Yar Zaman Wanka 4
️4️⃣
“Kai jama’a shi kuma irin tasa baiwar kenan?” Inna ta faɗa gabaɗaya jikinta ya ɗauki karkarwa, musamman da ta ji Hajiya Amina ta ce wai wasu maciji ake haifa ɗayan kuma mutum.
“Wallahi sai ma kin buɗe kin gani da idaonki kin san an ce gani ya kori ji”
Cewar Hajiya Amina.
Daidai nan Imran ya dawo riƙe da ledoji a hannunsa amma Inna ba wai ta ledojin take ba duk kwaɗayinta da son abin duniya sai ta ji duk bata cikin nutsuwarta.
“Ni Azumi barni in mutu maza su kai ni ba mata ba, ai in kin ganni a lahira kaini aka yi” Ta faɗa tana ɗaukan Husainin ta miƙawa Mama ta ɗauki Hassan ɗin hannunta na karkarwa har yaron ya so kuɓucewa ya faɗi.
“Haba Inna ya za kike garaje a kan jaririn da aka haifa yanzu” Imran ya faɗa a fusace dan yanayin da Innar ta miƙo yaron tamkar wacce ta riƙo kashi.
“Jakar uban nan kayya, ɗan malafar uba ka ce fa, ashe dai kana magana rainin hankali ne yasa kake maƙe murya kamar ka haɗiyi rariyar tankaɗe, to dukana za kayi fa da hayayyaƙo min, yo wa ma ya sani ko haka bayanka yake irin na miciji abu a duhu, wa ma ya sani ko kai yaron ya gado na san ko haka naka bayan yake wannan yarinya Halima ba faɗa za ta yi ba, dan mu kaf danginmu babu masu fatar macizai”
“Me kika ce” Imran ya tambaya yana kafeta da idanunsa da suka masa jajir dan da ace matar nan bata da haɗi da matarsa wallahi sai ya shuka mata tsiya tunda ita bata san annabi ya faku ba.
“Yo ni kwa mai na ce, abin da wancan ya ce shi na ce kirarin mai tsoro” Cewar Inna tana kawar da kai gefe.
Hajiya kwa ta kasa furta komai dan yadda Innar ta jangwaɓar da yaron tamkar ɗan mutuntumi ba ɗan mutum ba.
“Ina ƴan uwan Sadiya Abdussamad wacce ta haifi ƴan biyu ɗazu?” Wata nurse da ke tsaye ta faɗa tana daga tsaye kan barandar ɗakin haihuwar sai wani yatsina take tana taɓe baki.
“Gamu nan” Cewar Ashrof tana miƙewa tsaye.
“Haba Asharofa bakya barin in bata amsa dai dai da ita, to in banda raini ta kallemu duk mun haifi uwarta ma mun yi jika da ita ta wani mere baki, ina ƴan uwan Sa’adiyya” Inna ta faɗa tana gwada maganar matashiyar.
Wani kallo nurse ɗin ta watsawa Inna, ta ce
“Ta falka ana buƙatar mutum ɗaya ya zo, dan sallamarta ma za a yi dan babu matsala” Ta faɗa tana gyara hijabinta da yake iya kafaɗarta.
“Bismillahi ku bari ni in je tun da ni kaɗaice banganta ba, ku duk a nan na sameku” Inna ta faɗa tana miƙewa ta gyara ɗaurin zaninta tare da ɗankwali, ta daidaita mayafinta.
“Haba tsohuwa ya ana neman masu ɗan gwaɓi -gwaɓi za ki taso bayan ke ma da za a taimaka miki kina buƙatar taimakon, ta ya za ki taimakawa wani?” Ta faɗa tana kama tsantsa.
“Ke ki kiyayeni da ganinki ko auren fari baki da shi amma sai a ɗaukeku aiki saboda kun yi karatun masu jajayen kunne, ku ke karɓar haihuwa kafin ku je gidan miji kun gama haddace komai, kun san ta yaya ake haihuwa har kun ɗinkesu tamkar wata ƙwarya, to ni nan har gozomanci na yi a ƙauyenmu” Ta faɗa tana hawa kan barandar da za ta sadata da
ɗakin haihuwar.
“Inna dan Allah ki bari ko Mama ko Hajiya su je mana ke fa ko ɗakin baki sani ba” Ashrof ta faɗa tana marairaicewa.
“Ke rufe min baki matambayi ai baya ɓata, zan tambaya kuma ma Allah na tuba ko daga bacci na tashi ai bazan kasa shaida Halima ba, duddubawa zan yi har in ganta, ke ɗin da gulma ajali in ba a yi ba a mutu” Ta faɗa tana wani gatsinen gefen hanci.
“Ki bari Mama ta je” Cewar Imran lokacin da ya ajiye ledojin hannunsa ya nufo wajen Innar dan ya ɗan bata baki, dan shi a kan matarsa zai iya yin komai ko da ba ya so. Mama kuwa ranta in ya yi dubu ya ɓaci ji take dama bata sanar da Inna Sadiya na naƙuda ba da yanzu duk haka bata faru ba ta rasa bakin magana tana da kara, bare kuma ƴar fari ce Sadiya a wajenta, kuma Inna sirika ce a wajenta ko da kuwa ɗanta baya raye uwa ce a wurinta.
Bare kuma Hajiya ita mai za ta ce tun da ba daga ɓangarenta Inna take ba.
“Lallai Imirana to wallahi in kuma ganin bakinka a ƙunshe kamar wani balangu a takarda, tun da har kana magana, kai da kake da aiki jajawur a gabanka, wato an haifa maka ƴaƴa biyu ai yanzu kamata ya yi ace kana kasuwa siyo sadakin gado (Raguna) Sai ka tsaya kana shiga shari ba shanu” Ta faɗa tana yin gaba ta barshi tsaye baki sake, tana shigewa ɗakin nurse ɗin ta ce “Mutum ɗaya ta taho dan wannan babu abin da za ta yi in ba surutu ba”
“To mun gode ki yi haƙuri kin san tsofaffin nan sai a hankali” Hajiya da ta baiwa Ashrof Hassan ta faɗa tana tahowa dan zuwa wajen Sadiya ganin Mama tana yiwa Inna kara ba za ta bita ba.
Ashe Inna tsayawa ta yi bata tafi ba, dan haka nurse ɗin na shiga ɗakin ta ganta a tsaye a hanyar shiba ɗakin dan akwai ɗan tazarar zuwa inda masu haihuwad suke.
“Ƴar nan an buga an barmu” Inna ta faɗa tana ƴar dariya.
.”Nonsense” Cewar matashiyar tana jan tsaki ta juya abinta.
“Uwaki ce nosi wallahi ba dai ni ba, ƴar kare kawai da kai tun na haihuwa, ai duk da ban san abin da kika faɗa ba yanayin yadda kika yi maganar da kuma yadda kika yi tsaki na san ba abin arziƙi bane, to aniyarki ta biki”
Ganin Hajiya ta taho ya sa ta yi shiru, haka ta bi bayan Hajiyar suka tafi har suka je ɗakin.
Suna shiga ɗakin gadaje ne sun kai talatin da yake ɗakin hutu ne inda ake ajiye masu haihuwa bayan sun haihu shi asalin cikin ɗakin da ake haihuwar yana daga ciki amma ana iya jiyo ihun masu haihuwar da ke naƙuda saboda kusa ne ƙofa ce ta raba.
“Ke rufewa mutane baki, lokacin da kika je kika karɓo cikin wa ya raka ki wajen mijin, to yanzu ma haka zaki sha wahalarki ke kaɗai” Cewar Inna cikin ɗaga murya, jin wata mai naƙuda ta daddage tana ihu tana cewa a kawo mata agaji.
Kowa bin ta yake da kallo kawai wasu na dariya.
“Sannunku kun ji, sannunku da ƙoƙari yau kowa ta san yadda ta zo duniya da irin rigiji gabjin da uwarta ta yi lokacin haihuwarta, da wanɗanda yau ne suka yi ta fari da kuma wanɗanda sakewa suka yi, sai a wasa haƙora kuma domin cin sadakin gado “Ragon suna” Cewar Inna da ta buɗe muryar tana ta faɗa wa matan da ke wurin su kwa mai za su yi in ba dariya ba. Hajiya kwa gadon Sadiya ta wuce, ta bar Inna tana ta yawan yi, kallon nurse ɗin nan Inna ta yi ta ɗazu ganin tana darawa kan maganar da Innar ta yi Inna ta mere baki ta ce
“To fa harda su kaza a cin danƙo?’ Bata jira cewar nurse ɗin ba ta wuce gadon Sadiyar tun kafin ta ƙarasa ta fara rafka uban salati
tana cewa.
“Wayyo Allah sannu Halimatus Sa’adiyya, sannu kin ji”
Wani uban bugawa kirji Sadiya ya yi da ta ga Inna.
“Na shigesu mai Inna ta zo yi kuma daga haihuwar ba dai ta zo bane har suna, in kwa haka ne to tabbas akwai matsala dan ta san kafin ranar sunan nan sai ta ginshi kowa” Ta faɗa a zuciyarta a fili kuma sai ta ce.
“Yawwa Inna” Ta faɗa a hankali kamar bata so.
“Ikon Allah ya wuce mamaki sai kallo, yanzu ke ma Halima halin mijin naki kika koya? Magana kamar mutum baya so ni na kasa ganewa gayu ne hakan ko kuwa rainin hankali ne, ace Allah ya tsaga maka baki dan kake magana amma kake tauyewa baki haƙƙinsa” Cewar Inna lokacin da ta ƙaraso ta samu gefen gadon ta zauna da yake Halimar ma a zaune take ta jingina da filo.
Shiru Sadiyar ta yi bata ce komai ba.
“To ni in baki so zuwana ba in tashi baki alekum in koma inda na fito, dama dan ke zan yi, dan ɗana kuma marigayi, ai dai yau kin ɗanɗana haihuwar kin ji kin banbance tsakanin aya da tsakuwa kin kuma ƙara sanin muhimmancin ƴaƴa a wajen iyayensu da na iyaye a wajen ƴaƴan ma baki ɗaya.
” Ni ban ce ba Inna”
“A’a to in ma bakya so ai ba faɗa za ki yi ba, dama abu ɗaya ya kawoni amma kuma yanzu ya zama biyu, zuwa na yi in miki barka in miki jaje duk a tare”
“Jaje kuma Inna?”
“Yo jaje mana, barkar Hussaini zan miki, sai kuma in miki jajen Hassa…
Ai Inna bata ƙarasa ba sai Sadiya ta fashe da wani kuka mai cin rai, dan ita zaton ta Hassan ɗin mutuwa ya yi.
“Haba Inna ya zaki sakata kuka?” Hajiya Amina da take haɗawa Sadiya shayi dan ta sha ta ji ƙarfin jikinta ta faɗa cikin fusata dan abin na Inna ya fara wuce gona da iri.
“Yo ba dole ba in mata jaje ba wannan yaro da fatar bayansa take ta miciji ai abin a jajanta ne, ko ba haka ba bayin Allah?” Ta faɗa tana kallon mutanen ɗakin da wasu hankakinsu ke kan su babu wanda ya ce wani abu wanda ta basu dariya dai sun ɗan dara a ɓoye wanda kuma ta basu haushi sun ji haushi.
Dafe kai Sadiya ta yi tare da sauke wata nannauyar ajiyar zuciya jin ba mutuwa ya yi ba dan ita sosai take jin son Hassan ɗin har ya fi na Hussainin saboda baiwar da ke tare da shi.
“Shi yasa aka hanaki shigowa amma kika shigo dama na san in banda surutu babu abin da za ki zo ki yi” Nurse ɗin nan da ta taso daga kujerarta da aka tanada domin su ta faɗa lokacin da ta ƙaraso wajen gadon domin yiwa Sadiya allura.
Hajiya kwa jin abin da Inna ta ce sai ta ce
” Allah kyauta”
Tana ga shan shayin, aka mata allurar, Inna dai bata ƙara yin magana ba har Sadiyar ta tashi suka je wurin nurse ɗin ta rubuta musu sallama tare da magungunan da za a siya. Da yake basu da kaya a ɗakin sai kawai kayan shayin Hajiya ta ɗakko suka taho Inna na yiwa ƴan ɗakin sallama tana ɗaɗɗaga hannu masu dariya suna yi ita kwa ko a jikinta dan ita iya gaskiyarta take komai ba dan wani abu ba.
Tafiyar da Sadiyar ke yi ce Inna da ke bin su a baya ta lura da hakan ya sa ta ce.
“Halima wannan tafiyar tantatan da kike yi fa sai kace wata wacce aka yiwa shayi?”
“Haba Inna yo wanda ya haihu har a haɗashi da ɗan shayi, ai haihuwa tafi gaban wasa, bare ita da ta haifi tagwaye kuma ɗinki uku aka mata a waje daga ciki kuwa huɗu aka mata dan bayan an ƙarata ta sake ƙaruwa da kan ta shi ya sa take tafiya…
“Halima ɗinki bakwai kenan aka miki sai ka ce wata ƙwarya? Yo ki ce min Sa’adiyya babu bayani yanzu Imirana zai daina wannan rawar kan da rawar ƙafar, tun da duk an miki faci a mafitar ɗa, shi kwa namiji dama wannan wurin yake wa da an ce babu to ke kuwa mace kin kaɗe a wurinsa har ganyenki dan wata zai nema ya aura”
“Faci fa Inna sai kace wata tayar keke?” Hajiya Amina da ta dakata da tafiya ta faɗa tana kallon Inna.
“Yo meye marabar dambe da faɗa Amina? Da bakinki fa kika ce ɗinki har bakwai to aikuwa bagaruwa ma bata yi wannan aikin ba”
Kunya ce da haushi duk suka kama Sadiya abin da Inna ke mata a gaban sirikarta idanunta har ƙwalla suka kawo.
Har suka fito babu wanda ya ƙara magana Inna kwa sai taɓe baki take yi abinta.
Suna fitowa suka samu an sanya komai a motar abokin Imran da Imran ɗin ya kira domin ya maida su gida, Inna tana hango Imran a zuciyarta ta ce
“Wannan ai shi ne sauna kira mana shasha sha in ka ga sakarai ku taho tare, wato dai har yanzu bai tafi neman sadakin gado ba (Raguna) Kar dai a ce ba zai yiwa yaran nan yanka ba amma kwa in haka ne da Imirana ya cuceni ya jayo min abin faɗa a ƙauyenmu, dan yo mai zan ce idan na gama zaman wanka zan koma ƙauye ne babu naman suna son ayi dani cewar ba a yiwa jikata yanka ba, ni da nufi na in a ban kashina in sanya a cikin mai (Kakide) Dan kar ya lalace amma ni ban ga yaron nan yana da niyya ba” Ta faɗa a zuciyarta lokacin da suka ƙaraso wajen motar.
Mama riƙe da Husaini, a baya, da Sadiya, sai Hajiya riƙe da Hassan wanda ta karɓa yanzu a hannun Ashrof, suka shiga gaba ita da Ashrof ɗin, Imran kwa dama a machine ɗinsa zai tafi.
“Inna can zaki shiga fa” Hajiya ta faɗa ganin Inna tana wani kalle-kalle
.”Haba Amina ai ban ce miki ban sani ba, ko kina nufin a ɗan sahu zan koma ai wallahi ko babu wuri sai dai ɗaya daga cikinku ta haƙura ni in shiga” Ta faɗa tana shiga bayan Imran ya rufe musu ƙofar yana jin haushin Inna. Abid kuwa abokin Imran sai dariya yake abinsa dan sosai yadda Inna ke magana ya bashi dariya ya daɗe yana jin labarinta wajen Imran idan ta zo gidansa wai baya son matar takura masa take sai kuma ɗazu da yake bashi labarin zuwanta a waya, sai yau dai Allah ya sa ya ga Inna da idonsa.
Tun da suka hau kan titi take ta kalle -kalle abinta babu wanda ya ce wani abu, zuwa can ta ce
“Oh yau ai na ga ta kaina da na biyo Imirana, ko kallon titi ban samu na yi ba, yo ni da lokacin ma ina zaman garin nan ko unguwa zani in ba wani nisan azo a gani gareta ba bana hawa abin hawa da ƙafata nake yawo, yo in a ƙafa ne sai ka gama kallon gidaje masu kyau da abubuwa a hanya amma in a abin hawa ne sai dai ka ke ganin wulgawarsu wul-wul” Ta faɗa tana taɓe baki babu wanda ya tanka ta sai Abid da ke tuƙi yana darawa abinsa.
” Ka ji yaro ya sunanka?” Ta tambaya tana ɗan ɗaga murya yadda zai ji ta.
“Abid” Ya faɗa yana ƙunshe dariyarsa yana kuma jiran mai zai biyo baya dan ya tabbata sai ta masa ƙwasƙwarima a sunan kamar yadda Imran ya ce ta jagwalgwala masa suna wai Imirana.
“Ikon Allah wai na kwance ya faɗi, Abid kuma ka dai ce Abida wato sunan mata ma kai aka saka maka”
Sosai Abid yake dariya.
“Ka yi dariya man ɗan nan a rasa sunan da za a saka maka sai sunan mata”
Har lokacin dariya yake. A haka suka gangara hanyar da za ta sada su da gidan Sadiya, a cikin tafiya aka zo gidan da Imran ya shiga wajen abokinsa, aikuwa idanun Inna suka sauka a kan abokin Imran da ke tsaye yana latsa waya lokacin sanye yake da riga da wanda na yadi.
“Abida ka ga wancan wanda ya ɗago maka hannu?”
“Na ganshi Inna kin san shi ne?”
“Yo ina fa na san shi ɗazu ne dai abokin ka kurma Imirana ya shiga gidan karɓar zaitun ni duk tunanina asibitin ne, ka san shi ba bayani zai yiwa mutane ba, aikuwa na bi bayansa, na shiga ɗakin, ka ga wannan kana ganinsa dai yanzu cikin shigar kamala ko to wallahi in ka ganshi a cikin gidan wasarere yake zama jiki babu kintsi”
“Ƙazami ne kenan Inna”
“Ashsha wane irin ƙazanta haka dai yake zama jiki babu kintsi ni na san abin da na gani ɗazu” Ta faɗa tana jan bakinta ta yi shiru ganin bai harbo jirginta ba ita kuma ba ta so ta yi ɓaranɓarama shi sa ta yi shiru.
A dai dai ƙofar gidan ya tsayar da motar, kowa ya fito Ashrof da Imran ya baiwa mukullin gidan ta buɗe suka fara fito da kayan ita da Abid, haka ta kwasa Abid ya ɗauki wasu kowa ya fara shigowa gidan, da mamaki kowa ke kallon ƙatuwar bakkon da ke shaƙe da kaya sai suka fara tunanin ko Imran ne ya siyo kayan jarirai amma ban da Sadiya da ta san cewa sun sayi komai na haihuwa dan dama tun lokacin da aka mata scanning aka sanar da su ƴan biyu ne.
“Allah darki jakata ki yafe mini, wallahi abubuwa sun sha kaina na barki duk kin sha sanyi a wofi, kuma ma dai da laifin wannan ja’irin yaro Imirana yana jin sanda na janyoki amma dan mugun hali ya rufe ƙofar ɗakin ban samu na shiga da ke ba” Inna ta faɗa tana kama makamar da ke jikin jakar. Abid kwa mai zai yi in ba dariya ba wai jaka ake cewa tana shan sanyi.
“Inna wai kina nufin jakarki ce wannan?” Ashrof ta jefawa Inna tambayar da mamaki, Sadiya kwa tuni ta buɗe ɗakin da ta karɓi mukulli wurin Ashrof ta shige ɗaki, Mama da Hajiya ma baya suka mara musu.
“To ta uwaki ce in ba tawa bace, wato ku kun raina mutanen ƙauye gani kuke mu ba za mu iya siyen jakar nan ba, to tawa je na siya tun lokaxin tana jaka shida da rabi(1300) Ba yanzu da farashinta ya faɗi ba.
“Ni fa ina nufin kayan da kika kwaso a cikinta ba wai tsadar jakar ba mai za ki yu da kaya har cikin jakar nan” Tunanin Ashrof kar Inna ta ce sati guda za ta yi sai an yi suna da kuwa sun banu.
“Ikon Allah haka fa Malam ya titsiyeni wai ina zani da kaya haka kamar wanda zan ƙaura, yo Allah na tuba kwana arba’in nan ne? Ga lokacin sanyin nan hatta bargona sai da na ɗakko saboda Imirana mai mugun halin nan” Ta faɗa tana zige zip ɗin aikuwa ta yi ido huɗu da abin sallarta. Wani salati ta rafka.
“Ni Azumi zuwa birni yau bai min rana ba, yo ina daɗi an manta da faɗar ubangiji, ashe duk abin nan da ake banyi sallah ba, ba azahar ba la’asar ga magriba ta kawo kai” Ta faɗa tana janyo abin sallar daga ciki.
“Wai Inna kwana arba’in ɗin me za ka yi da kaya niƙi -niƙi haka har da su bargo?” Cewar Ashrof tana kallon Inna Abid kuwa har riƙe ciki yake dan tuni ya harbo jirgin Inna “Lallai akwai dirama a gidan nan” Ya faɗa a ransa yana ƙara darawa.
Ashrof dai baki sake take kallon Inna dan ita ta gane manufarta kawai dai so take Innar ta amsa da bakinta dan ta ƙara tabbatarwa.
“Ka ji yarinya da tambayar ƙwaƙwa yo meye baƙo a nan da baki fahimta ba, ZAMAN WANKA na zo in yiwa jikata mana” Inna ta faɗa, hakan hankalinta kwance, hakan ya yi dai dai da shigowar Imran da ya ji maganar Inna tamkar saukar aradu a kunnuwansa, har wani amsa kuwwa maganar ta masa a kunnu, sakin ledar maganin hannunsa ya yi wacce ya biya wani kemis ya siyo…
Next page
Ba a fara ba zaman wanka
Masu son grp na ƴar zaman wanka
09030283375
…….
Mai son shiga grp ɗin dan samun cigaban buk ɗin ya mn mgn 09030283375 Wtsapp only
ƳAR ZAMAN WANKA
(KWANA ARBA’IN)
NA
MAMAN AFRAH