Adandi Hausa NovelHausa Novels

Adandi 36

Sponsored Links

*36*

 

Qwarara jinin yaci gaba dayi hankalin Samha yana qara gushewa tashin hankalin Mainah Abdu yana qara nunkuwa idanunsa suna qara qanqancewa Manson ne da yake cikin mota yaga tsugunnan yayi yawa kasancewar har lkcn akwai duhun dare lkcn 5:43am baya iya hango asalin abinda yake faruwa fita yayi daga motar ya nufesu da sauri kawai sai ya cambala qafarsa cikin jinin da yake zuba da sauri yakai kallonsa qasa ganin jinine yake malala ta jikin matar aminin nasa shikuma ya saki baki yana kallonta harta fara jijjiga yasashi baisan sanda ya sunkuce ya juya a sukwane ba ya nufi mota cikin tashin hankali sai lkcn Mainah Abdu ya dawo hayyacinsa shima ya miqe yana jiri zuciyarsa na bugawa da qarfi daqyar ya iya qarasa motar saboda 50 50 yake gani shiga yayi Manson yaja a guje suka fita daga gdan Amir’s hospital suka nufa yanda suka shiganne yasa hankalin kowa ya dawo kan motar wadda number motar kawai take nuna ta waye Mainah Abdu 4 haka number take da sauri duk wasu manyan ma’aikatan dake asibitin sukayo cahh a motar sunayin parking aka bude tare da dorata a wani gado saboda jijjigar da takeyi idanunta duk sun juye shiga akayi da ita emergency room aka fara checking dinta.

Related Articles

 

Daya daga cikin likitocin ne ya fito ya dubi Abdu da yake durqushe dafe da kansa duniyar gaba daya juya masa takeyi ya dafashi yace “matarka da abinda ke cikinta suna buqatar taimakoka cikin wannan lkcn bai kamata ka bata lkcnka cikin tunanin abinda bazai fissheka ba jinin da take zubarwa yayi yawa daqyar dai an samu ya ragu dole saidai ayi mata teather a cire abinda ke cikinta muna buqatar jini leda hudu” dagowa yayi ya busar da wata iska me zafi Manson yariga yasan halinsa idan ya shiga tashin hankali komai ma qwace masa yake yanda yake huci kadai ya isa ya nuna mawa wanda yasan ahlin gdan sarautar bashi kadai bane cewa Manson yayi “muje ayi duk abinda daya dace” binsa sukayi suka shiga Lab din saida ya fada gwada na Samha yaga group din jininta sannan ya gwada na Mainah Abdu irin jinin nanne dazai iya bawa kowa hakan yasa aka diba har leda biyu amma kafin nan saida aka nemi wani a freezer irin na Samha aka jorner mata shikuwa Manson fadu zuwa tayi daidai da qasa dan jinin nasu irin daya ne da Samha leda daya aka diba a jikinsa.

 

Wani daki aka rakasu wai su huta shikam gogan qeqashe qasa yayi yace shi matarsa kawai yakeson gani babu yanda Dr din zaiyi dashi dole ya qyaleshi suka shiga tare tana kwance kamar gawa sai cikinta kawai da yake motsi tayi wani fyau da ita ta dashe ga inda duk ta cije lebenta na har harshenta ta datse har yanzu ma haqoranta na cikin harshenta bakinta sai jini yakeyi shafa cikinta yayi idanunsa nayi masa gizon abubuwa da yawa ciki harda fuskar fulani Hadiza da Hajiya Lubabatu dama mutane da yawa da bazai iya tantance fuskokinsu ba juyawa yayi ya fita da sauri daidai lkcn da iyalen gdansu sukazo fulani Amina Mai martaba da Dr Hasina shidai kawai bin kowa yakeyi da kallo batare da yana fahimtar ko kalma daya da suke fada masa ba.

 

Yananan zaune cikin wannan yanayin mai wuyar fassarawa aka fito da files dinta likitan ya miqa masa yace “Kayi signing zaa shiga da ita teather room munyi iyakar yinmu mugano meye ke a cikinta mun kasa” baiyi mgn ba sai karbar files din da yayi yasa hanu ya miqa masa Mai martaba ne yasa hanu a matsayin mahaifinta saboda Dad yana Abuja sunyi waya yace duk abinda ya kamata ayi mata kafin ya iso Dr Hasina itace a matsayin Mamy saboda koda aka kirata ma domin sauke haqqinta na uwa aka fada mata murmushi ma tayi tace “Allah ya kyauta Amina may be idan na gama uzurirrika na zuwa jibi nazo idan kuma ta Allah ta kasance to dama lkc muke jira” tana fadin haka ta kashe wayarta tana dariya.
Wannan abu ya gigita duniyar fulani Amina tare dasa mata kokwanto akan cikar hankalin Hajiya Lubabatu haka aka fito da Samha aka shiga da ita dakin teather miqewa Mainah Abdu yayi zaibisu Mai martaba da yayansa Mainah Abubakar suka riqeshi ya kuwa girgijesu zai wucce daqyar Mainah Farooq daya shigo yanzu ya riqeshi ya hanashi gaba ya hanashi baya dama idan yana cikin wannan yanayin shi kadai ne yake iya control dinsa yanke jiki yayi zai fadi saboda juwar data debeshi amma sai sukayi maza suka riqeshi suka shigar dashi dakin da Mansoor yake kwance saboda shi tunda aka dauki jininsa yake jiri hakanne yasashi shiga dakin ya kwanta.

 

Kwantar dashi sukayi Mai martaba ya zauna a gefensa ya kalli Manson yace “Mansoor wai meye sanadin faruwar hakanne?” Miqewa yayi t zauna yace “lfy qlau na daukosu daga airport muna hirarmu har tana tsokanata tunda naqi aure idan ta haihu zata bani yarta ta fari na aura kawai na kaisu sun fita zasu shiga Mainah yanata zuba mata sannu kawai sai ganinsu nayi a tsugunne ganin tsugunon yayi yawa ne yasani fita ina zuwa naganta cikin wannan yanayin jini yana zuba a jikinta kamar famfo” numfashi Mai martaba yaja yace “Allah shine ya barwa kansa sani” “nasan komai kuma zan fallasa komai ka kira Dad ka fada masa kada ya taho a mota ya biyo jirgi kuma ka fada masa ya taho shi kadai kada ya taho da excourt dinsa ko daya” kallonsa Mai martaba yayi yace “meyasa gagarabadau?” Idonsa a lumshe yake kamar wanda yake bacci yace “kawai nidai nace ka fada masa haka banason tambaya idan lkc yayi zaka sani” saqo Mai martaba ya turawa dan’uwannasa haka kuwa akayi har ya fito zai hau mota ya fasa ya sallami kowa ya dauki mota shikadai ya tafi filin jirgi saida yaje sannan ya kirasu yace azo a dauki motarsa.

Goma a palace hospital tayi masa shima dai tambayar da yakeyi kenan “ya akayi hakan ta faru amsar da Abdallah yabawa Mai martaba shima ita ya bashi dole haka suka qyaleshi.
2:30pm aka gama Mata CX din cikin nasara suka fito Mata da zaratan yaranta maza guda uku dukkansu rayayyu duk da kasancewarsu guda ukun amma sunyi mamakin girmansu sosai hakanan aka sanyasu a Incurbetoor wayyohh Allah kuzo kuga murna gurin iyalan ne shikuwa Abdul da aka fada masa dagashi har Mai martaba da Dad sujjada sukayiwa lillahi rabbulsamawatih wal ardih suna qara miqa gdyrsu ga Allah yana miqewa kuwa kafin wani ya ankara ya fice daga dakin duk yanda likitocin sukaso hanashi yaqi hanuwa dole saida suka kaishi dakin da take kwance har yanzu kamar gawa bata ko motsi ya zuba mata ido yana hawaye yana roqon Allah ya bata lfy ta shayar masa da yayansa juyawa ya kumayi aka kaishi inda yaran suke ya qura musu ido ya kalli wannan ya kalli wannan yana murmushi yanda suke motsi abin gwanin ban sha’awa yana rayawa a ransa wadannan duk nasane sune fulani Hadiza da Hajiya Lubabatu suke yunqurin salwantar masa dasu dama uwarsu tabbas qiris ya rage rabon yarannan yayi kisa kuwa.

 

 

Daqyar ya fita daga dakin yana waiwayen yayansa da daidai da daidai saida kowa yaje yagansu Dr Hasina kuwa batasan sanda ta rungume Mainah Abdu ba tana hawaye tana cewa “ina roqon Allah ya azurtani da haihuwa nima kamar yanda ya azurtaku dasu don Allah Mainah kabani su ni zan dawo ma gdanku nake kula dasu” murmushi yayi yace “idan muka samu wasu zan baki amma wadannan bazan iya nisa dasu ba babban rabone daga Allah” Dad ne ya kira Mamy ya fada mata abinda yake faruwa saboda tsabar tashin hankali batasan sanda ta qunduma uwar ashar ba tace “yan uku Gidado Aishan ce ta haifi yan uku ya akayi ta haifesu?”…………

 

 

 

 

*UMMUH HAIRAN CE…✍*
[2/18, 8:07 PM] UMMUH HAIRAN CE…✍: *_AD_*

 

*_Dont read this book if you are not married. Mature content contained in it. Reader discretion is advised. You read at your own risk._*

 

 

Back to top button