Garin Dadi Hausa NovelHausa Novels

Garin Dadi 30

Sponsored Links

©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(Home of expert & perfect Writers)_

*GARIN DAƊI…..!*

*_NA_*

*_UMMI A’ISHA_*

PAID BOOK #500

*Wattpad:ummishatu*

30

*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma’abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA…..*

~~~Wani farin ciki ne ke faman ɗawainiya dani ina jin rayuwata da gangar jikina kamar tana tafiya akan iska, da zarar na tuna cewa nida samz gobe zamu zama ma’aurata kuma mallakin juna sai inji ƙafafuwana tamkar baza su iya ɗaukana ba saboda tsantsar shauƙi da tsananin ɗoki,

Hannayena na saka na sake maƙale shi bayan na ɗaga idanuwana ina kallon fuskarsa, zaune nake gefenshi amma ina cikin jikinsa nasa hannaye na zagaye shi kaina bisa kafaɗarsa, wata irin zazzafar soyayyarsa nake ji wadda ban taɓa jiba dan ji nake kamar zan koma cikin cikinsa dan so, kallo na shima yayi muka haɗa ido,

“ni kika yima rowa ko?” ya faɗa yana ɗan cije lips ɗin shi na ƙasa, farrr nayi masa da idanuwa na kafin nayi masa gwalo, goshinsa ya haɗa da nawa sannan ya bani amsa da,

“zan rama ne…. Ki gama naki iya yau kaɗai gareki…. Ni kuwa daga gobe nawa turn ɗin zai fara….. Zaki yi bayani”

Shagwaɓe fuska nayi na sake narkewa acikin jikinsa,

“nidai a’a”

“nima a’a” ya faɗa cikin kwaikwayon muryata, dariya muka yi gaba ɗaya daga ni har shi,

“ɗan gyara min zip ɗin rigata….” nace dashi jin alamun mun ƙaraso event center ɗin,saida ya turo baki kamar yadda nake yi masa sannan ya zuge min zip ɗin yana hararata cikin shauƙin so,ƴar pose ɗita ya buɗe ya ƙara min kuɗi ƴan ɗari biyar biyar sabbi fil wanda ya ciro daga cikin aljihunsa.

A tare muka jera bayan mun fito daga cikin hall ɗin muna riƙe da hannun juna kuma tun daga nan aka fara haskamu da camera, haske kake gani ko ta ina an zagaye mu ana yimana hotuna,

“Masha Allah…. My favorite couple” ƙawalli ta faɗa bayan ta tsaya kusa dani dan a ɗauke mu tare, mun jima awaje kafin aka yi mana jagora zuwa ciki kuma har lokacin hannuna yana saƙale cikin nasa, har wurin zaman mu aka rakamu sannan aka fara gabatar da abubuwan, addu’a aka fara yi daga nan aka yi jawabin maraba da ɗan taƙaitaccen tarihin kowannenmu daga bisani aka fara cashewa bayan an kira amarya da ango,

Anci an sha an raƙashe haka kuma an zubar da kuɗi babu laifi, misalin ƙarfe 10:30 aka tashi, yanzu kam ba tare dashi zamu koma ba, ina katarin anty wanda hakan ba ƙaramin daɗi yayi min ba dan nasan wataƙila idan dashi zamu koma ya nemi yimin abun neman magana daga ƙarshe muyi faɗa idan na bijire,

Muna komawa gida nayi wanka nabi lafiyar gado duk da ina ɗan jin yunwa dan yanzu bana cin abinci sosai. Kasancewar na gaji bacci na nayi haiƙan har sai da gari ya waye sannan na tashi, tunda na tashi kuma da zarar na tuna yau za a ɗaura min aure a kaini gidan miji sai inji gabana ya tsinke ya faɗi haka dai nake ta daurewa nayi wanka aka yimin kwalliya nayi shiga ta cikin wani tsadadden leshi wanda anty ta ɗinka min dark purple, da yake yau ake wuni shiyasa gidan namu cike yake taf da ƴan uwa da abokan arziƙi a nata cashewa da masu kiɗan ƙwaryar da aka ɗauko, wayata a kashe take banma san inda take ba, anty ce ta sakani a ɗaki ta bani wani farfesun kaza kuma ta sakani a gaba sai na cinye, idan ban manta ba irin wannan naman naci yafi sau uku kuma duk babu daɗi dan har ji na nake kamar zan amayo dashi, abubuwan da anty ta ɗura min acikin cikin nan nawa sun fi gaban lissafawa duk da sunan maganin infection da na gyaran jiki, haka dai na rinƙa yaga ina ci ina yatsine fuska da haka har na cinye sannan ta haɗa min maltina da madara na sha ƙawalli sai gwalo take yimin idan ta faki idon anty, bayan na gama ci mun fito muka ji alamun dawowar ƴan ɗaurin aure nan na sake jin jikina yayi sanyi shikenan aure ya ɗauru, ban sake gaskata hakan ba sai da yayuna suka shigo suna bada labarin an ɗaura akan sadaki naira dubu ɗari, kamar zanyi kuka amma anty tace idan na kuskura nayi hawaye nida ita ne, sake shiryani aka yi muka fita wurin angwaye, ya sha farar shadda ƙal da baƙin glasses a idonshi yayi kyau har ya gaji, hotuna aka yiyyi mana sannan suka tafi mu kuma muka koma gida kafin kace me har anfara maganar tafiya kaini, ji nayi kamar in gudu wani wurin in ɓoye amma babu dama domin duk inda nayi ƙawalli na biye dani, ita ta rakani wurin Abba ma yayi min nasiha irinta uba da ƴa sannan su mama, faɗan da suka yimin shine ya saka ni kuka kamar zanyi hauka, itama Anty nata faɗan tayi min kamar haka,

“To widat gashi dai Allah ya kawo mu ya nuna mana, rana bata ƙarya, yau zaki tafi gidan mijin ki, to wallahi kar naji labarin ƙazanta da rashin gyara, sannan banda raina miji banda rashin kunya, haka ƴan uwansa kisa aranki baza su taɓa sonki ba… Hakan shi zai sa ki zauna lafiya kuma zuciyar ki ta huta, dan duk tsanar da zasu nuna miki dama kin san hakan zai biyo baya, amma idan kika sawa ranki dole sai sun soki to zaki tabbata cikin damuwa dan baza su soki ba saboda kullum kallon wadda ta raba su da ɗan uwansu ta fitar dashi daga addininsu zasu yi ta yi miki amma Hakan kar ya hanaki kyautata musu idan sun zo gareki, kiyi musu dukkan wani nau’i na kyautatawa musamman ma mahaifiyarsa karki yarda ki wulakantata dan ta nuna bata sonki, ki tuna itace ta kawo mijin ki duniya tayi ɗawainiya dashi har ya zama abin da ya zama yanzu, kiyi mata biyayya iya iyawarki kuma ki girmama ta ki bata matsayin uwa…. Allah ya baku zaman lafiya ”

Duk faɗan da iyaye suka yi min na anty ne yafi tsaya min arai da naji tayi maganar ƴan uwan samz ba zasu soni ba, tabbas nima na fahimci hakan domin babu wadda ya taɓa nemana acikin ƴan uwansa ko danginsa, anty Amina ce kaɗai matar uncle ɗinsa da wasu dangin su ke fafutukar zuwa neman aure na dan yanzun ma sune suka zo ɗaukar amarya,

A can gidan su samz kuwa mahaifiyarsa bata san abin da ke gudana ba dan daddy baya shiga shirginta kuma baya sanar da ita komai akan batun auren mu da Samz, sai yau ta sani da taga Abdullahi ƙaninsa yayi shiga da manyan kaya nan take tambayarsa ina zai je? Amsa ya bata da wai ɗaurin auren Samz ai tunda taji haka ta yanke jiki ta faɗi bata sake sanin inda kanta yake ba saboda dama tana da lalurar hawan jini, asibiti aka kai ta aka bata gado amma samz kwata kwata bai san hakan yana faruwa ba dan babu wanda ya faɗa masa kuma ko auren nasa ma daddy ne ya gargaɗeshi akan ya ɓoye mata karya kuskura ya sanar da ita idan ba haka ba hanawa zata yi zata bi bokaye a ɓata lamarin wannan dalilin ne yasa bai sanar da ita ba.

Bayan sallar magriba aka kaini gidana dake unguwar hotoro, kuma ana kaini kowa ya kama gabansa aka watse aka barni inata shaƙar kuka na, ƙawalli kuwa saida ta gama yimin rashin mutuncinta kafin ta tafi daga baya kuma itama kukan tayi sannan ta tafi, ganin zaman shiru yana neman damuna yasa nayi alwala nayi sallolin dake kaina wato magriba da isha, bayan na idar na koma kan gado na takure ina kallon uban dukiyar da aka kashe min acikin ɗakina wanda komai silver colour, shi kuwa ango bai shigo ba sai bayan sallar ishah kuma shi kaɗai babu ɗan rakiya dama iya Ahmad ne abokin nasa to shi kuma tun bayan ɗaurin aure ya koma Abuja,

A kusa dani ya zauna yana ƙoƙarin buɗe fuskata,

“Kuka kike yi ne?” ya buƙata cikin tsokana, shiru nayi na sunkuyar da kaina,

“Ahmad yace akwai salla da zamuyi ta nafila raka’a biyu ko? Muyi sai ki ci abinci ki kwanta…. Zan bar ki ki huta yau”

Shiru nayi nai tsit kamar ruwa ya cinye ni, hannuna ya kama cikin nashi,

“Kin jima kina tambayar wacce irin rashin lafiya nake yi idan banda lafiya amma bana faɗa miki ko? To yau zan faɗa miki dan kece maganin…. Ciwon ciki ne kuma Dr ya tabbatar min da maganin yana wurin ki soo sau nawa zaki rinƙa bani? Da safe da yamma, ko da safe da rana da yamma da kuma dare? ” ai ban san lokacin da na kalleshi ba a tsorace, shi ɗinma ni yake kallo, murmushi naga yayi ya miƙe tsaye, nikam ji nayi kunyar duniya ta taru ta lulluɓeni kamar ƙasa ta buɗe in shige, gaskiya sai yau na yarda namiji bai da kunya, alwala ya ɗauro muka yi salla raka’a biyu muka karanta abin da ya sawwaƙa cikin Littafi mai tsarki muka yi addu’a, abin da ya shigo dashi ya ɗauko mana, gasasshiyar kaza ce sai fresh milk da fruits, kan cinyarsa ya ɗora ni yayi ta yimin ɗura har sai da ya cika min ciki dan wai ya fahimci ban ci abinci ba, wanka yace in je inyi nace nayi, bai takura min ba shi ya rage kayan jikinsa ya shiga daga shi sai boxer, sai bayan da ya shiga sannan nayi hanzarin saka kayan bacci riga da wando na shige cikin bargo, shima bai wani jima sosai ba ya fito ɗaure da towel, leƙensa nake yi ta yadda ba zai gane ba ina kallonsa ya shafa turare yasa kayan baccin sa baccin sa wando iya rabin cinyarsa da riga armless, kan gadon ya nufo nan nayi gaggawar rufe idanuwa na, gaba ɗaya a sanyaye yake sakamakon wayar da ƙanwarshi Mary tayi masa ɗazu ɗazun nan tana sanar dashi rashin lafiyar mommy wadda ke kwance a asibiti wannan abun da yaji shine musabbabin tashin hankalinsa kawai yana dannewa ne yana nuna min he’s ok. A hankali ya hawo kan gadon ya kwanta gefena wanda hakan sai da naji gabana ya faɗi, wayarshi ya kashe sannan ya ajiyeta kan bedside drawer kusa da tawa,

“Baby…. Yau rowa ta ƙare ko?” yace dani yana ƙoƙarin jawoni jikinsa da hannayensa masu taushi, ban ƙiba na shige cikin jikinsa nayi pillow da ƙirjinsa,

“kina jin bacci?”

“uhmm” na bashi amsa,

“yau baki ya mutu Babu magana? “Ya faɗa yana shafa gadon bayana a hankali zuwa can naji yana ɓalle botiran jikin rigar tawa,

“zaki fi jin daɗin bacci a haka” ya raɗa min bayan ya saɓule rigar daga jikina, manna ni yayi a jikinsa bayan shima ya cire tashi rigar, duk da ina cikin kiɗima tare da ɗimuwa hakan bai hanani jin daɗin ɗumin jikinsa ba dan kamar me zazzabi haka naji jikinsa,

“baka da lafiya ne?” na tambayeshi bayan na ɗaga kaina na kalleshi acikin duhun da muke kwance,

“a’a lafiya nake….. Me ya faru?”

“naji jikin ka ne kamar da zafi”

“a’a haka temperature ɗin jikina yake normally…..”

“kuma kaje hospital?”

“me zai kaini hospital alhali lafiya ta ƙalau”

Murmushi nayi na mayar da kaina na kwantar araina ina tunanin dalilin da yasa ya iya barina daren yau, tuno tsokanar da Ƙawalli ta rinƙa yimin ɗazu kafin ta tafi nayi, sake maƙaleshi nayi tsam ina shaƙar ƙamshin jikinsa, ina jinsa hannunsa yaƙi tsayawa wuri guda a jikina ya taɓa can ya taɓa can da haka har ya isa inda ya jima yana kwaɗayin zuwa, na san dalilinsa na auna ƙirjina saboda dab da lokacin bikin mu yake cemin wai matar uncle ɗinsa ta haɗo lefenmu yaje gani wai yaga ta saka manyan braziers wanda ko haihuwa nayi ba lallai su yi min daidai ba nikuma nace wallahi in dai wanda na ganine zasu yimin amma yace ƙarya nake wai ni ɗin nawa nake shi so yake ma ya samomin cream in rinƙa shafawa ko zan ciko, tsokana iri iri babu wadda bai yimin ba sai rabuwa nayi dashi, sai da yagama ganin ƙwaƙwaf ɗin shi sannan muka yi addu’a tare, wani bacci mai daɗi ne yayi awon gaba dani jina a alƙayyar da ban taɓa samun kaina aciki ba………….✍

Asuba ta gari Widsamz

*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*

 

*_Ummi Shatu_*

Back to top button