Auren Gado Hausa NovelHausa Novels

Auren Gado 69-70

Sponsored Links

*bazan rufe wannan lbr ba batareda godiya a gareku ba y’an uwa marubuta, kun nuna min kauna ta gaskiya kunbani goyon bayan da bazan taba mancewa ba*
Gareki my writer SA’ADATU BINT ABDULLAH,
tareda ke AUTAR MANYA, karamcin ki bamai faduwa bane Allahu yabar kauna da soyaya.
Hazika mai yayi fasihiya NIMCY LOVE jin jinar bangirma.
Hakurin ki abun kwatance ne my Aunty, BINTA UMAR ABBALE.
ina maganar hakuri karamci bazan manta dakeba MAMAN NURUL HUDA.
Addu’a tareda jinjinar bangirma mai rubutu da ilimi da hangen nesa HASSANA D’AN LARABAWA.
… GARKUWAR MARUBUTA uwa maba da’ mama Allah yasa ki gama labrin tubali lafiya,
Kunada matukar yawa bazaku fadi dukaba sai dai kusani duk kuna zuciya ta Allah yasadamu da Alkharin sa Ameen.
Sakon ta Aziya garemu baki daya na marubuta biyu da muka rasa kwanan nan Allah muma yasa mu cika da kyau da Imani, ina kewar ki Zinariya Allah ya Albarkaci Abinda kika bari. Amen Amen

…………..shiya rakata har cikin dakin Shukrah nata baccin ta, Nur yafarka tareda saka hannu yana wulwula kafafun shi na shirin yin kuka, da saurin shi yana dariya ya daukeshi tareda fita ya na mata ido ta biyoshi, dakin shi suka tafi ya shinfide shi a gadon shi ya na mai wasa, saida ta shige tayi wanka tafito takarbeshi yana kallon su ta bashi nono ya cafke yana sha, matsowa khaleel yayi tareda hadasu ya Rungume, “my boy na maka wayau nasha nima. A wannan daren baiyi wani baccin kirki ba yana nan makale da iyalin shi, harta ti bacci haka ya zuba musu ido yana godiya ga Ubangiji,
Tsabar gajiyar da tayi batasan gari ya waye ba, haryayi wanka ya shirya ya dauki yaron shi yafito falon dai dai momy na tanbayar Shukrah ina Y’ar uwar ki take? Bata kaiga bada amsa ba tayi wuki wuki domin ba Naziya ba har Nur batasan inda yake ba itama tayi baccin gajiya, “ga jikan ki nan Momy. Suka juya tareda zuba mai ido yana wani irin sheki da daukar ido, “kai ina uwar shi take? “Bacci takeyi Momy kinsan gajiyar taro. Kallon Shukrah tayi tace jeki nemi breakfast kinji, kai kuma mara kunya bani shi inyi mai wanka, Allah ya shirye ka, don iya shege don nayi bacci ka lallabo kazo ka takure yarinya bayan tagaji, kaga kabi yarinyar nan a hankali tana biki karkasa ta kwainuka. “Meye haka kuma momy? Ubanka modu ne. “Momy ba ruwana ita tabiyo ni dakanta fa narakota shine muka kwana anan. “Allah sarkin y’an sharri? “Oh yanzu baki Y’ar da ba Momy? ” get away. Ta wuce Abinta. Yayi dariya tareda cewa “sai kin shafa kinga takoma gidan ta zaki gane itama tana kewa ta.

A haka sukaci gaba da jegon su cikin gata da kulawar momy Shukrah dai sati biyu tayi dakyar inna tace abata Y’ar ta haka, momy tace ai mungode ma ko a hakan kulu. Shukrah ansaka ranar ta da Almajirin malam sadiq, tuni anfara shirye shirye, Wanda khaleel ya biyawa malam da Inna Ummara harma da Shukrah, yace su hajji zasuje bana shida Naziya in Allah yakaimu, sunyi murna sunyi farin ciki sunyi Addu’a tareda sa Albarka.
Momy ce ta tsaya tsayin daka ta hadawa Shukrah kayan daki dana kitchen kafin su Inna sudawo Ummara, Wanda koda suka dawo suka tarar da Abin Arziki, malam Yayi ta fada yace abun Yayi yawa, momy tace Shukrah Y’ar tace da Ace tanada wani d’an ma shi zata bawa ta hada su biyu a gidan ta, domin ba Wanda yaki irin Arziki a gidan shi, suna dawowa aka fara shirye shirye, Nur nada wata biyu, Yayi bulbul, kullum suna hanyar gidan malam a cikin motocin ta sai wadda taga damar hawa, wani lokaci harma ta khaleel tukawa takeyi, kowa yaganta yasan yes tana cikin lokacin ta a gidan mijin ta, tazamo Y’ar gata gidan miji da cikin d’an gi,su suka dage suka gyara kanwar su wadda itama tabi tana gyara kanta domin tasani tana tareda gwarzon miji, da baya gajiya da ita.

Related Articles

A haka sukayi Auren Shukrah cikin girma da farin ciki kowa ya koma gidan shi ya tsuguna, Wanda saboda karamci malam yabawa kawu modu wakilcin uban Amarya shi yayi na ango Wanda ya mugun farantawa kawu dasu khaleel rai, harma da momy tayi farin ciki Wanda wannan dalilin yakara musu Y’ar da da shakuwa a tsakanin su.

Ina labarin su Salifa? Tuni momy ta roki khaleel tareda sa bakin Naziya yasa aka kyalesu, sunyi matukar nadama domin sunga jarabawa don Salifa tuni tafara wani irin ciwo duk ta rame ta fita hayyacin ta Wanda koda aka kaita Asibiti gwajin farko aka gano ta daukeda ciwon zamani, tayi kuka momyn ta harda suma saboda tashin hankali haka ta zauna jinyar ta gata itama kwankwason ta sai a hankali tun buguwar da tayi, fadin halin da suka shiga ma bata lokaci ne, don haka Allah yasa muyi kyakkyawan karshe a rayuwar mu.

Bayan wata shida da haihuwar Nur, a zaune take tana share hawaye yana faman lallashin ta, kallon pregnancy test strip din takeyi tana share hanci, dariya yake hadiyewa ya kalli d’an shi dake zaune yana wasa da kayan wasan shi yayi kamar d’an larabawa saboda sha’awa, “what is your problem Momyn Nur? ” kaine matsala ta nafada maka tunfarko muyi planing kaki now look yarona six months ace inada cikin wata biyu, gaskiya kasan y’an da zakayi dashi. Hade fuskar shi yayi for the first time a rayuwar Auren su dayaji ta mugun batamai rai, ya mike zunbur ya fita sai gidan Momy yana huci.
Zaune take sanye da eye glass tana karatun jarida ya shigo a fusace ya zauna tareda dafe goshi. “Kai lafiya ka shigomin gida bako sallama?
“Please yarinyar nan ce fa momy zambata mata rai? “Wace yarinyar ka keda ko ka Haifa a gidan nan inji? ” Momy Naziya, wai… She is crying because she is two months pregnant, tundazu take kuka ina lallashin ta, can you imagine she have the gut tace incire cikina momy my baby. Yafada yana nuna kanshi, Ajiye jaridar tayi tareda zuba mai ido nadan lokaci kafin tace “now tell me how you react to her, kayi mata hauka ko? Jinan kar inji kar ingani wai ka hau Y’ar nan da fada, yoh badole tayi kukaba yaro d’an wata shida ace ciki wata biyu. “Ni bance komai ba kawai nafito ne. “Better.
Mikewa tayi taje gidan tareda barin shi anan, tana ganin Momy ta goge hawayen ta, matsowa tayi tareda zama kusa da ita Nur nata washe mata baki tareda mika hannu ta daukeshi tana mai wasa kafin ta koma kan Uwar.
“Naziya. “Na am momy. “Ina ilimin ki yaje? Ina hankalin ki ya shiga, bakin ciki kikeyi saboda Allah ya miki baiwa,? Kinsan cewa yaran nan biyu dana Haifa ba a son raina bane, naso in tara yara Allah yagani sai ya kasance tundaga Ahmed da Khaleel ban kuma samun haihuwa ba, kinsan me, ina matukar farin ciki kuma ina son duk Abinda zaku taramin koda dubu ne inda rai da lafiya zanrike muku su, kika sani ko biyun sune rabonki? Karki kuma fadar a cire miki ciki koda daga Arba’in kika samu wani kinji ni.? ” toh Momy kiyi hakuri. “No mijin ki zakibawa hakuri bani ba. Ta mike da Nur ta fita daga gidan dai dai yana shigowa, “ka Kara lallabata yarinya ce Ibrahim, ta wuce.
Yana shigowa ta tashi tareda nufar shi ta rungume shi gam, “Am sorry Abban Nur, bazan karaba kaji forgive me. “No problem karki damu am ready to take care of you and my child, cikin minti kadan sun gyaro Al amarin su tareda taimakon Uwa tagari a yanzu.

Alhamdulillah, cikin shekara biyar Naziya ta Ajiye yara Hudu bayan Nur, tayi twins maza sai Karamar su yanzu da take goyo balkisu wato Ummul khair, gaba daya batasan wahalar raino ba kakarsu ta dauke musu komai, haka take bin mijin ta duk inda zaije hankali kwance sun yawata kasashe a wannan shekarun, idanun ta sun bude sosai ta Kara wayewa tareda Aji, taso taci gaba da karatu Amma ganin khaleel bai so kuma ya bude mata hanyoyin samun kudi da yawa business center nata nakanta Wanda tafi karfin hidima tundaga dubu daya zuwa dari biyar har million, y’an uwan ta ma sun shaida ita din mai sa’ace.
Kudi na musamman tasa khaleel ya ware tareda gina wata babbar makaranta mai suna Ahmed foundation, wadda take taimakawa marayu da basuda karfi suke samun kulawa sosai batareda ko sisin suba,
Momy ta Ajiye aikin ta tuni bata zuwa sai kula da y’an jikokin ta, haka zata zuba Abinta a mota suje ziyara gidajen y’an uwa, har gidan malam sai suje su wuni susha hirar su sai sun ishi inna da barna tace “Hajiya balkisu ki kwashi mazajenki sun isheni da barna suna fama da jajayen kunnuwa. Haka zasuyi ta raha a tsakanin su, haka take zuwa gidan kanin mijin ta ma, ta canja sosai kamar ba itaba,
A cikin wannan satin su Naziya suka shirya fita bangkok kamar duk kowane karshen shekara yanzu saboda kasuwancin shi. A dai dai lokacin Ummul khair nada wata takwas kuma tagano tana daukeda wani cikin don haka ba wani dogon bayani ta cireta tareda Ajiye wa takwarar ta tabi mijinta domin su hole, tuni ta gano cewa Matar so ke gwarne don haka ta daina damun kanta domin duk cikin dazatayi khaleel na farin ciki, toh meye damuwar ta Sai muce Allah ya karo Arziki da zaman lafiya a tsakanin wainnan ma Aurata…… Pen’s 🖊
Alhamdulillah nagode wa ubangiji da ya nufeni da ganin karshen wannan littafin
Dubun godiya gareku masoya aduk inda kuke, my Real fan’s wato AUREN GADO paid grp one and two, domin kune real fan’s dina domin kun nunamin kauna da soyayya ta hanyar rububin siyan wannan labarin, fatan Alkhairi agareku bazan taba mantawa da Alkharin ku da hakurin ku gareni ba,
Ina rokon Afuwa saboda yanayi na jinkiri da aka samu akan wannan labari, ba son raina bane kana naka Allah na nashi, this is the though time for me saboda situation dina, am sorry duk Wanda na batawa rai a wannan tafiyar, saboda ajizanci na d’an Adam, ku yafemin don girman Allah.
Darasin da na ke son y’an uwa su dauka a wanna lbr shine, kaso mutum don Allah,mucire hassada son zuciya handama mugodewa ubangiji da duk Abinda yabamu a Rayuwa, sannan kuma Muna fatan muyi kyakkyawan karshe irin na momy Allah ka nufemu da gyara kura kuranmu kafin mutuwa. Ayi Amfani da Abinda zai amfane mu a wannan lbr sannan mu watsar da duk Wanda baida Amfani kuskuren da ke ciki Allah ya gafarta min Alkharin dake ciki Allah yasa Al umma su anfana dashi,
Dubun godiya gareku masoya da nake bawa a pc kunada yawa, lallai soyayyar ku babbace a wannan labr da kuma gareni Nafisa na yinku over Allah ya karo Arziki ya kareku daga dukkan sharri.

*TAMMAT BIHAMDILLAH*

Back to top button