Ikraam 103
Ikhram~By Khaleesat Haiydar
103…..ihu ta kwalla tana kuka sosai kaman mahaukaciya, cikin ihu da tsiwa tace “bana sonka ka sakeni ko dolene auren”, yana huci ya dagata yakara kifa mata wani wawan mari, tafashe da kuka sosai jikinta narawa, shaketa yyi idonshi sunyi jajir, banko kofa Maryam tayi arude tace” Dear kasheta zakayi, ka saketa, kasan yarinya ce karka biye mata”, ganin ko kallonta bayiba ga Ikhram na kakarin mutuwa yasa takama hannayen shi tana kokarin fizgesu daga wuyan Ikram, wurgar da Ikram yayi ya juyo ya kifama Maryam wani hadadden mari, ya Dakar mata tsawa “get out”, dafe kuncinta tayi tana hawaye tajuya tafita da sauri. Juyowa yayi ya kalli Ikhram data durkushe tana kuka kaman ta mutu yace” inkinga dama kill ur self, amma bazan taba sakinki ba,saidai inzakije ki auri wanda kikeso da aurena akanki”, yay tsaki ya juya yafita ya banko mata kofan.
Ikhram aranan ko bacci batayiba kuka kawai take idonta sun kumbura sosai, farar fatanta yay jajir, da asuba da kyar ta mike tai salla, tanajin fitan Khalil masallaci ta zira hijab dinta tafito, ahankali take tafiya harta bude kofa tafita, tafita daga gidan gabaki daya, dudda tsoro na kamata dan gari bai gama wayewaba amma baisa tafasa abinda tai niyyaba, kuka take tana tafiya tana waige waige, harta fita daga unguwarsu, tai tafiya sosai kafin taga wani mai adaidaita ta shiga, karfe 6 saura ya sauketa a gate din gidan Mami, naira dari uku tabashi tajuyo tana rusa kuka zata shiga gidan, Aliyu tagani tsaye jikin gate din da farin jallabiya ajikinshi da alamu daga mosque yake, ya folding hanunshi akirji yana kallonta, kuka sosai takara fashewa dashi tabi ta gefenshi tabude gate ta shiga batare datace mai komiba, da gudu ta shiga gidan tana kuka kaman ranta zai fita Aliyu yabi bayanta, dakin mami tashiga mami bata dakin, ta duba bayi bata ciki da sauri tafito ta sakko kasa tai hanyar kofa zata fita tana rusa kuka, hannunta taji anriko da sauri tajuya taga Aliyu ne, fizge hanunta tayi tajuya zata fita ahankali yace “maiya faru ikhram? Maiya sameke? Why re yhu crying?”, juyowa tayi cikin kuka tafada kanshi tana wani irin kuka mai cin rai, lumshe idonshi yayi yature ta daga jikinshi da sauri yace “wots wrong? ” cikin ihu tace ” oh tambaya kake wots wrong, u don’t even know wots wrong”, kama wuyan jallabiyan shi tayi cikin kuka sosai tace ” ya Aliyu maika min?Maisa nake sonka,Maisa nakasa son mijina mai sona, maisa dudda kai ka karyamin alkawri nina kasa karya nawa, why, why, why Aliyu?, maikamin mesa nakasa mantaka? maisa nakasa daina sonka?”, Sakin jallabiyan shi tayi ta durkushe agabanshi tana kuka sosai hawayenta na zuba a kafanshi, shiru yayi idanunshi sunyi ja, ahankali ya tsugunna yasa hannu ya dagota tana kuka sosai, handkerchief yaciro daga aljihunshi ya mika mata, daga idanunta tayi ta kallai da sauri ya kawar da fuska, karba tayi ta rungume handkerchief din akirjinta tana wani irin kuka, jin anbude kofan falo yasa Aliyu ya daga rinannun idanunshi Khalil yagani idanunshi sunyi ja, kallon Ikram yayi yanda ta rungume handkerchief din Aliyu tana kuka sosai agabanshi, da sauri ya juya zai bude kofa yafita, ahankali Aliyu yace “Khalil”, tsayawa yayi batare daya juyoba, takawa Aliyu yayi yaje wurin, hanun Khalil dake hawaye a wurin yakamo suka karaso cikin talon, ahankali Aliyu ya kamo hanun Ikram dake kuka kaman ranta zai fita ya hada hannayen su, Ikram da Khalil suka daga kai suka kallai, murmushi yay musu ya juya ya kalli ikhram ahankali yace ” Rabi’a”, da sauri ta kalleshi, yace” na dade da hakura dake,na dade da barma brother ke tunda nagane yana mugun sonki starting 4rm d 1st day daya ganki, koda brother zai sakeki bazan taba aurenki ba Rabi’a, dan nasan u were not meant 4 me”, Ikram takara fashewa da wani irin kuka tana kallonshi, girgiza mata kai yayi idanunshi sunyi ja yace “yes Rabi’a, sometimes Allah na amfani da So ya maka jarabawa, same happen to us, Rabi’a don’t u think Allah nason ya jaraba mune da ya kaddara aurenki da Khalil?”, takara kallonshi, murmushi yamata yace “yes, and dole muyi imani da kaddaran and take it, nadade da hakura dake, nabarma brother Khalil ke, Rabi’a learn to accept faith, ki kaddara all dis was destined, luv ur husband mai sonki mai kaunarki na tabbata bazai taba cutar dakeba”, Ikram ta juyar da kanta ta kalli Khalil wanda taga hawaye yake shima, takara kallon Aliyu zata fashe dawani kukan ya girgiza mata kai yace “no, inaso ki manta dani in ur lyf, ki daukeni as ur blood brother, ki manta muntaba soyayya arayuwa, kibi mijinki kuyi rayuwan sunna rayuwan aure”, da sauri yajuya musu baya hawayen idonshi ya share da sauri, yace “Rabi’a dagayau kibar kallon Aliyu a matsayin abin kauna, but look Aliyu as ur brodza kinjiko”,Ikram ta girgiza kai cikin kuka ahankali yace “2min”, hawa stairs yayi yaga mami tsaye tana kuka, da sauri yabi gefenta yawuce dakin Sudais Ya shiga, dakkoshi yayi yana bacci da nursing bag dinshi, kiss yama yaron yace” I luv yhu son” ahankali ya sakko kasa yasame su har alokacin Ikram kuka take, mikama Ikram sudais yayi ta karbai ahankali, ya mikama Khalil nursing bag shima ya karba yana kallonshi, Aliyu yay murmushi yashare gutun hawayen dake neman zubowa, ahankali yace ” daga yau sudais yadawo danku,nabar muku shi”, ya kalli Ikram dake kallonshi yace ” Rabi’a kindawo mum din sudais, wanan shine gift dina gareku amatsayin babban yaya ga both of yhu”, yace “Khalil nabarma sudais kabashi tarbiyya mai kyau, ka kula da mamanshi kuma shower dem with ur luv”, Aliyu ya juya da sauri jin muryanshi yafara rawa, ahankali yafara tafiya zaibar wurin harya hau stairs Khalil cikin muryan kuka yace ” Brodza”, chak Aliyu ya tsaya, da gudu Khalil yazo ya rungumeshi tabaya yafashe da kuka sosai ahankali yace ” I luv yhu Brodza, nd am sorry abunda nama abaya I was too selfish “.
[2/25, 08:43] Zjy: ~Ikhram~By Khaleesat Haiydar