidda rai da ƴan uwan su zasu rayu, Tun suna iya jiyo sautin shessheƙar kukansu har ta kai ga yanzu basu Iya jin komai, A bakin ƙofar ɗakin tsohuwa Tamira suka zuzzuƙuna, Zuciyoyin na tafarfasa Gabriel yasha kuka Idanuwanshi har sun ƙafe, Haka zalika Naufal da javed babu sauran mai walwala akan fuskokin su, Mubeen kuwa Dama ba ƙoshin lafiya ce da shi ba tun lokacin da aka dawo dashi kamar mutun mutumi ko magana bai Iya yi, Daƙyar ne yai tsawaicin kwana.

A firgice su ka ɗago Da idanuwan su Jin Dirar mutun a Cikin ɗakin su, jiki na kerma suka miƙe suna kallon shi ba su san wanene shi ba, ganin su da Salsabeel ya yi ba ƙaramin karya mashi zuciya su ka yi ba, tausayin su ne ya kama shi, Cikin sanyin murya ya soma yi masu magana.

“Ku kwantar da hankalin ku, Ba cutar da ku nazo yi ba, Nima ɗan uwan ku ne nasan ba ku ta6a gani na ba, Sunana Salsabeel Ni ɗa ne ga tsohuwa Tamira”! Duk da basa acikin hayyacin su sai da suka zazzaro idonsu akan fuskarshi.

Cikin shessheƙar kuka Haris yace”ƴan..uwan mu suna a cikin ɗakin tsohuwa Tamira, Zafreen Ta kashe mana su, Muna jin sautin kukan su sai dai mun gaza ceton su saboda ta datse ƙofar…..” tun kan ya kai ƙarshen maganar, Salsabeel Ya wuce da wani irin sauri Ya sanya hannu Ya daki Jikin ƙofar Nan ta ke ƙofar Ta buɗe.

A fujajen Ya faɗa Cikin Ɗakin Hankalin shi a matuƙar tashe Ya ke binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya, tun daga kan su azeeza dake kwance cikin Jini saman gadon Tamira har izuwa kan su Parveen da ke a sume ƙasa Babu kaya a jikinsu, Ga Uniform ɗin su yashe a kasa da ta Cire masu, Da ƙarfi Ya ambaci kalmar Inna lillahi wa’inna ilaihirraji”un runtse idon shi yai sosai tare da bugun iska da hannun shi daya dunƙule, Tsabar ƙunar da zuciyar shi ke yi mashi zafinta tamkar zai fasa ƙirjin shi, Zafafan hawaye ne su ka soma wanke fuskarshi Kamar ya haɗiyi zuciya ya mutu haka ya ke Ji.

“Ya Allah ka ɗauki raina In huta Idan ba haka ba zan kashe kaina ne” Muryar Batul ce ta janyo hankalin shi ga Kallonta, wa’iya zubillah Wani mugun bugu Zuciyar shi ta yi ganin mahaifiyar shi kwance cikin Jini, Kunnuwanta Biyu babu su Ga kuma gawar tsohuwa Zafreen A can gefe ɗaya, tangal tangal yai kamar zai kife ƙasa Da sauri ya tsayar da kan shi Yana faman fitar da huci mai ɗumin gaske, Ba dan Zuciyar Imani ba wlh da ɗaya daga cikinsu baƙin ciki ba zai bari Ya rayu ba. Daga Salsabeel ɗin har su Haris Allah ne bai nufa zuciyar su zata buga ba, Amma tashin hankalin da su ka fuskanta a wannan baƙar ranar baya misaltuwa. Batul sam bata lura da shi ba, Ta zama mahaukaciyar ƙarfi da ya ji kamar ma ta zauce, Agaban gawar mahaifiyarshi ya zuƙunna cikin rauni na murya ya furta”ya za ki yi mini haka mommy na? Meyasa za ki mutu ba tare da mun cimma burin mu ba, why ki ka tafi ki ka barni ni kaɗai a cikin wannan Duniyar mai cike da ruɗani”? Daƙyar ya ke iya furta maganar, cikin rauni na murya yayin da hawaye ke cigaba da yin sintiri saman kuncin sa, tun da ya soma magana Batul ta ɗago da runannun idanuwanta waɗanda suka kaɗa jawur dasu ta ƙura su akan fuskarshi ba ta Iya gane wanene ba saboda batasan shi ba, A halin da ta ke a ciki bata Iya Fahimtar Kalaman shi.

“Hada kai Aka kashe min Ƴan uwana ko! Kai ne ka kashe su wlh kaine”! ɗago wa yai tare da kallonta, Kafin yai yunƙurin furta magana, Batul ta daddage ta Haye saman jikinshi tare da dunƙule hannunta tadinga kai mashi bugu ta ko’ina tana faɗin Mugaye azzalumai wlh ba zamu ta6a yafe ma ku ba, Kun cutar da rayuwar mu, kun kashe mana ƴan uwa, wai laifin me muka aikata ma ku ne….? bata ƙarasa maganar ba kuka Yaci ƙarfinta, Rashin sani yafi dare duhu, sam bai ji komai da abunda ta yi mashi saboda hankalin shi ba akanta Ya ke ba, Yana akan gawar mahaifiyar shi, Bawan Allah Ya ji mutuwarta Fiye da tunanin mai tunani, Ya yi danasanin irin rayuwar da su ka ɗaukarwa kansu yanzu gashi ta mutu tana aikata sa6on Allah, Sai dai shi Allah gafurirrahim ne mai rahama mai Jin ƙai, Maganar su ta ƙarshe ya soma tariyo acikin kanshi.

“Salsabeel ko bayan ba raina inason yaran nan su ku6uta daga KURKUKUN ƘADDARA! Ka yi min alƙawarin nan, ka taimaka masu ko dan su isar da saƙon mu zuwa ga mutanan duniya, Bana so acigaba da aikata zalunci agidan kurkukun nan Ina mai jin takaici da baƙin Cikin ganin yadda ake tauye wa ƙananun yara haƙƙinsu na rayuwa, basu ji ba basu gani ba, An hana su more rayuwar su ta duniya, Ana kashe masu rayuwa a lalatasu A ƙasƙantar dasu kamar dabbo bi, sannan a kashe su, kuma su mutu a wulaƙance! Ka faɗa min Laifin me suka aikata da su ka cancanci Yin irin wannan rayuwar? Idan har kana so In yi alfahari da kai a matsayin ka na Jini na to ka cika min burina, Bana so Ganin mutuwa ta yasa zuciyarka ta raunata nafi so a lokacin da ka yi tozali da gawata ka ƙara Jin ƙwarin gwiwar aiwatar da umarnin da na baka, idan mutuwa ta risƙe ni a gidan kurkukun nan bana so kabar gangar jikina a gidan kurkukun ƙaddara Ka yi nesa dani kafin ka binne ni………” lokacin da tsohuwa Tamira ta yi mashi maganar sosai ya fashe mata da kuka yana faɗin zai yi duk abunda take so amma tadaina maganar zata mutu, ya ta ke so ya yi da rayuwar shi? Bashi da kowa a duniyar nan bayan ita, murmushi ta yi tare da ce mashi Kana da Allah sannan bayan shi ga ƴan uwanka nan suma basu da gatan daya wuce Allah da kuma kai, Don haka ka daina tunanin cewa sai da ni zaka Iya aiwatar da komai. Ni dai fatana Ku tarwatsa tarihin kurkukun ƙaddara, Azzaluman shuwagabannin da suka ƙirƙire shi ku tabbatar tun agidan duniya sun ɗanɗani kuɗarsu kafin su koma ga mahaliccin su bana so kubar hukuma ta hukunta su saboda duniyar nan acike take da marasa gaskiya idan kunga ba zasu baku goyan baya ba ku yi amfani da ƙarfin ikon da ku ke dashi wurin yi masu mummunan kisan da sai sun yi danasanin haihuwarsu da uwarsu tayi acikin duniyar nan, Kafin su mutu ku Azabtar dasu ta yadda zasu manta da duk wani jin daɗi da su ka yi a duniya, Idan har ku ka yi min hakan to zan jin daɗi, zan yi kuma alfahari da ku, Bayan ta yi mashi wannan maganar salsabeel yana kuka ya roƙe ta alfarma ɗaya kafin faruwar duk waɗannan abubuwan yace mata yana so ta kar6i musulunci akaro na biyu ta yi imani da Allah, Numfasawa tayi tare da ce mashi”Ba zai yiwu ba saboda Allah ba zai ta6a kar6ar tubanta ba ko da ta musulunci saboda ɗumbin zunubban da ta aikata sun yi muni sosai, Salsabeel ya yi ƙoƙarin fahimtar da ita ta hanyar Yi mata nasiha ya nuna mata cewa shi Allah gafurirrahim ne yana son bayinsa waɗanda su ka aikata zunubi suka gane kuskuran su kuma su ka tuba zuwa gare shi, daƙyar ya samu tsohuwa Tamira ta sake kar6ar shahada maganarsu ta ƙarshe data furta mashi”Zan je wurin Yaran can inaji araina wani abu yana faru a ɗakin su, Kafin na isa wurin su inaso ka yi gaggawar zuwa Ɗakin Madubin sihiri Ka canza ganin su ta yadda ba zasu fahimci abunda ke faruwa ba……wannan itace magana ta ƙarshe da tsohuwa tamira ta furta mashi kafin tabar wurin shi, akan hanyar shi ta zuwa ɗakin madubin sihiri Ya ga duk wani abu da ya faru da Angel kun ji yadda akai har yaje gare ta.

Cakumar Batul ya yi da hannun shi tare da janyota ta dawo saman faffaɗan ƙirjin shi, Rungumeta yayi da hannayenshi tamkar zai mayar da ita cikinshi, Hakan da yayi mata ne yasa ta sassauta kukan nata……

Tsoro da fargaban abunda idanuwansu zasu nuna masu ya hana su shiga Cikin ɗakin, Bayin Allah suna atsaitsaye Bakin ƙofar suna sauraron gunjin kukan da Batul ta ke yi.

Idan mu ka koma 6angaren Angel kuwa tun bayan tafiyar Salsabeel tana zaune cikin matsanancin tashin hankali, Da fargaban farfaɗowar Danish, Ba zato ba tsammani ta ga yatsun ƙafarshi na motsi, A gigice ta yunkura da niyar ta miƙe Sai dai kash ƙafarta ta ƙi bata haɗin kai, Wani irin tsami ta yi mata, a tsananin tsoroce take ja da baya tana kallon shi jikinta nata 6ari

A hankali Ya ware kyawawan idanuwanshi Akan ceilling ɗin ɗakin na tsawon daƙiƙa talatin kafin Ya yunƙura ya miƙe zaune…. Ta wutsiyar idon shi ya ke hango kamar mutun na motsi, hakan yasa shi yin saurin kai idon shi gare ta, unexpected idanuwan shi su ka sauka acikin nata, da wani irin kallo ya ke bin ta da shi, gani ta ke yi kamar bai dawo hayyacin shi ba.

Ya kasa tantance wacece ita? Saboda daskararren jinin da ke a jikinta, ta koma mashi kamar aljanna, ranta ne ya bata cewar ko dai ya dawo hayyacin shi? Wata’ƙil saboda munin da ta yi ne yasa bai gane ta ba, Cikin jin shakkar shi muryarta na kerma ta ambaci sunan shi”Da..nish..its me ur Angel” Ware fareren idanuwan shi yai sosai akan fuskarta, jin muryar da ya daɗe yana mararinta, ba zai ta6a mantawa da muryarta ba, A ruɗe ya motsa la66ansa tare da furta sunanta”Angel? Is that you”? Ita kanta batasan ya akai ta iya miƙewa ba, Tsabar farin Ciki da gudu ta nufe shi tana ƙarasawa gaban shi slowly ta zube saman gwiwowinta tare da faɗawa saman faffaɗan ƙirjinshi sosai ta rungume shi tana ku ka, Bai damu da ƙarnin jinin da ke a jikinta ba, sai dai zuciyar shi ta rikice ya shiga ruɗanin ganin canzawar da ta yi, Jikinta duk raunuka ta yi muni kamar ba Angel ɗinsa ba, Tunawa da Ƴan uwanta da kuma ƙurarren lokacin da ke gare su yasa tace mashi”Ka tashi mu tafi Danish ka kaini ɗaki, na bar su Azeeza suna jiran mu” shiru bai motsawa ba saboda ya rasa tunanin shi.

Bugun bayan shi ta dinga yi da hannunta Cikin shessheƙar ku ka ta ke faɗa mashi Ya tashi ya ɗauke ta suje ɗaki ƴan uwan su na acikin haɗari, ” daƙyar ta samu Danish Ya miƙe ɗauke da ita saman faffaɗar kafaɗar shi, daga ina ya ke a tsaye Ya 6ace bai dura a ko’ina ba sai A cikin ɗakin su, Tunkan ya sauke ta ta riga zame jikinta, Su Haris da ke a tsaye bakin ƙofar ɗakin tsohuwa, a ruɗe su ke kallon shi Musamman Gabriel yasha ruwan mamakin ganin Danish da idon shi Garas.

Muryar Angel na rawa ta soma ambaton sunayen su”Ha..ris..Mubeen..Naufal..Javed..”! akace labarin zuciya a tambayi fuska, Tun kan ma su yi mata bayanin abunda ya faru da gudu ta faɗa cikin ɗakin tsohuwa Tamira da ke a buɗe, Idanuwanta Azazzare take kallon Ƴan uwanta dake kwance ƙasa ba numfashi, Wata irin gigitacciyar ƙara ta saki ta fitar hayyaci wadda tayi silar faɗowar Danish dasu Haris cikin ɗakin sai lokacin su ka ga mummunan abunda tsohuwa zafreen ta aikata ma ƴan uwan su. Silar ƙarar da Angel ta fasa ne yasa Batul raba jikinta daga na salsabeel fuskarta jaga jaga da hawaye ta ɗago idanuwanta, tana yin tozali da Angel da gudu ta nufota tare da faɗawa saman ƙirjin ta suka ƙanƙame juna suna yin kukun zuci, Cikin shessheƙar kuka Batul ta labarta mata duk abunda ya faru bayan tafiyarta, Tasha kuka kamar ba gobe, ta yi fatan ace dukkan su ne suka mutu hada ita, gaba daya shirin su ya tarwatse taya zasu iya barin kurkuku Bayan ƴan uwansu duk sun mutu, Alƙawarin data ɗaukar masu bata samu cika shi ba, Ga danish ɗin ta ci nasarar dawo dashi sai da kash Ta faru ta ƙare, ƙaddara ta riga fata, Cikin raunatacciyar murya ta wanda ya gama sarewa da rayuwar duniya ta furta”Nashiga Uku na bani na lalace! Ya Allah zunubin me muka aikata mu ke fuskantar irin wannan mummunar jarabawar daga gare ka? Idan ba ka son mu, ka ɗauki ran mu mu huta, Mun gaji mun gaji Wayyo Allah na Na rasa Azeeza na rasa jemimah na rasa Deeja da sauran Ƴan uwana, To ni zaman uban me zanyi acikin duniyar nan wlh bazan rayu ba dole in kashe kaina……” Cikin fitar hayyaci ta furta kalaman, kamar mahaukaciya, ta juya da niyar ta je nemo makamin da zata halaka kanta dashi, Cikin zafin Nama Salsabeel Ya damƙi hannunta, tare da juyo da ita ta yadda zata fuskance shi”Meye ribar ki idan kin kashe kan ki? Dama ba sai da na faɗa maki Ba lallaine ku rayu ku dukan ku ba, Yanzu idan kika mutu Kinsan adadin rayukan da za’a cigaba da 6arin jinin su a gidan kurkukun nan? Idan har bamu lallashi zukatan mu ba mun kawo ƙarshen Azzaluman da suka cutar da ƴan uwan mu Duk wani ƙoƙarin mu ya tashi abanza kenan! Ya ku ke so inyi da raina ne? saboda ku na rasa mahaifiyata Ni kaina ashirye nake da in rasa raina in dai akan ku ne, Don haka kada wanda Ya ƙara Yi mana kuka Ya isa haka !! Mutuwa dole ce ko muna so ko bamu so, Kuma mutuwa sauƙi ce agare su saboda rayuwar duniyar bakomai bane acikinta face ruɗani, cike take da ƙalubale iri iri, ni banga amfanin yin kuka don wani ya mutu a cikinmu ba, Saboda Allahn daya halicce su wanda yafi mu sonsu shine ya kar6i abunshi, Sai sunfi jin daɗi fiye da na duniyar nan……’ sosai Salsabeel ya yi masu nasiha har saida yaga sun dawo hayyacin su tukunna Yace dasu babu isasshen lokaci su wuce su tafi, Danish Zai buɗe masu ƙofa, shi zai kula da gawawwakin Ƴan uwansu da suka mutu, Tun shigowar Danish ɗakin kusan suman tsaye yayi, saboda tsabar Kiɗima da ganin halin da ƴan uwan shi su ke aciki, Ya rasa bakin magana, Ya yi matuƙar girgiza da ganin yadda aka wulaƙanta rayuwar Ƴan uwan shi, Hankalin shi yai mugun tashi, Zuciyar shi tamkar zata faso ƙirjin shi ta 6allo saboda tsabar ƙunar da ta ke Yi mashi, Ya fusata Iya fusatuwa, ganin yadda yake huci ƙirjin shi na motsi ga wata narkakkiyar zufa dake wanke mashi fuskarshi, yasa Salsabeel yin saurin dakatar dashi ta hanyar yi mashi magana”Danish ka sassauta fushinka idan ba haka ba giant’s heart ɗin ka zata iya motsawa, pls ka ceci rayuwar su ku gudu daga kurkukun nan, duk wani abu da ya toshe maka kai, Unaisah zata yi maka bayani idan kun fita” daƙyar ya samu Danish ya iya sarrafa fushin sa.

Muryar Angel adisashe tace dashi”Ni bazan Iya tafiya in bar gawar su Azeeza acikin wannan ƙazamin ginin ba, inaso na cika masu burin su duk da basa araye zan fitar da gawarsu waje in yaso sai mu binne su a akan hanya, dan Allah ku taimaka min” Tana magana hawaye Na wanke fuskarta.

“Unaisah bamu da isasshen lokaci pls ku tafi kawai ku barni dasu zan san inda zan 6oye gawarsu” fashe mashi ta yi da kuka kamar zata haɗiyi zuciyarta, Hankalin Danish gaba ɗaya ya dawo kanta, tsananin tausayinsu duk ya kama shi.

“Bazai yiwu ku iya tafi da su ba! Kubar su a wurina zan tsaga ƙasa In binne su” acewar Salsabeel

Ataƙaice zan yi bayanin yadda su ka gudu daga KURKUKUN ƘADDARA, Angel ce ta goya Jemimah abayanta tare da sanya Mayafin kayan su da ta ɗauko acikin akwatin su, Gabriel ya goya gawar Azeeza abayanshi ya ɗaureta da mayafi, Naufal ya goya Parveen asaman bayanshi, Haris yaso ya goya Deeja abayanshi sai dai Salsabeel Ya hana shi gudun kada su ja ma kansu wata wahalar, Iya waɗannan kaɗai su ka ɗauka sauran Sun bar su awurin shi bayin Allah badan sun so ba, kusan mutun shida daga Ciki hada Deeja, Sarah, Eve, Yasmin, Rubina da Hibba, Danish ya yi ƙoƙarin yin amfani da sihirin shi wurin farfaɗo dasu, mutun ɗaya kaɗai ta samu damar tashi Hannah, a ƙarshe ya tabbatar masu da cewa Heart attack ne Yai silar mutuwar su, zuciyar su ce ta buga.

Ƙululun baƙin Ciki kamar su Zauce, Kafin tafiyar su Mubeen ma ya yanke jiki ya faɗi, Don dole suka haƙura da shi, Lamarin ya yi matuƙar gigitar da su.

Salsabeel ya yi masu alƙawarin Zai yi nesa da gawarwakin Ƴan uwan su, tare da ta mahaifiyarshi ba zai bari a wulaƙanta su ba, sun yi kukan rabuwa dashi, har magiya Angel ta dinga yi mashi akan ya zo su tafi atare da shi, amma yace masu ba zai iya bin su ba, su yi haƙuri su tafi idan Allah yasa yana da tsawaicin kwana zasu sake haɗuwa ne duk da yasan abune mai wuya ya rayuwa ko dan saboda 6arnar da suka aikata dole matsafan su azabtar da shi.

Rabuwar su ta yi matuƙar ta6a zuciyar kowannan su, a gurguje su ka nufi sashen makewayin su, Tsabar tashin hankali yasa Gabriel mantawa da zancen Ƴar uwar shi Gabriella da ke a cikin kurkuku, tun da ya ga mutuwar ƴan uwan shi prisoners, yasa wa ranshi dangana.

Suna shiga Cikin Toilet ɗin, Danish Ya datse ƙofar da sihirin shi, ya Janye tukunyar fulawar daga kan ƙofar, nan ta ke ta bayyana duk irin wahalar da suka sha ta ƙi buɗewa shi Bugu ɗaya yayi mata gaba ɗaya ta 6alle murfin ƙarfen ya dare biyu, Sun yi mamaki da al’ajabi yace da su”Ba zai bi su ba, zai tafi da Akwatin kayan su tare da back pack ɗin su, za su tarar dashi a bakin ƙofar da zasu 6ula idan sun ƙarasa” hankalin su bai kwanta da maganar shi ba, gani su ke yi kamar wani mummunan abun zai faru da su idan baya atare da su, ganin sun toge sunƙi tafiya yasa shi Kwantar masu da hankali, daƙyar ya samu su ka Zuƙunna ƙasa tare da kutsa kai ɗaya bayan ɗaya su ke shiga cikin ƙofar da rarrafe, Bayin Allah ga yunwa ga ƙishin ruwa, ga raɗaɗin da zuciyarsu ke yi masu, Ita kanta hanyar da suka biyo Wata uwar ƙura ga yanar girgizo da ƙwari sai hawan masu jiki su ke yi, Amma saboda rashin kwanciyar hankali yasa basu damu da su ba. Babu mai magana acikinsu saboda ƙunar da ran su ke yi masu, Angel ce tai ƙoƙarin tunasar dasu akan suci gaba da ambaton addu’o’in data koya masu ko sun samu sassaucin a wurin Allah, sun ɗau ki shawararta ahaka suka Dinga tafiya da rarrafe babu ƙaƙƙautawa, idan suka gaji su kan ɗan zauna su huta kafin su dasa da wata tafiyar, A ƙalla sun shafe tsawon awanni Takwas suna rarrafawa ba tare da sun kawo ƙarshen Ƙofar ba, a takure su ke Bayin Allah sun ga rayuwa gwiwowin ƙaffuwan su duk sun gurje sun sage, maƙoshinsu ya bushe ƙamas, tun suna ambaton ƙishir ruwa suke ji har sun gaji sun yi shiru………”

Prisoners

Sun ci baƙar wahala saboda tsohuwar hanyace da ta yi shekaru aru aru a datse ba tare da an yi amfani da ita ba, Muggan ƙwarin da ke a ciki sai ɗallinsu su ke Yi, amma saboda azabar raɗaɗin da zuciyar su ke yi masu yaci uban raɗaɗin harbin da ƙwarin ke yi masu yasa ba su ji, A makance suke tafiya basu ji basa gani, ga wani azababben zafi daya addabe su, kowan nan su ya haɗa uban gumi burin su kawai su cimma ƙarshen ƙofar, wani ƙarin tashin hankalin fitilun da ke a hannun su Batul hasken su ya fara ƙoƙarin ɗaukewa abunda basu ta6a yi masu ba, sun fuskanci matsanancin tashin hankali har sai da suka fidda rai da fita saboda ganin tsawon awannin da suka shafe ba tare da sun kawo ƙarshen ta ba, tun da suna rarrafawa Hannah ke kuka tana faɗin ƙaiƙayi ta ke ji a jikin ta, duk da halin da su ke aciki hakan bai hana su rarrashin ta ba akan ta yi haƙuri, a lokacin da ba su yi tsammani ba kwatsam! hasken fitilun hannun su Ya ɗauke ɗuff Innalillahi wani irin duhu baƙiƙƙirin ya mamaye idanuwan su, ko fuskokin su basa Iya gani, duk sunbi sun firgice saboda hanyar ta 6ace masu, Sunan Danish su ke ta kira a bakunan su, sun manta cewa baya atare da su.

“Danish ka taimaka mana, duhu bamu iya ganin komai, bamu san ya za mu yi ba,” abu biyu ya haɗe masu ga fargabar kar a rutsa su ga kuma Rashin haske gani su ke kamar Aljalinsu ne zai risƙe su awurin, Sautin koke koken su ne ya cika hanyar, sun kasa jurewa tsananin tsoro suke ji, Danish ka yi mana magana pls Ya zamuyi? Kada a rutsa damu, idan ba mafita ne ka faɗa mana…..” Cikin shessheƙar kuka Angel ta yi mashi maganar, kamar zasu yi hauka, sun rasa gane me ke shirin faruwa dasu ne?

“Innalillahi wa’inna ilaihirra’un! ya Allah kawo mana ɗauki! Wai ina Danish ɗin ya ke bai jin mu ne ko baya atare damu”! Naufal ne yai maganar, tsabar matsewar da su ka yi yasa wani bai iya motsawa daga inda yake balle har su iya gano inda Danish ɗin ya ke, Yadda kasan kifin gwangwani haka suka cunkushe, Bawan Allah Haris gaba ɗaya baya acikin hayyacin shi, Damuwar shi Deejarshi da ya rasa, Yaji ƙuncin da har abada bazai ta6a goge mashi ba, zuciyarshi ta yi mashi nauyi ga dukkan alamu wani mummunan ciwon ne ke shirin kama shi.

“Nifa ina jin tsoro ace Danish Ya canza ra’ayin shi na taimakon mu, zai iya komawa giant”! Gabriel ne yai maganar cikin rauni na murya
“Ni da ma na fidda rai da rayuwa, bansawa raina zan bar kurkukun nan araye ba.” Javed ne yai maganar cikin rauni na murya.
Suna Cikin Jimamin rashin Jin motsin Danish da fargabar me zai Biyo Baya.

Ba zato ba tsammani suka soma hango haske Yana kurɗaɗowa ta Cikin wata ƙofa Yana gauraye inda su ke zazzaune, Tsabar ruɗani Ya sanya su ka Waro idanuwan su waje Kamar ƙwayar Zasu faɗo ƙasa Sun kasa gane hasken menene ke isowa gare su.

Ba kowa ba ne abakin Ƙofar fa ce Garkuwar kurkuku shine ya buɗe ƙofar Kogon Bishiyar, Ashe ta inda zasu 6ullo Cikin kogon bishiya ne Mai girman gaske Wurin Ya wawake……..

Saboda rashin wadataccen haske basu Iya ganin shi da kyau, Cikin sanyayyiyar murya ya furta masu “You ave reached the door. Today, you will finally leave the prison of destiny, am happy for the first time that you will live a happy life. am ready to be your shield, and I will not let you get hurt by the lows and difficulties of life.”

Abun farin Ciki sai dai ba halin nuna shi saboda ba haka suka tsammaci zasu bar kurkukun ba, Ƴan uwan su duk sun mutu, duk irin burin da suka ɗaukarwa kansu na son Yin rayuwar Ƴanci gaba ɗaya ya tashi abanza, Cikin su goma sha takwas mutun goma suka tsira, ahakan ma basu da tabbacin zasu ƙarasa da ran su da lafiyar su ba tare da wani abun ya kuma faruwa da su ba, Kusan atare suka rushe da matsanancin kuka tamkar ana zare rayukansu, Kukan baƙin Ciki da ƙunci da raɗaɗi, Kuka mai matuƙar tsuma zuciya, Tsananin tsauyin su ne ya kama Danish A hankali ya ke ƙare masu kallo, Cikin sanyin murya yace da su Idan nace Ku yi haƙuri Na cuce ku, I can’t stop you from shedding your tears, except to encourage you to cry. It’s the only thing that can ease the pain in your heart.”

Fuskar shi ɗauke da matsananciyar damuwa yai maganar, kamar ya ƙara tun zura su aiko suka ƙara sautin kukan nasu, Idanuwansu duk sun kumbura Fuskokinsu sun yi jawur. ganin basu da alamun motsawa yasa shi matsawa tare da ruƙo hannun Angel dake goye da gawar jemimah abayanta, ya turo ta waje a hankali, Tana fitowa ta runtse idanuwanta da ke tsastsafo da ƙwalla.

ƙurmin Daji ne mai nau’ikan tsirrai da dabbobi iri-iri. Manya manyan bishiyoyi masu tsayi da faɗi suna da Dogayen rassa, Faɗaɗan Ganyayyakinsu Sun toshe hasken Farin watan da ke a sararin samaniya kaɗan ne ke samun damar haskowa ta tsakankanin Ganyayyakin, yau shekara Uku da watanni rabon da ta tsinci kanta A waje, Ina ga sauran ƴan uwanta Prisoners waɗanda tun da uwar su Ta haife su basu ta6a tozali da haske rana ba, Ɗaya bayan ɗaya Danish ya dinga janyo su kamar basu son fitowa, Kaf ɗin su Ya fiddo da su, kafin Ya maida ƙofar kogon tamkar ba’a ta6a ratsa cikinta ba.

Sai faman zazzare idanuwansu suke yi suna bin Dajin da kallo duhu Ya hana su ga komai da kyau, Tsananin tsoro ne ya kamasu, Ga wani irin bala’intaccen san yi kamar Jaura ta gifta, Haƙoran su sai kakarwa su ke yi, muryoyinsu Na rawa suka soma ambaton sunan Danish Suna faɗin sanyi su ke Ji.

Da sauri Ya buɗe akwatin kayan su dama shi ne ya ɗauko shi Tare da back pack ɗin Unaiza, Ya zaro masu bargunan su, A saman bayan su Ya lullu6a ma kowannansu bargo, Tunani ya shiga yi ya zaiyi dasu? Ga dukkan alamu sun gaji basu Iya motsawa gashi yana fargabar kada akawo masu hari yasan dole abiyo bayansu. Babu mai ƙoshin lafiya acikinsu kowa takan shi ya ke yi shiyasa ko farin cikin fitowar ba su yi ba duk da irin ɗaukin da suka dinga yi, su fa har yanzu basu yarda cewa sun fito daga kurkukun ƙaddara ba, gani su ke yi kamar har yanzu suna aciki, saboda duhun daya mamaye idanuwansu basu Iya gani dakyau hada ƙarin nauyin da idonsu yai masu sakamakon kukan da suka sha, wasu ma daga cikin su ciwon ido suke fama dashi, Danish ne kaɗai yake Iya ganin su da kyau.

Yanke shawarar ya yi da zuciyarshi nan take ya haifar masu da jin matsanancin bacci, Asaman dogayen ciyayin da ke shimfiɗe masu cukowa, Kowan nan su Ya kwanta hada masu goyan cikin su, Ajiyar zuciya ya sauke tare da miƙewa, Ya ɗauki bargo ɗaya daga Cikin wanda Ya lullu6a masu Kamar walƙiya ya 6ace Bai dura a ko’ina ba Sai acikin kogon dutse mai girman gaske, da sihirin shi ya kawar da duk wani abun cutarwa Ya gyara wurin tsaf babu ko ƙura balle aje ga batun halittun da ke rayuwa a cikinshi, Bayan ya tabbatar da babu abun cutarwa Ya shimfiɗa bargon dake a hannun shi, Kafin Ya juya tare da 6acewa ya dawo wurin da yabarsu kakkwance suna bacci, Cikin mintuna Biyar Yai aikin da acikin awa biyu mutun zai iya yin shi, Bai da banbanci da Jinni, kamar walƙiya ya dinga ɗaukarsu ɗaya bayan ɗaya yana kaisu saman shimfidar da yayi masu a cikin kogon dutse bai bar kowa ba, Bayan ya kammala kwashe su ya ɗauke masu akwatin kayansu da jakar ya shigo dasu Cikin kogon ya ajiye shi. Komawa yai cikin dajin Ya haɗo itace dayawa ya shiga dasu ruƙe a hannun shi Cikin kogon dutsen, Ya jera su a ƙasa nesa da inda su Angel su ke akwance, Ya tsinto duwatsu guda Biyu ya gurzasu jikin juna nan take wuta takama Ya cinna ta a jikin itace sosai Wutar ta ruru, a ƙalla ya sauke ajiyar zuciya yafi sau a ƙirga, ya hada uban gumi shi kaɗai, jiki bai saba da wahala ba, fuskarshi sai naso ta ke yi kamar an watsa mashi ruwa, Ya jima zuƙunne abakin wutar Yayin da idanuwanshi ke akan ƴan uwanshi dake lullu6e cikin bargo suna bacci, wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarshi kamar an kora ruwan san yi, haƙika yayi danasanin duk wani abu da ya faru dasu, Ya ji ƙunci sosai A cikin ran shi, miƙewa ya yi a hankali ya ke tafiya yana tunkararsu a gaban shimfiɗar su Ya zuƙunna tare da miƙa yatsun hannayenshi Ya ruƙo bakin bargon dake lullu6e dasu Ya yaye shi, Hasken wutar da ke cini ne Ya haskaka mashi fuskokinsu, Idanuwanshi na akan Marasa ran cikin su, idan ka kalle su a yadda suke kwance baka ta6a cewa gawawwaki ne, Tuni idanuwanshi sun kaɗa jawur, Zuciyarshi ta ƙara karaya tsananin tausayin rayuwar ƴan uwanshi ne ya kama shi, Ya rasa ya akai duk waɗannan abubun su ka faru ba tare da sanin shi ba? Shin me ya faru da su bayan An ɗauke shi daga Cikin su? tambayoyi ya shiga jefa ma kanshi. Ataƙaice Daren Ranar Danish bai runtsa ba, Kwana yai a zaune yana gadin su.

*MIDDLE STEP THE PRISONERS BOOK TWO*

*BIRNIN ABUJA*

*Boss Bature✍️ Mu haɗu Gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

 

First bank

 

3196407426,

 

*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08103884440, Banda kira whatsapp kawai*

Back to top button