Hausa NovelsYar Aikin Karuwai Book 2 Hausa Novel

Yar Aikin Karuwai Book 2 Page 61-65

Sponsored Links

Auta bai dade ba ya warke ras da shi ya fara zuwa makarantarsa shi kadai,Mami ce ta bugawa Baso waya tace naga kamar Salma tayi laushi haka duk tsiyar nan ta daina,Baso yace Ina ai bata daina ba ni nasan halin kayata,Mami tace to a canja mata gate gaskiya da wahala,Baso yace bafa ta jin magana yarinyar nan amma shike nan ku Maida ta sharar tsakar gida duk uban girmansa ta share sannan taci gaba da girkinta komai tayiwa Auta karku daga mata kafa,Mami ce ta Kira Salma daga bakin gate ta taho da sauri ta bata waya,tasan Baso ne yace kina ji na? tace ae yace an canja miki aiki kin koma share compound ko Ina da Ina na gidan nan,Sannan an canja miki yiwa Auta wanki ki masa girki sannan ki gyara masa daki duk abinda yace kiyi Idan ba haka ba nazo garin nan na lahira sai ya fiki jin Dadi,sannan Zaki koma Makaranta,ita dai Salma hawaye take,suna gama waya Mami tace kuka kike Salma? Kai ta girgiza da sauri,tace gidan nan na hango girmansa gari guda Mami Dan Allah ni marainiya ce ku tausaya min,Mami tace ai baki duba maraiciinki ba Salma,zanyi duk ko mene wlh bazan sake masa rashin kunya ba ni ba ruwana ma da shi inshallah bazan sake masa magana ba,Mami tace to ashe Zaki ci gaba da shara kuwa,tace dauki tsintsiya kawai,Mami taji tausayinta sosai bata son wahalar nan amma Salma bata jin magana ana barinta Idan ta mike kafa sai tsiya wasu gata da jin dadi hauka yake sasu.

Washe gari Salma da sassafe ta fito yin shararta tana yi tana hutawa har tazo garden bayanta ya kage,Auta yana ta Exercise yana motsa jiki yana kallonta tsugunawa tayi a wajen ta fashe da kuka, dariya ta kama Auta ya danne,tausayi ta bashi ya tako har inda take da kayan gym dinsa bakake,tsintsiyar ya karba a hannunta ta dago a hankali ta kalle shi,sharar ya duka ya fara mata ya karasa mata yana tattarewa tazo tace bani kar azo a ganni na Saka Dan Gold aiki ka jawo min a Kira Baso,fuska ya daure tace na gode to,Auta ne ya shiga Palon Mami ya sameta yace Mami tace Ina jinka,yace please ku kyaleta haka duk sai ta lalace tayi duhu,Mami tace oh ashe? yace ae Baso fa Dan kwaya ne ba dai dai yake da mutane ba,Mami tace ji nake nan kace ka tsaneta,to Dan na tsaneta shike nan sai a wahalar da ita,Mami tace shike nan Auta Kai da Salma ba ruwanmu.
Salma ciki ta shugo ta hada zufa ta sha shara ta shiga dakin Auta hannu ta Kai saman bed din zata gyara taji an rike mata hannu tasan Auta ne,yace jeki, ta furta nifa bance maka komai ba ka kyaleni nayi aikina,yace daga yau kin daina to shike nan? Kai ta girgiza tace kawai gwara nayi,Salma taci gaba da aikinta ba ji ba gani,ta fito ta dora girki tayi me Dadi kuwa tunda ta iya tazo ta shirya a dining.

Wanka taje tayi ta fito ko abincin bata ci ba ta tattaro kayanta Dana Auta Dana Mami ta fito taje part din Wise tace a bani kayan wanki,Wise bata San dalili ba ta kwaso nata ta bata ta zaci ita kadai zata yiwa,ta fito ta fada bangaren Iyamami tace kawo kayan wankinki zan Miki,Iyamami ta washe baki tace Allah ke,irinku ake so ba irin surukaina ba gasu nan basu da mutunci,ai ni dama nafi son wankin hannu yafi kyau,Iyamami ta kwaso kaya ta bawa Salma tace Sabreen kawo wankinki muna ganin yarinya kamar marar kunya ashe itace ta kirki,Sabreen ta tattaro ta Miko itama,Salma ta karba ta taho tana cewa Allah yasa wahala ta kashe ni kowa ya huta ,tayi zuciya yanzu a zuciye ta fita can fanfom garden ta zauna da uban wanki ta wani tare shi na kowa daban daban kamar me kashin dankali.
Dana Auta ta fara,Auta ne ya fito yana waya ya ganta da tarin wanki, na mutane daban daban,baki ya bude yana kallon ikon Allah,ga hadari ya hado sosai amma Salma ko a jikinta wankinta take yi,Auta ne yayi magana yace wai meke damunki ne,aiki fa ake so nayi wahala ake so na sha ba shikenan ba,kin ma yi breakfast? tace a’a, sanye take cikin Riga me siririn hannu da skert,tana wanki gaba daya wuyan rigar ya zazzago dukiyar fulanin ta rabi a waje,Auta ya kalleta ya dauke Kai yayi tafiyarsa ya kyaleta.

Sai da ta gama wankin tas Allah yasa ruwan Bai sakko ba,jikinta har rawa yake sabo da yunwa ta shiga kitchen ta hado tea me kauri ta shanye da bread.
Baso ne ya kirata a waya ta daga,yace ga matata ku gaisa
Auta yana Palo yana kallon Salma a dining,Salma taji muryar mace kuwa tana cewa Kanwata kina nan lafiya? Salma hawaye ya zubo mata ta daure tace lafiya Alhmdllh,Baso ya zaci ya kashe wayar bayan sun gaisa da Salma taji yana bawa macen labari yanda ya siyar da ita,yace Million Daya aka siyi Salma ai tayi tsada ban zaci zata Kai haka ba,yaron nan Auta Dan mutunci wlh ya aureta yanzu ji Alkhairi da yayi min ta tsaya tana shashanci a kaina,Salma tashi tayi ta shige bedroom dinta ta dinga kuka,a fili tace na tsaneka Baso ba ni ba kai yanzu da wani mugun ya bawa ni fa,ranar Salma Sam bata samu sukuni ba,washe gari ma sukuku ta fito zasu tafi school tana tsaye Auta ya gama karyawa ya mike yace muje ta Yaya Baso yana Shan ruwa,harara ta watsa masa ka daina hadani da wannan marar mutuncin ni ba Yayana bane,Auta ya zaro idanuwa yace Bason? tace ae shi din tana kumbura baki,suka fito tace da Auta ka Bude min mota,ya zaga ya Bude mata ta shiga ya rufe yace shike nan? tace ae,ya shiga yayi driving suka tafi, mota a hanya ta shiga security ta kulle kanta da kyar Auta ya gangare kasa yayi parking yace ta mutu fa,Salma tace Kai dai baka iya mota ba kawai,murmushi yayi kawai ya fita tare da Bude gaban motar ya tattaba ya dawo ya mata key taki tashi ya fita ya rufe yace bari na Kira me gyara ya duba ta,waya ya Kira me gyara yace gashi nan su inda yake an fara ruwan sama sai ya tsagaita,ruwa ne ya sakko me karfin gaske kafin Auta ya shigo mota har ya jika shi Salma tace baza ka shugo ba sai Mura ta kamaka a salon a sa mutum jinya,Auta har zai shugo sai ya fasa tunda Salma tace haka ya leko ta glass yace wanka zanyi,baki Salma ta bude tace sai kace yaro, motar ta balle ta fita tazo inda Auta yake ruwa na dukansu ta Bude mota ta tura shi ciki tana dukan hannunsa tace shiga mota baza ka jawo min sabuwar Jinya ba ka kyale ni naji da sharar tsakar gida ma,bayan motarsa akwai kayansa da ya karbo daga wajen guga,Salma tace ka canja kaya gasu nan,yace duk shaddoji ne Kuma a gabanki zan shirya,to me zan gani indai jikinka ne na dade Ina gani,kawai yar Smally ce ban gani ba,Auta yace Amma baki da mutunci Bananar tawa ce yar Smally? tace to ba yaro bane Kai kawai sai ta fika girma haka ake yi,dai dai shekarunka dai dai yanda take,haka aka ce miki? Ya jinjina Kai yace wlh duk ranar dana kamaki duk wannan maganganun sai kin maimaita s…atishawa ya fara jerawa,tace an gamu shike nan dama ai na fada maka,Kaya ya dauka wata milk shadda ya canja,rigarsa ya cire ya Saka wata sannan ya cire wandon nasa har boxers ta cikin Riga ya Saka wani boxers din ya sa wandonsa.
Ya kalleta yace ke baza ki canja ba? tace ai ban jike sosai ba yace to ai shike nan jiki magayi, tace to kayanka zan Saka na zama yar daudu ta juya kanta jikin window ta kwanta a jikin kujera bata Dade ba sai bacci har me gyara Yazo yace ai security ta shiga,ya mata abinda zai mata sannan Salma ta Farka suka tafi.

Yau tun safe suke cikin school kuma sai 5pm zasu tashi,suna fita break Auta yaje ya mata take away har aji ya kawo mata,Yan ajinsu suna ta Kallonsu,Salma ta turo baki tace ka bude min ta koma ta kwanta,Auta ya bude Mata yace gashi nan ya tashi ya fita,tashi tayi da sauri ta leka shi ta window,taga mata sai tare shi suke yi suna gaisawa gashi Auta popular ne a school din,abincinta ta dauka ta dawo bangaren su Auta ta zauna a nan taci abincin duk inda Auta yayi idonta na Kai,shi bai kula da ita bama,sai da suka fito shi da wasu maza biyu suna submiting assignment mata suka zo wajen wata ana ce mata Chima ta dafa kafadar Auta,Auta ya Kalli gabas yamma kudu da arewa yaga Salma a wajen data fiye zama,kanta ta dauke da sauri,da sauri Auta ya janye jikinsa daga bangaren su Chima ya koma gefen Emeka,Inda Salma take zaune ya nufo Yazo ya zauna a gefenta tare da tambayarta me yasa kike son zama a nan? Ae kace haka mana tunda ta’asa kake aikatawa ba alkhairi ba dole kace na fiye zamar muku a waje,wlh duk abinda kakeyi Ina gani sai na fadawa Baffa tunda Kai Dan gatan Mami ne Baffa zan fadawa abinda kake yi a school,Auta yace Allah ya baki sa’a wai mene damuwarki Dani tunda Baso kike so Ina ruwanki dani,tashi tayi ta tafi.

Suna komawa gida sai bangaren Baffa yana nan kuwa Mami tana wajen ta shiga ta durkusa ta sake gaishe su suka amsa,Salma tace Baffa Karar Auta na kawo,Baffa yace Ina jinki Salma me yayi Miki Kuma,tace Auta fa ba karatun yake ba,abinda aka kaishi baya yi Kuma ance indai kana zaune da mutum kaga abinda zai cuce shi ka fada,gaskiya Auta asarar kudi akeyi kamata yayi ma a cire shi daga school ya dauki hanyar lalacewa,ko wacce mace tazo ta dinga rike shi wlh kala kala ko Ina yake mata suna nan,dama an San Auta da shegen son mata a baya,Baffa yace zai aikata zan masa fada Kuma kin kyauta da kika fada min,Mami tace Ina Autan? Salma tace ai yasan bashi da gaskiya ya buya a daki,murmushi Mami tayi tace to za a masa fada, tace to ta tafi tana murna tace Allah yasa a cireshi daga makarantar, Su Mami su dariya ma ta basu ko zancen nasu yiwa Auta ba,ita Kuma Salma ta zaci an masa fada.

Bayan taci abinci ta huta sai da ta yiwa Auta girkin dare.
Washe gari da sassafe tayi sharar compound tazo tayi Shirin school suka tafi tana murna an yiwa Auta fada suna zuwa taga mata dai Basu fasa abinda suke ba,Salma sai ta koma gadin Auta sai ta bar lecture ta fito tana leken Auta,ana tsaka da lecture ta dauki Escuse ta fito taje ta lallaba a boye ta gano Auta yana nan lafiya a zaune shi kadai ba mace ta koma aji,ba a Dade ba ta sake ficewa ta zo saitin window inda Auta yake zama ta leka shi ya juyo da sauri,ya ganta tana lekawa ciki,yace mene ne ko Kun tashi ku? yana Mika zazzabi yake ji Mura yake,tace a’a ta juya tayi tafiyarta,baki Auta ya tabe yaci gaba da duba littafinsa,sai da suka gama lecture suna jiran 1hr su shiga wata,Salma ma ta fito su sun gama gaba daya,inda Auta yake zaune taje ta tsaya tare da Mika masa littafinta tana kumbura tace Assignment ne ni ban iya ba Allah,nayi nayi na kasa ni ban ma gane ba,gefensa ya nuna mata yace sit,zama tayi yace Allah yasa Nima na iya,tace yo ai da kyar zaka iya din tunda ba karatun kake ba burinka mata su tabaka,Auta yace ae Allah ai mata akwai dadi,ta kule sosai tace dama ai dama dadi kake ji Kuma Allah yana rubuta maka zunubi,littafinta ya duba ya kwala mata biro a kanta yace wannan ne kika kasa ganewa sabo da bakya ja duk katon kan nan a banza,baki ta turo masa hannunta me kyau fari ya sha lalle maroon ta Mika masa tace bani abina,Hannun nata yabi da kallo yayi kyau,yace kalli yanda zanyi zan koya Miki,yana mata explanation ta zuba masa Ido har ya gama yace kin gane? Salma Shuru,kafadarta ya girgiza tayi firgigit yace Zaki kashe kanki da tunani fa akan Baso,kin Hana kanki sukuni,gaki kyakyawa sai cutar kanki kikeyi,Salma taji kanta yayi wani girma an yabeta,Ido ta lumshe tayi murmushi,murmushi yayi yace yar Baso an fara hankali kwayar ta fara sakinki ne? Kanta ta dauke ta mike zata tafi ya jawota ta zauna jagwab yace Ina zuwa? ta zaro masa ido lokaci Daya ta lumshe,kallonta ya sake ta sake zaro Ido ta Maida abinta normal,murmushi yayi ya mike yace time dinmu yayi bye,ya barta a zaune tana jiransa, Headphone ta makala a kunnenta tana jin Waka tana kallon Auta ta window,Shima jefi jefi yana kallonta.

Washe gari Babu school Auta bazai je Office ba yana gida a kwance yana zazzabin Mura,Salma kamar kullum tayi aikinta Share ko Ina na gidan ta dawo ta dauki break fast dinsa ta nufi dakinsa tana zuwa ta ganshi a kudundune cikin bargo,tace dama daga ganinka kalar cuta ne sai da nace ai Karka shiga ruwa ka shiga ai gashi nan,ta Bude bargon ta ganshi daga shi sai boxers,tsoro taji ta rufe shi da wuri ganin Antenar Auta,tace Kai wannan ta mussamman ce kaga yaro,Zarangade sunan wata ciyawa, a’a wannan yayi aurensa ya samu Industry me kyau wannan sai dai manyan mata masu Industry a baje Ina mu Ina wannen , kitchen ta Koma ta masa shayin ginger kaninfari da masoro yayi yaji tare da saka sugar ta matsa lemon tsami kadan ta hada da Zuma ta kawo masa,Mami ta iske a wajen Auta,Mami ta Kalli Salma tace wannan fa tace tea din ginger na masa ko zai samu lafiya yana magani,Mami tace an gaisheki an fara hankali ashe,dariya tayi tace Mami ai sabo da ku nake yi badan shi ba,Mami tace kuna waya da Baso kuwa? tace a’a Baso ai ya zama Mugu Ina kiransa zai bani wani aikin Allah Mami Kalli hannu na tsabar rike tsintsiya har ya canja,gidan yayi girma a tausayawa Marainiya,tayi magana tana marairaicewa,Mami tace so muke kiyi hankali ai,tace nayi Allah,Mami tayi murmushin jin Dadi tace ban yarda ba,Salma ta marairaice tace a canja min wani Dan Allah Mami Allah naci ubana yanzu,Mami tace to bari a Kira Baso a ji,Salma ta zaro Ido tace shike nan na shiga uku,Mami ta sake Kiran Baso bayan sun gaisa Mami tace Salma ta gaji fa ta nutsu yanzu,Baso yace da saura ku Daina tausayinta mage ce me kwanciyar daukan rai,Mami tace a’a na canja mata ta Daina komai yanzu zata dinga yin aikin Auta kawai,Baso yace a Kara mata da goge windows na gidan duka,Mami tayi dariyar muguntar Baso,ta mikawa Salma waya,yace kina jina? tace ae yace goge windows duka na gidan,Salma ta hango Uban windunan tace Dan Allah a Maida min sharata,dawo sharar Yaya,Baso sai da yayi dariya yace to yanzu dai zan Miki sassauci yace kinga Mami Idan kika sake tayi girki da kanta ta bada wanki wani waje da shi Kansa Auta to wlh sai na kusa halaka ki,Kuma yanzu a dakinsa Zaki dinga kwana Idan naji baki je ba sai na zo garin,tace to,yace saura ki masa rashin kunya Dan ubanki,Salma tace indai wannan ne ai da sauki zanyi,yace yawwa sannan ke Zaki dinga shirya shi kullum kaya Idan zai Saka sai kin Taya shi Idan ya fada min baki yi wayyoooo Salma kin gama yawo Idan nazo,Salma Kam ita an rage mata wahala murna take tace to,yace Banda fadar sunansa gatsal,tace ai bana fada ka tambaya kaji ban taba fada ba,yace yawwa Idan kinyi abinda nace to Baso yana kaunarki,Salma farin ciki ya kamata Baso yana sonta sai washe baki take yi.

Mami tana kallonta tace Allah ya kyauta ni Kam me Baso yake baki ne Salma Wanda babu a gidan nan? Salma tayi shuru tace Babu Mami komai kunfi Baso kawai shakuwa ce da yanda yake kula Dani duk da yana dukana amma ni nake cewa ina sonsa shine yake dukana akan haka,Baso yana da kyawun halaye Wanda sai Wanda ya zauna da shi zai gane,Ummm Mami tace,kin san dai kina da aure Kuma babu kyau a Musulunci son wani kana da aure,tace ba kyau na sani Ina so na Daina na kasa ne,Mami tace Allah ya kyauta, Auta yana jinsu a cikin bargo,Mami ce ta bude bargon tace tashi kasha magani,Salati Mami ta saki ganin Auta yana kuka,bata kawo komai ba tace duk cutar ce,ae kawai yace, Salma ta dawo gefensa da sauri ta zauna tana taba wuyansa tace a lallai jikinka da zafi lallai kayi kuka kayi hakuri baza ka mutu yanzu ba,ai cuta ba mutuwa bace,Mami tashi tayi ta fice jikinta a sanyaye tasan Auta karya yake ba kukan cuta yake ba,Salma ce ta haura saman bed din tace sanyi?

Kai ya daga mata kawai,ta goge masa hawayen da hannunta tace haba sabo da Kai Auta ne sai shagwabar tsiya,dariya yayi yace ke yar fari ce ai shi yasa kike baki da saiti,gaki kwaila gaki yar fari,gaji rainon Baso dole baza a ga daidai ba,Salma tace kwaila tana gidansu, maganin ta bashi yana sha tare da sarkafo hannunta ta kafadunsa tana bashi a baki sun jere a tsakiyar bed,sai kallon Auta take kamar ba gobe,a hankali tace Auta me gemu,juyowa yayi suka hada Ido suna kallon juna sun tsurawa juna Ido,A hankali yace a aske bai Miki ba? tace a’a ka barshi mana ya maka kyau.

Yace ai Baso ya fini kyau ko? tace haba Karka cuci kanka ai ba hadi, tace kwanta bari naje na maka girki,yace ki barshi ni bana jin yunwa,no kazo ka fara yiwa mutane kuka gwara a baka ni ai Kuma naga ta kaina wajen Mugun Bawa ta mike ta fita,bata Dade ba ta dawo da abinci ta ajiye a gefe,yaji sauki har waya ma yake dannawa tace ga abincin,yace haka aka ce a bani abinci? Zama tayi a gefensa ta bashi a baki yana Dana wayarsa,Salma tace Enjoyment Allah ya biya dai Auta.

Yana gama ci tace wanka fa,ya tashi ya shiga toilet,ta fito masa da kayansa na sawa,yana fitowa ta shiga toilet garin wankewa santsin tile ya kwashe ta damfara da kasa ta bige kwankwasonta da jikin sink,kasa tashi tayi,Auta yaji faduwar Abu yace lafiya? Kuka ta saki ya shiga toilet din tana cewa wayyo kuguna ta rike kugu tana cewa bazan iya tashi ba,Auta ya dauketa ya kawota saman bed tana kuka wayyo kuguna,Auta yace Sorry ba tarbiyya,yasa hannunsa a kugunta yana murza mata yace Babu lafiya yanzu haka nan ma duk part of industry ne ko? Hannunsa ta bige yayi dariya yace ki tsaya na iya gyara targade inji karyar Auta.
Hannaye yasa a mazaunanta ba inda ta bige ba can tudun mazaunan yace wannan ai mountain ne me zaman kansa,tace tsauni Kuma gaskiya Kai Dan duniya ne dama abinda zaka min kenan haka ake gyara targaden? ta kifa cikinta ta nuna masa daidai kugu ba mazaunai ba tace nan ne fa,Auta yaki tafiya yace ai a faro shi tun daga tushensa harda tofa mata Addua tup tup yana lagudewa yarinya mazaunai,dariya ta fara tace wlh kamar kana min cakulkuli wannan ai ba haka ake yi ba,Auta yace ke Addua ta karye ba a magana Idan ana yi ni sai an dawo farko,ni nawa lakanin haka yake ba a magana kiyi shuru tam,sai da ya lagwigwite mata mazaunai yace yarinya dake sai abubuwa haka tashi saura na tsaye, tace har na tsaye Kuma,yace ke Zaki koya min aikina ko me zan fadawa Baso,Salma tace bazan iya tashi ba da zafi ka daga ni ,Auta ya riketa ta mike tana dingishi,.
Jikinsa ya manna a nata sanye cikin boxers yake kacal,ya tallafo mazaunanta,Salma rudewa tayi jin Antena a bayanta ga Auta yana ta gyaran mazaunai,tace ya gyaru haka naji sauki,Auta ya fara fita ma a hayyacinsa da kyar yake magana yace ai ciwon zai waiwayo ki nan gaba a ka’ida sai an yanka kaza nake gyarawa mutane amma sabo da kece ma ake Miki kyauta yanzu sai nayi sadaka da kudina,Salma wani bakin ciki ya kamata tace yanzu haka kake yiwa mutane gyaran targaden har mata?

Cele suna zaune a Palo ita da kaka tana duba yanda ake aikin hajji ingantacciya a cikin wayarta suna karantawa tana koyawa kaka,Kaka yace yanzu dawafin bankwana bazan juya na Kalli ka’abah ba kallon karshe Idan zamu tafi? Cele tace babu kyau Idan akaje dawafin ban kwana ba a juyawa a Kalli ka’abah kana gamawa fita zaka yi ba juyowa fahimtun? Kaka yace Na’am.
Bayan aikin hajji Yazo su Cele aka dauki niyya suka harami suka fita,su Mairo ma duk sun fita aikin hajji,Ahsan ma yana ciki da shi ake aikin hajji bana sabo da Cele,motar da zasu tafi filin Arfa shi yasa karama aka dauke su Basu sani ba,haka suka yi aikin hajji ingantacciya cikin kwana uku kaka yayi aski Cele ta Yanke gashinta dai dai Gabar karamin yatsa sabanin su masu gashi kawai sharbe shi suke yi yanda suka ga dama,Cele anci sa’a dake aikin hajji ne bata yiwa kowa masifa ba sabo da kar ta bata aikin Hajjin ta har sai da suka gama lafiya sun gama duk wani Shirin dawowa Nigeria Cele ta fara zazzabi sosai,Hammad driver Ahsan yana ta Kira ba a daga ba ga Kaka ya tafi yiwa mutanensa Sallama Idan tafiya ta tashi kawai sai dai su wuce,Hammad jin ba a daga ba sai ya tafi gidan ya buga shuru ba a Bude ba,kofar ya Murda ya shiga ya samu Cele tana kudundune a bargo tana rawar Sanyi,dawowa yayi gida da sauri yace Ahsan na samu Cele bata da lafiya tana ta rawar Sanyi da Alama zazzabi take,Ahsan hankalinsa ya tashi ya dinga yiwa Hammad masifa Kuma sai ka taho ka kyaleta haka Idan ta samu matsala ya ja tsaki ya karbi key ya fita da sauri a mota,yana zuwa direct gidan ya shiga,ya Samu Cele ta sume ma bata hayyacinta,hankalinsa tashe ya sunkuceta sai asibiti,aka bata gado yana ta zirga zirga ya rasa inda zai sa kansa.

Komai da sunansa aka cike mata,bata Dade ba ta farfado ta Bude idonta sai ga likita ya shugo bakin fata ne yana jin Hausa sabo da Cele Ahsan ya nemo shi,ya tsaya a kan Cele yace sannu kin tashi jini ne ya Miki karanci a jiki bakya shan magunguna,Cele tace ai na zaci abinci ya Isa jinin yayi yawa,yace ai dole sai kin sha magani,Bai Kai a Kara Miki jini ba amma sai kin sha magani dole,yace Wanda ya kawoki Ahsan dama ya damu yana zaune baida sukuni sai zirga zirga yake ya rasa inda zai sa kansa,Cele tace Ahsan Kuma? Yace ae balarabe ne shine ya kawo ki,yanzu Ahsan ne ya kawo ni? Yace ae bari a turo Miki shi,Doctor ya fito ya samu Ahsan ya rasa inda zai kansa,likitan yace zaka iya shiga ta tashi Dan Allah a kula da ita ta dinga Shan magani,yace Inshallah ya nufo dakin da Cele take a hankali ya turo kofar ya shigo,Cele farin ciki ya cikata amma a zuciyarta,a fili Kuma harara ta watsa masa ta dauke Kai,Murmushinsa me tsada ya sakar mata.

Kujera ya samu a gabanta ya zauna tare da dora hannu a wuyanta Hausa taji yayi yace ya jiki,mamaki ya kamata tace la kaji Hausa,yace yanzu ya jikin? tace da sauki naji normal yanzu za a iya sallamata,yace anjima zasu sallame mu,hannu ta Mika masa ya rike suka damke hannaye waje daya,tace Ina bakar kadara? ba komai yake ji a hausar ba yace dai wa? tace Maheerah,tsaki ya ja yace kar ki sake min zancenta,Hammad ne ya shugo Cele ta Bude Ido tace Karka cuceni masoyina Yazo Karka sake naji bakinka kace kana so na a gabansa ni wannan nake so,Ahsan tashi yayi ya koma gefen Cele ya zauna kamar zai hadiyeta,Hammad zaiyi magana Cele tace ahir Dinka taimakon da ka mana ka kyauta mun gode Dan Allah Karka kashe min aure,dariya Hammad yayi,tace Idan kana yiwa Allah ka kama gabanka harda hawayenta,Hammad yace hear me out please ki saurareni.

Ya fara bata labarin komai yace ni fa bani nake Miki kyauta ba ni yaron Ahsan ne komai kike gani shi ya turo ni,yace har sadakar da aka taba tareku aka baku shi ya tura balaraben,gidan da kuke,siye awararki,kuje Shopping ace an biya muku duk shine ba ni bane,dama sani yayi sabo da ya sake gwadaki kina da son kudi ko babu Zaki so ni ko a’a,sannan ya auna irin son da kike masa,Cele ta Kalli Ahsan tace to bazan zauna a saudiya ba sai dankwali yaja hula Idan kana so na sai dai ka siya min gida a Nigeria ko muyi 50-50 Idan muka yi wasu months a Nigeria sai mu dawo nan muyi watanni sannan sai da kaka a kusa Dani ayiwa kaka bangarensa,Ahsan murmushi yayi yace yanda kike so,yaushe zaku tafi? tace nan da sati biyu,yace a daura mana aure sai ku tafi zanzo bayan satikai,Cele tace ba matsala da larabci,ana sallamarsu daga asibiti.

Aka siya mata magungunan, Ahsan mota ya Bude mata ta shiga ya rufe bayan motar ya shiga shima su biyu a baya,juyowa tayi zata saci kallonsa Shima ya juyo suka hada Ido,Cele tayi fari da Ido,hannu ya Mika mata ta Miko masa hannunta zoben Gold ya zaro a aljihunsa a cikin gidansa ya sa mata a Hannun,Cele tayi masa godiya tana kallon yatsunta
Suna zuwa gida suka iske Kaka yayi tagumi baiga Cele ba,ai ganinta da mutane yace Ina kika shiga batan kai kika yi? Cele tace kasan ka fita bani lafiya ta kwashe labarin komai ta fadawa Kaka, tace Wanda na gani nace maka kamar Ahsan ai kuwa shine din,Kaka yace Alhmdllh Masha Allah,ya bawa su Ahsan wajen Zama suka zauna,,ya Kalli Hammad ya masa ambola dakuwa yace ungo nan,Ahsan ya kalle shi Shima kaka ya masa dakuwa yace Kaci ananinka zaka yi wasa da kwakwalwar mu,Kaka yace Cele to ke yanzu kin yarda Zaki aure shi? Cele tace dari bisa dari Kaka,a nan wajen akayi maganar aure da kaka da kudin da za a kashe.
Kaka yace to mufa duk sharudanmu sai ka cika har lefe,Ahsan yace ba matsala Idan Yazo kasar Nigeria zai taho da lefen karsu damu.
Sai dare su Ahsan suka tafi, Cele tace Kaka na karo wulakanci Yasin,Kaka yace yo ai ba ke kadai ba Nima na karo wulakancin harda rashin mutunci ma, Cele tace dole na gayyaci Yan madugo Yasin suzo suga yanda ake abin arziki.

Washe gari da yamma Ahsan ya dauki wanka na kirki Yazo zance,Cele harda kwalliya aka Saka sabuwar Abaya kamar a Nigeria ta fito tana taku dai dai,Ahsan ta hango shi yake driving ya harde a jikin motarsa yana kallonta yana wani murmushi,Cele tana karasowa dama suma ba ruwansu ba wata doka suke bi ba, ya rungume ta a jikinsa Cele tana shakar kamshinsa me Dadi kiss ya mata a goshi yace ta shiga mota suje yawo,to akwai freedom, ya zaga tare da Bude mata mota ta shiga ya rufe ya koma ya shiga Shima suka tafi,suna tafiya suna Hira yana cewa dagewa yayi ya koyi Hausa wajen Hammad,yace Kuma na shiga Makarantar turanci zalla yanzu Shima yana tsinta.
Wuraren shakatawa ya Kai Cele,suna nishadinsu ,da zasu dawo Cele tace ya kaita tsohon gidan su na yan lesbian,Bai san me zata yi ba ya kaita ta fita ta shiga gidan da gadara ta kwala Sallama tace Yan Iskan gidan nan ku fito Ina gayyatarku bikina ranar Friday daurin Aure kuje za ayi walima,fitowa sukayi tace da gaske nake ana daurawa washe gari zamu wuce Nigeria,yanzu ma tare muke da shi,sabo da gulma sai da suka dinka lekawa suka ga hamshakin balarabe,Meenal tace na yarda ai kin Kai a so ki nima ba gashi Ina cikin jerin masoyan ba,suka ce sai munzo,Cele tace Idan ma baku zo ba kanku kuka yiwa domin za a bankare raguna za a soke rakumi ato, ta juya ta tafi,ta shiga mota ya mata take away na kayan makulashe ya sauketa a gida.

Ranar juma’a kuwa Kaka da Wanda ya sani takari maza suka je masallaci inda Yan uwan Ahsan da abokansa mutum biyu suka taru aka daura Auren Cele da Ahsan akan Sadaki Million Daya a kudin Nigeria,Cele kuwa tayi gayya sosai ranar da yamma takari suka dinga layi,Ahsan ya kama musu wani joint an gasa raguna ga su Madara da kayan ci iri iri Kaci iya cinka ka barshi,da kanka zaka eba ka yanki rago a bankare,Takari banza ta fadi bakin kowa da maiko,Cele taci gayu cikin Arusa rigar Amare fara komai fari an mata make up gashi rigar da kalar mayafinta ta musulman larabawa sai tsada,Kidan labarawa na tashi a wanjen ana laftar raguna,Babu Namiji ko daya a wajen tunda walima ce amma Kaka yana wajen shi yaja gefe yana ta kwasar gara ko magana baya yi,Sai dare suka gama Ahsan Yazo da Kansa ya sha kayansu na larabawa harda Dora Alkyabba golden color irin shigar masu kudin larabawa,Sun zuba pics iri iri,Ahsan yana daukan Cele yace yau tare zasu kwana,Cele tace a’a wallahi ban yarda ba ni,ta fututtuke masa ita bata yarda ba,Ahsan yace mene aciki Matata ce fa ke,Cele tace wlh ban yarda ba ni gaskiya azo ayi min kaca kaca na tafi gida da rubabben fada baza ta yuwu ba,lah..lah.Ahsan yayi murmushi yace to ko romancing? Cele tace zero wallah kayi hakuri kazo can mu gama shirya komai sannan,Ahsan harda wa’azi wai ba kyau ta guji mijinta,Cele tace daga baya sai ka yafe min, wallahi Yasin Ina sam Alqur’an bada ni ba,tana nunawa da hannu, parking yayi a kofar gidansu,har tasa hannu zata fita sai Kuma ta fasa ta juyo ta turo masa baki tace ungo yi kaji,ka ganka harda wani komawa maraya da Kai, ta fada da larabci,yayi dariya ba musu kuwa ya tallafi fuskarta a hankali yana tafiya a hankali da fuskarsa zuwa tata,Cele tace ah naga ta kaina komai sai anyi cikin sanyin jiki haba Salihu komai style baza a tafi straight ba,a dinga komai da jiki,na auri iyayen soyayya ya zanyi dole na koya nan ba kaskon suyar Awara bane ba fa,dole Ina komawa na tafi wajen Nazifa ta koya min slow motion Nima,bakinsa ya hade da nata ya fara mata wani irin kiss na mussamman,Cele tace eho kaji kaina wani yammmmm,duk da bai gane hausar ba yanda ta danyi ihun ya bashi dariya,yaci gaba ta sake janye bakinta tace taratsatsi akeyi a cikin kaina ta rankwashi kanta tace muje zuwa Malam Hafizu,a soyayyar ma Kai Hafizi ne ja muje,Ahsan yaci gaba Cele ta sake kwace bakinta ta sheke da dariya harda bugar jikin motar tace Allah Dadi shegu ashe haka ake ji,ta sake conowa Ahsan baki ,yanda tayi sai da ya dinga dariya,tace wallahi Fada wani zuut zuut take ta karbi kidan,suka ci gaba da kiss Cele harda tafi tace yau Ina karbar darasi wallah yo in da wannan ai masifar ma dainawa zanyi,sai da yayi kissing dinta yanda yake so duk Cele ta zurma ta zauce a kiss kawai,zata tafi harda manta Jakarta sai da ya sauke glass ya Kirata ta dawo ta dauka suka yi Sallama yana ta murna kamar an sashi a Aljanna.

Cele da gudu ta shiga gida kaka Yace ya akayi har na rigaki zuwa gida tun dazu Ina kuka tsaya ne? Cele tace Kaka soyayya muka yi,Kaka ya Dafe kirji yace ki bari sai an kaiki dakinsa,Cele tace ai dama ta wuce bedroom ta fada saman bed dinta tana ta murna harda tsalle tace wayyo Allah dadi kashe ni,Guy nan ya hadu matsiyaci kaga kiss,jikin mudubi taje ta tsaya tana kallon bakinta tace ya bani ta nan ya bani ta can a’a,Gaskiya kullum sai munyi,boobs dinta ta kalla ta lumshe ido tace sai naji Ina so a taba su,to Kai kuyi hakuri sai next time ku dai abinda nake so da ku shine ku cika masa hannaye kunga dai tsohuwar matarsa tana da su karku bani kunya kunji yawwa, ta baya baya ta ja ta fada a saman bed tace yau bazan iya bacci ba.
Washe gari Ahsan shi ya Kai su Cele Airport da kayansu,a mota ma sai da suka Kara kiss amma kadan tace sai kazo suka tafi Yana daga mata hannu ,sai da jirginsu ya tashi sannan Ya koma gida Shima zuwa dare ya koma Riyad,Maheerah ta haukace jin labarin Ahsan yayi aure tace ba a Isa wata ta shiga gidan ba ta dauki alkawari.

Mami ce ta shigo da niyyar duba Auta taga ya jikin nasa ta same su a tsaye yana faman lagudewa Salma duwaiwaka tana cewa nan haka nefa,Karar Bude kofa suka ji da sauri Auta ya sulale kasa yana taba kafarsa yana cewa har yanzu kafar nan bata karasa warkewa ba,Salma itama ganin Mami da gudu ta duka tana cewa Sannu ai sai a koma asibiti,Mami juyawa tayi tare da rufe musu kofar su tana mamaki,tana fita Auta yace na shiga uku,Salma tace Kai tafi can dama ba abin kirki kake min ba tunda gashi nan kaji tsoro,Auta ya harareta yana kallon hannayensa yana cewa daga gyara sai ya zama abin tsiya,tace ae Karka sake taba ni bana so,ta juya ta fice abinta.
Tana fitowa suka yi Ido hudu da Mami a zaune tare da Miracle,Sosa Kai ta fara tana maurmushin borin kunya tace Mami Auta gaskiya yana jin jiki sai an dage a Kansa,Mami tace au haba?tace uhm ta zauna tana kame kame Mami yaushe za ki min kitson? Mami tace sai gobe tana ganin kinibibi a fili,dariya tayi a ranta Kuma ita Kam taji Dadi,Miracle tace Salma kina da gaskiya kuwa sai wani soshe soshe kikeyi,da sauri tace Wallahi Aunty Ina da ita ba abinda muka yi bamuyi komai ba,Mami tace kawo min ruwa a kitchen,ta tafi da sauri dama kadan take Jira ta fece.
Miracle ta dawo gaban Mami da kwana sabo da cikin,Nawwar ya hanasu sakat da sintiri watarana ma a nan yake kwana, yau Monday Nawwar yana Office daga ita sai Mami a Palo tana jin ciwo sama sama tace Mami wallahi kamar nakuda nake yi,Mami tace haka ake nakudar lallai baki San nakuda ba ai sai kin tubure mana tukun,Rabi tace to ta tashi da kyar ta shiga bedroom ta kwanta ciwo ya fara maguzata bayan awanni tun tana daurewa har ta gaza ta fito fakat daga dakin tace Mami har yanzu ban tubure din bane? Mami tace ahhh kin tubure kwarai kuwa nakuda ta kankama bakya hayyacinki tunda kika ce haka muje asibiti,a wajen ta tsuguna ta dafe mara tace wayyo Allah, La’ilahaillallahu kasusuwa na suna farkewa suna budewa wayyooo shike nan kasusuwana sunyi warka warka,Salma ce ta fito ta rike Rabi kamar itace zata haihu wayyihuhu jama’a ku kawo agaji,Auta ne ya fito sanye cikin jallabiya,Mami tana hado kayan haihuwa,Auta yana zuwa ya dauki Rabi cak ya fita da ita har cikin mota Salma ta fito da gudu tace ni zan karbi haihuwa ta shige gaban mota,Auta ya rude ya manta ya tafi ya bar Mami,tana fitowa su har sunyi nisa,Salma ta cikin motar ta tsallaka baya tana dannawa Rabi ciki tana cewa daure,cije,manne,ke kamar ba mace ba Nawwar da kike Kira me zai Miki kyale Nawwar ki Kira Allah.

Rabi ta samu Salma ta kankameta tana jijjigata ta buga kan Salma da jikin glass din mota sabo da azaba tana cewa wayyo Allah Nawwar wayyo zan mutu,Salma ta dafe Kai tace ka Kira Mami zata sumar Dani,Auta ya dinga dariya yace uban wa yace Miki ana zuwa a dinga yiwa me nakuda katsalandan,Salma zata gudu Rabi ta riketa Kam tana cewa Idan kika tafi mutuwa zanyi wayyo Allah,Salma Idan kika tafi mutuwa zanyi ki rikeni ta Miko hannu,Salma ta riketa Rabi ta fisgi Salma kamar zata karyata,Salma ta fashe da kuka tace Nima zata aikani lahira,Mami sai driver tasa ya kaita can,Auta ya kirawo su Star kafin kace me duk sunzo har Wise,Nawwar kasa driving yayi sai Auta ne yaje ya dakko shi,gaba daya ya haukace ya rude,Santana har da shi ya wani falfalo yana wayyo miracle yau za a yabawa aya zakin ta,da a baya ne ai nine zan karbi haihuwar lokacin Ina Hajiya Santana ta,yanzu kuwa na koma Kai maimakon ke.

 

 

Kuyi hakuri wallahi bani da lafiya zabbabi nake malaria da kyar nayi typing.

 

 

AsmaBaffa
08061929616’YAR AIKIN KARUWAI 2
MATAFIYA

BOOK 2

66-70

Official

By
AsmaBaffa

 

SADAUKARWA GA
ZAINAB USMAN

 

Adashin kudi kamar haka
20k kwasa 200k
Slt 1 2 4 7 8 9 10

30k kwasa 150kslt1 2 4 6 8 9 10

50k kwasa 500kSlt1 2 3 4 5 7 8 10

10k kwasa 100k Slt2 3 2 4 7 9 10
Mebukata yaneme wannan numbern
09049197049

Munayin adashi kamar haka
Kayan daki set na kujera da gado
Kayan kitchen
Freezer fridge
Injin wanki
Gas
Dasauransu
09049197049

 

Page naku ne

Ummu Minnah
Ummu Annur
Aunty Nurse Zariah
Princess
Maman Ahmed
Mrym
Maman Aslam an Abdul
Mamar Bintou
Ummey Muhammad
Maman Murtalah
Sumayya Auwal
Ummu Lateefah
Mommy Sadiq

Ummin Sadeeq
Ina gaisuwa

 

Back to top button