Hausa NovelsIkraam Hausa Novel

Ikraam 8

Sponsored Links

8…..
Ikram ta mike bayan ta rasa inda xata yi da naman gabanta kmr xata yi kuka tana kallon Mami dake gaban computer tace “Anty ki kai ni gidanmu kar Ammina tayi min duka,” Mami tace “ynxu xan kai ki Ikram, shiga bayi ki wanke hannunki ki kuskure baki,” Ikram tace “ina bayin yake, waje xan je?” Mami ta nuna mata kofar bayi ta shige da sauri, tana shiga da minti uku ta fasa ihu, mami ta mike da sauri ta shige bathroom din a rude, tsaye ta ganta karkashin shower ruwa na xuba tayi jagab, Mami tace “me ya kai ki nn Ikram, ga buta nn kina gani ki tsallake sa,” tsalle Ikram ta shiga yi tana cewa “ina son in ga ko menene, ashe abun ruwan sama ne,” mami ta kashe showern ta jawo ta tace “haba Ikram dubi ynda kika jika jikinki, to maxa ki cire kayan,” ba musu ta fara tube kayanta, Mami ta dauko towel dinta ta mika mata tace “daura wnn,” ta karba ta daura, tabi Mami suka fito, dai dai nn Aliyu ya shigo dakin da sallama, Mami ta amsa tace “amma ba dae daga gida kke ba,” ya tsaya daga bakin kofar yana kallon Ikram yace “A’a nn kusa nake,” Ikram tace “lah wnn yaron naki ne na ranan n Anty,” Mami tayi dariya tace “ashe kin ganesa,” Aliyu ya xauna kan kujera yace “ina yini Mami,” Mami tace “lfya lau ya aiki,” murmushi yyi bae ce komai ba, Ikram ta matso kusa da mami a hankali tace “amma Anty yana da kyau yaron nn naki,” Mami ta fashe da dariya tace “ko Ikram,” tayi fari da ido tace “wllh” dariya ssae Mami take, shi ko sae kallonta yake bae dae ce komai ba, Mami tace “Aliyu don Allah siyo mata dan gown nan kasuwa ta jika kayanta,” ya girgixa kai yace “a gajiye nake Mami,” Mami tace “to bari in aiki Khaleel, ka bude fridge ka dauki lemo mana,” bae ce komai ba Mami ta fita, ya hade rae yana kallon Ikram yace “xo nan ke,” ta taho gabansa ta tsaya tana kallonsa tace “gani,” ya kauda kansa yana murmushi ganin ynda ta taho ko tsoro bbu, hannu ta daura kan dimples dinsa tace “lah irin abu na,” ya juyo da sauri yana kallonta, ta nuna masa nata tana dariya, ya kamo hannunta yace “me kika ce ma Mami” tace “nace mata yaronta na da kyau,” wara ido taga yyi yana dariya, ita ma ta fashe da dariyar har da kyakyatawa, baki ya bude yana kallonta, dae dae nn Mami ta shigo dakin, ta hade rae tana kallon Aliyu tace “meye hka Ali,” sake hannun Ikram yyi, cikin harshen turanci ta shiga ce masa bata son hka, murmushi kawae yyi ya mike ya fice daga dakin, Mami na kallon Ikram tace “dariyar me kike,” Ikram tace “shi naga yana dariya shine nima nayi,” Mami bata ce komai ba ta shiga goge mata ruwan jikinta da towel, ta gama ta dauko manta ta shafa mata snn ta gyara mata fuskarta tace “bari Khaleel ya kawo maki sabon kaya ki sa kin ji ko,” tana washe hakoran jin ddi tace “to,” gefen Mami ta xauna tana ta kallon cartoon har Khaleel yyi sallama, mami ta amsa ya shigo ya tsaya daga bakin kofar yace “gashi Mami,” Mami tace “ikon Allah to ka karaso mana ka tsaya daga bakin kofa,” karasowa cikin dakin yyi ya mika mata, ya juya da sauri xae fita Mami tace “ka ci abincin Khaleel,” bae ce komai ba har ya isa bakin kofa, Ikram tace ” kmr tsorona yake Anty,” juyawa yyi ya galla mata wani mugun harara snn ya fice, Ikram tace “lah ashe mugu ne ma harara na yake Anty, ni dae na fi son wnn mai kyan, meyasa kika haife shi Anty” murmushi kawae Mami tayi ta fito da ready made din gown din da ya siyo kmr an gwada ta ko dae dae ita, nan ikram aka shiga tsalle tsalle ana juye juye har da rawa, Mami sae dariya take tana kallonta cike da sha’awa, makullin mota mami ta dauka, tasa Ikram ta sa Hijab dinta snn ta kama hannunta suka fita, kwance suka tarar da Aliyu a falo, ya mike da sauri yace “ina xaku Mami” Mami tace “gida xan mayar da ita mana” yace “to bari in kai ku” Mami tace “kai da ka gaji, kayi xamanka kawae xanyi drivn din” da sauri yace “A’a na huta” Mami bata ce komai ba suka fita a tare ta bude back seat suka xauna da Ikram, snn ya tada motar suka fita daga gidan, Ikram ta dasa surutunta daga inda ta tsaya yi take ba full stop kmr radio, mami murmushi kawae take, shi ko sae kallonta yake ta madubi, wani babban supermarket Mami tace ya tsaya, ya samu waje yyi parkin, snn Mami ta fita tace tana xuwa, juyawa yyi da sauri yana kallon Ikram da ke bin Mami da kallo kmr xata yi kuka yace “Ikram” ta daga kai tana kallonsa yyi mata murmushi yace “tana xuwa kin ji,” kai ta gyada masa snn tace “wa ya koya maka tuka mota,” yace “dawo nn in gaya maki” ta dawo front seat din da yake nuna mata, yana kallonta yace “babana ne ya koya min” ta wara ido tace “lah, to ae ni babana bae da mota bare ya koya min” dariya yyi snn yace “to ni xan koya maki” tace “da gske” yace “eh mana” ta fara tsallen jin dadi daga xaunen da take, kallonta kawae ya tsaya yi har ta nutsu don kanta snn yace “Mami a gidanku ta dauko ki ta kawo ki gidanta,” tace “A’a a kasuwa ta daukeni” yyi shiru yana kallonta, xae yi magana Mami ta bude motar rike da manyan ledoji ta shigo motar, “me ya kai ki can Ikram?” Ikram tace “shine yace in dawo wae xae gaya min wani abu”

Back to top button