Garin Dadi Hausa NovelHausa Novels

Garin Dadi 47

Sponsored Links

{47}

*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma’abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA…..*

~~~Bazan iya kwatanta yanayin tsoro da firgici da na shiga a lokacin ba domin gaba daya komai ya kwance min haka na nemi addu’a a bakina ko daya na rasa, jikina kuwa tamkar mazari dan tsabar rawa da kakkarwa, tamkar zan suma dan tsabar tsorata to abune da baka san dashi ba kuma baka kwana dashi ba sannan na tabbata a gidan babu kare kuma babu mage to idan da akwai ma tayaya zasu shigo har cikin part dinmu? Koda na bude idanuwana baƙake na gansu sidik gwanin ban tsoro kowanne ya bude baki babu kyan gani sai lokacin na samu addu’a tazo bakina na fara ƙwallawa da ƙarfi cikin rawar murya da rawar jiki, da rarrafe da jan jiki na samu na shige cikin bedroom har lokacin cikin tsananin tashin hankali nake, ina shiga na sakawa ƙofar key wayata ma ashe can na barota,

Da wannan tashin hankalin na wuni ranar ina cikin bedroom kunshe na kasa koda bude kofar ne bare in iya fita falo duk da ina jiyo karar wayata anata kirana tun jimawa, har cikin bedroom ɗin ma tsoronsa nake dan ko toilet na kasa shiga saboda gani nake kamar zan gansu aciki gashi sai gizo suke yimin acikin idanuwana, addu’a naketa yi ina karawa amma har lokacin a firgice nake, zuwa yamma ya dawo ko time din tashinsa bai bari yayi ba ya taho saboda yanata kirana amma wayar nata ringing ba a dauka shiyasa ya taho da wuri dan ya dubani yaga ko lafiya,

Ina bude ƙofar bedroom din bayan yayi knocking na tabbatar shine na fada jikinsa ina kuka daga ni sai rigar bacci wadda ko wanka ban samu damar yiba haka na wuni cikin tsoro da fargaba,

“baby…. What’s happening??”

“Wallahi wani baƙin kare ne da bakar mage acikin gidan nan, muna gama waya da kai na gansu kamar zasu cinyeni….”

“what? Acikin gidan nan?”

Tare muka koma falo ina makalkale dashi muka je ya shiga duba ko ina har su kitchen amma babu alamar komai aciki daga karshe ya tisani da tambayar wai anya ba mafarki nayi ba ko kuma kawai firgita nayi ba?

“baby are you sure ba mafarki bane?”

“wallahi sweet ba mafarki bane da idona na gansu”

“ok am sorry”

Har bathroom sai da ya rakani sannan nayi wanka na fito ga uwar yunwa dake ciciyata, sama sama na shirya ban bata lokaci wurin kwalliya ba muka wuce kitchen na dora mana abinci. Tun daga wannan rana na kasa sakewa acikin gidan kullum cikin fargaba nake saboda zan iya ganinsu kowanne lokaci kamar yadda suke yimin gizo ba dare ba rana amma sunfi yimin a lokacin da baya nan, idan yana nan koda weekend bana ganin komai kuma bana jin kukan komai amma da zarar baya nan shikenan nikuma zaman lafiyata ya kare sai gane gane da jin koke koken mage da haushin kare gaba daya duk sai zaman gidan naji ya isheni ya fita a kaina kamar in tattara in gudu haka nake ji duk nabi nayi fiki fiki dani shi da kansa sai ya fara tausaya min yace bari mu kira anty mu sanar mata, da kansa ya kirata ranar bayan ya dawo daga aiki da daddare bani wayar yayi na zayyane mata komai da nake ji kuma nake gani nan anty tace to in dage da addu’a sannan in kiyaye duka azkhar haka kuma in yawaita karatun alqur’ani mai girma da saurarensa daga karshe tace mu samo ƴayan habbatussauda in rinka zubawa a garwashi ina turara gidan dashi kamar yadda ake saka turaren wuta,

Bani ba shi kansa gidan ya fita masa akai saboda gaba daya yaga a takure nake wannan dalilin yasa ya fara neman gida babu shiri dan yace gara mu tashi mu canja gida sai dai baya son nesa da wurin aiki yafi son inda yake dan kurkusa da wurin aikinsa, cikin sa’a ranar yazo min da labarin an samu wani estate kamar wannan wanda muke ciki kuma wani dan office din su ne ma ya sama masa saboda shima aciki yake tare da matarsa wadda basu wuce 4 months da aure ba wai itama kuma daga Kano ya aurota amma shi asalinsa dan zaria ne,

Cikin lokaci kanakani yabiya kudin gida yayi komai muka fara harhada kayanmu nidai farin ciki ai kamar zanyi tsalle akan kaya saboda na fishi matsuwa da mubar gidan daman,

Compound ne mai kyau upstairs kuma kowanne akwai mutane aciki ma’aikata, mu dai muna sama kuma opposite muke da wannan ɗan office din su samz mai suna Kabir kamar yadda naji yana faɗa sai dai ban taɓa ganinsa ba har zuwa lokacin da muka tare, bayan mun tare da kwana biyu sai gasu sun zo mana bayan sallar magriba, muna zaune muna kallon series a tashar zee world suka yi mana knocking, dogon hijabina na saka saboda daga ni sai riga armless iya cibiya da dan wando rigar iya cinyata shikuma boxer ne kadai a jikinsa ma ko riga babu, ciki ya shiga ya sako farar jallabiya sannan ya wuce ya bude ƙofar, ganin Kabir yasa shi fadada fara’arsa tare da mika masa hannu bayan yabawa Samha hanya alamar ta shiga ciki,

Ina zaune kan kujera na nutsu ina kallo dan bana son kallon ya wuceni naji sallamarta, fuska ta da fara’a na amsa mata duk da ban santa ba kuma banma taba ganinta ba sai yau, tasha turare babu laifi dan sai da yafara yimin sallama kafin ita tayi,

Harga Allah tun daga shigarta da yanayinya nasha jinin jikina dan tamkar yar duniya haka na ganta saboda yanzu rayuwa ta canja duk yadda mutum yake yanayinsa kadai zai fassara maka wanene shi, kuma ko ada dinma hakane,

“sannu da zuwa…” nace da ita ina karema shigarta kallo dan duk da bani nayi shigar ba amma ji nayi kunya ta rufeni,

“yawwa sannu, yakike”

“lafiya lau” nace lokacin da nake tashi na wuce kitchen, wanda shi zaka fara wucewa kafin ka shigo falo daga nan sai wani dan corridor wanda aciki bedrooms dinmu suke guda biyu daya da toilet aciki dayan kuma toilet dinshi awaje yake ta kusa dashi, duka dai komai a wadace yake dan har yafi wancan gidan da muka baro wadata a girma da komai koda yake lokacin yana shi kadai may be shiyasa ya kamashi a haka, juice na dauko mata da ruwa sai dambun naman kaza wanda dama dashi na taho tun daga Kano cikin wani madaidaicin bokiti wannan mama ce tayi min na taho dashi shikuma samz bai dameshi ba sosai yana ci amma kadan kadan nice ma dai kusan kullum sai na dan damka nasa a bakina,

Komawa nayi wurin ta muka gaisa bayan na gabatar mata da kayan motsa bakin da na kawo mata,

“sunana Samha, nice matar abokin mijinki Kabir kuma makociyarki wanda gidanmu ke opposite”

“ayya Allah sarki ashe matar Kabir ce, ina jin labarinku ai amma bamu taba haduwa ba”

“ehh nayi tunanin zanga kun shigar mana sai muka ji shiru”

“wallahi riga mu kuka yi kin san har yanzu bamu kammala gyara kayanmu bane amma Muma muna da niyyar shiga, bama gidan ki kadai ba ai duk gidajen zamu shiga Insha Allah”

Allah sarki, to ai yanzun ma ina zuba ido ”

” Insha Allah zaki ganni da rana ma ni zan zo muku ko yamma ba zuwan dare ba”

“to shikenan ina nan ina zuba ido”

Mun dan sha hira sosai duk da bamu san juna ba kuma naji mutukar mamaki da naji cewa wai matar aure ce, ya ilahi wannan wanne irin zamani wai muke ciki? Nidai gaba daya ji nayi bata wani yimin ba dan kamar bata da kamun kai amma zan bata lokaci dai in karanceta dan lokaci shi ke sanar dakai wanene ainihin mutum. Munata hira har lokacin sallar ishah yayi nace mu tashi muyi salla amma bata maida hankali ba saboda kallo ya dauki hankalinta sosai sai bayan da na idar sannan itama ta samu tayi, tana idarwa kuma samz yana shigowa kiran ta inji kabir nan na tashi na rakata har waje nida shi yana rike da hannuna muka gaisa da mijin nata sannan muka yi sallama ina ce musu Insha Allah Muma zamu shigo musamman ma tunda muna kusa,

Ƙofa na jirashi ya rufe yana juyowa na dage kafata daya ina yamutsa fuska,

“what?” ya bukata yana kama hannuna,

“na taka kaya bazan iya tafiya ba ka goyeni….”

“you want to stress me dai….” ya fada tare da sunkuyawa, da tsallena na haye bayansa muka karasa ciki ina makale wuyansa da hannayena,

“baby Kin sake nauyi fa…..”

“haba sweet ni din har nawa ma nake”

Dariya yayi ya kwanto dani kan cinyarsa yana cire min hijabin,

“my sweet 16 baby….”

“ai bazan fi hakan ba love”

“I know…” yace dani yana dariya sau tari haka dama yake biye min muyita shirme kamar wasu kananun yara to yau dinma hakan akayi dan har fin 11 muna ta shiririta afalo daga bisani muka yi shirin bacci nan dinma bamu hakura ba sai dariya yaketa sakani yana yimin cakulkul, alhamdulillah dai yanzu na daina wannan gane ganen da jin kukan abubuwa tun bayan da muka baro tsohon gidan da muke,cikin farin ciki da nutsuwa nayi bacci na barshi yana yimin tausa a kafafuwa na……….

*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*

*_Ummi Shatu_*

Back to top button