Ikraam 61
~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 61…… Ikram na xaune
dakinta da yamma rike da literature book dinta bayan
ta gaji da kukan da take tun safe taji an bude kofar
xaure, mikewa tayi da sauri tayi waje don ganin waye,
ita kadae ce gidan Ammi ta tafi gun yayarta yakumbo,
karo suka kusan ci da Aliyu, ta koma baya da sauri
tana kallonsa, shi ma kallonta yake, murmushin ta mai
kyau tayi tace “yayana” shima yyi murmushi yace
“kanwata” hannunta ya kama suka karasa tsakar gidan
ya xauna kan tabarmar dake shimfide ya xaunar da ita
gabansa yana kallonta yace “Ammi fa” ta dan yi shiru
snn tace “Ammi ta tafi gidan yakumbo” ya daga kanta
yana kallon idonta da ya rine, da mmki yace “me ya sa
ki kuka Ikram?” Ikram tayi shiru tana kallonsa, hannunta
ya kamo yace “kiyi min mgna mana Ikram” kmr xata yi
kuka tace “momynka ce ta xo gidanmu da safe take
ma Ammina da Abbana Masifa,” “innalillahi wa’inna
ilaihi raji’un” abinda ya iya furtawa kadae knn ya dafe
kansa, xuciyarsa na bugawa, to wa ya kawo ta gidansu
Ikram, dago kansa yyi da kyar idonsa yyi jajur yana
kallonta, xae yi magana Ammi ta shigo gidan, tana
ganinsa ta hade rae, Ikram ta mike da sauri tana kallon
Amminta tace “Ammi sannu da dawowa” Ammi bata ce
komai ba tayi cikin kitchen da ledan hannunta, tana
fitowa Aliyu ya gaisheta kansa a kasa, ta amsa bbu
yabo bbu fallasa ta shiga dakinta, Ikram ta juya tana
kallonsa snn ta bi ta cikin dakin a sanyaye, ba ajima ba
ta fito ta dan durkusa kusa da shi a hankali tace
“yayana xan je in yi karatu na a daki” kai kawae ya
gyada mata ya mike yace “kice ma Ammi na tafi” ita
ma ta gyada masa kan snn ya fita daga gidan, juyawa
tayi tana kallon kofar dakin Ammi hawaye cike idonta
ta nufi dakinta tana murguda baki. Da daddaren ranan
suna xaune da Amminta a tsakar gida, Ammi ta rafka
uban tagumi, ita ko sae kallon tuwon gabanta take taki
ci, Abbanta ya shigo tare da Kawu na lado, ko gaisuwar
arxiki ba ayi ba Na lado yace “dama na xo da kaina ne
in gaya maki cewar ni Na lado na yanke shawarar hada
‘ya ta Rabi aure da dan wajen abokina Dan lami, surajo,
kuma insha Allahu jibi asabar xa a daura auren” yana
kai wa nn ya juya ya fice, Abba ya bi bayansa don
rakasa, kuka Ikram ta fashe da kmr warce tasan meye
aure, Ammi kam bata ce komai ba sae hawaye take
don tasan bbu abinda xata ce a nn da xae shigesu,
Ikram ta mike tana rusa kuka kmr xata tsaga gidan
tana cewa “wllh ni bana son surajo, ni baxan aura kowa
ba sae yayana, ni yayana nake so” Ammi ta dago tana
share hawayenta tace “waye yayanki” cikin kuka tace
“yaya Aliyu mana, ni shi kadae xan aura bana son
kowa, baxan aura kowa ba” Ammi ta fixgota a fusace
tace “to don ubanki ki bisa ki auresa mana, shegiya
kawae, ke har kinsan wanda xaki aura ko” har karfe
sha biyun dare Ikram bata bar kukan da take ita kadae
a daki ba duk da dukan fitar hankalin da Ammi tayi
mata. Da safe idonta duk ya kumbura lebbanta yyi jajur,
alwala kawae ta fito yi ta koma daki, bata kuma fitowa
ba har rana ta fito, Abba bae bi ta kanta ba ya fice
xuwa gun kasuwancinsa don shi har Allah Allah yake
gobe yyi ya aurar da Ikram ya huta, karfe tara Ammi ta
tura mata break fst dinta nn bakin kofa ba tare da ta
ce ta dauka ba tayi gaba, bata ko kalli break din ba ta
ci gaba da kukanta daga inda ta tsaya. Karfe sha daya
saura taji muryan Mami tana sallama bakin xaure da
gudu Ikram ta fito daga dakinta tayi gun Mami ta
rungumeta tare da fasa mata ihu, a rude Mami tace
“subhanallahi, me ya same ki Ikram” cikin kuka tace
“ko ba Ammi da Abba ba ne” Mami ta dago fuskarta da
mmki tana kallonta tace “suka maki me” Ammi na
tsaye bakin kofa fuskarta a daure tana kallonsu, Mami
ta daga kai tana kallonta tace “me ya same ta Mmn
Ikram” kasa mata shiru Ammi tayi don tana ganin
mutuncin Mami ssae, Ammi ta dan kirkiro murmushi da
kyar tace “iskancinta ne kawae Hajiya” Mami ta kamo
hannunta suka kara cikin tsakar gidan ta xauna kan
tabarma ta xaunar da ita ta dago kanta tana kallon
kumburarrun idonta, Ammi ta juya a sanyaye xata koma
daki Mami tace “wajen ki naxo mmn Ikram” ba musu
Ammi ta dawo ta xauna ba tare da ta kalli Mami ba,
Mami tace “kuyi hkuri da abunda ya faru mmn Ikram,
duk ni na ja komai….” Ammi ta dakatar da ita da sauri
tace “dama ba ke kika haifa Aliyu ba Hajiya?” Mami ta
dan yi shiru snn tace “ehh bani na haife Aliyu ba,
kawae dae na rikesa ne kuma na taba auren ubansa
shekaru masu yawa da suka wuce don ina gidan aka
haifesa ma, kuma yana da shekaru biyu na bar gidan
duk da karancin shekaransu kuwa ba karamin shakuwa
yyi da ni ba don uwarsa bata da lkcnsa, matar da ta xo
nn jiya ita ce mahaifiyarsa, kuma kishiyata yrs bck,
bamu yi xaman ddi da ita ba kuma ita ce sillar
rabuwata da Mahaifin Aliyu, kuma har muka rabu bamu
samu haihu da shi ba, ina gama idda Allah ya hada ni
da mahaifin Khaleel, shekaranmu daya na haifi Khaleel,
kuma na ci gaba da karatuna na likita don Mahaifin
Aliyu bae barni na ci gaba ba a gidansa, Khaleel na da
shekaru goma sha biyu Mahaifinsa ya rasu ya b[truncated by WhatsApp]