Garin Dadi 5
©️ *HASKE WRITERS ASSO*
_(Home of expert & perfect writers)_
*GARIN DAƊI……!*
*_NA_*
*_UMMI A’ISHA_*
*5*
~~~Sama sama nayi bacci ranar sakamakon tunane tunane da na kwana dasu fal raina, babu kalar tunanin da banyi ba akan aurenmu da yaya faisal,washe gari haka na tashi duku duku duk bacci bai isheni ba na kammala shirina cikin haɗaɗɗiyar jar gown wanda tasha adon stones, duwatsunne suka sake ƙara mata kyau tare da bayyanar da tsadarta, kamar koda yaushe rolling nayi da ɗan mayafin rigar bayan nasha turaruka masu sanyin ƙamshi. Saboda saurin da nake yi na inje in duba hashim yau ko breakfast banyi ba hakanne yasa Annie mita tana ta faɗan wai bana son cin abinci, ina ƙoƙarin fita kiran yaya faisal ya shigo cikin wayata, gaisawa kawai muka yi na sanar dashi cewa zan kirashi idan na ƙarasa office,
Yau ma napep na shiga kamar koda yaushe, gidansu hashim ya ajiyeni na biya shi kuɗinsa na shiga cikin gidan bakina ɗauke da sallama yayin da farin ciki ya cika zuciya ta wanda ba zai misaltu ba, kamar jiya yau ma suna zaune cikin ƴar ƙaramar runfarsu shi kuma yana kwance kan tabarma, cike da fara’a dukkaninsu suka amsa sallama ta, tun kafin na ƙaraso iya ke cewa Amira tayi gaggawar ɗauko tabarma ta shimfiɗa min, hakan kuwa akayi,
“lale marhabun, lale da maimunatu….. Yanzu kike tafe?” Iya keta faman faɗa cikin farin ciki,
“wallahi iya, ina kwana ya me jikin kuma?” na faɗa kaina a ƙasa cikin girmamawa,
“lafiya lau maimuna, ya mutanen gidan naku? Me jiki da sauƙi sosai, mun gode fa, mun gode Allah ya saka miki da alkhairi”
Murmushi nayi ina amsa gaisuwar Amira wacce ta tsugunna kusa dani tana gaisheni,
“Amira yi maza ki ƙarasa girkin mana ki zubo mata….” iya ta faɗa yayin da take ƙoƙarin shiga ɗaki, sai lokacin na maida hankali na kan hashim wanda ke kwance yana sauraren dukkan abubuwan dake wakana,
“barka da zuwa ranki ya daɗe….”
“sannu…. Ka tashi lafiya, ya jikin?” Na faɗa ina murmushi,
“lafiya lau, jiki kuma ai tuni ya samu lafiya tun lokacin da kika bashi magani…”
“ohh nice ma na bashi maganin?”
“kece mana….. Maimunatu haƙiƙa ban san da waɗanne irin kalmomi zanyi amfani wurin gode miki ba, tabbas ke WANI HASKE ce acikin rayuwa ta wadda nake sa ran zata magance min duk wani duhu dake lulluɓe dani….”
Jin kalamansa ya sani ƙura masa ido ina kallonsa tsawon mintuna daga bisani nayi murmushi nace,
” ba godiyarka nake buƙata ba hashim, Allah ya kamata ka godewa, tun da har nayi maka abunda kaji daɗi ai nima ban san ta inda Allah zai yi min sakayyar kyautata makan da nayi ba, karka damu wannan ba wani abu bane…..”
“hakane…. Sai dai duk da haka bakina ba zai gushe wurin yi miki kyakkyawar addu’a ba, Allah ya saka miki da mafificin alkhairi…..”
“amin yaya hashim” Amira ta amsa wadda zuwanta kenan tana ƙoƙarin ajiye min abincin da ta zubo min cikin wata madaidaiciyar silver mai murfi,
A zahirin gaskiya bani da sha’awar cin abincinsu amma saboda gudun kada su ji babu daɗi sai na buɗe nasa spoon ɗin da aka ɗoro min akai na fara ci, jalop ɗin taliya ce wadda tasha manja, ina ci muna hira da hashim har na ɗanci irin cin da ba zasu ga kamar na raina musu ba,
Sallama nayi musu domin zan wuce office, iya da Amira rakiya har ƙofar gida har sai da suka ga na samu napep na hau sannan suka koma muna masu ɗagawa juna hannu.
Misalin ƙarfe biyar na yamma na tashi daga office kai tsaye gidan su hashim na nufa bayan na tsaya wurin masu fruits na siya masa ayaba, da kankana da apple harda abarba, lokacin da na shiga gidan yana zaune yana shafa mai da alama wanka ya fito, ita kuma Amira na zaune gefensa riƙe da littafin akhdari tana biya masa yana gyara mata abin da yayi mutuƙar bani sha’awa kuma ya ƙayatar dani, yanzu ace makaho yana da wannan ilmin shida bai da ma ido to kai da kake da lafiyar ido kake gani tangararau wacce hujja zaka bada na rashin neman ilmi alhali annabi yace neman ilmin farilla ne akan dukkan musulmi? Zama nayi fuskata ɗauke da murmushi,
“sannu da zuwa anty Maimunatu” Amira ta faɗa tana bani wurin zama,
“yawwa Amira, ina iyan fa? “
” yanzun nan ta shiga maƙota amma ba jimawa zata yi ba ”
” malam sannu da ƙoƙari…. Ashe muna tare da shehun malami, to ka shirya samun ƙarin ɗalibai ciki kuwa harda ni ”
” wane ni, ina marar ido zai koyar da mai gani, ai iliminki yafi nawa ranki ya daɗe, ke ga arabi ga boko duk kin haɗa nikuwa kame kame ne kawai ”
“duk da haka kai malami na ne, sai dai kawai idan ba zaka koyar daniba sai in haƙura”
“ni na isa, kaina bisa wuyana ranki ya daɗe”
Cikin wasa da barkwanci muka ɗan shafe lokaci muna hira har iya tadawo ta iske mu, ganin irin hidimar da nayo na kawo ya sanya ta rike baki tana faɗin wai ni bana gajiya ne, nan nace babu komai ai yi wa kaine daga ƙarshe nayi musu sallama na tafi nan Amira tabini ta rakani har titi.
Tsawon kwanaki biyar hashim ya ɗauka a gida yana rashin lafiya nikuma kullum sai naje gidan nasu safe da yamma har ya samu lafiya ya warke ras, nan muka cigaba da fita tare sannan kuma mu dawo tare hakan shi ya sake haifar mana da matsananciyar shaƙuwa a tsakanin mu, mun shaƙu ƙarshen shaƙuwa, nikuma na tsaya tsayin daka wurin ɗauke duk wata wahala tasa da ta gidan su, duk ƙarshen wata da zarar an yi salary zan je nayi musu siyayyar kayan abinci da dukkan kayan buƙatunsu na yau da kullum hatta sabulun wanka da omo sai na siya musu, hashim kuwa sittirar da zai saka ma nice ke siya masa kai daidai da ruwan sha wannan na hashim sai na siya masa saboda gujewa haɗarin kamuwa da cutar typhoid domin an ce tana dab da ta kama shi, wannan dalilinne yasa yanzu salary ɗina baya zama saɓanin da, kuma har yau ɗinnan na kasa sanarwa da kowa. Yau dai kam cikin nishaɗi na wuni sakamakon hirar da muka yi da hashim da safe lokacin da zamu fito ni zan zo office shi kuma zai je school,
“Maimunatu ba dan kar na zaƙe da yawa ba, ko kuma kar in yi kasada da nace wani abu…. Sai dai kuma bai kamata in faɗa ba duba da ko ni waye da kuma matsayina….. Ni bani da ido amma na jima ina dakon wani kaya mai nauyi acikin zuciya ta”
“hashim nifa raina yana ɓaci idan naji kana maganar idon nan, wai me kake nufi ne? Kawai ka fito ka sanar dani abin da ke ranka”
Murmushi yayi ya shafa haɓarsa,
“Maimuna tun ranar da na fara jin muryarki naji gabana ya faɗi, zuciyata ta buga da ƙarfi……. Tun daga ranar nake jin kamar bazan iya rayuwa ba idan babu ke…. Wallahi ina jin matsananciyar ƙaunarki acikin raina….. In short dai ni hashim ina son ki….. ”
Shiru nayi kawai ina kallonsa na tsawon mintuna ba tare da nace wani abu ba hakan yasa shi ɓata fuska sannan cikin rashin walwala yace,
” kiyi haƙuri na san tsaurin ido nayi domin matsayina bai kai ba….. Wallahi sharrin zuciya ne da take kamuwa da son wanda ba sa’anta ba….”
“hmmm hashim kenan….. Ka daina faɗin haka, shi so babu ruwansa da ido, ko ji ko kyau, faɗawa cikin soyayya ta da kayi hakan ba tsaurin ido bane kamar yadda kake tunani….. Nima ina son ka”
Take ɓacin ran dake kan fuskar sa naga ya washe farin ciki ya maye gurbinsa, shiyasa cikin farin ciki muka rabu, nidai hashim yayi min domin ya iya kalamai masu sanyawa mace nutsuwa sannan baya ga makantar da ke tare dashi bai da wani makusa, shiyasa babu wata wata muka tsunduma kogin soyayya muka fara linƙaya muna gudanar da soyayyarmu cike da burgewa.
Yau dai na ƙuduri niyyar sanar da ƙawalli dan jin ra’ayinta wannan dalilinne yasa nayi tattaki ƙafa da ƙafa naje har gidan su na sameta,
Kwance na sameta tana karatun novel dama ƙawalli badai karance karance ba,
“wannan karance karancen naki ya kai yanzu ace kin zama marubuciya….”
Zaune ta tashi tana murmushi,
“Kisha kuruminki nan bada jimawa ba zan zama ƙwararriyar marubuciya tamkar phertymah Xarah ko Ayusha Mohd”
Dariya nayi sannan nace “ya dai kamata, yanzu dai na zo miki ne da wani labari ƙawalli, ki tayani ganin abin da ya dace, nayi sabon saurayi kuma wallahi ina jin sonsa a raina fiye da duk wani ɗa namiji…..”
Tagumi tayi tana kallona tana sauraren labarin da nake bata na tun farkon haɗuwata da hashim har kawo yanzu…………… ✍
*Garin daɗi na kudine ga mai bukatar cigaban labarin sai ya turo 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sannan a tura shaidar biya ta 07044644433 ko kuma katin waya da shaidar biya ta wannan no 07044644433*
*_Ummi Shatu_*