Garin Dadi Hausa NovelHausa Novels

Garin Dadi 35

Sponsored Links

©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(Home of experts & perfect Writers)_

 

*GARIN DAƊI……..!*

*_NA_*

*_UMMI A’ISHA_*

*Wattpad:ummishatu*

 

PAID BOOK #500

{35}

*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma’abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA…..*

~~~Tun bayan lokacin da yaci maganin da mommy ta bashi yaji garin Kano gaba ɗaya ya fitar masa arai irin fitar da ko sunan garin baya ƙaunar yaji an ambata bare har ya taka ƙafafuwanshi yaje,

Tsakanina dashi kuwa babu wata matsala sai ko ta rashin zuwansa dan tun last week yace min zai zo weekend bai zo ba gashi wannan weekend ɗinma shiru abin da yake damuna kenan a halin yanzu saboda sati biyu kenan bai zo ba duk rashin zuwan nasa sai ya fake da aiki,

Kasancewar weekend ne kuma bai zo ba tare muke da Bishra, ita tana can falo tana yi min gugar kayana yayinda nikuma nake cikin ɗakina, shigowar kiranshi cikin wayata shine ya katse ni daga shafa man da nake yi,

“Hello my sugar baby…..”

Sai da na turo masa baki kamar irin yana ganina ɗinnan sannan na narkar da murya nace,

“Bayan munyi faɗa da kai….”

“Am soo sorry baby…. Ki shirya anjima kina da baƙo na aiko shi zai kawo miki wani gift na auren mu da na siya miki”

“Ni wallahi bana son ganin kowa kai nake son gani” na faɗa ina diddira ƙafafu a ƙasa idanuwana har sun taru da ƙwalla,

“ok to karki yi kuka please….. Kiyi haƙuri insha Allah next week zan zo”

“koda yaushe haka kake cewa, last week ma haka kace”

“am very sorry, ba zan sake ba”

Rarrashi na yayita yi har sai da na haƙura na ware na bar wannan maganar sannan muka yi sallama na cigaba da shiryawa, bayan na kammala na koma falo wurin Bishra wadda har ta kammala gugar da take yi ta ɗora mana abincin rana,

Zuwa ƙarfe uku na yamma baƙon da samz ya aiko ya ƙaraso kuma ba kowa bane illa abokinshi Ahmad, hijabi nasa na fita na yi masa iso har cikin falonmu sannan na gabatar masa da abinci da sauran kayan motsa baki muna cikin gaisawa oga ya iyo waya, tashi nayi na wuce ɗayan bedroom ɗina domin Bishra tana ɗayan waya da samz kuwa sai an keɓe dan yanzun nan zaka ji yana let me see your chest, aikin kenan kullum,

“Ahmad ya ƙaraso?” ya buƙata,

“ehh bai jima da zuwa ba”

“ok kin dai saka hijab ko?”

“No” na faɗa cikin tsokana,

“haba baby….. Dan Allah ki rufa min asiri ki rufe jikinki mana”

“Uhmm uhmmm”

“To shikenan nima zan ƙi zuwa ki ganni tun da haka ne”

“Nifa da wasa nake…. Na sa hijab”

“That’s my sugar girl”

Murmushi nayi muka yi sallama sannan na koma wurin Ahmad duk da dai ba mu wani sake ba, abincin ma sama sama ya ci ya mike wai bari ya shigo da sakon sai ya tafi, duk tunani na wani kaya zai shigo dashi amma sai naga ya buɗe gate ya shigo da wata tanfatsetsiyar arniyar mota Benz mai numfashi Ash colour sabuwa dal dan sai ƙyalli take tana ɗaukar ido, key ɗin ya bani sannan ya tafi, ni dai duk kaina a kulle a raina ina cewa oga ya sai mota muma munyi ƙafa dama na jima ina mamakin daliliin da yasa har yau baida mota saboda nidai na san ba wai kuɗin siyan ne baida shi ba sai dai ko ra’ayi,

Tun kafin in koma ciki na kira shi,

“Ashe mota ka siya….”

“No, Na siya miki dai…. Ai nace miki taki ce ko kin manta ne?”

“Tawa kuma?”

“Yeah…. Taki ce baby”

“Oh my God….. Tawa fa kace love? Wayyo Allah dadi, am deeply grateful….”

Bishra na soma ƙwalawa kira ina tsalle cikin murna da farin ciki duk yana jina, tana fitowa na kama hannunta muka fita ina cewa,

“Muje kiga abin da love ya siya min….”

“Kai masha Allah Yaya Widat…. Yanzu wannan taki ce? Kai….. Ai yanzu taki ce on top a gidan mu dan tafi ta Anty ma kyau…. Allah ya sanya alkhairi ya tsare yasa rabonki ce”

Har muka gama kallon motar muka koma ciki samz yana jin mu, bayan na zauna na ɗauki wayar da zummar kiran mama naga yana kan layi,

“baby…. Kamar tsalle naji kina yi ko?, are you not pregnant?”

Turo baki nayi kafin in bashi amsa,

“ni am not pregnant…..”

“Ba kince ba kiyi period ba this month?”

“Ya canja lokaci ne, am off now”

“ok, but am not happy”

“nikuma am very happy”

“Na san dama ke murna zaki yi, anyway when i comes to you, u will realize that”

“Am waiting for you” na faɗa with full confidence, dariya naji yayi sannan muka yi sallama nan fa nida Bishra muka fara yaɗawa ƴan uwa samz ya sai min mota, murnar wannan motar ne ya ɗauke min hankali daga ɓacin ran rashin zuwansa wannan satin domin bai zo ba kuma koda na tambayi dalili sai cemin yayi har weekend suna da aiki nan ya ɗan rarrasheni da kalamai masu daɗi sannan yace sun yi magana da yaya Abdul hakim akan zai rinƙa koya min mota amma ya sake tunani gara inje driving school inyaso sai in koya a can yanzu dai yasa a bincika masa,

“Nagode, amma kuɗin da ka turo min su kuma na menene?”

“Idan kina da buƙata sai kiyi amfani dashi baby….”

“Ni banda buƙatar kuɗi, kai nake buƙata” na faɗa kaina tsaye dan sati uku kenan fa rabona dashi ana neman shiga na huɗu,

“Dagaske? To baby kizo Abuja”

“Nidai wallahi a’a”

“ok to shikenan ni zan zo”

A haka muka tsaya akan zai zo amma bai zo ɗinba har zuwa lokacin da ya samar min wata driving school zan fara zuwa koyo, duk yan gidan mu babu wanda bai zo yaga mota ta ba sai waɗanda ke nesa, yaya Abdul hakim ne ya siyo min sabuwar plate number ya ɗaura min, cikin satin na fara zuwa driving school ɗin wanda da hakan samz ya fake yaƙi zuwa koda nayi masa maganar zuwa wai ai yanzu ina fita ya bari ne in gama koyon motar ta yadda zan iya ɗaukoshi ma daga Airport, Sam bai fito ya faɗa min ainihin abin da yake damunsa ba dan har Kaduna yana zuwa amma tsakaninshi da Kano sai dai a baki ni ɗince Allah bai basu ikon shiga tsakanina dashi ba amma Kano dai an shiga tsakaninshi da ita. Cikin kwana biyar aka gama theory aka fara koya min mota practically kuma a ranar nima na fara tuƙawa duk da ina ɗan tsorace kaɗan amma sunce insha Allah cikin kwana uku zan iya ana jima inyi 5 days kuma hakan kuwa aka yi dan cikin kwana ukun na iya sai dai reverse dake bani wahala, yanzu da motar tawa ma nake zuwa wacce aka saka tambarin L gaba da baya.

La’asar liss na dawo gida daga makaranta kuma daga yau na gama bazan sake komawa ba dan har sun bani certificate ɗina, waya nayiwa samz ina sanar dashi cike da farin ciki, shima murnar ya taya ni sannan yace to yana nan zuwa, murna awurina abin ba acewa komai kuma tun daga ranar Laraba na soma shiryawa zuwanshi, dan har kitso naje, mai lalle ce dai ban samu ba, ranar Juma’a sassafe na tashi na gyara gidana na kimtsa ko ina sannan na ɗora girki, white rice da chicken sos nayi haɗe da coconut milk shake nasa a fridge,ƙarfe 3 da wani abu Bishra ta tafi nikuma na zauna zaman jiran zuwanshi duk da muna ta waya yana sake jaddada min wai zai zo amma har magariba shiru, bayan magriba nan ma shiru kai ataƙaice dai har zuwa lokacin sallar isha anan ne na fitar da rai da zuwanshi kawai sai na fara kuka yana ta kirana awaya ban ɗauka ba dan yanzu na fara zargin akwai wani abu a ƙasa in banda haka sati biyar kenan bai zo ba kuma kwata kwata lokacin da ya tafi sau uku wani abu ya shiga tsakaninmu bare ko in ce gajiya yayi dani, kusan kwana nayi ina kuka wayata kuwa tuni na kasheta dan na gaji da ganin kiransa, sai bayan sallar asuba sannan na samu bacci lokacin naci kukana na ƙoshi, wurin 10 na tashi na zauna nayi tagumi kawai ina tunanin rayuwa, a haka dai lami lafiya muke dashi yana tattali na yana nuna min soyayya duk abin da nake buƙata yana yi min amma yaƙi zuwa inda nake idan nayi magana sai yace aiki kuma dan tsabar rainin hankali jiya maimakon yace min ba zai samu zuwa ba sai yayi ta yaudara ta yana yimin yawo da hankali, sake fashewa da kuka nayi nan na sake ɓata lokaci ina kuka, haka na wuni daƙyar na iya cin abinci, bayan azahar sai ga Yaya Abdul hakim harda ƙawalli,

Bayan mun gaisa yaya ya kalleni da ɗaurarriyar fuskarshi domin samz ne yayi masa waya wai yazo ya bani hakuri kuma ya rarrasheni saboda tun jiya nake kuka baya jin ma ko abinci na samu naci sannan na kashe wayata,

“Me yasa kika kashe wayarki? Sannan mijin ki yana ta kiranki shine kika ƙi ɗauka ko?”

“Yaya amma me zaisa yayita raina min hankali yana cewa zai zo bayan ya san karya yake ba zuwan zai yi ba”

“Mijin naki keyi miki ƙarya? Ki ɗauko wayarki ki kunna yanzun nan, kuma idan ya kara cemin ya kira yaji a kashe ko baki ɗauka ba zaki ga yanda zamu kwashe dake, bar ganin yanzu kin yi aure, har gobe zan iya lallasa ki idan kika yimin hauka” daga haka yatashi ya fita ya bar mu tare da ƙawalli nidai tuni har na fara hawaye,

“Kiyi haƙuri ƙawalli…. Wannan hakurin da kika ji ana cewa ayi idan za ayi maka aure to dama irin wannan ne, dan Allah kar ki ɗaga hankalinki”

Tashi nayi na shiga bedroom na kunna wayata ina kunnuwa sai ga kiransa, ɗagawa nayi amma banyi magana ba,

“Am very sorry baby…..” haƙuri yayita bani amma banyi masa magana ba dan nayi bala’in jin haushin abin da yayi min, ya jima yana bani hakuri sannan na haƙura nayi masa magana muka yi sallama na koma wurin ƙawalli bayan ya roƙoni akan dan Allah kar in sake kashe wayata,

” Lallai ke kinma samu dama har kina iya faɗawa mijin ki haka, shi yayanki ina mutum yaga fuskar da zai yi masa wannan cin kashin?”

Dariya nayi nace “nima raina ne ya ɓaci ai”

“Wato tsabar kin zama ƴar gari har fushi kike yi dan bai zo ba?”

“Baiwar Allah sati biyar ba abani hakki na ba ai dole inyi complain”

Dariya naga tayi, “Au har neman hakkinki ma kike?”

“Kinga laifina? Ai wallahi duk ranar da muka haɗu sai yayi biyan bashi”

“lallai ƙawalli lamarin naki azimun ne”

“dole ki ce haka tun da ke kina tare da naki mijin akusa dake….”

Har magriba muka kai tare da ƙawalli, bayan munyi sallah yaya yazo ya ɗauketa suka tafi, sun tafi babu jimawa Bishra tazo saboda dama nayi mata waya akan tazo, ɗaki na ƙule muna video call dashi duk fuskata a ɗaure babu walwala,

” Please baby….. Please show me your chest” maƙale kafaɗa nayi dan na fara gajiya da wannan let me see your chest ɗin na koda yaushe idan muna waya,sai da ya jima yana shan kaina sannan na buɗe masa ya gani,

“Boxer ne a jikin ka wai ko trouser?”

“Gashi ki gani na san abin da kike son gani kenan, kalli don’t be shy” ya faɗa yana ƙoƙarin hasko min abin da yafi ƙarfin idona duk da a zahiri abin da nake son gani ɗin kenan, wannan yana ɗaya daga cikin abin da yake burgeni dashi yana saurin fahimtata koda ban magantu ba, ko idona ya kalla ya kan fahimci abin da nake so ko nake buƙata, mun jima muna yi wa juna kalaman soyayya sannan yabarni nayi shirin bacci na kwanta.

Haka rayuwar taci gaba da tafiya shiru shiru bai zo ba har watanni biyu suka shuɗe tsakanina dashi sai dai waya, kuɗi kam yana ta saka min su a account ba ƙaƙƙautawa, yau tun da na tashi na shirya kayana kala biyu zan je gida kuma kwana zanyi dan na gaji da kwana ni ɗaya saboda Bishra tabi Anty Rivers, jiya a tsorace na kwana danma mun kwana muna waya dashi shine yace zai samo min mai gadi, 11 saura na rufe gidan na nufi gidan mu, ɗakina yana nan kamar da asashen mama babu kowa aciki, su Annie dai faɗa suka yi da nace wai kwana biyu zanyi ku san daƙyar suka yarda daga ƙarshe na yankewa kaina shawarar bin mijina nima tun da gashi Bishra bata nan kuma ba asan ranar dawowarta ba, sannan na gaji da wannan tsokane tsokanen da muke yiwa juna ta waya, mijina kawai nake buƙata yanzu, Anty na yiwa waya nace mata ina buƙatar kayan gyara nan ta haɗani da wata mata ƴar Sokoto ta aiko min da kayayyaki bayan na tura mata kuɗi, gumba ne, turaren tsugunna, zumar mata, tsimi da dai sauransu, sam ban sanar dashi shirina ba dan zuwan bazata nake son yi masa, da wayo da wayo na samu address ɗinshi ya faɗa min komai har estate ɗin nasu da part ɗin da yake zaune, a raina nace Insha Allah sai dai kawai ka ganni, kitso da ƙunshi naje bayan na gama da kayan ƴar Sokoto tsaf, ticket na siya online na biya nayi komai na gama duk bai sani ba shi dai kullum maganar ɗaya ce zai zo in ƙara haƙuri shima yana da buƙatata, kwata kwata ban bari ya san shirina ba har ranar da zan tafi, munyi waya bayan asuba kamar yadda muka saba amma ba video call ba dan bana son yaga ƙunshina da kitson da nayi shiyasa idan ya kirani video call tun daga shekaran jiya sai in katse in ce network ne, flight ɗin da zanbi ƙarfe 1 zai tashi na rana kasancewar weekend ne, sai da na tarkata komai nawa da na san zan buƙata sannan na shirya cikin babbar jaka na rurrufe ko ina a raina ina addu’ar ubangiji Allah ya kare min gidana ya tsare min dukiyata duk da an kawo mai gadi amma kariya tana wurin Allah,

Drop na ɗauka na taxi bayan na sauka, tiryan tiryan har unguwar da samz yake zaune, unguwar tasu ba hayaniya sannan babu gidaje barkatai a tsare take tsab da ita, ina sauka na samu wani ya fito daga cikin estate ɗin da nake sa ran nasu samz ne, tambayarshi nayi dan Allah ko anan samz yake yace min ehh ga part ɗinshi can na ƙasa by left side,

Jakata na ja har zuwa ciki babu ɓata lokaci na buɗe na shiga domin a buɗe ƙofar take, har ina mamakin dalilinsa na barin ƙofa a buɗe, kitchen zaka fara wucewa sai falo sai kuma bedroom, a falo na ajiye jakata na wuce bedroom ɗin fuskata ɗauke da murmushi dan na san zai yi mamakin ganina ba kaɗan ba, a hankali na buɗe ƙofar na shiga, turus nayi na ja na tsaya ina jin ƙafafuwana na rawa kamar ba zasu iya cigaba da ɗaukata ba saboda abin da idanuwana suka gane min, tabbas wannan shi ne mafi munin gani da idanuwana suka yi a cikin tarihin rayuwa ta take naji kaina ya soma juyawa jiri yana kwasata kamar zan faɗi……………….

 

*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*

 

_*Ummi Shatu*_

Back to top button