Hausa NovelsNi da Patient Dina Book 2

Ni da Patient Dina Book 2 Page 34

Sponsored Links

Washe gari 5:30am

Tana zaune akan sallaya ta idar da sallah tana azkar se karfe 6:30 ta tashi takoma kan gado takwanta dan bacci be isheta ba, se karfe 10 ta farka ta shiga toilet tayi brush tawanke fuskanta fitowa tayi tana shafa cikinta dake kukan yunwa falo tafito jikinta nasanye da kayan baccin dube_dube takeyi tana neman kitchen wata kofa tagani akusa da inda dinning area yake wajan taje tabude kofar katon kitchen ne irin nayan gayu komai akwai aciki kamar wanda tundama mace na ciki tunani tafarayi to dama Mr azaad na girkine karewa kitchen din kallo takeyi yaburgeta sosai wani kofa tagani tabudeshi store ne kayan abinci ne aciki iri_iri kwalin idomie tabude tadauki guda daya se kwai biyu da gesher tafito standing gas takunna tadaura tukunya akai tahada indomie ta jollof da gesher kwai din ta dafashi daban kamshine kawai yaketashi a kitchen din tana gamawa tazuye a plate tasa cokali tafito falo tazauna kure A.C tayi dan tasamu yahuce dawuri seda tafaraci ne talura da basket din dake kan dinning ashe ankawo musu abinci cigaba tayi da cin indomie ta se shishitan yaji takeyi sekace wani ne yasata sawa dayawa ahaka tacinye abincinta , fitowa yayi daga bedroom dinshi babu riga ajikinshi dagashi se short din three quarter kokadan beyi tunanin zesameta ba bema kawo apart dinshi zaa ajiyetaba zama yayi akan kujera yana amsa kiran Faisal dake sanar dashi komai ready su kadai kawai BBC news suke jira okay kawai yace jin muryanshine yasa tadago tace ” Ina kwana Mr azaad” kamar bejitaba yacigaba da danna wayarsa tabe baki tayi aranta tana fadin ” kaika sani karka amsa din ” haka suka zauna a falon kamar wasu kurame can yamike haryakai bakin kofar bedroom dinshi yace ” kishirya yanzu zamu tafi and banason jira” yashige bin bayanshi da harara tayi tana kwaikwayan yanda yayi magana sannan tamike tayi wanka tafito da atamfa super wax me touches din pitch da sky blue riga da skirt dinki yayi kyau sosai duk pattern yasha stones ajiyesu tayi tadauko gyale da takalmi half cover se jaka masu matukar tsada zama tayi agaban mirror tadanyi light make up tayi kyau sosai ta gyara gashinta tayi packing dinshi se kyalli yake kayan tasaka sun zauna mata ajiki kamar dama sundauki measurements dinta das das da ita dawuwa gaban mirror tayi da dankwali ahannunta dauri tayi mekyau me shigen ture kaga tsiya wanda akesa mishi kwali aciki amma ita batasa komai ba tayi abunta daurin yazauna sosai akanta akasan daurin kuma gashinta ne wanda tayi packing dinshi feshe jikinta tayi da daddadan turare masu masifar kamshi, gyale tayafa yanada dan girma yarufe mata jiki tadau jakanta tasa takalmi tayi masifar kyau dan karamin bakin nan seyayi kamar tasa janbaki kasancewar libs dinta ja ne gashi tasa mishi libs gloss se shinny yake. fitowa falon tayi tazauna zaman jiranshi seda takusa 10mint tana jiranshi se gashi yafito, yana sanye da tsadadden yard milk color half jumfa gashin nan yasha gyara yayi matukar kyau , wuceta yayi abinshi bece mata ci kanki ba ganin haka yasa tamike tabi bayanshi suka gangaro main falo su Abba da ummi da kowa suna zaune afalon jin takun takalminsu ne yasasu juyawa suna kallonsu bakaramin burgesu sukayi ba sunyi making perfect match zama Mr azaad yayi, tsungunawa fanan tayi har kasa tana gaishesu suka amsa fuska asake zama tayi akusa da zeenat ” kai anty fanan wallahi kinyi kyau sosai dama wai kin iya kwalliya shine bakyayi wallahi baki ganki bane ” hararanta tayi jin takirata da anty tace ” bansan wani iyayi dazaki wani cemin anty tam ” batagama magana ba taji areef nafadin ” antynmu Ina kwana ” waro ido tayi cikeda mamaki qin amsawa tayi kara nanatawa yayi ” anty ina kwana” kwabe fuska tayi da shagwaba tace ” Abba kanajin su ko kace musu subari banaso ” takarashe maganar kamar zatayi kuka dariya sukasa banda azaad daya wurga mata harara , Abba yace ” to ai fatima dole suce miki anty tunda yanzu ke matar yayarsu ce ” Kara daure fuska azaad yayi jin abinda abba yace karsusa ta renashi mikewa yayi yace ” ke tashi mutafi ” yayi gaba tashi tayi tace ” to muntafi semun dawo ” Allah kiyaye hanya suka musu tabi bayanshi ganin motoci har guda goma sunyi shirin fitane ga securities da Sojoji suna fitowa suka dinga kwasar gaisuwa ganin ogansu da wata macen dake jikin hotunansu da aka yada yasa suka fara tunani bude musu motar tsakiya akayi yashiga tsayawa tayi bata shiga ba dagowa yayi yace ” dallah malama kishigo mutafi karki batamin lokaci mana” bashiri tashige tazauna nesa dashi fita motocin sukayi agidan suka hau kan titi.

Tunda suka fara tafiya babu wanda yakula dan uwanshi harsuka iso bude musu motar akayi suka fito kusan atare shiga ciki sukayi manager jikinshi na rawa yamusu sannu da zuwa yakaisu har inda zaayi hira dasu.

Photographer’s masu shooting videos duk sun hallara suna jiran afara saboda direct live zaayi kowa zega shirin alokacin da akeyinsa , wanda ze gabatar da shirin ne yace start nan da nan suka fara shooting.

Gyara zama yayi yafara da ” assalamualaikum warahmatullahi wabarakatuhum jamaa kamar yanda kuka sani nine naku me suna jamilu abubakar wanda yau nazo muku da manyan baki wato bakowa bane bace wannan shahararren dan kasuwan damuka dade muna jiran opportunity samun hira dashi Allah beyi ba seyau wanda ayanzu ake zargin kancewa shidin womanizer ne ahausance manemin mata zakuji komai de daga bakinshi wannan kuma itace Fatima muhammad Umar mahaddaciyar Al qur’ani wacce ta taciyo kyaututuka da dama saboda kwazonta itama zamuji komai daga bakinta ”

Seda azaad yayi kusan 5min fuska adaure kamar wanda akawa wani abu cike da izza yace ” kamar yanda kuka sani am azaad muhammad mainasara sauran labarina kuma beshafe ku ba dan bawan nan ne yakawo niba nazo ne akan qazafin dakukamin nida wife dina kuka bata mana suna saboda kawai biyan bukatarku saboda kawai kusamu kudi kuke watsa abinda ze taba rayuwar mutane batare da bincike ko wani abu ba acikin abinda befi 20 mint ba kuka bata mana suna” mamaki dauke akan fuskar jamilu yace ” shin kana nufin kace mana hafeza fatima matarka ce? Amma tayaya? yaushe ? Kayi aure ba tare da sanin duniya ba Mr azaad? Zamuso Karin bayani ” azaad kamar bazeyi magana ba yace ” itadin matatace anyi aurenmu nida ita a lokacin da saukanta saura 1week aka bari se anyi sauka tukun nan ayi biki nasan jamaa da dama sunganni awajan walimar to bari kuji infada muku nayi shuru ne saboda wasu yan dalilai narabu daku amma ayau din nan banfito ba seda natsayar da matakin dazan dauka akanku kukuma al umman duniya wayanda basawa yan uwansu musulmai kyakyawan zato hakkinmu nakanku irin mugayen alkaba’in dakuka dinga binmu dashi ku kuka sani da Allah ” bakaramin sanyi jikin duk wani wanda yake kallon gidan tv yayi ba dasu kansu BBC news seyanzu sukasan sun tabka babban kuskure .

Sallama tayi da muryanta me dadin sauraro sannan tace ” Kun batamin suna dukda ni matar aure ce amma haka yayi matukar taba darajata abisa kalaman dakuka rubuta ko tsoron Allah bakuji ba kuka kirani da dadiro harda cewa wai nasha zubar da ciki innalillahi wainna ilaijiraji unnn karku manta kuma kunada yaya mata in baku dashi kuma kunada kanne mata ko kun mantane khamatu dhinu tudanu kunjefa ni ama wuyacin hali saboda bakowa bane sukasan munyi aure ba bakomai nayafe muku amma kusani inkunwa wasu sun yafe wasu fah sede ku hadu agaban Allah tunda ku kwata_kwata bakwabin yan uwanku da kyakyawan alkhari se sharri ” sosai jikin jamilu yayi sanyi saboda shi yayi editing da printing din labarin. Murya asanyaye yace ” to jamaa ansamu babban kuskure domin labarin nan ba gaskiya bane duk masu bukatar karin bayani ko tambaya zasu iya kiranmu awannan layin wayanmu ayanzu ” aikuwa yana gama fadin haka telephone din dasuke amsa kira dashi tayi ringing dannawa yayi yadaga wanda duk maganar dazaayi acikin duniya zataji . ” Assalamualaikum warahmatullahi wabarakatuhum sunana sheikh Sulaiman Ahmad gombe nakirane domin bada shedan ido! Aranar da malama fatima tayi sauka nida kaina naje nasamu malama fatima domin nayaba da dabi’un ta nabukaci tabani daman insamu iyayenta da maganar aure amma taban hakuri ta shaida min ita matar aure ce agaskiya musulman duniya muji tsoron Allah muguji yada karya da jita_jita kokuma sharri ” jamilu ne yace” to masu gani da sauraranmu fatan kunji abinda sheikh Sulaiman Ahmad gombe yace muna gdy da shaida sheikh Allah yakara girma ” yakatse kiran yaci gaba” agaskiya mun tabka kuskure…

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD
‍⚕️‍⚕️ NIDA PATIENT DINA

 

Story & written by
MRS ISHAM

Back to top button