Hausa NovelsIkraam Hausa Novel

Ikraam 85

Sponsored Links

85…..
Khaleel na xaune cikin mota yana jiran Ikram
bayan ya sallami Maminsa, ya kwantar da Driver
seat yasa earpiece a kunnensa idonsa a lumshe
yana jiran fitowar nata, tare Ikram suka fito da
Mami da Jummai dake rike da jakar kayanta, ya
gyara xamansa ya cire earpiece din kunnensa
har suka karaso gun motar, Ikram da har lkcn
fuskarta ke daure ta bude baya xata shiga Mami
tace “nan xaki shiga Ikram” tace “eh” ba tare da
ta kalleta ba ta shige motar, Jummai ta saka
jakar a Booth din motar, Mami ta xaga ta inda
Khaleel yake tace “ga amanar Ikram Khaleel,
Allah ya kai ku lfya, ya kiyaye hanya, snn ina
hada ka da Allah kar kayi tukin gangancin nn
naka Khaleel” yyi murmushi yana shafa kansa
yace “ae na daina Mami” Mami ta juya tana
kallon Ikram tace “kin dae ji abinda na gaya maki
ko dotana, xa mu dinga waya” Ikram ta gyada
mata kai, Khaleel ya tada motar, Mami tace “to a
dae yi Addua” yace “Anyi Mami” Jummai na
washe hakora tace “to Allah dae ya tsare, kuma
yasa a dawo mana da bby” Mami tayi murmushi
ta juya ta bar wajen, Ikram ta xaro ido tace
“baby kuma mama Jummai, a ina xa a kawo
maku bbyn?” ta karashe mgnr fuskarta a tamke,
Jummai tayi dariya tace “to ai ni ba da ke nake
ba da Babana nake” Ikram tace “ayyo” ta Madubi
Khaleel ke kallonta, suna hada ido ta galla masa
harara yyi murmushi ya dauke kansa, ya ja motar
suka bar gidan Jummai na daga masu hannu, sae
da suka hau Main road yana kallon titin gabansa
yace “kinsan da cewar ni ba Drivern ki bne dae
ko?” bnxa tayi masa, ya gyada kai bae kuma
cewa komai ba ya maida hankalinsa ga tukin da
yake, cikin awa daya suka fita daga Abuja shima
sbda hold up din safe, ya dauki hanyar kaduna,
lkci lkci ya kan daga kai ya kalleta ta madubin
mota, suna kusan kaduna ya juya ya ga bacci
take, ya ci gaba da tukin nasa a hankali har suka
shigo kaduna wajen karfe sha biyu da rabi, ya
juya yana kallonta ya ga har ta tashi daga baccin
tana kallon tagan mota, yace “kina son wani abu
ne” ta kauda kanta tace “ni ruwa xan sha” gun
Hawkers din titi ya siya masu table water guda
uku ya mika mata daya ta karba ya ajiye sauran
snn ya ci gaba da drivin dinsa, suna kusa xaria
tace “ka tsaya” ya dan rage gudun da yake yace
“me xa ki yi” kmr xata yi kuka tace “ni Amai
nake ji fa kmr” ya samu gefen titi yyi parkin yace
“Amai kuma” toshe bakinta tayi da sauri ta bude
motar ta fito ta xaga ta gun daji ta shiga kwarara
Amai, ya dan yi tsaki ya fito rike da roban ruwa
daya, yana tsaye har ta gama snn ya bude ya
mika mata ta wanke bakinta da fuskarta snn ya
bude mata mota ta shiga, ya xaga ya shiga
shima suka bar wajen, Amanta hudu kan su isa
kano duk ta wahala ssae, komai ya siya mata
taki ci sae apple daya da take ta fama da sbda
Amai, kuka ta dinga masa wae ita ta gaji da
tafiyan har ynxu basu kai ba, shi dae bae tanka
ta ba har suka shigo kano karfe uku da rabi,
direct hotel ya nufa suka yi lodge, yana bude
dakin da aka basu ta shige ta fada kan gado a
gajiye, shi kuma ya shiga bathroom don yin
alwala, ko da ya fito ya tarar tayi bacci, yana
idar da sllhnsa ya fita siyo masu abinda xa su ci,
har karfe biyar Ikram bata tashi ba shi har ya ci
abinci yyi wanka, xaunawa yyi kusa da ita ya
shiga tashinta, ta fara juye juye yace “ke” ta
mike xaune da sauri tana murxa ido yace “tashi
kiyi sllh ki ci abinci” tace “ya Khaleel amma baxa
mu sake tafiya ba yau ko” yace “anjima da
daddare xa mu tafi” kmr xata yi kuka tace “A’a
wllh amai xan dinga yi” yace “kije kiyi alwala in
wanka xaki kiyi, tun daxu Mami ke son mgna da
ke” mikewa tayi ta shiga bathroom don yin
wanka, tana gamawa ta shiga kwala masa kira
yace “meye hka” tace “ka bude jakata ka dauko
min xanin da xan daura na manta bbu tawul a nn
ashe” yace “to ki fito ki dauka mana” tace “Ha’a,
to hka xan fito? ae bbu abinda xan daura ne
shiyasa, miko min kawae fa xaka yi ga hannu na”
ta karashe maganr a fusace, yyi murmushi yana
kallon kofar bathroom din, tace “ka taso?” dariya
ta basa, yana gyada kai yace “ehh” snn ya mike
ya bude jakarta ya dauki xanin atamfa ya nufi
bathroom din da shi.

Back to top button