Adandi 43
*43*
Hakanan cikin damuwa na daure saboda banason mutuwa na bawa Gidado damar kusantar Maryam amma fah saidai yaje yayi abinda zaiyi da ita ya dawo mu kwana tare kada ku manta na fada muku dukkansu a cikin halwar sihiri suke mukaci gaba da zama a haka wata biyu tsakani Maryam ta fara laulayi na hana akaita asibiti na rinqa kula da ita har cikinta ya isa haihuwa nice na karbi haihuwar nida Barirah qawata sai Gidado da ranar yakasa fita ko Ina ta haifo yarta mace me kama da Gidado amma yanayin fatarta irinna Maryam ne tana haihuwa na shaqa mata wata hodar tsafi ta shaqa mukuma muka fice muka gyara jaririya ina zaune a parlourn na hakimce sai kwainane nakeyi waini me jego naga Maryam ta fito tazo ta tsaya akaina sai kuma naga ta fashe da dariya ta kwasa da gudu ta fice daga gdan tun daga ranar banqara ganinta ba.
Shikuwa Gidado yasan banice na haifi jaririyar ba amma koda wasa bai taba neman Maryam ba haka ya kira yan uwa ya fada musu na haihu akayita murna ana zuwa tayani barka da arziqi har Abdu Saida akazo dashi Abuja nayita zuba rashin mutunci waini na haihu a idon mutane nasawa jaririyar nonona wanda babu ruwa a ciki a bayan idonsu kuma na bata madara ranar suna Gidado ya mayarwa da yarsa sunan mahaifiyarsa Aishatu nan fah na rinqa bala’i nace me zaisa yasawa yata sunan uwarsa wlh saina canza mata suna baizai iyaja Dani ba haka ya qyaleni dashi da yan’uwansa suna kiranta da Aysha ni kuma da mutane na muna kiranta da Samhanatu haka rainon Samha yaci gaba da tafiya inasonta saboda burukana a kanta nayi burin maida Samha jarina a gurin samari saboda kyawun halittar ta amma babanta yaqi bani dama abu daya da nayi nasara baya mata fada duk abinda takeso shi takeyi da hanuna ban taba dinkawa Samha atamfa less ko material ba saidai qananan kaya sannan bantaba cemata tasa hijjab ba saidai mayafi mayafin ma qarami Gidado yana gani bashi da ikon mgn saboda kada raina dana tilon yarsa ya baci hakanan ya qyaleni ban damu da duk wani abu daya shafi addini ba saboda ko sallah sai naga idon Gidado nakeyi hakan ce tasa ya dagewa Samha kaida fata akan tsayar da sallah da kuma bata ilimin addini da lallami da kulawa yake koyar da ita dakansa kasancewar Samha tana cikin jerin yaran da ake Kira Tellant tanada qwaqwalwa sosai amma wasa ne akanta saboda rashin kwaba hakanne yasa lkcn data isa zuwa makaranta Gidado yasata a wata Tahfiz ta yayan manya da ake kira Khulafa’urrashidun duk da wasanta amma malamanta suna alfahari da ita saboda tasha ciyo musu gasar musabaqar karatun qur’ani da wasu daga cikin littatafan addini wanda su kansu sunsan ba iyakar koyarwarsu bace harda ta mahaifinta.
Shekaru sunata tafiya har lkcn da Samha ta gama secondary kwarai naso ta fita waje tayi karatun ta amma taqi tace qawayenta duk Bayero University zasuyi saboda haka itama ita zatayi dole hakanan muka qyaleta ta tafi can din da farko bata wani saki jiki ba kuma na fahimci taqi sabawa da maza wannan dalilin ne yasa nasa akayi mata asiri ta fara bare bare itace shaye² yawon zuwa club sosai abin yake damun Gidado amma bashi da yanda zaiyi saboda har lkcn a cikin giyar asiri yake tafiyar da rayuwarsa saidai idan tazo gda hutu yaga yanda ta zamz yar maye yasata a gaba yayita kuka nikuwa nayita dariya a daki nasara daya da yayi wata rana ya sameta a daki yana kuka yace “Aishatu nasani wannan abinda kikeyi sakayya ce ta abubuwan da nayiwa iyayena akan Mamynki a baya amma duk da haka bazan fasa roqon Allah ba kuma bazan qi neman alfarma a gurinki ba Aishatu duk abinda zakiyi a duniya kada kiyi Zina kuma kada kiyi lesbian wadannan abubuwan guda biyu sune bana fatan ina raye yarda na haifa a cikina tayisu don Allah kiyimin alqawarin haka”
Itama tana kuka ta amince masa akan bazatayi ba haka kuwa akayi Samha taci gaba da kare kanta duk da tururuwar samarin da suke nemanta amma taqi basu hadin kai ciki harda yaron Ministan lfy wato Na’im kudi sosai Na’im yake kashemin saboda ita Samha tace bashi da abinda zai bata ubansa Minister of health ubanta Minister of Finance har gida Na’im yazo ya sameni yace shi da aure yakeson Samha saboda haka nasan yanda zanyi na rarrasheta ta aureshi Idan kuma taqi to ta amince ya rinqa hutawa da ita bayan ya fadamin ya cakemin kudi har two million aikuwa na bazama na tafi Ghana Ina zuwa na fadawa boka Jegus ya buga qasa yace babu aure tsakaninsu mijinta yananan kuma a cikin dangin Ubanta zai bullo amma abu daya da zasuyi shine zasu sanya Mata sha’awa ta saki jiki dashi su lalace ta yanda ko tayi auren mijin bazai ganta da daraja ba……
*UMMUH HAIRAN CE…✍*
[2/27, 9:29 AM] UMMUH HAIRAN CE…✍: *AD*