Garin Dadi Hausa NovelHausa Novels

Garin Dadi 45

Sponsored Links

{45}

*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma’abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA…..*

~~~Tunda nazo Kano sai naji kamar kada na koma Abuja saboda yadda na shiga na sake cikin ƴan uwana kullum gidan ƙawalli cika yake da ƴan uwa da abokan arziƙi masu zuwa barka, ayi ta shan hira ana tsokanar juna wannan dalilin yasa naji kamar aware nake idan na koma Abuja, su mama dai tunda suka zo suka ga baby lokacin banma zo ba har yau basu dawo ba,

Kullum wuni ake ana kai kawo a gidan har suna ya ƙarato, kaya na ɗauko acikin kayan lefe na guda hudu leshi biyu atamfa biyu na bawa Bishra taje ta kai min dinki emergency, ranar da za ayiwa ƙawalli kunshi da kitso kuwa har dani duk da bana jure zaman amma wannan kam na jure tsaf nan nima na fito fes dani, bayan da aka gama yimin samz ya kirani yana ganin ƙunshin ya soma santi yana cewa,

“baby yaushe zaki dawo? Ko ni in zo?”

“da naji daɗi kuma nayi farin ciki….”

“ok zan zo Insha Allah, dama ina so in zo inga baby…..”

“Allah ya baka iko ya kawo ka lafiya”

A lokacin yake faɗa min cewa sunyi magana da matar uncle ɗinshi wato Anty Amina kuma zata zo Insha Allah, ai kuwa naji daɗi sosai dan babu dadi ace ana abu agidanmu dangin mijin kowa yana zuwa banda nawa, mun jima muna hira wadda duk rabi shiririta ce amma haka ya biye ni ya koma kamar wani mate dina, sallama muka yi sai lokacin na samu na koma cikin mutane inda aketa aikace aikace saboda taron sunan da za ayi duk da dai ɗagawa dama akayi saboda mai jegon ta ɗan sake jin ƙarfin jikin ta. Ai ranar suna nima zama nayi tamkar mai jegon saboda irin yadda nake ta shiga ina fita, taro yayi taro jama’a sun cika ko dan dayake sunan fari ne oho, gajiya kam na gaji liss harda su ciwon jiki, wanka nayi da ruwan dumi na zo nabi lafiyar gado sai kuma me? Kiran samz nagani ya shigo cikin wayata, cikin kasala na ɗauka ina lumshe idanuwa duk da lokacin ba a fi ƙarfe 8:30 ba dan wasu ma basu tafi ba har lokacin,

“sweet yakake…”

‘baby zan zo mu tafi yanzu” jin abinda ya fada sai kawai nayi murmushi dan duk tunanina tsokanata yake dan haka na amsa masa da,

“toh sai kazo…” na katse wayar tare da gyara kwanciyata, zuwa 9 na dan fara bacci naji ƙawalli na cemin “ƙawalli ki tashi ga jelarki can yazo…. Wai kije ku tafi”

Tashin nayi cike da mamaki nasa hijabi na fita falo nan na samesu shida angon ƙarnin ya wani kama jaririn ya riƙe kamar wanda zai tafi dashi, zama nayi na gaida su sannan na zuba masa ido ina kallon sa bance komai ba saboda naga hankalinsa yana kan hirar da suke yi shida yaya Abdul hakim, shi bai tashi mun tafi ba haka kuma bai ce in koma inje inyi kwanciyata ba haka na sasu gaba ina kallo ina saurare har 10 saura sannan na shiga na debo kayana ƙawalli ta rakoni, da yake dare ne shi ya ja motar, muna fita daga gidan na kwanta ajikinsa dan a mutukar gajiye nake gefe daya kuma nayi missing dinshi,

“Baby ko bakya son zuwa na? Banga kina murna ba”

“Ba haka bane kawai dai na gaji ne sweet” murmushi yayi ya kama hannuna guda daya ya rike tare da kissing ɗinsa yana shafa kunshina,

“zamu fara biyawa in siyo suya…… Ina jin yunwa sama sama”

“zan sha ice cream….”

“no baby…. Baki ganin situation dinke ne? Idan kika sha ice cream sanyi zai iya kama babynmu fa”

“yanzu ta baby ma kake yi ba tani ba ko?”

“am sorry baby, ba haka nake nufi ba”

Daru na tayar masa saboda ina sha’awar shan ice cream din harga Allah amma sai cemin yayi wai ko zan sha sai idan zan barshi ya narke ya huce nikuma jin hakan yasa nace ni na hakura amma da naga dagaske zamu bar wurin bai siya min ba sai nace na amince nan ya sake fita ya siyo min roba ɗaya ya dawo kuma ina ji ina gani ya hanani sha wai sai ya huce, har muka je gida ina turo masa baki ban huce ba,amma da yake yafi kowa sanina sannan ya san ta inda zai sauko dani jikinsa yajani ya sabule rigar baccina ya soma yimin tausa duka jikina abinka da gajiyayya ai lokaci ƙanƙani na fara bacci,

“baby nikuma fa? Zaki fara baccin nan naki kibarni ko?” ai ni ina nasan ma yana yi dan tuni na fara nisa cikin baccina, ban san lokacin da yaje ya gyara bedroom dinba ya goggoge sannan yazo ya dauke ni ya mayar dani ciki ya kwantar akan gado, wanka yaje yayi kafin shima yazo ya kwanta gefe na.

Washe gari shi ya taimaka min muka gyara ko ina muka tsaftace sannan ya fita ya iyo mana cefane nayi mana girki zuwa yamma muka fita kuma bawai wani wuri zamuje ba kawai zaga gari sai magariba sannan muka wuce gidan uncle dinsa duk da matar tashi mun hadu a sunan ƙawalli,

Dukkansu suna zaune cikin babban falon gidan suna kallon wani ƙayataccen series a tauraron ɗan adam, da murna duk suka tare dani daga anty Aminan har yaran sai dai banda mutum ɗaya wato Munira wacce itace babbar ƴar Anty Amina wadda a haife na san bazata girmema ƙanwata Bishra ba, tamkar bata ganni ko bata san da wata halitta ba awurin haka tayi duk kuwa da tana jin mahaifiyarta da sauran ƴan uwanta sunata lale marhabun dani, idonta yana kan tv tun bayan zuwana sai ko kan wayarta wacce ke ajiye kan cinyarta,

“Anty banyi salla ba a hanya ta samemu…. Shima sallar ya tsaya yi shiyasa bai shigo ba”

“Ah to shigo ki fara salla tukunna sai ki zo kici tuwo gashi nan….”

“wallahi kuwa kamar kin san shi nake so yanzu anty Amina”

“to kuwa gashi nan zaki ci har ki tafi dashi idan kina so”

“ai kuwa nagode” na fada ina murmushi ina biye da ita har cikin bedroom ɗin ta duk da inata ce mata ta nuna min ɗakin yaran sai inyi acan amma tace a’a a ɗakinta zanyi, sallata nayi a nutse bayan na idar na shiga mamakin wannan yarinyar tata Munira lallai kowa da halinsa sannan albasa bata yi halin ruwa ba banda haka anty Amina mace mai kirki mai haba haba da mutane amma ita kuma sai bata ɗauko halinta ba tayo nata halin daban na wulakanci da shan kamshi dan inba wulakanci ba mutum ya zo gidanku ai ka girmama shi ka karramashi gami da mutunta shi, ban wani damuba dan dama ni na saba da irin wannan wulakancin na dangin miji sai dai abinda ya bani mamaki kuma ya daure min kai shine ita kuma me nayi mata ko menene damuwarta dani?

Ganin bani da wannan amsar ya sani tashi na fita na koma wurin su, mamakine ya so sumar dani ganin Munira ta sake tana hira da mijina sosai harda su kyakyata dariya ban bi ta kasu ba dan ko babu komai yar uwarshi ce na maida hankali na kan tuwon da Anty Amina ta ɗumama min ta kawo min tuwon semo miyar busasshiyar kuɓewa harda yajin daddawa da man shanu ai nan na zauna na kwashi abina son raina ina jin hirar da suke yi. Sai dai abinda ya so ɗaure min kai guda ɗayane irin shisshigewar da naga yarinyar tana yiwa samz wanda nidai ban san dalili ba amma zaƙewar naga kamar taso tayi yawa sai dai ban saniba ko dama can haka suke yi duk lokacin da yazo gidan ma’ana ko haka suke zama su sake suyita shan hira shiyasa naketa fafutukar ganin na kori shaidan daga cikin zuciyata batare da yayi tasiri ba amma sai na ji na gagara hakan abinka da kishi nan ya fara rufe min duk wata kofa dake cikin zuciyata,kame bakina nayi na kama kaina wuri guda dan bana ko tanka musu bare in sa musu baki cikin abinda suke tattaunawa wanda su ya shafa atoh su ya shafa mana tunda maganar karatun ita Munira din suke yi, koda aka gabatar masa da abinci yace bazai ci tuwo ba nan ta tada fi’ili da fallin wai zata dafa masa noodles, ina jin kunyar gwasaleta yaji shiyasa bai hana ba yace toh nan ta shiga cikin kitchen kanta yana rawa jim kaɗan aka fito,

“uncle Samz da ƙwai zaka ci ko da geisha?”

“Any one…” ya bata amsa a takaice nan ta sake komawa nidai duk ina zaune ina kallon ikon Allah amma ban tanka ba,

Lokacin da ta kawo noodles ɗin kirana yayi wai in zo inci ai kam take naga yarinya ta ɗaure fuska tamau ta wani ɓata rai kamar wadda aka aikowa da saƙon mutuwa, murmushi nayi nace masa “ai ko kai kaga na sake cin wani abincin yanzu sai ka bincikeni tunda kaga uban tuwon da na haƙa” dariya suka yi gaba ɗaya banda Munira wadda har lokacin bata saki fuskarta ba nidai ban saurareta ba lokacin salla nayi na mike na gabatar, bayan na idar yace ya kamata mu tafi kamar kuwa dama ya san na gaji da zaman gida kawai nake son tafiya washe gari kuma agidanmu nake son inje in wuni dama zuwan shi ne ya hanani zuwa. Tun a hanya ya fuskanci akwai matsala saboda yadda nayi gumm da bakina bana amsa shi haka kuma naƙi nayi koda murmushi bare dariya, kayan da anty Amina ta bani kuwa Humra da turaren wuta tunda na cillasu kujerar baya ban sake bi ko ta kansu ba haka kuma sama sama nake amsa masa daga uhmmm sai uhmmm uhmmm na ɗauke kaina na juya ina kallon window, hannuna naji ya riko yana yimin magana,

“Baby….. Kina fushi dani ne?”

Shiru nayi masa ban amsa ba, kai a takaice dai har muka je gida ban saki fuska ba sannan muna shiga na kwaso masa abincin da na girka da rana dan kawai ina so yaki ci in tada daru,

“Haba baby a gabanki fa naci abinci….”

Cikin bacin rai na katse shi dan dama a wuya nake kuma kiris nake jira,

“to akan me zaka ci abincin acan tunda ka san ka tafi kabar wani anan wanda na dafa maka…. Oh wato ni gani ban iya girki ba abincina babu daɗi shiyasa zaka je ka zauna ka saki fuska kana dariya kana kwasar girkin wata….”

“baby…… Why are you like this? Come here, wannan cikin yafara saki masifa bayan da ba haka kike ba”

“babu wani masifa da ciki ya sakani maganar gaskiya ne, yarinyar da ko magana bata yimin ba tunda naje gidansu take daure fuska tana hararata ashe saboda kai take ta bina da kallon banza and the same girl da kaje ka saka a gaba kana yiwa dariya harda tayi maka abinci Kaci ni ka dawo ka ki cin nawa…. ”

Kallona naga ya zauna yana yi kafin daga bisani ya mika min hannu alamar inje gareshi amma sai na wani dauke kai naki zuwa na tsaye masa aka ina jira inga zai ci ko ba zai ci ba, ni bakin cikina yadda ya zauna yaita wani yi mata dariya harda cin abincinta,

“am very sorry baby, zan ci anjima kinga yanzu am full…..”

“Nifa ban yarda ba sai Kaci abincin nan…” daga haka na wuce cikin bedroom dina ina hawayen sakarci saboda ni kaina na san baida wani laifi akan abinda nake tuhumarsa dashi………

*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*

*_Ummi Shatu_*

Back to top button