Garin Dadi 37
©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( _Home of experts & perfect Writers_)
*GARIN DAƊI….*
_*NA*_
_*UMMI A’ISHA*_
*Wattpad:ummishatu*
PAID BOOK #500
{37}
*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma’abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*
~MAI DA TSOHUWA YARINYA
~FEMALE CARE
~REODEO
~VIGOR MAX
~ LONGZIT
~B CLEAR
*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA…..*
~~~Ko kallonsa banyi ba bare yasa ran zan kula shi ma, yana kwanciya akan gadon na sauka na bar masa gadon gaba ɗaya, ina turo baki, can kan sofa na koma na yi zamana inata faman harare harare, jin yunwa na neman illatani ya sanyani ɗaukar abincin da ya yi mana order daren jiya,shinkafar sanyi ƙarara amma haka na cuccusa sannan na ci shawarmar dake ajiye gefe,
Ban sake bi ta kan Samz bawan Allah ba dake kwance zazzabi yayi masa kamun kazar kuku domin ruf ya rufeshi irin rufewar da ko numfashi ya fitar to hucin zafi yake, ni duk a tunanina lafiyarshi ƙalau shiyasa nake ta sabgar gabana ban kula shi ba, har azahar, lokacin ne na farga da irin rawar ɗarin da jikinsa keyi, ɗan matsawa nayi dab dashi,
“Baby lulluɓeni…..” yace dani jikinsa na karkarwa, hannu na kai jikinsa nan naji zafi sosai,
“sorry…..” na faɗa ina lulluɓarsa, duk da ina cikin fushin abin da yayi min amma ajiye fushin nayi a gefe a raina ina cewa sai ya warke zan ɗora daga inda na tsaya, abubuwa nake ta lulluɓa masa amma cewa yake wai inƙara lulluɓarsa dan ji yake kamar ban lulluɓa masa komai ba,
Irin halin da naga yana ciki ai tuni na fara kuka ina yi masa sannu tare da cemasa ya tashi mu tafi asibiti, hannu naga ya miƙo min, ina kamawa yajani jikinsa wanda ya ɗau zafi,
“Sannu…. Dan Allah ka tashi mu tafi asibiti kaji”
“shhh…..” yace min tare da sake matse ni, shiru nayi ina sauraren bugun da zuciyoyinmu keyi domin kaina yana ta saitin ƙirjinsa ne, a haka naji ya samu bacci, buɗe idanuwa na nayi ina kallonsa, sai kakkame jikinsa yake yi kamar wanda yake razana cikin baccin, addu’a na soma tofa masa zuwa wani lokaci, can naga ya buɗe idonsa, yunƙurawa yayi ya ɗau wayarsa ya kira Ahmad,
“Dan Allah ka kawo min maganin zazzaɓi mana……, ina hotel bana gida”
Sai da ya sanar dashi hotel ɗin da muke sannan ya ajiye wayar, kallona yayi yace,
“ki buɗe ƙofa Ahmad yana nan zuwa yanzu”
Tashi nayi naje na buɗe sannan na dawo na zauna gefen sa,
“sanyi fa nake ji…..” naji ya faɗa yana sake curewa wuri ɗaya na gane nufinsa so yake insake komawa jikinsa, babu yadda na iya jikinsa nasake zuwa na shiga nan ya rufeni ruf haɓarsa bisa kaina. Koda naji motsin shigowar Ahmad lumshe idanuwana nayi nai luf kamar me bacci, har ciki ya ƙaraso bayan Samz yayi masa izini,
“Sorry…. Ya jikin? Wai tun yaushe ne zazzaɓin?”
“Da shi na kwana wallahi…. Gashi ni matsala ta magani bai fiya zama a cikina ba”
“Daurewa zaka yi, Allah ya baka lafiya”
“Amin, dan Allah ka samoma baby abinci”
“ok to ina zuwa”
Saida naji fitar sa sannan na bude idona na kai kallo na kan kyakkyawar fuskarsa,
“Kaga kasa abokinka yazo ya samemu ahaka…. Ko kunya baka ji….”
Turo baki naga shima yayi sannan cikin zafin zazzabi naji yace,
“Dama ai ya san abunda muke yi, soo dan ya ganmu ahaka babu wani abu…..”
“Ni dai babu ruwana… Babu abin da muke yi” na bashi amsa ina ɓoye kai na a ƙirjinsa,
“uhmmm” shine abin da yace kawai ya sake matse ni, ahaka Ahmad ya dawo ya same mu inda ya kawo mana abinci cikin take away daga nan yayi masa sallama ya fita, ƙofar naje na rufe bayan fitarsa sannan na dawo wurin samz abincin na taimaka masa yaci kafin ya sha maganin ya koma ya kwanta babu ɓata lokaci bacci ya ɗaukeshi. Nima ɗan taɓa abincin nayi sannan na shiga wanka nayi na fito ɗaure da towel har lokacin bacci yake zama nayi gefensa na kai hannuna ɗaya na taɓa jikinsa, akwai zazzabin sai dai zafin ya ɗan ragu,
Ban ɓata lokaci sosai wurin yin kwalliya ba dan cream kawai na shafa sai turarena na touch na saka doguwar riga marar nauyi onion pink dan gaba ɗaya kayan nawa dama waɗanda na taho dasu na hutawa ne da shan iska dan duk ƙananan kaya ne amma kuma abun haushi sai ga abin da na tarar wata ƙatuwa tare da mijina, wallahi har bana son tunowa wannan abun dan da zarar na tuna sai inji kamar in shaƙe kaina dan ko yawu da ƙyar nake iya haɗiyewa tsabar zafin da zuciya ta keyi,
Salla nayi bayan na idar na zauna nayi addu’o’ina sannan na tashi na koma bayanshi na kwanta tare da rungumeshi ta baya duk da har lokacin bai farka ba, ni na san ina masifar son mijina amma duk da hakan ba zai hana in nuna masa ɓacin raina akan cin amanar da yayi min ba, son da nake yi masa bana jin zan iya rayuwa da wani namijin wanda bashi ba kamar yadda shima ya jima yana sanar dani wai ba zai iya zama da wata mace ba indai bani bace shine lokacin nace masa to kuma idan na mutu fa? Wai wallahi idan na mutu to shi ma haka zai yi ta zama har tashi mutuwar ta zo ta iske shi amma ni dai koda ya mutu kar in zauna haka in yi aure, haɗe rai nayi nace saboda nice baya kishi ko shiyasa zai faɗi haka wai ba rashin kishi bane shi yana baƙin cikin wani ya shiga gonar nan tasa dan dai kawai dan kar yace in zauna kar in yi aure wani yaga sirrinsa inga kamar ya fiya son kai shiyasa yace in yi kuma ni mace ce wata rana ta yuyu inji kewarsa shi kuma gashi ya mutu ai sai asamu matsala, turo baki nayi nace ni babu wani kewa da zanyi saboda azumi zan yi ta yi, dariya yayi yace ashe dai ana yinshi,
Kwantar da kaina nayi a bayansa ina mai lumshe idanuwana, hannuna naji ya riƙe da nashi tashi nayi shima ya tashi, bathroom ya shiga yayi alwala ya fito yayi salla sannan ya sake kwanciya gefe na yana shafa ƙunshin hannuna da tun zuwansa yake ta faman kallo, jikinsa ya jani har lokacin da zazzabi a jikinsa amma tsabar ƙarfin hali haka ya fara kissing ɗina nima ina ramawa, salon soyayyar yau da ya nuna min ta dabance daga ƙarshe ya rungume ni yana mayar da numfashi a hankali zuwa can naji yace,
“Am very sorry baby…. Wallahi banci amanarki ba…. Ban taɓa sanin wata ƴa mace ba bayan ke…..”
Saurin rufe masa baki nayi da hannun na domin yanzu bana buƙatar jin komai daga gareshi saboda yanayin da muka tsinci kanmu kaɗai ya isa gamsar dani hakan, kan shi na ɗora bisa ƙirjina na rungume ina shafawa, shima a nasa ɓangaren godiya yake yi wa Allah da ya tsare shi bai biye wa sharrin zuciya da na shaiɗan ya tafka saɓon Allah da Felicia ba da tuni ƙila yanzu ita zai bawa abin da ya jima yana buri,
Ni kaina naji a jikina kamar yanayin na yau ya banbanta da na baya,kallona yayi cikin sanyin murya yace “Gashi bana son taɓa ruwa ya za ayi kenan?”, rufe idanuwana nayi ban bashi amsa ba, a daren ranar muka tattara muka bar hotel ɗin muka koma gidansa muka sake buɗe shafin soyayya,zazzabin a yanzu ya sauka gaba ɗaya, ina kwance jikinsa sanye da rigar bacci na naji yace,
” Kamar mun samu baby yau ko?” kafaɗa na maƙale nace, “Ba yanzu ba sai nan da 2 years lokacin mutane sun manta lokacin da muka yi aure, amma yanzu kunya zan ji kowa ya san abin da muka yi”
Dariya yayi ya sumbaci goshina yace “To menene solution?”
“Planning…” na bashi amsa kai tsaye, murmushi naga ya sake yi sannan yace “Da wanne method zaki yi amfani?”
“I don’t even know…”
Wayarshi ya ɗauka yana ce min “Ok let us check and see……” ya faɗa kamar gaske nikuma ban san wayo yake yi min ba harda ƙara shigewa jikinsa ina kallo nima,
“Kina son Pills?” kafaɗa na maƙale, murmushi yayi yawuce yace,
“Implan?” kafaɗa na sake maƙalewa alamar bana so,
“ok Injection?”
“No”
“Withdrawal method?”
“uhmmm uhmmm”
“To wanne zaki yi? Kowanne kince a’a”
“ni bana son period ɗina ya rikice…. Kai kayi mana”
Ware ido yayi kafin yayi murmushi yace “ni idan kin yarda withdrawal method zanyi”
Shure shure na fara na shagwaɓe fuska nace ni ban yarda ba sai dai ya je asa masa irin wanda ake sakawa maza shi kuma ya kafe akan lallai ga wanda zai yi saboda kawai ya san ba zan yarda ba.
Bayan sati biyu da zuwana na fara fama da tashin zuciya da amai haka kawai ko babu abin da naci sai inji amai yana taso min gashi kwata kwata na kasa gane abin da nake sha’awa takamaimai dan gaba ɗaya abincin duniya ji nayi na tsanesu duk wanda na sani da ma wanda ban sani ba, shi kansa tun da na fara aman nan ban sake yi masa girki ba sai dai idan ya fita yaci nikuma maltina kaɗai nake iya sha itama tunda nayi amai shikenan naji ta fita a kaina,
Kasancewar yau weekend ne yana gida yana bacci, zuwa 11 ya tashi yayi wanka ya fito ina zaune falo sanye da farar riga iya cinya mai ɗan siririn hannu dama shi nake jira ya tashi, zama yayi kusa dani ya dafa kafaɗa ta yajani jikinsa yana shafa cinyata, kallonsa nayi yana sanye da milk colour din trouser da brown ɗin riga a gaban rigar an rubuta _Beyond Reality_ “nifa yunwa nake ji” na faɗa kamar zanyi kuka,
“Me zaki ci?” ya tambaye ni cikin kulawa, shiru na ɗan yi zuwa can nace,
“Waina da kunun tsamiya”
“Wainar shinkafa?” yatsina fuska nayi nace “Wainar gero da ƙuli ƙuli”
“To shikenan bari in fita in samo miki….” ya faɗa cikin kulawa duk da can cikin ransa tunani yake ta inda zai fara neman wainar gero a garin Abuja dama dama da a ce wainar shinkafa ne ma da dasauki,
“wannan kwaɗayin da kike yi 2 days baby anya na lafiya ne?” ya fada cikin zolaya,
“kai ma ka sani ai…. Ni wallahi bazan koma kano ba sai na haihu”
Kissing ɗina yayi a goshi sannan naji yace “I love both of you”
“We love you too…” na bashi amsa ina kissing lips ɗinsa, fita yayi ina jin sa yana tambayar Ahmad a waya inda zai samo waina da kunun tsamiya Ahmad yace sai dai yaje Zubah kuma ina sa ran can ɗin ya tafi, murmushi nayi na zame hular kaina na soma tsefe kitson kaina dan tuni ya fara damuna amma kuma da zarar na tuna inada ciki sai inji wata mummunar faɗuwar gaba irin wadda ban taɓa jiba……………..
*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*
_*Ummi Shatu*_