Cuta ta Dau Cuta 18
*_Typing_*
*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_
_ _
_Shafi na goma sha takwas_
______________
https://chat.whatsapp.com/CKY0xZDtpby6MTkGrPkXLr
*_Assalamualaikum warahmatullah_*
*_Kin dade kina neman gurin da zaki siya kaya amintattu masu quality cikin farashi me sauqi?_*
*_ina marabtarku zuwa cikin wannan gida tare da kasancewa da juna,WANNAN GIDANNA HUGUMA CLOSET NA BUDESHI NE SABODA NA BAKU DAMAR SIYAN KAYA MASU KYAU QUALITY DA KUMA SAUQIN KUDI CIKIN AMINCI DAGA GURINA,MASU SIYAN D’AI D’AI DA MASU SARI,NATION WIDE DELIVERY cikin aminci da izinin Allah,Kayan haihuwa na jarirai har zuwa girmansu,ina muna fatan alkhairi ni da ku gaba daya_*
_________________________
……A matuƙar hargitse JJ ya iso anguwar. Hakan ya tabbatar da dama yana gari babu wata Kaduna da yaje. Amma da yake su basu san komai akan batun ba sai tausayin yanda yake kuka ana riƙesa kamar wani mace ƴan anguwar sukeyi. Da yaje asibiti yaga su Anoosh kuwa sai ya yanke jiki ya faɗi wai ya suma. Sai da aka yayyafa masa ruwa tare da bashi gado. Dan da gaske razana yayi ganin Anoosh bata mutu ba ita. Sai dai bata san inda kanta yake ba tana cikin wani hali mai wahalar fassara…
JJ shine ya zama tamkar ɗan uwa na jini wajen jana’izar Hajiya Lailah, dan shine akan gaba, sannan shine ma ake ma gaisuwar. Shine ya kawo ƴan sanda akan shi bai yardaba sai a bincika a tabbatar da dalilin gobarar da alamu da yawa suka nuna akwai lauje cikin naɗi. Ba komai ya saka JJ yin hakan ba sai tsoron kar Anoosh ta rayu al’amari ya zama wani abu daban. Ƴan sanda sunyi bake-bake akan case ɗin, yayinda cikin ikon ALLAH suka samu wani ɗan alama da ya sakasu jin cewar lallai maganar JJ nada ƙamashin gaskiya, dan haka suka jajirce akan son binciko komai. A zahiri JJ na sake ingizasu da tsayawa tsayin daka akan binciken, a baɗini ko hankalinsa tashe yake da bin matakan toshe komai da zai bayyana gaskiya, tsabar son a yadda da shi ya kawo iyayen ƙaryar nan dai an ɗaura masa aure da Anoosh dan ya tabbatar musu da akowane hali take shi dai yana sonta. An jinjina ma wannan sadaukarwa tashi ƙwarai da gaske a anguwar, duk da ma auren an ɗaurashi ne kawai bayan idar da sallar magrib kamar yanda ya buƙata tare da waliyansa na ƙarya. Komai na Anoosh ya koma ƙarƙashin JJ batare da sanin kowa nashi ba, dan hatta ƴan san jin yanda akai idan sun so yin magana da shi baya yarda sai ma ya hau musu kuka akan shi su barshi yaji da abinda ya damesa. A haka Anoosh ta kwashe tsahon shekara kusan ɗaya kwance a asibiti. Tako ina al’umma na kawo taimako da gudunmawa, duk kuma abinda aka bada kai tsaye a asusun JJ yake tafiya. Duk da dai ana cire wasu ai hidimar asibitin. Tana da shekara ɗaya da wata uku likitoci suka bada shawarar fita da ita ƙasar waje yimata wani ai. Ɗari bisa ɗari JJ ya yarda da batun, har ma an fara shirye-shiryen hakan, sai dai kwanaki uku dayin maganar ALLAH yay mata rasuwa. Ta rasu idanunta ƙyam akan JJ tana hawaye.
Yanke jiki JJ yay ya faɗi a wajen, sai da doctor ya tsaya kansa ya farfaɗo. Yanda yake wani irin kukan tashin hankali dole ka tausaya masa, dan harga ALLAH da gaske kukan yake yi. An kai Anoosh makwancinta na gaskiya JJ na a wani hali, bai kuma samu kansa ba sai a washe gari. Kamar yanda ya zama komai a yayin rasuwar Hajiya Lailah a ta Anoosh ma dai shi akema gaisuwar har akai addu’ar uku. Bayan ƙura ta lafa ya ɗan cigaba da zuwa anguwar har bayan wasu watanni, dan haka gidan su Anoosh ya cigaba da kasancewa a ƙarƙashin kulawar ƴan sanda da dattijan anguwar. JJ ma dake zuwa jefi-jefi ya rage zuwa. Watanta bakwai da rasuwa ya haɗu da Alimah. Ƙyaƙyƙyawar yarinya mai kama da larabawan Sudan. Dan Alimah ba fara bace, sannan bata kasance baƙa wulik ba. Mace ce har mace a tsaye da sura ga ƙyawun fuska da ko mace ta kalleta sai ta sake kallo.
Alimah dai ƙawa ce ga Rabi’ah ƙanwarsa. Department ɗin su ɗaya a F.C.E. A wata ranar babbar salla tajema Rabi’ah yawo gida sukaci karo da JJ a ƙofar gida. Cikin masifa ya ɗago a zatonsa a cikin ƙannensa ne. Amma sai yaci karo da halittar data nema gigita rayuwarsa. Dan kuwa dai sumar tsaye yayi har Alimah ta gama magiyar bashi haƙuri baima san tanai ba sai da Rabi’ah ta taɓashi ya dawo hayyacinsa. Bai iya cewa komai ba, face gyaɗa kai tamkar wani dole. Bayan shigewarsu gida sai shima ya fasa fitar ya koma ciki. Zama yay a falo tare da su, dukkan wani motsin Alimah akan idonsa ne. Tun ma bata farga ba har dai ta tsargu. Al’amari kamar wasa dai sai ga magana ta zama babba, dan lokacin da Alimah da ƙanwarta suka tashi tafiya sai JJ ya dage akan zai kaisu gida. Badan taso hakan ba ta amince aka tafi harda Rabi’ah suka maidasu gida. Wannan shine sanadin da JJ yasan gidan su Alimah. Bayan sun dawo gida kuma ya titsiye Rabi’ah da tambaya akan Alimah. Itako ta sanar masa komai. Tun daga lokacin JJ ya koma kai Rabi’ah makaranta da kansa, yakan je kuma ya ɗakkota duk dan Alimah, sai dai duk yanda yaso Alimah ta kulashi hakan ya gagara, iyakarta da shi gaisuwa matsayin yayan ƙawarta Rabi’ah.
Irinsu JJ idan ALLAH ya tashi kamasu ba’a magana, dan kuwa dai da gaske neman zaucewa yake akan Alimah, yayinda itako ta cigaba da jansa a ƙasa. Bawai wulaƙanci take masa ba ko zaginsa, kawai dai bata shiga sabgarsa ne bayan gaisuwa. Taƙi kuma bashi fuskar tunkararta koda da magana ne. Haka ya cigaba da haƙuri da jurewa dan so yakema Alimah na gaskiya, soyayya ta aure. Har faɗama abokansa su MB yake shikam ya samu matar aure. Hakama gidansu kowa yasan yana son Alimah. Dan danan JJ aka fara gini, sannan ya rage abubuwa da yawa musamman akan harkar mata. Da farko iyayensa sunyi mamakin inda ya samu kuɗin gini haka, dan filin kansa ba wannan suka sani nashi ba. Amma sai ya musu bayani akan kasuwanci ya shiga shi da wani uban gidansa aka samu yay albarka, hasalima ubangidan nasa ne ya bashi filin. Sanin wanda yake kira da uban gidan nashi yasaka su yarda, duk da kuwa ya kamata a matsayinsu na iyaye su bincika uban gidan nasa tunda bawai ya wani jima da kawoshi garesu ba ne. Amma tunda kudi na shigowa yana ɗaukar wasu daga cikin ɗawainiyarsu sai babu wanda ya sake masa magana akan hakan.
Ya cigaba da ginin gidansa da yaƙin campaign ɗin soyayyar Alimah, wadda da ƙyar da ƙyar ya samu ta fara kulashi. Ya fara rawar jikin kashe mata kuɗi mahaifinta ya taka masa birki, tare da shimfiɗa masa dokoki na neman ƴarsa in har da gaske yake. Babu musu JJ yabi kowace doka, dan hatta hira bayayi da Alimah sai a falon mahaifinta tare da ƙannenta biyu. Sannan akwai cctv camara a falon da mahaifin nasu ke ganin duk wani motsinsu da ga bedroom ɗinsa. Sannan a sati sau biyu yake zuwa kawai hira, dokace bazai tsareta a hanya ko makaranta ba ko dan ya ganta a gidansu. Ako ina suka haɗu gaisuwace kawai, hira dole sai yazo gidansu. Da yake da aure JJ keson Alimah duk ya amshi waɗan nan dokoki da hannu biyu kuma yana kiyaye wa har iyaye suka shiga cikin lamarinsu. Ahakan ma dokar bata sauya ba, dan duk da mahaifinsu ba wani mai kuɗi bane akwai dai rufin asiri tsaye yake akan ƴaƴansa. Shekara ɗaya aka saka bikin, akwana a tashi ta cika aka shiga shagalin biki. A gidan su Alimah ɗaurin aure kawai sukayi babu wata bidi’a a ciki, sai dai bayan an kaita gidan su JJ ne suka ɗora da nasu bikin a yanda suke so. Shine akai dinner da dare bayan an kaita gidansu, washe gari aka kaita ɗakinta….
★______________★
Hayaniyar mutane a kanta da zafin hantsin rana daya fara fitowa suka farkar da ita. A hankali take ƙoƙarin buɗe idanunta da sukai mata matuƙar nauyi, bata iya gane komai sai cakai-cakai ɗin mutanen da kowa ke faɗar albarkacin bakinsa game da ita. Wasu na ganin accident ne, wasu na ganin ɓarayine sukai mata haka suka yardata a bakin titin. Sai dai an kasa samun ko mutum ɗaya da zai taimaka mata. Hasalima kowa tsoron taɓata yake yi. Dai-dai tana ƙoƙarin sake buɗe idanunta a karo na biyu wata mota baƙa wulik mai ƙyawun gaske ta iso wajen. Kasancewar a hankali motar ke tafiya harta ɗan gotasu sai kuma aka gangara gefen titi ta gabansu kaɗan. Wasu hankalinsu akan motar yake, yayinda wasu ke cigaba da surutansu akan Khadijah.
Da sauri drivern motar ya fito domin cika umarnin ogansa da yace yaje ya duba mike faruwa a wajen, ya nufo taron mutanen da ƴar sassarfa yana faɗin, “Bayin ALLAH lafiya kuwa? Mike faruwa kuka taru anan haka?”.
“Wlhy wata yarinyace aka samu kwance anan kamar ma ta mutu duk raunuka a jikinta. Sai dai bamu san miya sameta ba ko dalilin yasar da ita anan ɗin. Gadai tanan da alama ta farfaɗo ma”. Wani magidancin dattijo ya bashi amsa cike da kulawa. Mamakine ya kamashi har ya bayyana a saman fuskarsa. Amma sai baice komai ba ya juya ya koma motar. Saitin sit ɗin baya ya tsaya tare da ɗan rissinawa yanda zai iya gani wanda ke ciki. Glass ɗin aka sauke a hankali, wani ƙyaƙyƙyawan kamilin matashin mutum ya bayyana. Cikin dattako da tausasa lafazi ya furta “Mike faruwa ne Awwal?”.
“Wata yarinya ce Yaya aka yasar a wajen, sai dai suma basu san accident tai ba ko jefar da ita akayi, amma dai tana cikin wani hali kuma duk suna jin tsoron taimaka mata”.
Shiru yay yana kallon Awwal ɗin cikin yanayin mamaki da ɗan ɓacin rai, sai kuma ya girgiza kansa batare da yace komai ba ya buɗe motar ya fito. Da sauri Awwal ya matsa ya bashi hanya. Tun fitowarsa motar ƙamshin turarensa ya baɗe wajen, hakan yasa mafi yawan mutanen waigowa suna kallonsa, sai kuma wasu suka shiga rawar jikin gaishesa duk da kuwa basu san wanene ba, sai dai kuma a duk inda mai kuɗi yake a cikin al’ummar mu ta yanzu zakaga an ɗaukesa ne da muhimmanci koda ba’asan wanene ba ko inda ya fito. Hannu kawai ya ɗaga musu cikin gyaɗa kai da faɗin, “Barka”. Sai kuma ya ɗan bisu da kallo da sake faɗin, “To mizai hana da wannan zagayetan da kukai ku ɗauketa ku kaita asibiti bayin ALLAH”.
Ai kamar wanda yay shela a kunnuwansu, a take suka shiga darewa. Yayinda wasu ma suke ƙoƙarin barin wajen suna ƙunƙuni alamar dai su bazasu taimaketa ba kenan. Mamakine yake neman halakashi a tsaye, sai dai kuma bai gama haɗa mamakin nasa ba idanunsa suka sauka akan yarinyar dake kwance a wani yanayi mai ban tashin hankali da al’ajabi. Duk da shi ba ɗan sanda bane a kallo ɗaya da yayma Khadijah ya fahimci ba accident taiba dukane wannan. Bai ma san lokacin daya ƙarasa gareta da sauri ba yana baton sunan UBANGIJI.. Har ya kai hannu zai taɓata sai kuma ya dakata, sake ɗagowa yay yabi mutanen dake wajen da ido, babu abinda yake buƙatar gani, wato ƴar uwarta mace, hakan ya sashi ɗaukarta cak batare da ya kalleta ba zuwa motarsu dan gaba ɗaya mutanen wajen ma haushi suke bashi. Da sauri Awwal ya buɗe masa gaban motar alamar ya sakata anan. Amma sai ya girgiza masa kai da masa nuni da sit ɗin baya. Babu yanda Awwal ya iya sai cika umarni, a bayan ya kwantar da ita, shi kuma ya koma gaba ya zauna, yana ƙoƙarin rufewa Awwal ya miƙa masa takardar data faɗo daga jikin Khadijah. “Yaya daga jikinta ta faɗo.”
Takardar ya ɗan zubama ido kamar bazai amsa ba, sai kuma ya amsa batare da yace komai ba ya ajiye gaban motar. Zagayawa Awwal yay mazaunin driver, yana ƙoƙarin ma motar key ya ce, “Zamuje asibiti ne Yaya?”.
Kai ya gyaɗa masa alamar eh.
Jin sun fara tafiya Khadijah dake jinsu ta kai hannunta da ƙyar saman fuskarta ta share hawayenta. Cikin muryarta dake fita da ƙyar ta ce, “Dan ALLAH na roƙeku kada ku kaini asibitin garin nan ku wuce dani Kano. Idan ma mutuwa zanyi na mutu gaban iyayena ko zasu yafemin kar naje ga UBANGIJINA yana mai fushi da ni”.
Da mamaki Awwal da yasan ba lallai Yayan nasa ya tanka ba ya ɗan dubeta ta mirror da faɗin, “Haba ƴar uwa wane Kano za’a wuce da ke a wannan halin, babu abinda kike buƙata ai sama da kulawar likita a yanzu”.
Kuka ta sake fashe musu da shi tana cigaba da magiya. Har sun ɗauki hanyar asibiti idanunsa akan wayarsa tamkar baima san mike faruwa a motarba a hankali ya furta, “Muje airport ɗin”.
Sosai Awwal yay mamakin jin abinda Yayan nasa ya faɗa, dan shi dai yasan sun riga sun sayi ticket ɗinsu guda biyu tun a jiya da dare. Sai dai bai iya cewa komai ba sai amsawa da “to” cikin girmamawa. Daga haka ya ɗauki hanyar airport ɗin. Suna isowa airport ɗin yay kiran wani Attahir. Cikin mintuna kaɗan sai gashi ya isa. Fita yay yana bama Awwal umarnin zama a motar ya jirashi, shi kuma suka nufi wata hanya shida Attahir ɗin bayan ya leƙo yaga Khadijah da barcin wahala ya figa….
★Koda gari ya waye Dafeeq yayi zaton Khadijah na gidan bata wuceba. Dan shi a tashi wautar bazata iya barinsa ta tafi ba kodan wasu dalilai. Ƙwaƙwƙwara a cikinsu shine bazata iya tunkarar iyayenta ba saboda tsoro. Sannan tana masa matsanancin son da bazata iya taɓa rabuwa da shi ba. Ko sakin da yay mata guda biyu yayine dan gargaɗi, zai kuma maidata amma sai ya wajiga rayuwarta ta yanda ko kallon banza bazata sake marmarin sake kwatanta yimasa ba. Sai ta koma masa tamkar baiwa ta yanda kozai maidata ƙasa dan takawa bazata sake koda tari ba. So yake ta koma jin tsoronsa fiye da yanda takeyi a baya.
Baibi takan Kainaat ba sai ma hidimarsa yake hankali kwance kamar baida wata damuwa. Nan ko can ƙasan ransa addu’a yake ALLAH yasa Khadijah tazo ta bashi haƙuri da wuri. Anci Sa’a kamar yanda ya share Kainaat ɗin itama ta tattarashi ta watsar a wannan yinin ita a dole fushi take da shi. Hasalima yini tai a ɗaki kwance. Sai kusan uku na rana aka kawo mata order na abinci da tayi sannan ta sakko ƙasa. Sun fito kusan tare da Dafeeq da ke kwance shima a ɗakin, sai dai rashin jin motsin Khadijah ya damai ya ce bara dai ya fito ya duba. Sake tamke fuska yay lokacin da suka haɗa ido da Hajiyar tasa. Itama sai ta ɗauke nata kan batare da tace komai ba ta haura sama abinta cike da takun izza da taƙama. Ƙwafa yay da cije lips ɗinsa, yayinda yake ayyana abubuwa a ransa kawai. Sai da yaji shigarta ɗaki da rufe ƙofa sannan ya nufi ɗakin da Khadijah take da sassarfa. Sosai gabansa ya faɗi ganin ɗakin wayam, amma sai ya ƙarfafa kansa ya nufi toilet. Nanma babu kowa, babu ma alamar anyi amfani da ruwa dan ko’ina a bushe yake. Ji yay zuciyarsa na motsi a cikin ƙirji, dan haka ya fito har ƙafafunsa na harɗewa. Ƙofofin ɗakunan ƙasan ya shiga buɗewa, sai dai ko’ina babu ita babu alamarta. Shine har kitchen, nan ma wayam, ya sake komawa sama ya dudduba, nan ma dai shiru. Da sauri ya sakko ƙasa zuwa wajen maigadi……..✍️
_Huummm Dafeeq. JJ _
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu _*