Garin Dadi 43
{43}
*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma’abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*
~MAI DA TSOHUWA YARINYA
~FEMALE CARE
~REODEO
~VIGOR MAX
~ LONGZIT
~B CLEAR
*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA…..*
~~~Fitarshi tayi daidai da shigowar kira wayarta, cikin rashin ƙwarin jiki ta miƙa hannu ta ɗauka saboda ganin aminyar tata ce madam comfort,
“Maman Mary komai lafiya?” ta fada daga cikin wayar dan son bugar cikinta da mararin jin yadda ake ciki bayan ƴarta ta gama tsegunta mata komai,
“Ina fa lafiya maman Feli… Ai babu maganar lafiya anan, wallahi na rasa ya zanyi da wannan yarinyar dake neman rabani da yarona, komai da muka yi last time yanzu duk ya lalace, duk wani shirinmu am quite sure ya lalace akan yaran nan…..”
“to yanzu menene mafita? Ai ba wai zamu hakura bane zamu sake samo solution ne, we most definitely need to find a solution to this problem…..”
“hakane to amma ke ya kike ganin ya dace ayi?”
Dama abinda take son ji kenan shiyasa sai da ta kiftawa Felicia dake zaune kusa da ita ido sannan ta bawa mommy amsa da,
“ki bani time zan yi tunani inyaso sai in zo….”
“babu matsala…. Nagode sosai madam comfort, Thank you”
Katse wayar suka yi har lokacin dai mommy bata gama jin dacin da take ji game dani ba na kiyayyar da take yi min.
Shi kam bayan yabar wurin mommy sallama ya koma suka yi da daddy daga nan ya bibbiya ta wurin friends da abokan arziki wanda har yanzu da ya musulunta bai daina mutunci da zumunci da su ba shiyasa bai baro Kaduna ba sai la’asar lokacin nikam na zuba ido har na gaji gashi na kasa cin abinci shi nake ta jira amma ganin bai dawo ba yasa na dafa noodles naci, jin na ɗanji karfin jikina yasa na gyara ko ina nayi wanke wanke na shasshare ko ina na goge shiyasa na gaji lis,
Zuwa bayan magrib ya karaso lokacin nayi jiran har na gaji, zumburo baki nayi lokacin da naje taroshi, murmushi yayi ya dagani sannan ya sakani ajikinsa tare da sunkuyowa yayi hugging dina shima yana dariya,
“baby me kuma ya faru? Kin matsa min sai naje Kaduna, na yarda naje na dawo kuma na samu kina fushi, me ya faru?”
“ni ba fushi nake yi ba….. Ya ka baro su mommy? Ta hakura?”
Har lokacin muna rungume da juna kamar wadanda suka shekara basa tare,
“mommy fa ba zata taba hakura ba my love…. Ki cire wannan tunanin da damuwar daga ranki dan na san halin mommy, if she says yes is yes and her no is no, soo ki daina wahalar da kanki wurin ganin sai mommy ta so ki ko ta kaunaceki saboda is hardly hakan ta kasance….. ”
Hawaye ne suka fara zuba daga cikin idanuwana dandanan saboda jin kalamansa, wannan wacce irin kaddara ce? Menene laifina a rayuwa dan kawai na kaunaci ɗanta saboda Allah kuma da zuciya daya? Menene laifina dan na zauna tare da ɗanta a matsayin matarsa? Jin alamun kuka nake yi yasa shi saurin ɗago fuskata yana lashe hawayen dake fita cikin kulawa, daukata yayi zuwa saman kujera ya fara lallashi na,
“baby menene abin kuka? Ni ai ina son ki ina kaunarki, i love you with all my heart….. And zan cigaba da sonki har zuwa lokacin da zan daina numfashi”
Na san duk yadda zanyi masa bayani bazai taba fahimtata ba amma ta yaya zan iya samun nutsuwa da kwanciyar hankali alhali mahaifiyarsa da danginsa basa sona kuma basa kaunata kai bama su da burin da ya wuce na suga sun rabani dashi, rarrashina yacigaba da yi har na samu nayi shiru na daina kukan buy akwai hawaye saman kuncina basu daina sauka ba,
“Ga abinci muje kaci…..”
“no baby, you are the real meal that i want now……”
Harararshi nayi yana goge min hawayen,
“am not in the mood….” na fada ina turo baki,
“Haba baby yau fa 3 days kenan….”
“Bana jin dadi ai….”
“to shikenan baby….”
Gaba daya jikina yagama yin sanyi da lamarin mommy da danginsa shiyasa komai cikin sanyin jiki nake yin sa ni ban san me zanyi musu su soni ba haka ban san me zanyi in wanke kaina daga zargin laifin da suke yi min ba wanda ban san na aikata ba gashi bana son tattauna maganar da kowa a family dinmu dan gudun abinda zai je yazo, dama idan ban manta ba sai da anty ta fada min tace min insa araina bazasu taba sona ba kuma gashi dagasken hakane gashi yanzu nagani da idanuwana,
Shirin bacci ma duk a sanyaye na yi na kammala nazo na sameshi yana ta fama da aiki a system dinshi yau daya da bai je office ba aiki har ya tarar masa yayi masa yawa, ajiye laptop ɗin yayi a gefe yayi min masauki a jikinsa yana taba wuyana dan jin halin da jikina yake ciki shin akwai zazzabi ko babu,
“baby ya jikin naki?”
“da sauki sweet” na fada ina hadiye bakin cikin da ni kadai na sani dan har na fara tambayar kaina wai meyasa ma na aure shi ne? Yanzu da ace bahaushe na aura asali dan uwana wanda kowa nasa gaba da baya musulmai ne ai da ban fuskanci kalubale irin wannan ba amma yanzu gashi tun aure bai je ko ina ba na fara fuskantar damuwa danma bada gareshi bane daga danginsa ne,koda yake haka fa gaba daya rayuwar take kowa da kalar irin tashi kaddarar, kuma ko babu komai akwai dunbin lada ga wanda yayi sanadiyyar shiriyar wani musamman ma ya karbi musulunci,
Nayi nisa cikin tunani na naji ya dage sai kokarin birkita min tunani yake da soyayyarsa mai mutukar sanyi kai samz akwai nacin jaraba yau dai tunda ya rantse sai ya karbi hakkinsa sai ya karɓa din shiyasa na hakura na daddaure na biye shi har ya samu abinda yake so. Da kanshi yaje ya hada mana ruwan wanka sannan yazo ya daukeni muka je muka tsaftace jikinmu tare sannan muka dawo yaci gaba da aikinsa nikuma nayi baccina na barshi, nidai duk da abin yana damuna amma ban yarda na sakashi araina har ya hanani samun farin ciki da mijina ba haka na hakura na cire komai daga raina muka cigaba da zaman lafiyar mu, kullum sai munyi waya da yan gidanmu da ƙawalli haka nayita kirkirarma kaina abubuwan debe kewa a duk sa’ilin da baya nan dan karma wata damuwa ta shigeni har ta hanani sukuni.
Tun cikina yana wata biyar muka fara siyan kayan baby duk wani abu da nagani online wanda yayi min haka zanyi order na biya dama bani da matsalar kudi saboda yana ajiye min kudi a account dina every month shiyasa duka abubuwan ma ba sai na tambayeshi kudin siyansu ba, ko yau ma sai da naga wata baby walker a wani page nan ruwan ido ya hanani zabar wadda tayi min shiyasa lokacin da ya dawo bayan ya huta nake nuna masa dan ya tayani zaba,
“to baby idan kuma twins ne fa?”
“sai mu kara daya daga baya”
Dariya yayi yace “kawai muyi order din biyun yanzu”
Ku san komai tare dashi muke siya dan yanzu cikin yana da watanni bakwai,ita kuma ƙawalli haihuwa ko yau ko gobe dan cikinta ya girma sosai, duk da ina cewa bazan je Kano ba har sai na haihu amma yanzu ji nayi bazan iya ba saboda gaba daya hankalina ya koma kan gida ina so inje inga halin da kowa ke ciki,
Yau kam cike nake da murna saboda zuwan bakin da ban san da zuwan su ba saboda zuwan bazata suka yi min wato yaya Abdurrahman da matarshi anty Rahinatu harda yaransu guda biyu Amir da Amira, kasancewar weekend ne shima yau yana gida, muna ta sharar bacci wayata ta tada ni, ba karamin dadi naji ba saboda zuwan su babu shiri na tashe shi dan bani da cefane nan ya fita dan zuwa kasuwa,
“ikon Allah ashe masu haihuwar suna da yawa, weedat kice da bamu zo ba sai dai muji haihuwa muyi ta mamaki……” anty Rahinatu ta fada cikin tsokana dariya kawai nayi na kasa bata amsa saboda kunya, duk da na saka hijabi kan doguwar rigar jikina ta atamfa sai da cikina ya fito saboda ya girma babu laifi,
” uwar mita koda yaushe yaya kun ki zuwa kunki zuwa to yau dai gashi mun zo shikenan?” yaya Abdurrahman yace dani lokacin da na kawo masa kayan motsa baki gabanshi,
“wallahi naji dadi sosai yaya, Allah ya saka da alkhairi yabar zumunci”
“weedat an girma, Masha Allah ubangiji Allah ya kara zaman lafiya yabar soyayya”
“amin anty, yagida ya aiki? Ai da baki zo ba anty da fushi zanyi muku Kota chat in daina kulaku”
“gashi mun wanke kanmu, ayi mana afuwa”
Tare da anty Rahina muka shiga kitchen muka yi girki bayan samz ya dawo daga kasuwa ya iyo siyayya kaca kaca,shinkafa muka dafa muka yi vegetables soup hadaddiya wadda ta wadatu da naman kaza da ganyayyaki sannan muka hada fruits salad, sosai shima naga samz ya sake da yaya Abdurrahman suna ta shan hirarsu Muma muna tamu nida Anty Rahina, ni duk atunanina kwana za suyi amma sai yaya yace tafiya zasu yi, nidai ban so haka ba amma babu yadda na iya, lemuka da chocolate yaya ya kakkawo min ni abinma har dariya ya bani sai kace wata karamar yarinya, sai ko gurasa kamar yasan ina ta sha’awarta kwana biyun nan, nidai bani da abinda zan basu sai ko kudi da samz ya bama su Amira wannan dinma dakyar iyayen suka barsu suka karɓa, sallama muka yi dasu suka tafi anty tana cemin sai mun hadu a Kano idan ƙawalli ta haihu, ƙwalla naji ta taru a idona bayan sun tafi nan naji kamar inbisu nima kai gaskiya dole inje Kano kwana kusa Insha Allah,
Riƙo hannuna yayi muka dawo ciki yana tsokanata, “haba baby dama har yanzu baki daina kukan ganin ƴan gida ba? Na zaci kin waye tunda kika gane daɗin zama dani….” na san ba haka yake son faɗa ba kawai kaucewa yayi ganin na tsareshi da idanuwana,
“ba gaskiya na fada bane? Dan Allah yanzu zaki iya yin wata ɗaya batare dani ba? Kema kin san nasan ba zaki iyaba…” yana gama faɗa yaja baya dan yasan yanzu bana iya binsa da gudu muyi tsere shiyasa sau tari duk abubuwan da yaso faɗa fadinsu kawai yake ya gudu ina ji ina gani babu yadda na iya sai dai kawai nasa masa ido,
Murmushi nayi na sunkuyar da kaina dan tabbas abinda ya fada gaskiya ne ayanzu dai bana jin in ba wani ƙadari na Allah ba bana jin zan iya koda sati biyu batare dashi ba dan ya gama mamaye raina,
“in zo in duba baby? Yau throughout ban duba shi ba…”
Rabuwa nayi dashi na nemi wuri na zauna kan kujera ina bubbude kayan da su yaya Abdurrahman suka kawo min, harda dakakken ƙuli ƙuli, kusa dani naji ya dawo yana shafa cikina,
“na san kin gaji ko?” kai na ɗaga masa ina sake narke masa, ƙafafuwa na ya fara matsa min a hankali kamar yadda ya saba yimin koda yaushe.
***
“kamar yadda na alƙawarta miki cewa zan zo miki da mafita to gashi na cika alƙawari, ungo wannan, karki yi wasa dashi maman Mary ki tabbatar duk yadda zakiyi wannan yarinyar taci a abinci, idan har taci ina mai tabbatar miki da shikenan burinki zai cika dan ɗanki bazai cigaba da zama da ita ba duk da yana sonta dan dole zai rabu da ita…. ” madam comfort ta faɗa tana mikawa mommy wani ɗan ƙullin garin magani dake nannade cikin bakar leda wanda ta ciroshi daga handbag dinta, karba mommy tayi tana yi mata godiya sai dai kuma tunani take shin ta ina zata ganni bare har ta saka min maganin in ci? Ta san dai koshi idan ta bashi bazai yarda da hakan ba bare har ya bani in ci, kamar madam comfort ta shiga zuciyarta taga abinda take tunani taji tace,
“yanzu aiki ya rage ga naki domin ni na gama nawa…. Kiyi duk iya yinki ki aiwatar da wannan aikin batare da jinkiri ba, idan har kika yi jinkiri kuwa to fa kina ji kina gani komai zai fi karfinki….” daga haka ta saba jakarta ta kara gaba saboda dama church zata je ta biyo ta nan……….
*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*
*_Ummi Shatu_*