Cuta ta Dau Cuta 28
*_Typing_*
*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_
_ _
_Shafi na ashirin da takwas_
________________
_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_
_KU MARMATSO KUSA…_
_ZAFAFA BIYAR 2024_
_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA’ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_
_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI… DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR…WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_
_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR… CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_
_________
_1_
*_AMEENATUH_*: _MAMUH GEE_
_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)_*_:BILYN ABDULL_
_3_
*_GUDUN KADDARA_*:_SAFIYYAH HUGUMA_
_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)_*_:NANA HAFSATU (MX)_
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYARALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE_
_______________
…….Shiru falon yay kowa ya zubama aunty Kubra idanu dake ma Khadijah guɗa da zazzaga mata turare.
“Aunty gafa amaren nan”. Wata Rumaisa ƙawar Ni’ima ta faɗa tana nuna su Zuhrah. Kai tsaye Aunty Kubra ta bata amsa da “Ai itama amaryar ce”.
Kallon juna aka koma yi, yayinda Zuhrah da Ni’ima suka wani irin miƙewa daga jikin Khadijah a zabure. Khadijah kam kamar wadda ta suma a zaune idanu kawai ta zubama aunty Kubra kamar ta sami hoton bango.
“Aunty Kubra kin san mi kike cewa kuwa? Aunty Khadijah ce amarya?”.
“Kwarai ma kuwa, itama an ɗaura mata aure tare da ku. Ayyyiririrrrriiii!!!!!”. Ta sake sakin ghuɗa akan Khadijah da su Zuhrah gaba ɗaya. Dai-dai nan Inna Zulai ta shigo kiran amaren su duka. Ganin tace harda Khadijah yasa mutane suka fara gaskata zancen aunty Kubra da kowa ke tunanin tsokanar Khadijahn take da farko. Sake dabircewa Khadijah tai dan har tana neman faɗuwa sai da Inna Zulai ta riƙota tana faɗin, “Hankali mana Khadijah”. Bata iya cewa komai ba, sai rawa da jikinta ke cigaba dayi. A haka suka fito ƙofar gidan dake cike da maza ƴan ɗaurin aure. Yawanci duk dangi ne sai ƴan anguwa da abokan Baba. Anguna daga ɗaurin aure sun tafi walimar da suka shiryama kansu, sai anjima kaɗan zasu iso nan wajen saukar Alkur’anin da za’ayi mai haɗe da walima da islamiyyasu Khadijahn ta shirya musu. A ɗakin soro aka shiga dasu, inda Baba ke tare da shiƙiƙan ƴan uwansa harma da kawunai. Bayan an zaunar dasu suka gaishesu, sai dai Khadijah har yanzu da alama bata gama dawowa dai-dai ba. Nasiha kowa ya fara musu mai ratsa jiki, hakan ya sake rikita Khadijah ganin su dukansu kamar ana musu ishara da sabuwar rayuwar da suka shigan, tsabar yanda komai ke mata yawo ji take kamar tacema kawunan nasu itafa banda ita. Sai dai babu damar hakan dole ta nutsu har suka gama faɗansu da nasihar. Kiran sunanta da Kawu Bala yayi ne ya sa gabanta sake faɗuwa. Muryarta har rawa take wajen amsa masa da “Na’am Kawu”.
“Matso nan kusa”.
Matsawa tayi kamar yanda ya buƙata. Sake cemata yay ta ɗago fuskarta, anan ma babu musu tai yanda yace. Dukansu dake ɗakin ya nuna mata, murya a dake ya ce, “Miye matsayinmu a wajenki?”.
Da rawar murya ta ce, “Iyayena”.
“Kin tabbatar da wannan sunan mun cancancesa a gareki?”.
Kanta ta jinjina musu hawaye na silalo mata a kumatu. “Alhamdullah” ya faɗa tare da cigaba da faɗin, “Munji daɗi da kika tabbatar da mu ɗin iyayenki ne. Dan haka a matsayinmu na iyayenki mun ɗaura miki aure kema a yau tare da ƴan uwanki. Kuma insha ALLAHU zakiyi alfahari da hakan da mukai miki. Ba kuma muyi haka dan ƙasƙantar da ke ba ko tauye miki hakki. A’a haka ALLAH ya ƙaddara wannan kuma ikonsa ne da tsarawarsa. Amma muma abin yazo mana ne a bazata. Dan kwata-kwata bai wuce sati biyu da suka shige zancen ya shigo ba, ba kuma muyi tunanin zai zama gaskiya ba sai a kwanakin satin nan da suka gabata. Mun ɓoye miki ne saboda gudun komawa ƴar gidan jiya. Muna fatan zaki kasance ƴa mai biyayya a wannan lokacin, dan in sha ALLAHU sai kinyi alfahari da wannan auren Khadijatul-Kair. ALLAH yay muku albarka. Ya baku zaman lafiya ku da mazajenku da zuri’a mai albarka. Ku zauna lafiya dan ALLAH kodan ku sake kwantarma mahaifinku da hankali kun daiga halin da ya shiga ciki a baya. To yanzu ku ya rage ku sakanka masa da ƙoƙarin sa gareku ta hanyar zama lafiya da mazajen aurenku kamar yanda kuka ga mahaifiyarku tana zaune da shi lafiya kunji. Aita haƙuri kuma, dan shi aure ba zaman nanaye bane da shargalle kamar yanda ku yaran zamani kuke kallo. Auren bautar UBANGIJI ne. Shi kuma bautar ALLAH sai da jajircewa ake yinta da tsafta sannan ai mata kwalliya da haƙuri sai a samu aljanna da ake fata.”
Sosai Khadijah ke ƙoƙarin riƙe kukanta. Harga ALLAH gaba ɗaya ma ta gama ruɗewa da gigicewa. Itafa aka ɗaurama aure a yau. Ya arrahaman ya akai haka ta kasance? Rashin amsa yasata ƙara daurewa, dan tayi alƙawarin a wannan gaɓar, koda mijin nata zai kasance gurgu ne. Makaho ne. Zata zauna dashi kasancewar su iyayenta suka zaɓa mata shi. Kai koda ace ƙazami ne, ko da ace jahili ne. Kai koda ma ace yanada wani mummunan hali in har bazai sakata saɓama UBANGIJI ba, zata zauna da shi. Ta kuma san ma iyayenta bazasu taɓa aura mata wanda zai ɗorata a hanyar zuwa wutar jahannama ba.
Nasiha sosai akai musu a ɗakin har iyayensu mata suma sun shigo suka ɗora nasu kafin a fito dasu saboda kiran sallar la’asar. Cikin gida aka shiga dasu wajen Mama. Kasa daurewa Khadijah tayi ta faɗa jikinta tana hawaye mara sauti. Rungumeta kawai mama tai batace komai ba. Dan harga ALLAH tana tausayin ƴar tata. Amma tana mata fatan alkairi a wannan auren. Suma su Ni’ima jikin Maman suka shige suna kuka. Hakan yasa dangi abokan wasa sukai musu caa da sheri wasu na karesu….
Bayan idar da sallar la’asar duk aka ɗunguma babbar harabar islamiyyar su da za’ayi taron. Komai an gama shiryawa manyan baƙi kuma duk sun iso dama sallar dai ake buƙatar fara gabatarwa sannan. Zaman amare da aka sakema shiga cikin dogayen rigunan abaya farare da adon golden da mintuna kaɗan tawagar anguna ta iso wajen. Nan take wajen ya ƙara cika taf. Sauka aka fara gabatarwa, inda komai ya tafi a cikin tsari da birgewa. Yayinda bakunan anguna ya kasa rufuwa. Sai dai babu wanda yasan wanene angon Khadijah har zuwa yanzu idan ka cire iyayenta maza. Sun sami ƙyaututtuka da suka bada mamaki musamman wanda suka fito da ga ogan abokan ango Abaan Omar Modibbo. Dan kuwa mukullayen motoci har uku ƙanana dai amma masu ƙyau da ɗaukar hankali ya bama amaren su duka ukun dan sun birgesa matuƙa. Bayan wannan ma wasu ƙyaututtukan sun biyo baya dan islamiyyar sun gayyaci manyan mutane sosai, hatta da su Baba Hakimi da suka taso tun daga Adamawa basu wuceba suma sun tsaya domin saukar, kafin a fara gudanar da lectures masu ratsa jiki ga anguna da amare. Har zuwa yanzu bawai Khadijah ta fita a ɗimuwar da take ciki bane ba. Dauriya kawai take da son tilasta kanta zama a dake, amma duk da haka jikinta zazzaɓi ne mai zafi sosai dan tunda suka zauna a wajen ma kanta na a kafaɗar Ni’ima kasancewar duk sanda ya ɗago sai ta kama ogan anguna da ake kira Alhaji Abaan Modibbo na kallonta, sai ta daina ɗagowar har sai da aka kirasu wajen sauka. Suna dawowa bayan an kammala ma dai kwance take shiru a jikin Zuhrah data koma kusa da ita a yanzun. Sauka ta ƙyatar sosai. Ansha hotuna kamar babu gobe. Anan ne ma dai mutane suka fara tsarguwa da hasashen wanda kowa kema kallon angon Khadijah ganin duk sanda za’ai hoto yana a kusa da ita ne, amma kuma basu da tabbas har aka tashi gab da magrib.
Bayan sallar isha’i akai shirin miƙa amare ɗakunansu. Sai dai kuma banda Khadijah. Ayanzu ne fa sukai asalin kukan rabuwa. Dan da ƙyar aka raba su Ni’ima da ga jikin Mama da Khadijah. Da aka kaisu yima Baba sallama ma nan ma ansha ɗan ƙaramin bidiri kafin. Har ƴan kai amarya suka je suka dawo Khadijah na kwance a ɗaki zazzaɓi yay mata rijif. Koda mama ta bata magani ma fakar idonta tai ta ajiye ta koma ta kwanta. Anata sam barka da gidajen amare. Abin farin ciki kuma suna a jere da juna ne komai nasu kuma iri ɗaya kamar wanda suka aura tagwaye. Koda yake Ibrahim da Adams kowa na iya kallonsu da tagwaye saboda shaƙuwarsu da ƙaunar fa sukema juna. To sai muce ALLAH ya sanya alkairi ya kuma basu zaman lafiya mai ɗorewa….
*_WASHE GARI_*
Duk da yanda Khadijah ta tashi a yanayin rashin lafiya Baba ya tabbatar da yau za’a wuce da ita nata ɗakin mijin. Dan kuwa ya tabbatar da ƴan uwan ango da motocin ɗaukar amarya tun jiya suna Kano yau kuma zasu wuce da ita. Dan haka ƙarfe goma duk wanda zai rakkiyar Khadijah ya shirya tsaff. Dan motocin har sun iso tare da masu amsar amarya. An musu tarba ta mutuntawa kamar yanda suma suka shigo da dattakonsu. Matane guda biyar sai abokan ango da galla-gallan motoci har kusan ashirin. Al’amarin ya bama kowa mamaki daya kawo maganganu suka fara tashi a anguwa. Kowa na faɗin albarkacin bakinsa. Ƴan ɗaukar amarya ke sanar da amarya ita a jirgi zata wuce tare da mutum biyu, dan haka motocin da suka ɗauki dangi tuni sun ɗauki hanyar Abuja.
Bayan kammala shirya Khadijah dake ta faman kwasar kuka aka kaita ga baba. Sai da ya sanya mata albarka tare da nasiha mai ratsa jiki da addu’a kamar yanda yayma ƴan uwanta jiya sannan ya ɗora da faɗin, “Naso ace na baki damar zaɓar Miji da kanki Khadijah domin ki tabbatar da na huce na kuma yafe miki. Sai dai tsarin UBANGIJI ya banbanta ne dana kowa. Amma in sha ALLAHU idan kikayi haƙuri a yanzun ma zakiyi farin ciki fiye da zaɓin da zaki iyama kanki. Dan mutumin nan mutumin kirki ne da tabbas aurenki da shi wata hikima ce ta UBANGIJI. Naso na faɗa miki dukkan yanda al’amarin ya kasance haka. Sai dai ya roƙi alfarmar na barsa ya sanar miki da kansa. Dan haka dan ALLAH ina roƙonki kije kuyi haƙuri a gidan aurenki Khadijah. Kima mijinki biyayya, ki ƙyautatama ƴan uwansa da maƙotanki. Ki manta da abinda ya faru baya sunansa ƙaddara. Ita kuma ƙaddara ai babu mai iya tsallaketa. ALLAH yay miki albarka ke da sauran ƴan uwanki”.
A tare aka amsa da Amin. Yayinda Khadijah ta sake fashewa da kuka da faɗin, “Baba in sha ALLAHU zan kasance mai biyayya a gare ku. Kuma dan ALLAH ku yafe min ku yafe min. In sha ALLAH zan tabbatar muku da ni ɗin ɗiyace tagari akan wannan auren”.
“Mun yafe miki tuni Khadijah. Fatanmu dai ki bama mara sa ɗa kunya kawai. Ki zauna lafiya ki kuma ringumi sabuwar rayuwarki ta yanzu da hannu biyu da kuma haƙuri”.
“In sha ALLAHU Baba”.
Sauran ƴan uwa sun sake mata nasiha sannan aka fito da ita zuwa motar da zata kaisu airport ɗin ita da wasu dangin angon 2 da aka bari, sai Inna Zulai da Gwaggo Safina da zasu mata rakkiyar suma. Har suka isa airport kuka sosai Khadijah keyi Inna Zulai dai na lallashinta. Sun ɗan yi zama saboda kai kawo da jiran lokacin daya rage dan sai 12:30 jirginsu ya ɗaga. Khadijah ta sake hawa jirgi a karo na biyu. Yayinda su Gwaggo Safina ya kasance musu na farko. Cikin mintuna ƙalilan suka iso Abuja. Anan ma sun tarar da motoci na jiransu har guda biyu. Ɗaya Khadijah da iyayenta suka shiga. Ɗayar kuma ƴan uwan ango biyu dake tare da su ne. Khadijah dai na kwance jikin Inna Zulai har suka iso inda taji suna faman santi ƙasa-ƙasa, duk da dai dama tunda suka fito airport bakinsu bai huta ba sai faman ƙus-ƙus sukeyi.
Tun daga gate su Gwaggo Safina suka sake tabbatar da ƴarsu Khadijah ta sake shiga cikin zuri’ar fulani kamar dai mijinta Dafeeq na farko. Banbancin kawai shi Dafeeq sun jima a birni a yanzu ko fillancin ma babu maiji a iyayensa. Suko wannan sunata yara yarensu a baki tabbacin basu bar gida ba. Tarba akai musu ta girmamawa da mutuntawa. Yayinda suma suka nuna nasu dattakon. Dan duk da an nuna musu sashen amarya basu yarda sun nufi can da ita ba suka buƙaci a kaisu sashen mahaifiyarsa tunda ance suna tare ne a gida ɗaya. Aiko sunji daɗin wannan ƙarancin.
An fara kai Khadijah wajen surukata. Katafaren falo na gani na faɗa da yaji kayan more rayuwa kamar ba’asan ciwon kuɗi ba. Kai tsaye suka gane wacece mahaifiyar angon. Dan dai-dai Khadijah da fuskarta ke lulluɓe da mayafin da aka rufa mata na kaiwa duƙe kamilalliyar dattijuwar matar dake zaune cikin kujera 2sitter ta kamo hannunta ta zaunar a kujerar kusa da ita tare da rungumeta. Ta tsufa kam, sai dai ba wani tsufa ba irin na takwarkwashewa. Dan akwai jin daɗi sosai tattare da ita. Kasa daurewa Khadijah tai ta zamo ƙasa kusa da ƙafafunta ta zauna. Hakan datai ya sake birge ƴan uwan ango dama mahaifiyarsa sosai……….✍️
*_ZAFAFAN DAI_*
*_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*❤❤❤
*_KASANCE D’AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_*
_WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_
*_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_*
*KWANKWASON JIMINA miss xoxo*
*TSUTSAR NAMA Billynabdul*
*GUDUN K’ADDARA Huguma*
*AMEENATU Mamuhghee*
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR… ZAFAFA BIYAR NAKU NE_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu _*