Cuta ta Dau Cuta Hausa NovelHausa Novels

Cuta ta Dau Cuta 26

Sponsored Links

*_Typing_*

 

 

 

*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_

 

_ _

 

_Shafi na ashirin da shida_

________________

*_ZAFAFAN DAI_*

*_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*❤‍❤‍❤‍

*_KASANCE D’AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_*

_WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_

*_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_*

*KWANKWASON JIMINA miss xoxo*

*TSUTSAR NAMA Billynabdul*

*GUDUN K’ADDARA Huguma*

*AMEENATU Mamuhghee*

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR… ZAFAFA BIYAR NAKU NE_

____________

……Sallamar sassanyan ƙamshin turarensa kafin bayyanarsa ya sake zama wani ɗan jagora a fisgar mutanen hall ɗin da suka ƙwaɗaitu da son ganin wanene wannan ogan anguna da mc ke kwarzantawa da kurantawa haka da kirari. Masha ALLAH na ambata a ni karan kaina a lokacin da matashin cikakken mutum ya bayyana. Lallai babu ƙarya, dan mai kallo ya isa fassarawa da yarda da kalaman mc akan wannan matashin mutum. Bawai zamu kirashi ɗanyen kai sharaf ba, dan shekarunsa a ƙalla zasu iya kai 37+ ma. Sai dai yanayin jin daɗi da kwarjinin da ALLAH yay masa ga cikar kamala zai iya sa kace bazai iya kai shekarun ba ma. A take flash na camaras ya fara harska shi tun daga farkon shigowa har zuwa mazaunin da aka tanada domin sa. Sai da ya zauna tamkar wani gwamnan jiha kafin muƙarrabansa da suka tako masa baya suma su sami wajen zama.
Ƙus-ƙus ne ya fara tashi a tsakanin ƴammata da zawaran dake wajen, kai hatta ma masu auren wasu sun gaza haƙuri sai da suka tanka. Dan kuwa dai tabbas babu ƙarya wannan oga na anguna ya kai ace wani abu akansa. Ƙyawu da kwarjini ziryan da babu gauraye ALLAH ya azurtashi da shi, cikakken bafulatani ɗan usil, ga nera da ta zama babban ado wa rayuwar koda mai ƙarancin ƙyau ne a wannan rayuwar. To shi sai ya zam UBANGIJI ya haɗa duka biyun ne garesa. Dan ko adon dake jikinsa ka kalla kasan naira ta zauna koda baka san minene darajar kuɗin kaya ba kuwa.
Abun zai baka mamaki idan nace duk wannan kai kawo da kace nace da ake akan ogan anguna ko sau ɗaya Khadijah bata ma kalla sashen da zai shigoba balle inda ya zauna. Ta tattara hankalinta ne gaba ɗaya a wayar Ni’ima dake hannunta tana buga game hankalinta kwance. A haka mc ya sake jera kirarin barka da zuwa ga babban baƙo. Kiran sunan Khadijah da mc ya sake yi tare da roƙon sake zuwa ta sake buɗe wannan taro da addu’a a karo na biyu ya sakata jin tamkar ta fasa kuka. Amma yaya zatayi, bazata iya bari ƙannenta shiga damuwa ba. Dan haka bayan ta kwashe kusan mintuna uku da har sai da mc ya tako inda take sannan ta miƙe tana ɗan harararsa ƙasa-ƙasa. Cikin takunta na nutsuwa ta fito sautin takalmanta na shiga kunnuwan duk wanda ke wajen sakamakon komawar hall ɗin shiru. A inda ta tsaya ɗazun yanzu ɗin ma dai ta tsaya, cikin nuna takura ta fara karanto addu’oi zazzaƙar muryarta na ratsa kunnuwan duk wanda ke’a wajen.
Cak ya dakata daga latsa wayar da yake, ƙirjinsa na wani kalar harbawa da motsawa tamkar ɓera na sukur-sukur a drower. Wani irin ratsa ɓargon jikinsa muryar tata tai kamar wanda aka watsama ruwan sanyi cikin jijiyoyi maimakon jini. Wayar ya damƙe sosai cikin hannunsa tare da ɗago idanunsa ƙasa-ƙasa ya sauke a kanta. Sai dai baya iya gano fuskarta sai bayanta da gashin kanta dake a tsakkiyar ɗan kwali samakamakon zamewar gyalen daga saman kanta…
Duk jinta take a daburce ganin yanda aka zubo mata idanu fiyema da ɗazun, dan haka tai addu’ar a takaice tana miƙama mc m.p ɗin harda balla masa harara. Shiko babu sirri ya ce, “Oh ƙyaƙyƙyawa irin wannan harara haka ai sai ki hanani barci wlhy”. Ya ALLAH ji Khadijah tai kamar zata zube a tsakkiyar hall ɗin sakamakon yanda ya sake jawo attention ɗin mutane kanta musamman mazan wajen. Da ƙyar dai ta iya maida kanta mazauninta tana sauke numfashi guda-guda.
(Tsarki ya tabbata ga UBANGIJI) zuciyarsa ta sake ayyanawa tare da bugawa da ƙarfi kamar an daki ganga sakamakon saukar idanunsa kan black beauty face ɗin Khadijah da akaima kwalliya a taƙaice ta yanda kamanninta sam basu ɓace ba. Haka kawai yaji a ransa kamar ya taɓa ganin fuskar, to amma a ina? Wannan shine ya kasa tunawa sam. Isowar anguna inda yake domin miƙa masa gaisuwa ya katse tunaninsa. Yanda suka gaishesan ma da matuƙar girmamawa ya sake tabbatar ma kowa dake gurin shiɗin na musamman ne a garesu. An musu hotuna a tare kafin su koma wajen zamansu. Da ga haka aka fara abinda ya tara mutane. A dai-dai lokacin da ake kiran babban abokin anguna domin faɗar tarihinsu a lokacin wani baƙon matashin saurayi kuma ke isowa hall ɗin shima. Shima dai mc ya sanar da zuwansa matsayin Uncle ɗin mijin Ni’ima. Sai dai kasancewar sa’an ango ya zama abokine, ya kuma taso tundaga kudancin Nigeria domin wannan biki. Sai da aka bashi wajen zama sannan abokin angunan yay bayani akan tarihinsu su biyun. Yana gamawa akai kiran Khadijah matsayin wadda zata bada na amare suma. Taji kamar taƙi zuwa, amma ganin fuskokin su Zuhrah yasata miƙewa badan taso ba. A yanda kansa ke duƙe bazaka taɓa tunanin ita yake kallo ba, amma kaf hankalinsa na kanta, ƙoƙarin son tuno inda ya santa kawai yake yi dan tabbas shi yasan wannan fuskar. A hankali Khadijah ta fara abinda aka kirata tayi cikin harsuna guda uku datai matuƙar birge mutane jin yanda take fidda kowanne da ƙwarewa duk da a rubuce koman yake. Hausa, larabci, turanci. A bazata kawai akaga saurayin nan daya iso yanzun nan Uncle ga mijin Ni’ima ya iso gabanta ya fara zuba mata liƙin ƴan 200. Ihu mc ya ɗauka yana wani zigashi, shiko idonsa ya rufe sai zubama Khadijah da ke jin wani irin tashin hankali sabbin 200 yake yi yana mata wani shegen kallon daga sama har ƙasa dan tun fitowar Khadijah yaji ta gama tafiya da duka imaninsa. Dan haka ya kasa jurewa kawai ya zaɓi hanyar da zata ɓille masa tun da wuri.
Duk yanda yaso daurewa da danne ransa hakan ya gagara. Duk da ya kasa tuno a inda yasan yarinyar sai yake jin kamar yana da wata babbar alaƙa da ita. Sai kuma yanda saurayin ke mata liƙi da zagayeta yana mata wani kallon gogaggun maza yaji ya zafesa. Wayarsa da saƙo ya shigo ya duba, kamar wanda aka zabura tsamm ya miƙe cikin nutsuwarsa da cikar kamala batare da kowa yay tunanin ina zaije ba shima dai aka gansa gaban Khadijah. Ƴan 500 sabbi ƙal da yaronsa ya iso da sauri ya miƙa masa kawai yayma wata kalar farkewa ya fara liƙama Khadijah. Ganin haka saurayin nan da yaji zuciyarsa ta sosu shima ya watsar da ƴan 200 da suka rage hannunsa ya zaro dubu-dubu. Ihu hall ɗin ya ɗauka yayinda jikin Khadijah ke neman fara rawa dan ita bata fahimci manufar hakan ba gareta face kallon al’amarin a wulaƙanci da son nuna fariyya. Ɗagowa tai cikin ɓacin rai idonta karaf akan yaronsa. Ai ko a magagin barci bazata mance wannan fuskar ba, shima Awwal da tun fitowarta ya ganeta ya sakar mata wani murmushi. Da sauri ta janye idonta a kansa ta maida ga ogan nasa da ke kallonta shima, sai dai saɓanin yanda ya tasanshi yanzu fuskarsa a ɗaure take. Awwal da dama gaba ɗaya saurayin nan ya gama baƙanta masa rai da ganin yana son nuna takara da yayansa cikin sauri yakai kunnensa ya gwargwaɗa masa maganar da Khadijah bata ji ba, sai kuma ya miƙa masa wasu kuɗi da bata taɓa gani a zahiri ba sai a hoto ana ce dasu dollars. Wani irin jan gadara yayma takardar samansu yana wani yamutse fuska ya fara zuba mata su saman dubu-dubun da saurayin nan ke liƙa mata. A yanda fa hall ɗin ya ɗauki ihu yanzu sai ka rantse zai fashene. Ina Khadijah bazata iya jurar haukar nan ba. Da sauri tai ƙoƙarin barin wajen amma suka cigaba da binta suna liƙa mata kuɗin har wajen zamanta. Mc ya matuƙar haukacewa, dan ogan anguna dai sai farke dollors yake kamar baisan ciwon kuɗin ba. Yayinda ran wancan guy ɗin ya ɓaci matuƙa ya koma liƙama Khadijah bandir na dubu-dubun a dunƙule. Mijin Ni’ima da ya gama sanin waye Yassar a fitina da kuma sanin waye ogansa a rashin son raini yasa ya aiko wani cousin brother nasu jan Yassar ɗin daya gama cika fam da takaicin wannan mutumin. Taya ma zai fara nuna interest ɗin sa akan yarinya shi ya fito yana nuna masa gadara akan kuɗi. Waye shi! Ɗan uban waye ne!.
Awwal da ke jin kamar ya fasa ihu dan daɗi akan abinda yayan nashi yayi sai murmushi yake yi. Dan duk wanda yasan yayansa yasan babu abinda ya damesa da mace duk ƙyanta, duk jin kanta. Amma lokaci ɗaya ya nuna damuwarsa akan Khadijah. Duk da yana tunanin yayi hakanne saboda tuna wacece ita amma dai zuciyarsa na ƙaryata hakan. Tuni yaran mc sunzo sun fara tsince kuɗin dake zagaye da Khadijah da tunda ta zauna kanta a ƙasa taja mayafi ta rufe fuskarta tana hawaye. Kirari mai suna kirari mc ya fara ga ogan anguna.
“Tabbas idan kaji ana ƙi gudu sai idan sa gudun bai zoba. Ai na faɗa muku shi ɗin uban mara uba ne, har masu uban ma fa ubansu ne. Oga *_ABAAN OMAR MODIBBO_* ake faɗa muku, sune shinkafa a ƙasar nan, dan sai sun so a dafa muku a tukwanan gidanku kuci zaku ganta. Sawun giwane take na raƙumi koda kuwa raƙumin tsohon amale ne….” yanda mc ke zabga kirari zai tabbatar da ruwan kuɗin na ya gama gigitashi. Shiko tunda ya koma mazauninsa ya sake maida kansa ga waya baiko ƙara kallon kowa ba sai dai abinda basu sani ba idonsa nakan Khadijah ne ƙyam ko yaya ta motsa. Gashi taƙi sake yarda ta buɗe fuskarta a cikin mayafi har lokacin da amare da anguna suka fito sannan ya tashi nan ma ya zuba musu liƙi da ƴan dubu-dubu. Taro ya cigaba da tafiya sai dai duk yanda mc yaso Khadijah ta sake hawa sama bai samu ba. Dan ko da amare da anguna suka fito aka buƙaci ganin jinin amare suyi rawar jini da jini ita bataje ba. Sai amaren ne sukazo inda take sukai mata liƙi tare da angunansu amatsayin girmamawa ga babbar yayarsu. Sai hakan ya sake ƙayatar da mutane sosai.
Awarsa kusan biyu a wajen ya miƙe, a tare da muƙararransa su Awwal suma duk suka miƙe dan kowa yasan yayi ƙoƙari, babu ma wanda yay zaton zai yi mintuna talatin a wajen, amma sai gashi da awanni har kusan biyu. Ya amshi mp daga zaune yay addu’a da fatan alkairi ga anguna da amare harma da godiya ga jama’a sannan yay sallama. Idonsa ƙasa-ƙasa akan Khadijah har sai da ya gota ta sannan ya ɗauke… Fitarsu da kamar mintuna goma sai ga Awwal ya dawo wajen, kai tsaye inda anguna suke yaje yay magana dasu batare da kowa yasan miya faru ba akaga angon Zuhrah ya tashi. Fita yay, baifi minti biyu ba shima sai ga Jamilah tazo har inda Khadijah take ta kama hannunta bayan itama ta gwargwaɗa mata magana. Da alama dama Khadijah kamar akan ƙaya take, dan kafinma Jamilah ta gama maganar tamiƙe. Bata buɗe fuskarta ba a haka Jamilah ta taimaka mata suka fice a hall ɗin gaba ɗaya kamar wata amaryar da za’a kai gidan miji.
“Aunty to ki buɗe fuskar tunda mun fito”. Cewar Jamilah tana ƴar dariya. Ajiyar zuciya Khadijah ta sauke mai nauyi tare da janye mayafinta a hankali. Tana ƙoƙarin yin magana da ƙara sauke ajiyar zuciya mijin Zuhrah ya iso wajen fuskarsa da murmushi. “Auntyn mu tuba muke. Gaba ɗaya sun hana mana ke sukuni ko. To ayi mana afuwa dan ALLAH. Idan babu damuwa kizo a maidaki gida kawai dan na fahimci gaba ɗaya a takure kike a wajen nan muma yanzu zamu tashi ma insha ALLAHU ”.
Jitai hakan ya mata, dan haka a sanyaye ta ce, “Nagode sosai Ya Ibrahim. ” yanda Muryar tata ke fita da sanyi sosai zai tabbatar maka kuka tayi. Murmushi Ibrahim ɗin yayi da faɗin, “Babu komai auntynmu ai yima kai ne. Bissmilla ko”.
Bata kawo komai a rai ba ta bisa har zuwa inda ƙatuwar zuƙeƙiyar baƙar mota ke a fake. Baya ya buɗe mata da matsawa gefe. Itako a tunaninta babu kowa a ciki kamar ɗazun, kanta tsaye ta shiga tana masa ɗan murmushin ƙarfin hali da faɗin, “Ya Ibrahim thanks you”. Murmushi ya mata da rufe motar bayan ya gyara mata mayafinta da ya ɗan sakko waje…….✍️

_Gaskiya zanci ganda irin mai yajin nan da romo da ake cema ragadada sanda muna yara. (Kai jama’a Bily da son girma, irin mu mun girma ɗin nan yanzu fa ko wai sanda muna yara)._

_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_

_KU MARMATSO KUSA…_

_ZAFAFA BIYAR 2024_

_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_

_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA’ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_

_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI… DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR…WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_

_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR… CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_

_________

_1_
*_AMEENATUH_*: _MAMUH GEE_

_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)_*_:BILYN ABDULL_

_3_
*_GUDUN KADDARA_*:_SAFIYYAH HUGUMA_

_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)_*_:NANA HAFSATU (MX)_

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYARALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE_

 

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu _*

Back to top button