Adandi 44
*44*
Rayuwa taci gaba da tafiya a haka koyaushe da kalar sabin mugun nufin da nake bullowa dashi wa Samha da ubanta amma har lkcn basa ganewa banyi nasara ba saboda duk yanda naso da Samha ta saki jiki da Na’im su lalace taqi yarda hakanne yasa nikuma na dage kan sai ta aureshi ana haka suka hadu da Abdu babu yanda banyi ba don narabata dashi tunda na fahimci ya fara canza mata rayuwa amma abin ya gagara dole tasa na qyale duk wani hali da Samha ta samu kanta bayan aurenta da Abdu nice sanadi nice na sanya mata ciwon ciki da nufin cikin yarannan ya lalace nice na binne musu asiri ta taka a qofar parlournsu har yayi sanadin zuwan yayannan duniya lkcnsu baiyi ba nice nayi sanadin komai da ya faru dake Samha La’ilaha illallah Samha na cutar da mutane da yawa…”
Tana mgnr tana kuka miqewa Samha tayi jikinta na rawa ta juya zata fice daga dakin Dad ya riqota yace “Bazan taba yabewa Lubabatu ba Samha ta zamemin masifa a cikin rayuwata wannan wanne irin bala’i ne kin kashemin iyaye kin raba yata da uwarta sannan kinyi qoqarin lalatamin yata Allah bai baki saa ba yanzu kuma kin hanata farin ciki da mijinta kullum cikin jifansu da mugayen kaba’irai kike to kiyi ki warke zamuyi shari’a dake wlh sai kinyi bayanin komai yanda yake” sake fashewa da kuka Samha tayi tace Allah ya isa bazan yafe miki ba mamy kin rabani da dumin jikin mahaifiyata tun Ina zanin goyo kawai saboda wata manufa taki ta qashin kanki bazan ce miki komai ba Dad kada kayi qararta ka barta da azabar duniya ma ta isheta” juyawa tayi zata fita Abdul ya riqota yace “likita ya tabbatar da mamy tanada cuta me karya garkuwar jiki wato HIV…”
Gaba daya dakin juyowa sukayi cike da tashin hankali itakam Samha baya tayi luuuu ta suma hankalin kowa ya koma kanta shikam Dad bai iya tabata ba saboda tashin hankali wasu hawaye yake zubarwa masu zafi yana kallon Mairo da har yanzu ya kasa gane wace ita yana kallon Dr Hasina duk da hawayen da suka zubowa Dr Hasina hakan bai hanata yiwa mijin nata murmushin qarfafa gwiwa ba daukan Samha akayi aka shiga da ita wani daki inda daqyar Mai martaba ya rarrashi Dad sukaje Lab aka dauki jininsu domin yi musu text sai yamma Samha ta dawo hayyacinta ta fashe da kuka tace “HIV yanzu Dad yana HIV aunty ma haka Innanillahi wa Innah ilaihir raji’un wannan wacce irin masifa ce…” Rufe mata baki Abdu yayi yace “waye ya fada miki Dad bashi da ita yanzu akayi masa text kingama results din a hanuna” riqeshi tayi tana dariya tace “da…da gaske Abdul Dad da aunty basuda HIV wayyoh Allah na gde maka” dariya Dad dake shigowa yayi yace “banida ita daughter” rungumeshi tayi tana dariya shima dariyar yayi suka fita suka nufi gda.
Bayan kwanaki biyu labari ya ishesu Hajiya Luba ta rasu abin mamaki tana rasuwa Dad ya shigo afujajan yana kiran “Maryam Maryam ya akayi kika barni meye ya faru kika gudu kika barni”
_Marnege_
*UMMUH HAIRAN CE…*
[3/1, 12:04 PM] UMMUH HAIRAN CE…: *AD*