Ni da Patient Dina Book 2 Page 43
Tunda sukayi sallar asuba suka koma bacci karfe 10 fanan ta tashi daga bacci tsareshi da ido tayi tana kallon yanda yake bacci he looks innocent kamar ba ruwanshi sosai ta shagala da kallonshi murmushi ne ya subuce daga fuskanta hannu takai zata shafa fuskanshi ya dan motsa da sauri ta janye hannun baya ahankali ta furta ” Mr azaad zanso ka cikamin burina a yan kwanakin nan amma naga you’re very arrogant dole senayi sena cusa maka hakan a ranka ” ta karishe magana tana kallon body packs dinshi bargon da yake rufe dashi ya yaye time din data tashi sexy body dinshi awaje ,sauka idonta ya yi akan nipples dinshi dasuke ja sosai ga wasu kana_kanan gashi sun zaga nipples din murmushi tayi tace” kana da kyaun fuska kyaun jiki da sura tako ina ka hadu amma de kyaun hali ya maka wuya ” sulalewa tayi ahankali daga dakin dan karta tasheshi daga bacci tashiga nata bedroom din wanka tayi hade da kwalliya tasaka wando pencil crazy blue color tasa riga fara da kadan yarufe mata cibiya me guntun hannu gaban rigan akwai hoton teddy , lallausan gashinta kuma ta rabasu gida biyu ko wanne tasa mishi ribbon ta tubke , seta fito kamar slay queen , takalmi me yar tudu tasaka kallon kanta a mirror tayi taga tayi kyau sosai wayarta dake bedside drower tadauka tafara selfie , tayi sunfi kala goma kafin tabari zama tayi tana kallon hotunan, murmushin dake kara mata kyau tayi dan duk hotunan sun mata kyau , tunawa tayi da Mr azaad a ko wani lokaci ze iya tashi daga bacci yasa tayi saurin ajiye wayar tanufi kitchen.
Simple breakfast ta hada musu ta jera a dinning table, aranta tace ” anya wannan Mr arrogant din ze yarda yaci ma kuwa?” da wannan tunanin tashiga bedroom dinshi har time din yana bacci be farka ba , zama tayi a bed din ta sunkuyar da kanta har kumatun shi ta sake mishi fresh kiss a kumatu , ahankali ya fara bude wayan nan rikitattun idanunshi dake rikita mata da kuma razana abokan gaba, kallonta yayi yana mamakin sudden change din datayi jin kiss din data mishi wanda yaji tundaga tafin kafarshi har tsakiyar kanshi.
_____ sunkuyar dakai kasa tayi dan bazata iya kallon cikin idonshi ba dan yanzu zasu rikitata , yasa tayi kasa da kanta tana wasa da yatsun hannunta.
Se yanzu ya kalli dressing din jikinta, kyau tayi mishi aranshi yana fadin ” yarinya me jikin manya komai tasa yana fitting dinta” kafin afili yace ” me yakawo ki bedroom dina?” langwabe kai tayi tana yatsina fuska tace ” Mr azaad I made some breakfast shine nazo tashinka muje muyi” tana magana tana jujjuya kai gefe da gefe kamar wata karamar yarinya, yanayin yanda tayi yaso bashi dariya se yabasar, tsareta da mayun idonshi sannan yace ” dama tare mukeyi ne! Ko duk cikin shirin kine?” Satan kallonshi tayi jin abinda yafada tunani tafara anya wannan ba aljani bane kuwa daburcewa tayi ta rasa amsar da zata bashi , hakan datayi ne yasake tabbatar mishi da zarginshi ya tabbata, tabbas akwai abinda take shiryawa wanda ita kadai tabarwa kanta sani se Allah. tashi yayi ya zauna riko hannunta duka biyu yayi yana matsawa kadan kadan ” ki kalli cikin idona fanannnn ” cike da al ajabi da mamaki take kallon nashi jin yafadi sunanta , bata taba jiba ko da yaushe sede yace mata kee amma baya kiran sunanta duk tunaninta besan sunan bane, se taji yanda yafadi sunan da wani irin style ya burgeta jitayi shikadai ne ya iya fadan sunan , kyasta mata yatsunshi yayi afuska ganin ta tafi duniyar tunani, kallonshi tayi hade da sakin murmushi me tafiya da zuciya , “ya salam” yafurta aranshi yarasa meyake damunshi da yarinyar nan kwanan nan ya lura inbeyi a hankali tabbas zata iya galaba akanshi dukda yanada yakini abinda take shiryawa bawai mugun abu bane .
Matsa hannunta yayi kadan yar kara tayi hade da turo dan bakinta gaba tana kunkuni , zaro ido yayi yace ” ni kike zagi ?” Tashi tayi zata gudu dan taga sharri yakeson mata wai ta zageshi , maida ita yayi tazauna hade fuska yayi yace ” ina zakije kuma?” ganin fuskanshi yakoma na ainihin Mr azaad ne yasa murya asanyaye tace ” babu ” ” fanannnn ! meyasa kikeson sa rayuwata a cikin hadari? ko dan saboda abinda na mikine yasa kikeson ramawa ta wannan hanyar ? shin kina ganin hakan zesa ki huce ne? Kinsan tafiya zakiyi shine kikeson azabtar da rayuwata? kinason nasha wahalar inkin tuna kinsani awannan halin zakiji dadi ko? ” Wasu irin zafafan hawaye ne suka fara zubowa daga idonta dama tasan dole se yayi tunanin hakan kancewa ramuwa takeyi bayan babu hakan aranta , tashi tayi da gudu tafita a dakin tana kuka , ajiyar zuciya ya sauke shi kadai yasan yanda yakeji toilet yashiga yayi wanka. fadawa kan gado tayi tana kuka me ratsa zuciya afili take fadin ” Mr azaad wallahi bantaba rikeka azuciyata ba balle inyi tunanin rama abinda kamin taya mutum ze cutar da abinda yakeso Mr azaad ina sanka bazan taba barin wani ya cutar dakai ba balle ni dakaina ya Allah ka kawomin sauki cikin raina ” .
Yana tsaye abakin kofan bedroom dinta duk wani abinda tafada akan kunnen shi idonshi sun rine sosai yayi ja da karfi zuciyarshi yake bugawa be bari tasan da yana wajen ba yakoma bedroom dinshi zama yayi akan kujera jikinshi duk ya mutu dafa kanshi yayi da ke sarawa kamar ze fita babu abinda yake furtawa aranshi in banda ” innalillahi wainna ilaijiraji unnn na cutar da baiwar Allah da take sona! bansan menene so ba amma zanyi iya kokarina in kyautata mata kafin tabar duniyarmu ” haka yata saqe_saqe aranshi cikin kankanin lokaci ciwon kai yasauka mishi . Haka suka kai har azhar batare da sunci komai ba ita tayi zatan baya nan yafita ne tayi sallah ,ta canza kaya izuwa riga wanda tsayinshi ya wuce guiwanta yanada fa di light green, falo tafito ta gyara ko ina tasa burner yana fitar da kamshi me dadi bedroom dinshi tashiga saboda tagama gyara ko ina saura nashi , akan kujeran tasa meshi yana zaune idonshi alumshe kauda kallonta tayi daga kallonshi tafara gyara bedroom din ya saura kan kujeran tsayawa tayi nesa dashi tace ” Mr azaad zangyara kujeran” shuru yamata bece mata ka la ba tayi magana yafi baki biyar amma shuru tunani tafara kode bacci yakeyi , har zata juya tafita saboda karta tasheshi daga bacci taga ya miko mata hannu alamun takama, batare da tayi tunanin wani abu ba tarike hannun tana kokarin janshi yatashi, tadage se janshi takeyi ko motsawa beyiba bare yatashi haki takeyi kamar wacce tayi gudun tsere harda hada zufa.
Jawota yayi tafado jikinshi ya rungumeta muryanshi baya fita yace ” patient dinki yana bukatar special care bayida lafiya” sa hannu tayi ta taba jikinshi tabbas bayajin dadi kamar zazzabi ne yakeson rufeshi jikinshi yayi zafi, amma dazun kuma lafiyarshi kalau , kokarin tashi takeyi dan ta dubashi yasake rungumeta sosai kamar wani zekwaceta murya anarke yace ” karki tashi ina bukatar dumin jikinki atare dani” yanda yake maganar kamar yana mata rada.
Tausayi yabata kamar ba Mr azaad ba hakan yasa tasake jikinta dashi shishigewa jikinta yakeyi sanadiyar warm temperature nata se yaji yana jindadin kasantuwar su a haka , ta takura sosai ayanda suke kujeran ya musu kadan gashi runguman daya mata ba karamin runguma bane , dede kunnan shi tace ” Mr azaad kirjina ze balle ” saketa yayi yana kallonta da sexy eyes dinshi yace ” yunwa nakeji ” kyaf_kyafta ido takeyi tana kallonshi dan yamata bazata batayi tunanin haka awajanshi dan so take ta tabbatar ko mafarki takeyi ko kuma da gaske ne, yasan mamakine yahanata magana yasa yasake maimaita ” yunwa nakeji” tashi tayi da hanzari tashiga kitchen tayi fast food noddles ta dafa ta soya kwai tajuye a plate kaiwa bedroom din tayi ta ajiye saman center table ta koma kitchen tadauko drinks da ruwa , yanda ta tafi ta barshi haka tasameshi bata zauna ba se tadauko mishi magani ta ajiye komai akan table kafin tace ” Mr azaad katashi nadafa maka noddles saboda yafi wuri” ” okay” yace tare da mikewa ya zauna nuna mata kusa dashi tazo ta zauna, faracin abincin yayi seda yaci kusan rabi kafin yakai bakinta ze bata dan yasan itama bataci abincin ba make kafada tayi tana ” uhmm uhmm ” tamke fuska yayi yace ” Ina wasa dake ne ?” ba shiri ta bude bakinta yafara feeding dinta har yakare yabata ruwa , fanan de yau gaba daya Mr azaad gani takeyi kamar ancanza shi sewani lallabata yakeyi sau daya kawai ya kalleta yadau magani yasha dan yasan abinda ke ranta. Toilet yashiga yadauro alwala ya shinfida sallaya adaki yayi sallah azhar yau kam yayi missing jam’i . tana zaune akan kujeran babu abinda takeyi banda binshi da kallo duk abinda yayi kyau yake masa takasa janye idonta akanshi dago kai yayi suka hada ido yar harara yawurga mata yace ” banason yawan kallo gudun kar acinyeni ” dariya tayi jin wai gudun kar acinyeshi , shagala yayi yana kallon yanda dariyan yakara mata kyau , ganin irin kallon dayake mata ne yasa ta tsagaita da dariyan ” Mr azaad dan Allah in nemi wata alfarma awajanka ?” ta karishe maganar tana komawa kalar abin tausayi, murmushi kawai yayi yace ” kishirya yau zamuje gida karfe 7 karki batamin lokaci ” da gudu ta tashi tafada jikinshi cike da murna se dariya takeyi yau zataje gida ,rabonta da gida tunda tayi aure rungumeshi tayi gam tace ” nagode sosai Mr azaad” yayi farin ciki da ganin irin murnan data shiga yau de yayi sanadiyar farin cikinta “asshhh” yafurta da dan karfi dagashi tayi tana tambayarshi meyafaru amsa yabata da ” kinmanta bana jin dadi kinwani zo kin daddan ne ni” tunawa tayi da hakan dan tsaban murna ne yasa ta shaafa kunya ne yarufeta yasa tafara sosa kai tana turo baki .
Hannu yasa yarike laben kasan yace ” zaki fara rashin kunyar takine” girgiza kai tayi gudun karta ja yace yafasa ” am sorry bari inje gun ummina ka kwanta kasamu kayi bacci kafin la’asar” ko jiran amsarshi batayi ba tafice yau de yasata murna se murmushi takeyi ita kadai, sake nanata abinda tafada yayi ” ummina” hakan yamishi dadi saboda yana matukar son dakuma daraja meson umminshi.