Cuta ta Dau Cuta Hausa NovelHausa Novels

Cuta ta Dau Cuta 24

Sponsored Links

*_Typing_*

 

 

 

*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_

 

_ _

 

_Shafi na ashirin da huɗu_

__________

*_ZAFAFAN DAI_*

*_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*❤‍❤‍❤‍

*_KASANCE D’AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_*

_WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_

*_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_*

*KWANKWASON JIMINA miss xoxo*

*TSUTSAR NAMA Billynabdul*

*GUDUN K’ADDARA Huguma*

*AMEENATU Mamuhghee*

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR… ZAFAFA BIYAR NAKU NE_

____________

……Wani irin duka zuciyarsa keyi matuƙa da ganin Kainaat ɗin. Dan duk yanda yaso dakewa yay fuska hakan ya gagara gareshi. Cikin ɗan rawar harshe da shan jinin jikinsa ya furta, “Mi kikeyi anan haka Hajiya?”.
“Zuminci”.
Ta bashi amsa a gadarance a kuma taƙaice. Batare data jira cewarsa ba tai gaba abunta ƴar rakiyarta biye da ita. Sosai yaji kansa yana juya masa, dan magana ta gaskiya ya fara tsoron shegiyar matar nan. Dan ya fahimci dole akwai abinda take ƙullawa, kai anya ma ba’itace ta saka aka kawo Khadijah da su Baba Hakimi Kano ba? Lallai biri yayi kama da mutum, dan ya kamata ma ace yay wannan tunanin, to amma bai zama lallai ita ɗin bace tunda yasan in har Khadijah gidan Baba Hakimi ta tafi a safiyar daya saketa dole Baba Hakimi zai iya cewa zai rakota gida. Gaba ɗaya kansa ya kasa haska masa komai game da abinda Kainaat take son shiryawa, bai da zaɓin kuma daya wuce tafiya su haɗu a police station ɗin kamar yanda akace masa.
Koda ya koma gida duk haukan daya dinga yi akan Kainaat ta sanar masa mitaje yi gidan su Khadijah ko kallonsa batai ba balle ma ya samu wata amsa. Hasalima ta tattarashi ta watsar ne tai kwanciyarta. Cikar lokacin tafiya station ya sakashi ƙyaleta ya wuce yana rayama ransa dole zai yi maganin ta ne.

*_POLICE STATION_*

Kowa da ake buƙatar gani ya iso, har D.p.o ya bada umarnin fito da iyayen Dafeeq da suka kwana a rufe. Sai dai abin mamaki sam hankalinsa ma baya kansu ya zubama Khadijah idone tamkar zai cinyeta. Shifa badan kar ace yay ƙarya ba sai yaga a kwanaki kusan goma sha ɗayan nan da rabuwarsu kamar harma ta canja. Tai masa wani irin fresh da ita, babu bandage ko ɗaya yanzu a jikinta sai ɗan alamun tabbunan ciwukan. Ga wani ƙamshi mai tada hankali da take zubawa. Tana sanye cikin doguwar rigar abayar Ni’ima baƙa da aka wadata da duwatsu sai walwali take. Shi shaida ne Khadijah ƙyaƙyƙyawace. Dan irin black beauty yaran nan ne masu taushin fata da ƙyalli tamkar ƴaƴan masu kudin na da rana bata ganinsu kullum suna ac. Gata da murzajjen jiki dan babu rama tattare da ita sam kasancewarta cikakkiyar mace da ALLAH ya wadata da komai dake tabbatar da mace a mace. Tunda suka haɗa ido tai masa wani banzan kallo daya girgiza zuciyarsa ta ɗauke kanta bata sake kallon ko sashen da yake ba. Amma shikam sam ya gagara daina kallonta. Jima yake kamar yaje ya rungumeta, dan wani irin mahaukacin sonta ne ke ƙara azalzalar zuciyarsa. Da gasken gaske yana matuƙar ƙaunar Khadijah, baima san miya shiga kansa ba ya saketa shikam, shiyyasa sam ba’a son yanke hukunci cikin fushi…..
Maganar d.p.o ce ta katse masa tunani, dole ya nutsu ya maida hankalinsa can. D.p.o ya fara bama Khadijah damar yin bayani akan duk abinda ya faru. Itako kanta tsaye babu ko shakka balle gargada ta shiga jero bayani tun daga marin da taima Dafeeq a makaranta har zuwa randa ya daketa ya kuma saketa bata ɓoye komai ba. Shima Baba hakimi ya maimaita tun daga randa sukaje wajensa har zuwansu nan Kano, wanda ke tare da shi suma sun tabbatar da hakan akai. Karo na farko ran mahaifin Dafeeq ya ɓaci. Bawan ALLAH muryarsa har rawa take wajen faɗin, “Amma kai ba haka ka faɗa mana ba Dafeeq. Yanzu nan kana tare da yarinyar nan tsahon shekara uku amma kazo kace mana ka saketa harma baka san inda take ba? Dafeeq wace irin rayuwa ce wannan ka zaɓama kan ka? Yanzu gatan da mukai maka a matsayinka na ɗa ɗaya tilo garemu domin nuna godiyarmu ga UBANGIJI kuma sai ya zama laifi kenan da ɗoraka akan wata hanya mara ɓillewa. Anji yarinyar nan itama nada laifi tunda bawai ka jata ta tsiya bane ka tafi da ita, da kanta ta zaɓi binka kuka tafi. Sai dai duk mai hankali da son faɗar gaskiya yasan Dafeeq ka fita laifi. Dan ita mace rauni ne da ita, sannan duk ƙanƙantar namiji a kanta zai iya yaudararta ya canja mata tunani, musamman ku yaran nan na zamani da kukai ma soyayya bahaguwar fahimta. Banji daɗi ba, dan kasa nida mahaifiyarka faɗa akan abinda ba haka yake ba. Duk da wlhy itace nidai ke zugani, koda naji bai kamata nayi abinda mukayi ba sai naji na kasa musa mata saboda soyayyar da nake muku kai da ita. Malam Muhammad dan ALLAH kayi haƙuri ka gafarcemu. Tabbas mun cutar daku kuma mun cutar da kammu. Dan kai mutumin kirki ne ka nuna mana dattako akan wannan al’amarin, saboda tunda aka fara bakace komai ba koda ɓatancine ga ɗanmu sai mune keta hauka a cikin anguwa batare da yin nazari da tunani irin na iyayen ƙwarai ba. Wannan shine mafi yawan kuskuren iyayen zamani akan kin amsar kuskuren ƴaƴansu saboda soyayya. Sai lokacin da abu ya ƙwaɓe yaro ya shiga cikin wani bala’i kuma mu kasa zaune mu kasa tsaye koma muce wani ne ya jefesa da asiri ko baki alhalin mune da kammu muka rusa masa rayuwa saboda gurguwar soyayya. Dan ALLAH ku yafe mana Malam Muhammad kai da iyalinka gaba ɗaya, yanzu da sanadin ciwon nan ka rasa ranka ina zamu saka kammu ne”.
Murmushi irin na dattako Baba ya saki, sai kuma ya nisa a hankali tare da furta, “Babu komai Malam Abubakar. In sha ALLAHU komai ya wuce a yanzu. Kuma dama can ni dai ban riƙe waninku ba face addu’ar kariya da nake bin su Khadijah da shi akan ALLAH ya hanesu aikata alfasha a ƙarƙashin inuwar shaiɗan. Kuma Alhmdllh na godema UBANGIJI daya kasance sun rayu ne a ƙarƙashin inuwar aure. Ko lokacin da kukazo kuke cemana Dafeeq ya saketa ta shiga duniya ban fasa gayama UBANGIJI na ba duk da mun shiga tashin hankali. Amma sai na dinga ganinta a mafarki cikin aminci akoda yaushe, na kuma dinga jin bana kokwanto akan tanada aure. Nayi imani da ƙaddara zata iya faɗawa akan komai, amma ina alfahari da fatan yanda ban taɓa taɓa ƴar kowa ba da nufin zina ko ɓata mata rayuwa nima in sha ALLAHU ALLAH zai bama nawa ƴaƴan kariya. ALLAH ya yafe mana baki ɗaya, ya kuma shirya mana yaranmu damu kammu dan aduk sanda suka aikata kuskure yakan zama wani lokacin muma iyaye da gudunmawarmu a ciki, duk da dai akwai tsayayyun iyaye da wlhy suna iya ƙoƙarinsu akan ƴaƴan amma zakaga abun sai dai addu’a kawai. Wasu kuma duk da suna ƙoƙarin zata iya yiyuwa suma sunma iyayensu wani kuskurene da suke girban abinda suka shuka akan ƴaƴan nasu kuma. Dan abinda muke mantawa idan fa ka aikatama iyayenka ƙyaƙyƙyawa kaima ƙyaƙyƙyawa zaka girba a wajen ƴaƴanka, idan mummuna ne kaima zaka girbi dai-dai da hakanne. Ni kaina ina danganta abinda Khadijah ta aikatamin da bijirewar da naima nawa iyayen akan auren mahaifiyarsu a farko, dan sai da takai bayan an aura min ita nai tahowata nan Kano kusan watanni biyar wai dan duk suji haushi su rabamu, amma koda na koma saina samu dai tana nan a gidanmu. Daga nan na karaya na sallama bayan ita da kanta tamun nasiha da tabbatar min itama ba sona take ba umarnin iyaye tabi, tana roƙona koda bazamu so juna ba muyima iyayenmu biyayya kodan darajar da ALLAH ya basu da fifiko a kammu na haihuwa. Wannan shine sanadin gyara komai harna ɗakkota muka dawo nan cikin Kano da zama. Duk da na roƙa iyayena gafara sun kuma yafemin gashi sai da na girba abinda na shuka ga ƴata ta fari dana ɗauki burin duniya na ɗaura a kanta da tunanin zata zama madubin ƙannenta a komai na rayuwa.”
Kuka sosai Khadijah ta saki hankalinta na ƙara tashi. Dan wlhy zuciyarta zata iya bugawa idan ƴaƴanta anan gaba akace zasu rama abin nan da taima mahaifanta. Cikin rawar jiki da kuka take roƙon dan ALLAH su yafe mata. Cikin murmushi Baba yace, “Ai komai ya wuce Khadijah na yafe miki. Mahaifiyarki ma ta yafe miki tun ma kan ki dawo garemu. ALLAH ya ƙara shirya mana ku”.
An amsa da Amin, yayinda Dafeeq ya durƙusa shima gaban Khadijah cikin sanyin murya ya ce, “Dan ALLAH nima kiyi haƙuri to ki dawo gareni Khadijah. Na miki alƙawarin wlhy zan koma miki kamar da yanda muke a farko. Abinda ya faru ma wlhy tsautsayi ne. Amma zan cigaba da riritaki fiye da yanda nai miki a farko”.
Wani banzan kallo ta masa hawaye na sauka mata. Sai kuma ta nuna kanta da faɗin, “Wai ni kake tunanin zan koma gareka Dafeeq? To kayi kuskure. Wlhy koda ace baka aikatamin komai ba hakan ta faru, zan hana kaina komawa aurenka saboda ya zama horo ga kuskuren dana aikata na bijirema iyayena. Koda ace kuwa ina jin soyayyar ka zata halakani wlhy. Balle ma a yanzu bana jin koda ɗigon soyayyar ka a raina. Kuma wlhy! Wlhy! Wlhy koda ace soyayyarka zata halakani, koda ace kaine autan maza na barka har abada Dafeeq…..”
Cikin rawar jiki da bugawar zuciya Dafeeq dake ƙoƙarin riƙo mata hannu ke furta, “Dan ALLAH Khadijah, dan ALLAH kada kice haka, kada kimun haka. Wlhy ina sonki, kuma kema nasan kina sona. Sharrin shaiɗanne kawai da munafuncin matar can. Amma wlhy kika barni zan iya rasa kaina gaba ɗaya. Sannan ni wlhy nama maidaki, na maida auren mu tun randa na ce nai sakin, kin san dai akwai sauran igiya ɗaya”.
Murmushi mai ciwo Khadijah ta saki. Sai kuma taja tsaki da taɓe baki. “Ka ɗauka ka maida banza Dafeeq, dan zama ni da kai har abada ya ƙare. Maganar matarka kuma kadai sone kawai ka ɗaura mata laifi. Amma ni zuwanta alkairi ma ya zame min. Tunda a sanadin zuwanta nasan kai ɗin nan, kai da kanka kake zubar min da ciki. Sannan kana zagayowa kazo ga iyayenka, ka kuma gyara mu’amalarka da su yayinda ni ka gama ɓata mun suna da mafi munin ɓatanci a wajen nawa iyayen da mutanen anguwa. Wai na shiga duniya! Kai jama’a na rasa miye ribarka kan aikata wannan shaiɗanar. Kaico da miji irinka, kaicona da bijirema iyayena nabi mutum irinka mara zuciya a ƙirji. Dan sam kai ɗin ba cikakken mutum bane Dafeeq. Kai azzalumi ne, kuma na barka da ALLAH, na kuma godema matarka dan alkairi ce nikan a gareni. Idan ma mafarki kake ka farka. Dan har abada ka rasa Khadijah Muhammad Kura, kasa wannan a ranka kama hutar da kanka okayyy”.
Sosai jikin Dafeeq ke mazari. Zaiyi magana d.p.o ya dakatar da shi. “Uhhm kaga magana taƙare kuma. Daga yau nima na kashe wannan case ɗin. Abinda ya rage shine dole ka bayyana ma duniya kai da iyayenka gaskiyar lamari domin wanke Khadijah kamar yanda kuka ɓata ta. Zamuyi a rubuce dan ya zama konan gaba wani abu ya taso ni da kaina zan ɗauki mataki akan duk wanda ya aikata”.
Baba ne ya amshe da faɗin, “Hakan yayi dai-dai yallaɓai kuma mun gode sosai. Sannan ina so yanzu a gabanka a gaban iyayensa dasu yallaɓai Hakimi ya janye maganar cewar ya maida Khadijah, yama cika mata ɗayan sakinta dan maganar gaskiya ni kaina bazan bar wannan auren sake komawa ba ya isa hakan nan. ALLAH ya haɗa kowa da rabonsa na alkairi”.
Sake rikicewa Dafeeq yay, hatta mahaifinsa roƙon baba yake akan yay haƙuri kada ya raba auren. Amma Khadijah ta rantse in bai saketa ba zata kaisa kotu kokuma ta faɗa rijiya ta mutu sai ya zauna da gawarta. Jin kalamanta yasa D.p.o tsare Dafeeq akan saifa ya janye maganar maida khadija da yace yayi. Dafeeq ya koma roƙon Baba Hakimi da Baba Harɗo. Suko sukace babu ruwansu, wannan zaɓin Khadijah da iyayenta ne ba nasu ba, basu da hurumi akan wannan batu. Dole Dafeeq naji na gani tare da zugar mahaifiyarsa data cika da takaici tai fam tun sanda babansa yay magana da bama Baba haƙuri ta shiga rantsuwar itama Dafeeq ɗin bazai sake zama da Khadijah ba. In ko ya cigaba da dagewa zata tsine masa ne. Garama ya saketa, idan kuma ya saketa bazai ragu da komai ba, shida keda mata ƴar arziƙi irin Kainaat miye dan ya rabu da wata Khadijah can da har zai wani damu kansa a banza a wofi har ana raina masa hankali da nuna tama fisa wani fifiko ne…….✍️

*_ZAFAFAN DAI_*

*_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*❤‍❤‍❤‍

*_KASANCE D’AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_*

_WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_

*_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_*

*KWANKWASON JIMINA miss xoxo*

*TSUTSAR NAMA Billynabdul*

*GUDUN K’ADDARA Huguma*

*AMEENATU Mamuhghee*

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR… ZAFAFA BIYAR NAKU NE_

 

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu _*

Back to top button