Yar Zaman Wanka 5
️5️⃣
“Zaman wanka?” Imra ya tambaya a fusace.
“Eh zaman wanka mana ko a kan ka zan zauna da ka wani hayayyaƙo min kamar wani ubana, ko da dai da duka zaka hauni Imirana” Inna da ta miƙe tsaye daga durƙuson da ta yi tana riƙe da sallayarta.
“Haba Inna wai mai yasa kike haka ne, Yaya Imran fa kamar siriki yake a wajenki” Cewar Ashrof kamar ta saki kuka ganin abin da take yiwa Imran ɗin a gaban abokinsa gashi mahaifiyarsa a gidan amma Inna duk bata gansu ba.
“Ashrofa, Ashrofa, Ashrofa, kin ji na kiraki sau uku to wallahi ki fita daga sabgata ko ke ce uwata mai daddawa da zaki takura min ko uwaki Rakiya ta yi kaɗan ta ce za ta sani abin da ban yi niyya ba”
Wani takaici ne ya sanya Ashrof juyawa da sauri ta shige ɗaki, Imran kuwa juyawa ya yi ya fice daga gidan, Abid da ya juya yana ƙunshe dariyarsa zai marawa Imran baya.
“Kai yaka ɗan nan, yo kai sunan naka ne wahalar faɗa gereshi, ka ce ba Abida ba, to koma dai menene zo ɗauka min jakar nan ka shigar da ita ɗaki, dan babu dalilin da zai sa ta ƙara zama a waje sanyin duniya ya ƙare a kan ta” Ta faɗa tana haɗa mayafinta da abin sallar ta rataye a kan igiya.
“To Inna” Abid da bashi da zaɓi sai bin umarninta dan haka ya ɗauki jakar ya shiga ɗakin bakinsa ɗauke da sallama. Hajiya ce ta amsa masa, shi ma gani duk sun yi jingum-jingum sai bai ce komai ba ya ajiye jakar ya fita, su duka suka bi jakar da kallo, suna jinjina ƙoƙari irin na Inna dan basa ce wauta ba a shiga uku.
Banɗaki ta wuce ta ɗauro alwala ta shimfiɗa sallayarta a waje ta shiga gabatar da sallolin da ake bin ta, tana sallar amma kunneta a ɗaki.
A can cikin ɗaki kuwa Hajiya ce ta katse shirun da cewa “An kawo tukunyar dafa ruwan wanka babba irin wacce ake dafa abincin gidan suna gata can a waje da kuma itace duk suna nan, dama yadda muka tsara da Imran cewa tun da gidana babu nisa da sassafe zan ke zuwa ina ɗora ruwan wanka in wanki jarirai, ita kuma Ashrof take zuwa tana wuni shi ya ce zai ke kwana da su, amma yanzu tunda Inna ta zo ZAMAN WANKA sai a ruguje wannan tsarin” Ta faɗa tana kallon Mama da gabaɗaya damuwarta ta bayyana a fili ƙarara.
“Haba Hajiya ya zaki ce haka bayan ga tsarin da aka yi kin san dai gidan nan ciki da falo ne kawai to shin a ina Inna za ta zauna?” Cewar Ashrof cikin sanyin murya.
“A gidan uwaki zan kwana, na ce a cinyar uwaki zan kwana Asharofa, wato ma saboda rashin ta ido har zama kuke ku yi da ni, Allah na tuba nawa ne kwana arba’in kwanci tashi asarar mai rai kamar yau ne fa za su ƙare, ban da abinku ma yarinyar da ta haifi ƴaƴa biyu ai kamata ya yi a yiwa Hassan arba’in ɗinsa da ban ta Hussainin ma da ban. Amma shi ne kuka zauna kuna ɗaya biyu, to ni nan gani nan bari farar tunfafiya ko sama da ƙasa za su haɗu babu yadda za a yi in fasa ZAMAN WANKAN NAN” Inna da idar da sallarta kenan ta faɗa tana tsaye a bakin ƙofa dama tana sallar amma kunnuwanta a wajen su Hajiya dan ta ji waye mai son ta zauna waye kuma wanda bai goyon bayan zamanta a gidan.
“Allah baki haƙuri Inna wannan fa tsari ne da aka yi tun kafin a san da zuwanki ne aka yanke wannan maganar”
“In ma ba a san da zuwana ba ai yanzu an sani, kuma ita Asharofa da take cewa ciki da falo ne a gidan menene aibu tun da har ciki biyu ne wato ɗakuna biyu, shi Imirana ya ɗauki ɗaya mu ma mu ɗauki ɗaya ni da mai jego da jarirai, ke ko ma ciki ɗaya ne a gidan nan sai dai muke yin kai da ƙafa da Imirana ehe”
Sadiya jin maganganun Inna suka tuna mata da maganar Imran lokacin tana da tsohon ciki.
“Ni fa wallahi ban son wannan al’adar da ake yiwa mace idan ta haihu ta ZAMAN WANKA saboda bana son abin da zai rabani da ke ko na second guda ne da, bare ma ba mu da wadatattun ɗakunan da za a zo gidan nan a zauna, ni zan ke muku komai ke da jariri daga magriba zuwa wayewar gari da safe Hajiya tun da kusa muke sai ta zo ta musu wanka ta miki abin da ya dace in ya so Ashrof sai take zuwa tana wuni tana yin girki”
Halima kin ci wake da shinkafar ki” Ta katsewa Sadiya tunani tana ƙarasowa kusa da ita ta zauna wani takaici ne ya tare mata a zuciya.Ganin Sadiya ta ƙyaleta ta ce
“Oh ni Azumi na ji na gani an kashe tsohuwa da ranta, ke ma bakya son zaman nawa ko me? Lallai in da ranka kasha kallo, yanzu ke Halima ZAMAN WANKAN ne bakya so a miki saboda ke mahaukaciya ce ke, kin manta gabaɗaya jikin ki faci ne sai fa da aka ɓarka ki kamar wata takarda aka maida aka ɗinke kamar wata ƙwarya, sai da aka miki ɗinki bakwai. So kike a barki daga ke sai wannan kurman yaro a gida cikin dare ya haike miki ya ƙara ɓarka ki, gabaɗaya ki tashi a aiki, dan da ganinsa fitinanne ne ido fici-fici yawa na ƴan cena (China) To wallahi kika sake aka barku ya nemi ya shiga rijiyar jikin ki kika bashi dama wallahi sai dai ke ba wata dan wallahi ko likitoci basa iya ɗinke ki ba tun da wurin ɗanye ne sharaf kuma wani cikin ne zai shiga nan da wata shekarar in dawo suna haɗe da ZAMAN WANKA amma in ina nan aradu ko hannunki bai isa ya kama ba bare ya shiga jiriyar ma, amma dai bari in yi shiru ciki ba dan tuwo kaɗai aka yi shi ba” Ta faɗa tana tashi ta nufi kan frige ɗin falon ta shiga bubbuɗe ledojin da Imran ya kai asibiti.
“Kai kurma ma ya san dai dai wallahi ashe siyayya ya iyo mana ta pan zaman jinya ɗan arziƙi, kun ga fa ta faɗa tana nuno musu hanta ce da kayan marmari (Fruit)” Da soyayyiyar doya, da ƙwai cikin ƙwai sai kuma maltina guda biyu masu sanyi”
“Ku ɗaɗɗauka ” Ta faɗa lokacin da ta ɗauki hanta ta sanya a baki, shi ne ta miƙa musu takarda.Gabaɗaya babu wanda ya karɓa.
“Kun huta wallahi ni gaba ta kaini gobarar titi, tabbas idan na yi ZaMAN WANKAN nan na koma Malam ba zai shaidani ba dan ɓulɓul zan yi, taɓɗi Tasalla kwa har baƙinciki ya so kashe ta” Ta faɗa tana neman wuri ta zauna tana cin hantar sai kuma maltina da ta ɗakko ta ajiye a gabanta.
“Ke ma Halima bakya ci kenan ai na ga alama ƙam baki kike na masu haihuwa da basa cin komai sai sun ɗan ware”
Babu wanda ya tanka ta can ta ce
“Asharofa ɗauki maltinar nam ki buɗe min in ke yi ima korawa kai ai wallahi kuna jin daɗin ku ƴan birni, gaskiya na yi wauta da bayan mutuwar kakanku na yi aure a ƙauye, gaskiya Malam ya tsinci dami a kale, yo in ba dan ƙaddara ba ina wanda ke zaune birni, birnin ma kamar Kano zai koma ƙauye da zama, wallahi ko kallon motoci kaɗai kake da dogayen gidaje (Gidan bene) Kaɗai ya isa ya sanya idanunka su yi ƙwari, amma a can ban da dai daga ka tashi karatun almajiran Malam ya hanaka sakat ka koma bacci, ga ka rinƙa haɗa ido da wasu alluna na Malam sai ko kake ganin shanaye da dabbobi in kwa kin ga mota to motar kasuwa ce ta Alhaji Tukur da take cika mutane wani kan wani idan za a tafi cin kasuwa yo Allah na tuba ganin motacin Alhaji tukur duk sun yi tsatsa wallahi ganinsu kaɗai ya isa ya kashe maka ido”
“Inna wannan fa kayan Aunty Sadiya aka siyo wa amma kin zo kina ci” Cewar Ashrof tana wani harar Inna.
“Oh wallahi ke dai ƴar nan bakya mutuwar tsakar ɗakin ki sai dai ta wani, to tun da na Halima ne kuma na ci to in ji didim” Ta faɗa tana juya wa Ashrof baya.
“Ni ban ce zan da ke ki ba Inna amma kike yin abin da ya dace ”
“Yo ai gwara dai ki dake ni ɗin, ban da ma neman magana ina ma mai ɗanyen jiki (Mai haihuwa) Da shan kayan sanyi ai sai dai ake bata ruwan zafi yanzu babu ita babu shan kayan sanyi sai jikinta ya yi ƙwari nan da watanni masu yawa”
“Ɗauki ni ki buɗe min in sha sanyin ya ratsa ni, kar ya huce”
“To” Ashrof ta ce ta ɗauka ta buɗe mata.
“Da dai da ya fi miki, ai zama lafiya ya fi zama ɗan sarki” Ta faɗa lokacin da ta karɓi kwalbar ta kafa kai ta shiga kwankwaɗa har wani lumshe ido take.
“Oh Allah mai yadda ya so tabbas rabon kwaɗo bai hawa sama, ai gaskiya in dai zan ke samun haka to babu abin da zai hana ni yin arba’in uku cikakku, kowane yaro a masa kwana murtala uku (60) Wai fa a hakan ma babu madara a ciki, humm yo mu a can daga shekara sai shekara wato da azumi muke shan lemomo dan bana ce lemo ba yo gasarar koko ce ake zuba mata ruwa zuba mata ɗan zaƙi (Sweetner) Shi Malam bai iya siyen lemon takarda (Vevi mis) Haka za a haɗa mu da almajira mu yi kamfata muna kwankwaɗa kamar wasu shanaye, yo ya ka iya da abin da ya fi ƙarfinka ai ko dan ƙishirwar azumi ma ka sha”
“Ashrof fita ki samo min ɗan sahu kin ga har an fara kiran sallar magriba” Cewar Hajiya jin ta gaji da sauraren Inna ko gajiya ma bakinta bai yi da yawan magana.
“Amina yaushe kuka tashi daga gidan da na sanku” Cewar Inna tana kama haɓa.
“Ba mu tashi ba” Hajiya Amina ta bata ansa a takaice.
“Wai kina nufin kuna can ɗin har yanzu, kuma nan da nan ɗin ne sai kin hau abin hawa? Tafiyar bata kai ta kawo ba, in ce dai kwana uku za a yi daga nan layin a je gidan naki?”
“Eh”
“Tabɗi jam” Ta ce tana jijjiga kai.
“To wai Inna meye naki a ciki? Sadiya da Ashrof suka haɗa baki wajen faɗa.
“Ikon lillahi ai kwa bari in mutu, kafin ku binne ni, ni fa wallahi na fi son tafiyar ƙafa, saboda kallon ababen hawa da gidaje masu kyau, ina tafiya gidan da na ga ya birgeni sai in tsaya in shashshafa shi, ko da dai bani da rabon shiga irinsa a duniya ai na taɓa da hannu na, akwai wani lokaci fa ina tafiya na a ɗan sahu na ga wani gida gabaɗaya an baibayeshi da fulawoyi gwanin sha’awa, da hanzari na cewa ɗan sahun a nan zan sauka hakanya sauke ni, yana tafiya na juya abuna na je jikin gidan na rinƙa shafa fulawoyin, sai ga wani matashi ina cikin shafawa ya ce menene kike yi hakan, na ce a’a ɗannan, ba abin da zan yi taɓawa kawai zan yi in bar muku kayanku ai ya kama dariya, wai ina da barkwanci da na tashi tafiya har tsinka min ya yi wai in ke shafasun, wannan ya sa ba na son hawa abin hawa, yo hawa abin hawa ko asarar kuɗi an wuce da kai baka ga komai ba komai yana wulgawa wul-wul…
“Ashrof yi sauri ki kirawo mini tafiya nake son yi” Cewar Hajiya ganin gabaɗaya su Ashrof suna dariya, ita kuma ranta duk ya dagule saboda ta san zaman Inna a gidan zia takura mata ɗanta kasancewar Imran ɗin nata mai yawan buƙata yana da ƙarfin sha’awa ne kuma mahaifinsa ya biyo dan ko da ba za su samu biyan buƙata ba in ma mace tana priod to suna son koyaushe su kasance a jikin matarsu dan su rage damuwarsu haka Allah ya halicce su.
“To Hajiya” Ta faɗa tana fita daga falon dan gabaɗaya har lokacin maganat Inna dariya take bata wai ta tsaya shafa gidaje kai wani kaya sai amale gaskiya Innarsu da ban take.
~IMRAN~
Tun da ya fita daga gidan ya je jikin machine ɗinsa ya tsaya ya ɗora hannunsa ɗaya a jikin machine ɗin ɗayan kuma ya dafe kansa da shi, ji yake kamar ya fashe da kuka dan takaici saboda ya san dole sai Hajiya ta ce a bar Inna ZAMAN WANKA amma ta ina zai fara rayuwa da wannan matar a gida ɗaya a ɗaki ɗaya, shi ba ma wannan bane damuwarsa, damuwarsa ɗaya yadda zai kwanta ba tare da matarsa a kusa da shi ba, dan ya san ko giyar wake ta sha idan ta gan su kwance a gado ɗaya sai ta musu ɗiban albarka shi ya zai yi. Zuwan Abid wurin ne ya dawo da shi daga tunanin da yake.
“Haba abokina ya za ka sanya kan ka a damuwa haka, tun ɗazu fa na zo kira uku na maka amma baka ji ba har sai da na dafa ka, mai ya yi zafi haka?”
Imran ji ya yi kamar ya rungume Abid ya saki kuka ko ya ɗan samu sassauci.
“Haba Abid ya kake so in yi to matar nan fa tana son kashe ni ne kai kan ka ka san saboda ina da yawan sha’awa na yi aure a yanzu, kuma ka san yanzu matar nan idan tana nan ko yatsan matata ba za ta bari ma taɓa ba, ni kuma ka san halina ba manemin mata bane, ko da a ce ta haihu ba zan kusance ta ba ai dai zan so na kwanta a kusa da ita saboda yadda Allah ya halicce ni”
“Haƙuri za ka yi, i kaina ban ji daɗin hakan ba amma kawai ka kyaleta”
“Wallahi idan matar nan ta sake Hajiya ta bata dama ta zauna sai ta gwammace kiɗa da karatu wallahi sai ta yi da na sanin zuwanta gidana ZAMAN WANKA dan ba zan raga mata ba sai na mata abin da za ta bar gidan da ƙafafunta…
Ƙaran wayarsa ne ya dakatar da shi daga maganar da yake, ganin sunan Hajiya ya marairaice fuska kamar ya saki kuka har kiran ya katse bai ɗauka ba, sai da wani ya shigo ya ɗauka dan ya san zancen gizo bai wuce na ƙoƙi.
‘Ka zo ina son ganinka “Hajiyar ta faɗa tana kashe wayar ba tare da ta jira cewarsa ba.
Sallama Abid ya masa tare da fatan Allah ya raya ya shiga motarsa ya tafi dan ya san yadda abokin nasa ya zuciya da kuma yadda yake da kafiya duk abin da zai faɗa masa ba yarda zai yi ba. Yana ƙoƙarin shiga gidan suka yi kiciɓis da Ashrof da ke ƙoƙarin fitowa , ratse masa ta yi ya wuce ta ita ma ganinsa rai ɓace ya taho a fusace kamar kumurcin maciji sai ba ta ce masa komai ba, dan ban da ma haihuwar nan da aka yi bakinta da shi gaisuwa ce kaɗai to ga kuma Inna ta zo ta hargitsa murnar haihuwar ta damawa kowa lissafi.
“Jama’a duk kun yi shirun kun yi jigum-jigum kamar masu zaman makoki, yo Allah na tuba ko gidan makoki yanzu an daina zama jigum-jigum kowa hirarsa yake da an binne mamaci, bare ku da aka muku haihuwa har biyu duk da ɗayan na ɗauke da lalura dan ba na ce baiwa ba” Imran da ke ƙoƙorin shigowa ya jiyo muryar Inna tana ta zuba. Da sallama ya shigo falon yana shigowa ya yi tozali da takardar hantar da ya siyo da maltina a gabanta. Kallonta yake baki sake.
“Imirana ya kake kallona ko so kake ka ci, zo ɗauki hantar yanka ɗaya ka maida mugun yawu.
” Ta faɗa tana ɗauko yanka ɗaya ta miƙa masa. Takaici ne ma ya sa ya ɗauke kansa ya maida kan Hajiya.
“Hajiya gani”
“Ka huta ka je can da mugun halinka, kake haɗiye yawu midik, aikin banza harara a duhu, da kuwa a asibiti ware murya ka yi kake magana, amma yanzu ka dawo kurmanka na asali to in hakan kake so Allah maida ƙoƙo masaki” Ta ce tana kai hantar bakinta.
“”Imran ni zan tafi, ga Inna nan za ta yi ZAMAN WANKA kar in ji kar in gani” Ta faɗa tana miƙawa Sadiya Hassan da ke hannunta.
“Hajiya a ciki da falon?”
“Kai bari ka ji in fito maka a mutum, ba ciki da falo ba idan ciki ɗaya ne Imiran sai na zauna sai dai muke kwanciya kai da ƙafa da kai, in kuma ka ga ba zaka zauna ba ka bi Amina gidanta ka koma ɗakinka na da na gwauro, yo dama meye marabar dambe da faɗa yanzu ma gwauron kake tun da matarka ta haihu, in kuma ba zaka gidan Aminar ba sai ka kama shago na samari kake kwana” Cewar Inna har da tafa hannuwa.
“Tashi mu je ka raka ni na ji ƙaran napep ɗin a waje ina ga Ashrof har ta kira shi, mu kwana lafiya Mamar Sadiya ”
“To Hajiya Allah tashemu lafiya ya huta gajiya mu ma yanzu za mu tafi ai” Cewar Mama.
Haka suka fita ita da Imran ɗin…
Masu son shiga grp na zaman wanka
MMN AFRAH 09030283375.
Beelal dai yana nan yana sauka da zafinsa ki nema ki karanta labari a kan nakasashshen yaron da wani bahagon gidan da aka rasa alƙiblarsu Alƙalamin mmn afrah ba ya rubuta shirme
* SDEENDTM DATA SERVICES*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500
*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦500
2GB = ₦700. 1.5GB ₦1100
3GB = ₦1050. 2GB ₦1600
4GB = ₦1400. 3GB ₦2000
5GB = ₦1750. 4GB ₦2500
*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
*08066268951*
A sayi data mai rahusa masoya
ƳAR ZAMAN WANKA
(KWANA ARBA’IN)
NA
MAMAN AFRAH
Na gode sosai da addu’o in ku gareni, da wanda suka min a grp da na pc har masu kirana ana tare masoya son so fisabilillah