Hausa NovelsKurkukun Kaddara Book 2 Hausa Novel

Kurkukun Kaddara Book 2 Page 1

Sponsored Links

_~*BOSS LADIES WRITERS*~_

*_KURKUKUN ƘADDARA_*

_The Prisoners_

~Middle step~

 

_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty._

*Episode 1*

Zaro ido su Parveen su ka yi bakunansu a sake, yayin da su ke kallon ƙofar, Wani irin farin Ciki ne Mara misaltuwa ya bayyana akan fuskokinsu Har sun wage baki zasu Fasa ihu Angel Tai saurin Dakatar da su ta hanyar cewa”Kun manta abunda na faɗa ma ku? Komi za ku gani ku ja Baki ku yi shiru idan ba haka ba asirin mu zai tonu har su gane abunda mu ke ƙoƙarin yi’ Fuskokinsu Haris da alamun ruɗu donsu basu son kan me ta ke magana ba, sun dai ga murfin ƙarfe jikin bango, bayan haka sunji batul tace ƙofar da su ke nema.

Naufal ne yai ƙoƙarin buɗe baki Yace”Angel Kun bar mu a duhu, bamu san kan me ku ke magana ba” ya ƙarasa maganar idanunshi akan fuskarta, har lokacin bata daina sakin murmushi ba, Haka zalika su parveen Bakin su awashe ya ke Kamar Gonar audugu Ji su ke kamar ma Har sun fuce daga Cikin kurkukun.

“Ki yi mana bayani mana, Wannan murfin ƙarfen na menene a jikin bango”? javed ne yai maganar, sautin Muryoyin su daƙyar ya ke fita saboda rashin ƙarfin jikin su, har ƙwara sauran mazan akan mubeen ko da su ka shigo toilet ɗin kan shi na asaman Kafaɗar Hannah, Sam babu kuzari a jikin shi.

“Na ruɗe Angel Ki fada mana mun ƙosa Mu ji,” acewar Gabriel.

duk wanda yai magana acikin su idanuwanta na akan la66ansa, Sai bin su ta ke yi da kallo, farin Ciki Ya hana ta yi magana.

“Idan ba zata Iya yi mana Bayani Ba, Deeja Ku faɗa mana Meke faruwa ne’? Haris ne yai maganar idon shi akan su Deeja dake a tsaitsaye Cirko Cirko.

Ganin sun fara fusata Yasa ta haɗiyi yawu tare da sauke nauyayyar Ajiyar zuciya, Cikin sanyin murya ta soma kora masu jawabi sannu a hankali ta fayyace masu komai dangane da ƙofar sai dai ta 6oye masu Game da tattaunawar da su ka yi Ita da Salsabeel.

Tsabar mamaki yasa su ka dinga jefawa junansu kallo Lokaci ɗaya wani irin Annurin farin Ciki Mara misaltuwa ya lullu6e zukatan su, Har basu san lokacin da suka ƙarasa gaban Angel suka ɗago da ita daga zuƙunnan da take abakin Bango, gaba ɗaya su ka rungumeta, Kamar zasu Karya ƙasusuwan Jikinta, Musamman Gabriel da ya fi kowa burin son ku6uta daga kurkukun ƙaddara, zafafan hawaye ne su ka soma gangarowa ta saman fuskarta, ta rasa gane hawayen menene? Shin na farin Cikin da ta ke yi ne ko kuwa na baƙin Ciki? Ɗaya bayan ɗaya ta ke kallon su Bayan sun sake ta, Maganar da ke yi mata yawo acikin kanta itace”kada ku sanyawa ranku cewa dukkan ku za ku Rayu! wannan maganar ta yi matuƙar tsaya mata aranta, ta ta6a zuciyarta, fatan ta Allah yasa Mutuwar kada ta rusƙe su agidan kurkukun ƙaddara, ba zata so wani daga Cikin su ya ƙara rasa ran shi a wannan Ƙazamin Ginin ba, Duk idan ta tuna Matasan Yaran da ta gani awannan ɗakin lokacin da ta dura taga taje ta gane ma idonta su Rataye Saman igiyoyi kamar dabbobi sai ta ji duk jikin ta ya mutu, Haƙiƙa ta yi matuƙar girgiza ganin yadda Suke feɗe Cikin mutun mai rai su kwashe sassan Jikin shi……..”

Hankalin su ba ƙaramin tashi yai ba, ganin yadda Angel ta fashe da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita har wani jiri ta ke gani acikin idanuwanta, Daƙyar ta jingina bayanta Jikim bango, taci gaba da riskar kukan ta Fuskarta jaga jaga da hawaye.

Murnar da su ke yi ce ta koma Ciki, Damuwa ta bayyana Akan faces ɗinsu, Har suna haɗa baki wurin furta Sunanta
“Angel! Why are u shedding ur tears? Dan Allah kada kisa zuciyoyin mu su karaya, Baki ji irin farin Cikin da mu ke yi ba, saboda Kin gano mana ƙofar da zamu bi, don mu ku6uta daga kurkukun ƙaddarar, Gidan da aka ƙuntata rayuwar mu aka hana mu sakat, Shekara da shekaru tun muna jarirai har zuwa lokacin da muka fara mallakar hankalin mu, Angel dukkan mu nan babu wanda bai haura shekara sha wani abu ba a gidan kurkukun Nan, Ta ya ya ba zamuyi farin Cikin Ganin ƙofar nan ba? muna so mu tsira kodan Muga ya wajen kurkukun nan ya ke, Muna so muga hasken dake awajen shi, koda da numfashin mu na ƙarshe ne, mu dai burin mu, shi ne mu ga mun ku6uta, Idan ma kina tunanin ba zamu Iya tsira mu dukkan mu ba, Zamu roƙi Allah da ya ara mana lokaci mu bar kurkukun nan wlh bamu fatan mu yi wulaƙantacciyar mutuwa acikin shi! Mun fi so Mutuwar ta risƙe mu acan inda zamu je koma akan hanyar Guduwar mu ne…….” Kalamansu sun ƙara karya mata zuciya, kallon da take binsu da shi da rinannun idanuwanta waɗanda suka canza launi kallo ne da ke nuni da tsantsar ƙaunar su, tausayin su da ta ke ji, Ko ɗaya daga Cikin su ba ta son ta rasa, sai dai tasan ba abune mai yiwuwa ba, Mutuwa dole ce!

Tsawon lokaci Suna ta shan kukansu musamman Batul da su Azeeza in ka cire mazan da ke a cikinsu, hawaye ne kwance acikin fararen idanuwansu.

“Muna 6ata lokaci Angel, Ni zan fara jaraba 6alle ƙofar,” Gabriel ne yai maganar, Shi da ba ƙoshin lafiya ba. A haka ya nufi ƙofar ya zuƙunna yana tatta6a Jikinta.

“Nima zan ta ya ka” acewar Naufal, yai maganar tare da matsawa kusa da Gabriel Ya zuƙunna, Atare suka dunga bugun ƙofar da niyar ta buɗe, sun haɗa uban gumi akan fuskokin su, murfin ƙarfen ko motsi bai yi balle su sa ran zai buɗe.

Matsawa Haris yai kusa dasu Shima ya sanya hannun shi, Hada matan kowa Ya shiga gwada ƙarfin shi akan ƙofar don ta buɗe, Duk wannan budurin da ake yi Jemimah Tana acan cikin ɗakin su kwance saman gado, ta lullu6e kanta da bargo baccin ne bai ishe ta ba.

Sun ɗauka cewa abun wasan yara ne shiyasa su ka dage akan sai sun buɗe ƙofar, Mayen ƙarfe ne murfin da ke ajikinta Yana da ƙarko Shekara da shekaru wurin yana adatse ta ya ya zasu iya buɗe shi? Yaran da ba lafiya gare su ba, Ganin yadda suke ta gabzar ƙofar ko sautin bugun da su ke yi mata bai fita sun Dage sun nace akan dole sai sun buɗe ta..

“Haris! Gabriel! Ku daina wahalar da kanku, Ƙofar ba zata ta6a buɗewa ba, saboda babu babban mukullin da zamu Iya buɗe ta da shi,”. Jin wannan maganar da Angel ta yi ne yasa su ka mimmiƙe tsaye sai nishi suke fitarwa ta ko’ina sufa ke tsastsafo masu a jikin su

Atare suka haɗa baki wurin faɗin”Makulli? A ina zamu same shi? Dan Allah ki faɗa mana inda ya ke”

Zuciyarta ba ƙaramar karaya ta yi ba a yayin da su ke tambayarta ina makullin , wani abu da ta lura dashi gaba ɗaya hankalin su ba’a kwance ya ke ba, duk sun furgice burinsu kawai su bar kurkukun.

“Angel kin yi shiru baki amsa mana ba” Jan numfashi ta yi tare da sanya tongue ɗinta ta ɗan lashi lower lip ɗinta da ya bushe Cikin sanyi murya ta soma yi masu magana

“Danish! Shine makullin Da zai Iya 6alle mana ƙofar, gashi baya atare damu Yana acikin kurkuku, Yanzu dole sai mun nemo shi idan har muna son mu ku6uta …….” a matuƙar ruɗe su ke jefa mata kallo, Dole su yi mamaki, Ta ya ya Danish da ya kasance Ragon Namiji acikin su zai zama Makullin buɗe ƙofa? How that can be possible? Ta ina Danish ya ke da ƙarfin yin hakan? ganin irin kallon da su ke binta dashi yasa ta fahimci cewa Basu gasgata maganarta ba. Suna buƙatar ƙarin haske.

“Bazan Iya yi ma ku dogon bayani ba, because you won’t understand me, but definitely Danish is the key to open the door, just believe my words, he can open it,”

Lamarin ya yi matuƙar ɗaure masu kai, Musamman Haris shi da yafi kowa sanin Danish, mutumin da ko ƙwaro Tsoron shi ya ke ji yau shine Angel ta ke kira da makullin buɗe ƙofa.

“Maganar ki gaskice! Ni shaida ne akan hakan! Danish ne kaɗai zai Iya buɗe ƙofar! kusan atare suka ɗaura Idanuwansu akan fuskar Gabriel da yayi maganar.

“Nasan za ku yi mamaki, Dalilin da yasa nace haka, Saboda kokawar da muka ta6a yi dashi, lokacin da Danish Ya shaƙi wuyana da hannun shi, Shaƙar da bana tunanin cikakken mutunne yayi mini ita, Ni nasan mai naji a lokacin da har yaja na naushi idonshi, ƙarfi ne dashi naban mamaki, tabbas shi zai iya buɗe ƙofar……” tunkan ya ƙarasa rufe baki Haris yace”Kun rikita mini tunani na, Taya mutumin daya rasa idon shi ɗaya zai Iya yin hakan? Bayan ni asani na Danish bashi da wani ƙarfi,” Fuskar shi da alamun ruɗu yai maganar.

“Danish Ya rasa ido”! Batul ce ta ambaci hakan Idanuwanta azazzare hankalinta ba ƙaramin tashi yai ba jin abunda Haris yace don ita bata san da zancen rasa ido da Danish yai ba, sun6oye mata don karsu tayar mata da hankalinta.

“Danish bai rasa idonshi ba, Sun samu sa6ani da Gabriel ne, Har takaiga ya naushi idon shi, wanda silar hakan Giant yazo ya tafi dashi, Na 6oye maki hakan ne saboda bana son hankalin ki ya tashi, Kuma Ni da kaina Danish ya faɗa mini cewa Lafiyar shi qalou ba abunda ya same shi, ‘ Angel ce ta kora mata jawabi, Hankalin batul yaƙi kwanciya da kalamanta, jikin ta yayi sanyi, hawaye tuni sun soma yin sintiri saman kuncin ta.

“Shikenan Yanzu ki faɗa mana Taya za’ae mu ga ɗan uwan mu Danish? Idan ma ta kama Ni zan bi ki mu shiga prison ne don mu nemo shi” Gabriel ne yai maganar da ƙwarin gwiwarsa, Har yanzu yana nan da rashin tsoronshi.

Girgiza kai Angel tayi”wannan aikina ne, Ni kaɗaice zan Iya dawo da Danish Cikin mu, In sha Allah, ”

“But how could you do that? Bayan babu wata ƙofa da zaki Iya shiga prison”? Har ta buɗe baki da niyar Ta amsa Ma Naufal tambayar da yai mata, kwatsam! ba zato ba tsammani Kunnuwanta su ka jiyo mata motsin buɗe ƙopar ɗakin su, hakan yasa tai saurin Katse maganarta, Idanuwanta azazzare Take kallon su.

“Kamar buɗe ƙofar ɗakin Mu ake yi? Mun shiga uku, Asirin mu zai tonu, wlh mu gudu daga Cikin toilet ɗin nan,” Parveen ce tai maganar, hankalinsu idan yai dubu toh ya tashi, Gaba ɗaya duk sun bi sun ruɗe, a sukwane Angel ta juya da gudu ta nufi Ƙofar toilet ta buɗe ta, Fucewar ta keda wuya suma suka bi bayanta, garin gudu har suna bangaje juna, Adai dai lokacin da suka faɗo tsakiyar ɗakin, kowannansu ya tsaya da tafiya, Idanuwansu azazzare su ke bin benan da kallo, sai faman haki suke yi babu mai sauran kwanciyar hankali acikin su, babban abunda su ke jima fargaba kada ace Tsohuwa zafreen ce, Ilai ko hasashen su Ya zama gaskiya, ƙofar na ƙarasa buɗewa kunnuwansu suka soma jiyo masu takun takalmanta Har wani sauti su ke badawa ƙwas ƙwas! Jikinsu Ya hau kakarwa zufa ta dinga tsastsafo masu ta ko’ina a jikin su.

Cikin muryar raɗa Deeja tace”Mun shiga uku Angel mun manta bamu maida tukunyar fulawar nan ba! Yanzu idan ta shiga toilet ɗin ya zamu yi?

Ƙasa ƙasa da murya Angel ta ce”In sha Allah ma ba zata shiga ba, Idan ma tai yunƙurin yin hakan zan dakatar da ita,” ita kanta da ta ke yin maganar a tsoroce ta ke furtata, ƙarfin halin ne kawai.

Ahankali ta ke tunkaro in da suke atsaye Cikin shigarta ta jajayen kaya, Yau babu mask a kan fuskarta, Daga bayanta Giants ne Guda Biyu masu ƙirar Samudawa, ko da ta ƙaraso dab dasu saita dakata da yin tafiyar A tsanake ta ke binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya, Saboda tsabar ruɗu da kama kai, Jikin Angel na 6ari ta russinar da kanta Ƙasa muryarta babu natsuwa ta furta”Ina kwana” Tun da tsohuwa zafreen ta kafe ta da ido sam ta kasa motsawa, Lamarin ne ya ɗaure mata kai, Yadda Angel ta duƙa mata wurin gaishe da ita…..
Da sauri su Haris suka russinar da kansu tare da gaishe da ita Cikin girmamawa.

Babu wanda ta amsamawa a cikinsu, Tsawon mintuna biyar kafin ta ɗan yi gyaran murya tare da basu Umarnin su ɗago da kawunansu, bayan sun ɗago ta tsare fuskar angel da blue eyes ɗinta, Suspicious looking ta ke binta dashi Hatta tsigar jikin Angel sai da ta tashi haiƙam, Sam takasa yarda su haɗa ido da tsohuwa zafreen, ta dage tana ta wasa da yatsun hannunta, ta harɗe su acikin na juna, Su ta ƙurawa ido.

Su Deeja duk sun sha jinin jikin su, ganin irin kallon da tsohuwa zafreen ke bin Angel da shi, Kuskuren da Angel ta tafka shine gaishe da zafreen da ta yi, Mace Dattijuwa irin zafreen wadda taga jiya taga yau, Taya zata Iya yi mata wayau? Yarinyar da bata ta6a gaishe da ita ba, sai yau Hakan ya ƙara sanya mata zargin wani abu na faruwa a ɗakin nasu, A hankali takawar da idanuwanta daga kan fuskar Angel ta soma bin fuskokin su Batul da kallo, Sai faman zazzare idanuwansu suke yi, sam babu alamun gaskiya atattare dasu, duk wani motsinsu akan idonta.

Ba zato ba tsammani suka ga ta tuntsire da dariya mai sautin gaske hankalinsu ya ƙara ɗugunzuma, a firgice su ke bin ta da kallo, Lokaci ɗaya ta dakata dayin dariyar ta ɗaure fuskarta tamau babu annuri.

“Meyasa ki ka yi gaggawar gaishe dani tun kafin in buƙaci hakan? Kamar daga sama Angel taji ta jefa mata tambayar.

Yawu ta haɗiya kutt a maƙoshinta, Idanuwanta na kallon Ƙasa azazzare ta soma magana Cikin rashin natsuwa

“Nagane kuskure na, kuma Na yi danasanin rashin kunyar da na yi maki a kwanakin baya, inaso na gyara tsakanina dake ne saboda nasan ban kyauta ba..” tunkan ta kai ƙarshen maganar tsohuwa zafreen ta soma sakin bazawarin murmushi, wanda silar hakan yasa ta kasa ƙarasa zancen da ta kamo.

“Saboda meyasa kike son gyara tsakanina da ke”? Ras taji gabanta ya faɗi, Daƙyar ta tattara natsuwarta kafin ta ci gaba da magana”Mahafina bai koyar dani rashin kunya ba, Tunkafin rasuwar shi yana yawan yi mini nasiha akan girmama na gaba dani, amma saboda rashin jin magana irin nawa ban bi abinda yake koya mini ba nayi danasani……..” Sosai ta fashe da kuka gaba ɗaya idonsu Hibba akanta, Tsabar mamaki yasa suka saki bakunansu suna kallon Fuskarta, Ba ƙaramar ƴar drama bace.

Da buɗar bakin tsohuwa zafreen sai cewa tai”well done Unaisah! Dila sarkin wayau! Da ace ke ƴar film ce tabbas zaki iya cin gasar wadda tafi kowa Iya wasan kwaikwayo, Tun da nake ba ata6a rainin mini wayau irin na yau ba, Ƴar ƙaramar yarinyar da na yi jika da ita….” maganar tsohuwa zafreen ba ƙaramin ƙara ɗaga masu hankali ta yi ba, duk sun sha Jinin Jikin su.

“Ku faɗa min Me ku ke shiryawa ne” Shiru su ka yi ƙirjinsu na bugawa , Mirmushin gefen fuska ta saki tare da cewa”Dama nasani ba za ku faɗa mini ba, Idan naso zan iya yin anfani da sihirin da nake dashi wurin jin abunda zuciyarku ke saƙa maku, Ko in sanya ku yi mini magana da kunan ku,’

Yanayin yadda suka zazzare Ƙwayar idanuwansu tamkar zata faɗo ƙasa, tsoro da firgici ne tsantsa akan fuskokin su.

Ganin tana ƙoƙarin buga sandarta ƙasa Yasa Angel tai saurin cewa”Zan faɗa maki gaskiya, ” tsayar da ido zafreen tayi akan fuskarta.

“Tattaunawa mu ke yi akan yadda zamu ku6uta daga Cikin kurkukun nan saboda mun gaji da rayuwar kulle, Muna so mu ma mu yi rayuwar ƴanci kamar yarda sauran mutane su ke Yi”

Daƙyar ta kai ƙarshen maganar tana mai haɗiyar yawu, Su Batul duk suna sauraronsu babu wani mai natsuwa a cikin su.

“Ban yarda da maganar ki ba, A iya sani na prisoners basu da hankalin Yin tunani mai kyau irin wannan balle har su baki haɗin kai ku tattauna da junanku, Ke ce kika tsara komai Unaisah, saboda kina son karkatar da hankalina don In yarda da maganar ki, ”

Tun kan ta ƙarasa maganar ta soma bin ɗakin nasu da kallo, Kamar sakarkaru haka suka dinga binta da ido Cike da fargabatar karta faɗa sashen toilet ɗinsu asiri Ya tonu, A hankali take tafiya tana ƙarewa ɗakin Kallo Kafin Ta Juyo a sukwane Ta tun kari sashen toilet ɗin su, Tashin hankalin A matuƙar tsorace suke kallon bayanta, Giants ɗin dake atare da ita basu motsa ba, suna atsaye Kamar gumaka

Su Angel Ido ya raina fata, Sai faman Cizon yatsa ta ke Yi, Ji take kamar ta watsa aguje tasha gaban zafreen.

“Innalillahi Ya Allah ta makance kafin ta shiga, Ya Allah ka taimake mu! ya Allah ka hanata gani” Acikin zuciyoyinsu suke furta hakan, Suna ganin ta shige Ciki, Zufa ta soma wanke fuskokinsu, Azeeza tuni ta fara matse kwallo, sun san dole Taga abunda suke aiwatarwa, Idan kuwa harta gano zasu ɗanɗani kuɗarsu ne, Kowa zaiji a jikin shi, Babban abunda yafi damun Angel gargaɗin da Salsabeel ya yi mata akan su yi takatsantsan Yanzu idan asiri ya tonu gaba ɗaya taja masu masifa da bala’e.

Runtse idanuwanta ta yi sosai, hawaye ta ko’ina suka shiga wanke fuskarta, idanuwansu Deeja akanta, Tausayin kansu ne ya kama su, Har sun fara hasashen irin Azabtarwar da za’ayi masu kafin akashe su, Sai bin Juna su ke yi da ido babu mai magana saboda Giants ɗin da ke tsaye akansu.

Fitowa tsohuwa zafreen ta yi daga sashen toilet ɗinsu, Fuskarta ɗauke da shu’umin murmushin nan nata mai wuyar fassaruwa, girgiza mata kai su ka dinga yi ba tare da sun iya furta komai ba, Sun riga da sunsan taga ƙofar nan shikenan ta faru da ta ƙare, Watan Cin ubansu ya tsaya, sun kirawa kansu mutuwa tunkafin lokacin su yayi.

“Wallahi Allah!….’ Azeeza ce ta yi su6ul da baka, da sauri Gabriel Ya toshe mata bakinta da hannun shi, ruwan hawaye ne kwance acikin idanuwansu, duk sun ƙagara su ji wani hukunci zata yanke masu tun da ta gano plan ɗinsu.

Walking magestically ta ƙaraso gabansu Tare da tsaida sandarta a ƙasa, Daya bayan ɗaya ta ke kallon su tsawon mintuna Uku kafin ta soma magana atsanake

“Furennin da ku ka shufka sunyi kyau sosai, Wanene ke basu ruwa A cikin ku? Zaro ido su ka yi akan fuskarta Mamaki Ya kamasu, Aransu suka shiga ayyana cewa” ko dai bata ga ƙofar ba ne? Ko kuwa Allah ne yaji kokensu ya hanata ganin komai.

“Kun yi shiru baku bani amsa ba”? Yawu Angel ta haɗiya Muryarta Na rawa ta ce”am..um..ni..nice..Ni nake bata ruwa, tare da ƴan uwana,”

Murmushi tsohuwa zafreen ta saki tare da cewa”Ku cigaba da bata ruwa inason furenni, Nan da wani lokaci zan ɗauke tukunyar fulawar in mayar da ita ɗakina…” tsabar zalama tunkan ta ƙarasa maganar Angel tai wuff wurin cewa”idan ma kinaso Yanzu saina ɗauko maki ita ki tafi da ita, ai mu mun fi son duk wani abu da zai faranta maki rai” kallonta tsohuwa zafreen ta yi da tsoffin idanuwanta”Kamar baki da gaskiya? Ina magana kina katse ni”! A kausashe tayi maganar.

Sunnar dakai ƙasa Angel tayi a tsananin ruɗe Batul ta ɗaura da cewa”Ae tun lokacin da aka canza mana abinci zuwa ganye, Angel ta soma Fita hayyacinta, sam babu natsuwa atattare da ita, Hakanan zaki ga ta zauna tana sambatu ita kaɗai” ta ƙarasa maganar hada murmushinta,

(Yara sun zama ƴan wasan kwaikwayo)

“Eyyah Hakane ashe, ” jinjina kai Angel tayi”dama ni tun ina agida idan na ci abincin da aka haɗa da ganye zaucewa nake yi, Bana son Cin ganye yana affecting ɗina” Fuskarta amarairace ta yi maganar.

Shiru tsohuwa zafreen ta yi a yayin da ta ke ƙare masu kallo kamar tana son gano wani abu da ke 6oye akan fuskokin su sai dai Allah bai bata ikon fahimtar komai ba, Abun da ya ɗaure mata kai yadda su ke yi mata magana ba tare da jin shakkarta ba.

“Da za ki bamu dama Yau na rana ɗaya kawai, Ki zauna muyi fira da ke, A matsayin ki na kakarmu…..” gaba ɗaya sun ruɗar da ita, sai kallonsu take yi tana faman jinjina kai kamar ƴar ƙadangaruwa

Sun kashe mata bakin magana, A hanzarce ta juya ta nufi bene Giants dake take mata baya suka juyawa tare da bin bayanta, Suna jiyo sautin rufe ƙofar ɗakinsu, Gaba ɗaya suka daka uban tsalle tare da rungume junansu fuskokinsu ɗauke da farin Cikin nasarar da su ka yi akanta, yau sun kashe tsohuwa zafreen da mamaki

“Alhamdulillah Ya Allah, Mun gode da taimakon ka agare mu, ” Angel ce ta furta hakan.

“Mun ji jiki yau Allah, ba kiji yadda gaba na ke faɗuwa ba, tun da ta shigo hankalina yaƙi kwanciya” acewar Yasmin, Hibba tace”Ae ba ke ka ɗai ba, ni kaina ƙiris ya rage in saki fitsari a wando, matar can bala’e ce’ Kowa yana tofa albarkacin bakin shi

“Amma wai ya akai da ta shiga toilet din bata ga komai ba? Kuma har ta ga Tukunyar fulawar”? Naufal nai yai tambayar mamaki ya ishe shi

“Ae Allah muka roƙo shine ya makantar da ita, shiyasa bata ga komai ba” Deeja ce tai maganar,

“Pls kudaina maganar nan kada Suji mu tunda suna ganin mu, Inaso mu yi magana amma dole mu jira zuwa anjima idan marece Ya nutsa, sai mu shiga sashen toilet dinmu saboda idan su ka ga zaryar Tayi yawa zasu fahimci wani abu” Atare suka hada baki wurin furta mata “Toh”

“Yanzu kowa yaje ya kwanta, Inaso ku huta, kafin zuwa anjima ” ɗaya bayan ɗaya suka nufi gadajen su tare da haye saman suka kwakkwanta, Mutun uku ya rage a tsaye, Zuciyoyin A cunkushe suke da tunanin taya zasu Iya 6alle murfin ƙofar nan? Taya zasu iya Gano Danish? Fatansu Allah yasa adawo masu da shi ba tare da sun sha wahala ba, A tunanin su Haris kenan su da basu san komai game da zamanshi giant ba.

Mutun uku da suka rage atsaye Gabriel ne sai Batul tare da Angel, Sunƙi tafiya ga dukkan alamu suna buƙatar jin wani bayani ne daga gare ta.

Kallon su ta ɗanyi kafin ta soma magana “Gabriel nasan me ka ke son ji, Ka ƙara haƙuri zan yi maka bayanin komai” amsa mata yai da toh tare da juyawa ya nufi gadon shi.

“bugun zuciyata me kike tunani ne”? Lumshe ido batul ta yi tare da ware su kan fuskar Angel”har yanzu ban fahimci komai ba, dangane da abunda ya faru da ɗan uwana Danish, hankalina bai kwanta da abunda kika faɗa mini ya faru dashi,”

Matsawa Angel tayi kusa da ita sosai har numfashinsu na kokawa dana juna

“Kin damu dashi”? Jinjina mata kai tayi alamar eh, ta ƙara da cewa”taya bazan damu dashi ba Angel, bakisan yadda nake jin shi acikin zuciyata ba, da ace ina da hanyar da zanbi inje gare shi nothing would stop me from going.”

Angel ba ta yi mamakin jin abunda batul tace mata ba, saboda sanin irin shaƙuwar dake a tsakaninsu, Hakan yasa ma taƙi sanar da ita cewa Ya zama Giant, gudun kada ta sanya damuwa

Ruwan hawayen da ya taru acikin idonta ne yaci gaba da gangarowa

“Ki kwantar da hankalin ki bana son kina shedding tears din ki, Ko dan saboda farin Cikin ki zan yi ƙoƙari wurin ganin Danish ya dawo gare mu,” kwantar da kanta tayi saman kafaɗar Angel taci gaba da yin shessheƙar kuka tana faɗin”Amma ai bashi da lafiya, An cire mashi ido ɗaya, bansan awani hali yake ciki ba, ”

“Ki daina kuka batul so kike hankalinsu Ya ƙara tashi? Nace ma ki lafiyar shi ƙalau shi da kanshi Ya faɗa mini cewa babu abunda ya samu idonshi”

lallashinta Angel taci gaba dayi har saida ta samu ta lafa, Abun da yaɗaure ma Angel kai, zazza6in da taji a jikin batul lokacin da ta kwantar da kanta saman kafadarta, Jikinta zafi sosai.

Hannayenta biyu ta ɗaura saman shoulders ɗin batul, ta ɗago da kanta, Idanuwansu acikin na juna,

“Baki da lafiya ne?naji jikin ki da zafi”? Muryarta adisashe ta ce”Lafiyata qalou, idan ma bani da lafiya damuwar rashin Danish ne” shiru Angel tayi kamar an ɗauke mata sautin muryarta, ta rasa tunanin me za ta yi, Ruƙo hannun batul tayi acikin nata

Calmly tace “You need to take a bath, mu je in raka ki toilet, girgiza kai batul tayi”A’a bana iya wanka, nafi so na kwanta zuwa anjima idan na tashi zanyi,”

Gyaɗa kai Angel tayi”shikenan muje mu kwanta da anjima nima zanyi wankan”

Atare suka nufi gadajen su, tafiya su ke yi kamar waɗanda aka zarewa laka, babu kuzari a jikin kowaccensu, Ita dai Angel akwai wani abu dake damunta acan ƙasan zuciyarta, Fatan ta Allah yasa hasashenta karya zama gaskiya don kuwa ba ƙaramar matsala za’a samu ba.

Ta yi niyar ta kwanta asaman Gadon Danish ganin Jemimah kwance saman nata gadon, sai dai kafin ta gama yanke shawara da zuciyarta batul ta riga ta kwanciya saman gadonshi, da ido ta bita da kallo ganin ta rungume pillow dinshi a ƙirjinta tare da lumshe idanuwanta, Jiri Angel ta gani acikin idanuwanta kamar zata faɗi kasa adaddafe ta nufi gadonta daƙyar ta haye gefen jemimah ta kwanta tana faman sauke ajiyar zuciya, lokaci ɗaya ta ji yanayin jikinta ya canza zuwa zazza6i, hakan yasa ta soma ambaton sunan Allah, sama sama ta fara jin bacci yana fisgarta har ya ci nasara akanta sosai ta nutsa tana bacci……………

Ɗakin ya yi tsit babu mai magana a cikin su, kamar masu bacci alhalin kuwa likimo su ka yi, sai da marece ya nutsa Angel ta umarce su akan su je su yi wanka saboda wunin ranar jikin su baiga ruwa ba, ba tare da 6ata lokaci ba kowannansu Yayi wanka, ta ɗauko masu sababbin uniform ɗinsu kowa ya zura nashi a jikin shi, tsaffin kuma suka cire su Angel ta kar6esu ta ninke su ta ajiye saman table.

Lokacin da dare ya gabato, dubara su ka yi wurin kashe Floor lamps ɗin da ke a ƙasan ɗakin su, Duhu Ya mamaye idanuwansu, saboda sabon da su ka yi da ɗakin yasa su ke iya gane hanya ko a cikin duhu, Kamar yarda Angel ta tsara masu mutun Uku ne zasu Haɗa masu kayan su A cikin akwatin da zasu gudu da shi, Rai da burin sufa shirin matafiya su ke yi tun kafin su gano Makullin Buɗe ƙofa, Babu wanda yai bacci acikin su Hatta Jemimah idonta biyu tun ɗazu da marece da ta farka Angel tayi mata bayanin komai dangane da gano ƙofa da kuma shirin su na guduwa, abunda yasa tayi mata bayani don kada ta basu matsala, da ya ke yarinyar tana da wayau ta fahimce ta sosai, yanzu haka suna kwance saman gadon Angel ita da azeeza sun rungume juna sunata saƙa wasiƙar jaki game da rayuwar da za su yi agidan daddyn Genie ɗinta.

Sauran Ƴan uwan nasu duk suna a zaune gefen gadajen su, duk wani motsin su Angel akan kunnuwansu.

“Bamu san Girman ƙofar ba Angel Kada mu gaza wuce wa da akwatin kayan mu” Gabriel ne yai maganar, Cikin duhu suke magana, zurfin tunani ta yi acikin kwakwalwarta, A Labarin da Salsabeel ya bata Na mahaifin shi habibullah ya tabbatar mata da cewa Ƙofar sai da rarrafe mutun zai Iya giftawa ta cikinta, mutun zai Iya rarrafawa ko ya zauna, Amma babu zancen miƙewa tsaye, abun zai zo masu da sauƙi tun da basu da girman jiki, yawancinsu dogaye ne amma babu ƙiba, haris ɗin ma da ke da jiki yanzu ya zabge ya koma kamar su Javed.

“Ae akwatin zamu Iya kwantar dashi mu dinga tura shi ta cikin hanyar, Ni abunda nake Jiye mana kada mu kwasa mu tafi zai Iya kasancewa ƙurmin daji ne bamusan ya weather ɗin shi zai kasance ba, Zafi ko Sanyi, Zamu sha wahala akwai sanyin da ma zai Iya kisa Haka zafi ma, Ni nafi so mu tafi da bargunan mu saboda tsaro, shiyasa nake so mu ɗauki akwati ɗaya sai Backpack ɗin Unaiza dole mu tafi da ita saboda gadon mu ce.

Duk maganganun da suke tattaunawa cikin duhu akan kunnan ƴan uwansu da ke zaune gefen gado Sun natsu suna sauraron su.

“Mu fara ɗaukar uniform ɗin mu jera su ciki, ” batul ce tai maganar, Angel tace”Ki je toilet ki ɗauko mana fitila ɗaya amma ki fara kashe ta tun acan dan kada su gan mu, a ɗakin tsohuwa tamira zamu aiwatar da komai” ta amsa mata da toh, kafin ta nufi hanyar sashen toilet ɗinsu cikin duhu har ta samu ta cimma ƙofar makewayin nasu, da hannu ta tura ƙofar ta kutsa kai ciki ta shiga ta ɗauko fitilar tare da kashe ta, Kafin ta dawo ɗakin tunkan ta ƙaraso tace dasu gata nan tafe, Ruƙo hannunta Angel tayi acikin nata ta kuma ruƙo hannun Gabriel da ɗayan hannun atare suka shige ɗakin tsohuwa tamira,

“Ki kunna fitilar yanzu, Ni kuma zan shiga ɗaki In ɗauko Akwatin kayan mu da backpack ɗin” ta amsa da toh, Batul na kunna fitilar Haske Ya gauraye ko’ina na ɗakin tsohuwa Tamira, Zazzaro ido su ka yi ita da Gabriel da mamaki akan fuskokinsu suke bin Bedroom ɗin da kallo, basu ta6a sanin haka ya ke ba, Yau ne rana ta farko da batul ta fara shigowa ɗakin tsohuwa tamira. Kallon Juna su ka yi ita da Gabriel Murmushi ne ya bayyana akan fuskokinsu ba tare da sun yiwa juna magana ba.

Turo ƙofar ɗakin akayi da sauri suka kalli mai shigowa, Angel ce janye da akwati ɗaya na kayansu, Ta goyo back pack ɗin Unaiza saman bayanta sai ta yi tamkar Ɗalibar makaranta, A tsakiyar ɗakin tsohuwa tamira ta ajiye akwatin saman floor, ta kwanto jakar bayanta ta ɗaura ta saman table.

“Angel Har yanzu ba ki yi mana bayanin ta ya ya akai kika gane inda ƙofar nan ta ke? Waye ya faɗa maki kiyi amfani da ruwan zafi don shafen wurin ya tsage? after that Mun yi mamakin yadda akai kika buɗe ɗakin tsohuwa Tamira ko dai itace duk ta faɗa maki hakan”? Batul ce tayi mata tambayar a ƙagare da son jin amsarta.

“Zan baki amsar tambayarki amma kafin nan inaso ki kira mini su Haris su shigo ayi komai agabansu” har ta juya zata fuce da fitilar hannunta da sauri Gabriel Ya cafko damtsen hannunta tare da janyo ta baya yana fadin”So kike asirin mu ya tonu? Ina zaki da fitila”? Murmushi ta ɗan saki tare da cewa”Na shafa’a ne” kar6ar fitilar yayi ita kuma ta fuce Jim kaɗan Su kaji an turo ƙofar Haris Ne agaba Deeja na abayan shi dasu Hibba a jere suka shigo Hada azeeza Hannah ce ta ruƙo hannunta.

“Wa ya ce ku zo da Azeeza? Ba a kwance ta ke ba”? Gabriel ne yai maganar Yana kallonta, Naufal yace”kasan halinta da rigima tafi son komai za’ayi ayi agabanta mutun na fama da makantar dare,”

Ranta ne ya 6aci sosai jin abunda suke cewa, fusge hannunta ta yi daga ruƙon da Hanna tayi mata, A ƙasa ta zuƙunna tana rera masu kuka.

Angel tace”Dan Allah ku rarrashe ta idan ba so ku ke ta tona mana asiri ba” Gabriel ne ya nufi wurin da ta ke a zuƙunne ya kai hannu ɗaya ya ɗago da ita kamar jira ta ke yi ta faɗa saman laps ɗinshi tana cigaba da kuka, Murmushi ya saki yana kallonta har mamakin Ƙarantarta ya ke yi,
“Its ok Share hawayen ki My Azeeza, kinsan bana son zubar hawayenki, Ko so ki ke Ajiyo sautin kukan ki asirin mu ya tonu”? Muryarta da shessheƙar kuka tace”A’a” yace”okey wipe ur tears, zan Goya ki abayana don bana son kisha wahalar neman ɗan jagora,” yai maganar tare da miƙa ma Batul fitilar hannun shi, bayan ta kar6a ya zuƙunna Azeeza ta haye bayan shi ta ƙanƙameshi sosai, Ya miƙe ɗauke da ita”

Angel na ƙoƙarin fara yi masu bayani muryar jemimah da suka bari ita kaɗai acikin ɗaki ya karaɗe kunnuwansu ta kware baki Tana ƙwala mata kira”Genie! Genie! ” da sauri Angel ta nufi ƙopar ta buɗe ta fuce, Bayan fitarta Hankalinsu Ya koma kan ɗakin da su ke a ciki na tsohuwa Tamira Sai faman wurwurga ƙwayar idanuwansu su ke yi, Parveen Acici Tana Hango Wannan Tea pot ɗin da ƴan kofuna biyu jiki na rawa ta nufi table ɗin dake ɗauke dasu, ta zauna saman kujera tare da ɗaukar pot ɗin tana jijjigata don taji idan akwai ruwan shayi aciki,

“Kada ki kuskura ki ce zaki sha, Kawai daga ganin abu bakisan tsawon lokacin daya ɗauka a ajiye ba kin ɗauka zaki sha da ya ke ba ki da linzami indai akan abinci ne” Deeja ce ke yi mata magana, Saboda kafiya irin ta parveen ko kallo bata isheta ba hada cewa”dama kin daina wahalar da kanki wurin yi mini magana don wlh saina sha tea ɗin nan” Tsawa haris ya daka mata”Zaki tashi ko saina 6ata maki rai”? Murguɗa mashi ƙaramin bakinta ta yi”Wai ku ina ruwan ku dani ne? Cikina ne ko naku”? dafe kai Hannah ta yi tare da cewa”ku ukun nan kunfi kowa jaraba dake da Azeeza sai waccan ƴar jemimah, Ni inaga Idan mun tashi tafiya mu bar su a kurkukun domin kuwa nan yafi da cewa dasu, in ba haka ba zasu ja mana ne” Jin maganar Hannah yasa azeeza dake kwance bayan gabriel ta ƙara fashewa da wani sabon kukan, saboda ance za’a barsu a kurkuku

“Pls Hannah stop saying that, na samu na rarrasheta gashi yanzu kinsa ta kuma fashewa da wani kukan” acewar Gabriel, ta6e baki hannah ta yi ba tare da ta tanka mashi ba.

Daƙyar ya samu yashawo kan Azeeza ta daina yi mashi kuka, Parveen kuwa harta Tsiyaya Shayin A cikin Cup hada lashe baki zata fara sha, Kamar daga sama taji an damƙi wuyan rigarta daga baya, da sauri ta ɗago don taga wanene, dama saida ranta ya bata cewar shi ne

Harara ta shiga jefa mashi tare da murguɗa mashi baki, Ya ɗaure fuskarshi sosai babu annuri

“Tashi ki bar wurin” kaitsaye ya bata umarni, tasan halin shi sarai miƙewa ta yi ranta a6ace, bata so ya hana ta shan tea din ba, ta ƙwallafa rai.

Acikin hannunshi ya ruƙe nata sosai don kada ta kufce mashi ta koma shan shayin, Naufal kenan.

“Angel shiru bata dawowa ba, Tabar mu atsaitsaye cirko cirko, Ni bari ma in haye saman gadon tsohuwa in kwanta”

Rubina ce ta yi maganar, bata kai ga zuwa ta hau gadon ba, Angel ta turo ƙofar hannayenta biyu rungume da uniform dinsu, Jemimah na kwance saman bayanta, Ta ƙanƙameta da hannayenta, abunda ya jawo har suka daɗe Jemimah ce ta buƙaci ta rakata toilet zata zazzage cikinta, Shiyasa basu dawo da wuri ba, Sai da Angel ta jira ta gama tukunna ta kamota suka dawo ɗakin.

Ataƙaice Cikin daren suka jera uniform ɗinsu acikin akwatin kayan, Hada barguna Deeja ta ɗauko masu guda takwas daƙyar akwatin ya iya ɗauke su, Har saida suka rage uniform din dake a ciki suka turasu cikin backpack ɗin Unaiza tukunna ya ishe su, Bayan sun kammala sanya kayan suka datse shi, daga cikin abubuwan da suka dauka bayan uniform da barguna hada cotton scarves dinsu da Hulunansu sai rigunan sanyi da takalmansu, A cikin jakar unaiza suka saka Madubin da tsohuwa Tamira ta basu kyauta, ba su bar cikin ɗakin ba saida Angel ta fayyace masu komai dangane da tattaunawarsu da Salsabeel.Abu ɗayane bata fada masu ba komawar Danish Giant bata so su sani gudun kada su tayar da hankulansu. Haƙiƙa tsohuwa tamira ta kafa tarihi acikin zukatansu, A yau ta amsa sunanta na mahaifiyar su wadda ta raine su, basu ta6a yarda cewa tana sonsu ba sai yau da Angel ta labarta masu komai dangane da taimakon da ta yi masu, sun ji ƙaunarta sosai har suna fatan Allah ya haɗa su da ita kafin subar kurkukun, sai da su ka kammala shirya komai tsaf na kayansu, Angel ta kalle su ɗaya bayan ɗaya Azeeza tuni bacci ya ɗauke ta abayan Gabriel, hankalinta kwance sai sharar bacci ta ke Yi, Jemimah kuwa Idonta biyu Sai faman baza ido ta ke yi Hannunta na a ruƙe dana Angel.

“Me yakamata Mu yi yanzu don ganin An dawo mana da ɗan uwan mu Danish”! Haris ne yai maganar

“I’ll go and get him back tonight!” da ƙwarin gwiwa Angel ta yi maganar.

“Ta yaya hakan zai yiwu? Angel muna jin tsoron wani abu ya same ki, Me zai hana mu tafi gaba ɗayan mu”! batul ce ta yi mata maganar fuskarta da alamun damuwa

“Zan bi ki Angel Mu tafi atare”! Gabriel ne Ya yi maganar” girgiza kai ta yi”Bana so wani abu ya samu ɗaya daga Cikin ku, Bazan bari ka bini ba Gabriel ni kaɗa nake so na jefa kaina cikin hatsari Zan roƙi Allah ya tsare ni…..” muryarta na ɗan rawa ta ambaci hakan kamar akwai rauni atattare dani, tabbas tana matuƙar fargabar abu biyu, Na farko tafiyar da zata Yi tabar su da jimamin Awani hali take a ciki, Na biyu Haɗuwarta da garkuwar kurkuku, Wani irin azababben tsoron shi ta ke ji tun kafin ta yi tozali da shi.

“Genie Pls don’t leave me Ki tafi dani…” cikin shessheƙar kuka Jemimah ta yi maganar tana ƙara damƙe hannun Angel dake ruƙe da nata.

“Wlh Angel hankalin mu ba’a kwance ya ke ba, Gani mu ke kamar wani abu zai faru da ke idan kika tafi kika barmu” Deeja ce ta yi maganar, ta fahimci kowannan su atsorace ya ke da tafiyarta.

“Angel bazamu ta6a yafewa kan mu ba idan har wani abu ya faru dake ta silar taimakon mu da ki ke ƙoƙarin Yi,”

Javed ne yai maganar, Tuni zafafan hawaye sun wanke fuskokin kowannan su, La66anta sai kerma su ke yi sam ta kasa buɗe baki ta yi masu magana sai binsu ta ke yi da ido, Zuciyarta ba ƙaramin karaya ta yi ba, Ita kanta tana ji a jikinta cewa wannan karan zaiyi wuya ta dawo cikin su ba tare da wani mummunan abu ya faru da ita ba.

“Idan har muka ji kin daɗe baki dawo ba, Zamu biyo ki ne”! Hibba ce tai maganar hawaye kwance saman kuncinta

Daƙyar Angel Ta iya tattara natsuwarta tare da cewa”Ku daina sanyawa ranku cewa wani abu zai faru dani, idan ma ya faru dani to ku sani ƙaddarata ce wadda ban isa in sauyata ba, Ni da Allah na dogara wani mutun ko Aljan ɗaya daga cikinsu bai isa ya cutar dani ba face da izninsa, ƴan uwana addu’arku kawai nake buƙata akan Allah ya bani Sa’a akan abunda zan je nema…….” Sautin shessheƙar kukansu ne ya gauraye Ɗakin tsohuwa.

Muryarta adisashe tace”Tunkafin ma na tafi kun fara kuka? Meyasa? Dan Allah ku daina kamar fa kuna discouraging ɗina ne, Nafi so inga kuna ƙarfafa mini gwiwa, ganin hawayenku da nake yi ba ƙaramin raunata mini zuciya ya ke yi ba.

“Ba zamu iya jurewa rashinki atare damu ba Angel, wlh muna ƙaunarki fiye da yarda muke son kanmu, bamu son wani abu ya same ki, saboda mu kike ƙoƙarin jefa kan ki ga halaka taya ba zamu yi kuka ba? Angel ke uwace agare mu, Kin fiye mana iyayenmu da su ka yi watsi damu, Dan Allah Angel karki bari mu rasa ki” Sosai suka sanya mata kuka

Itama ta fashe masu da matsanancin kuka mai cin rai tamkar ana zare ranta Cikin muryar kuka take magana

“Shiga prison Ya zamar mun dole, Idan har ban je ba rayuwar mu tana a cikin haɗari, sannan Alƙawari ne na ɗauka Dole na cika shi ku daina raunata mun zuciyata kada kusa Na gaza……” Kasa ƙarasa maganar ta yi saboda raɗaɗin da ta ke ji a cikin zuciyarta.

Tsawon lokaci suna kallon kallo a tsakanin su kafin ta tsagaita da yin kukan tace da batul”Ga amanar jemimah, Ki rungume mun ita a ƙirjin ki har sai ta yi bacci, da zarar na dawo zan kar6i abuna” cikin sanyin murya batul ta amsa mata da cewa In sha Allah zan bata kyakkyawar kulawa har ki dawo Angel, murmushin yaƙe ta ƙaƙaro kan fuskarta tare da kallon su Parveen da ke atsaitsaye tace”Zan tafi ba za ku rungume ni a jikin ku ba”? Jin haka yasa da sauri suka matso kusa da ita, Ɗaya bayan ɗaya suka dinga rungumeta a ƙirjin su, kamar karsu sake ta, a ƙarshe Ta Soma tafiya tana ja da baya tana kallon su idanuwansu akanta, Jiki amace ta juya tare da buɗe ƙofar ɗakin tsohuwa tamira, Da gudun gaske Cikin duhu ta nufi sashen toilet ɗinsu tana faɗowa Hasken sauran fitilun dake a cikin toilets Ya haskaka idanuwanta, buɗe ƙofar toilet ɗin ta yi tare da shigewa Ciki. Yatsun hannunta na kerma ta sanya jamlock ta datse ƙofa don kar su yi gigin cewa zasu bi bayanta, A jikin ƙofar ta jingina bayanta sosai ta fashe da kuka gudun kada su ji sautin kukanta yasa ta toshe bakinta da tafin hannunta, tsawon mintuna goma shabiyar tana sharar ƙwalla kamar ruwan hawayenta zasu ƙare sai da tayi mai isarta kafin ta soma tafiya tana tunkarar Tagar da zata dura, har zata gifta tukunyar fulawar nan ta ɗan dakata da yin tafiya kafin a hankali ta kalli inda ta ke a jingine jikin bango, duk da halin da take aciki na fargaba sai da tayi mamakin ganin an maida tukunyar a mazauninta na asali, shiyasa ɗazu tsohuwa Zafreen bata samu damar ganin ƙofar ba saboda an toshe ta, ajiyar zuciya ta sauke tare da lumshe idunuwanta daga bisani ware su sosai akan furen Danish da ganyayyakin shi su ka bubbuɗe gwanin ban sha’awa, Kyakkyawar fuskarshi ta ke imagining acikin idanuwanta, aranta kuwa tana ayyana koya Zata Ganshi a yanzu daya koma Giant? Da wannan tunanin Angel Ta ƙarasa gaban glass window ɗin Ta janyo bokitin Ta haye sama A hankali ta 6a66ako glass ɗin tare da curo shi ta dire shi ƙasa kafin ta daddage ta haura Saman tagar bakinta ɗauke da Bismillah.

Zuƙunna tayi a jikin bangon da ta faɗo, wani irin Sanyi ne ya mamaye sassan Jikinta, Ga tsoro daya mamaye zuciyarta, Biji biji take ƙarewa doguwar hanyar kallo, duhu sosai babu haske sai dai da alamun haske a ƙarshen hanyar Inda Babban filin nan ya ke.

miƙewa Tayi tsare tare da Sanya hannayenta Biyu ta ruƙo duguwar sumar kanta tare da nannaɗeta ta jefar da ita saman gadon Bayanta, tunawa da addu’oin da ta karanta a jiya da tayi fitar nan yasa a yanzu ma ta soma ambaton su acikin zuciyarta, A yayin da take tafiya tana nufar cikin kurkukun……..

*Boss Bature✍️ Mu haɗu Monday Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game neman ƙarin Bayani Ya tuntu6i Layina na whatsapp 08103884440 banda Kira just message*

Back to top button