Hausa NovelsIkraam Hausa Novel

Ikraam 20

Sponsored Links

By Khaleesat Haiydar 20….. Aliyu ya dago kanta a hankali yace “Ikram” ta daga idanuwanta tana kallonsa yace “kukan me kike yi” tace “gurin Ammi xan tafi dare yyi” ya juya yana kallon Mami dake kallonsu snn yyi murmushi yace “to gobe xan kai ki, kinga nan ba a fita da daddare” ta turasa kmr xata yi kuka tace “wllh ka kai ni wajen Ammina ni baxan xauna a nn ba” da harshen turanci Mami tace “Aliyu bari in kai ta gida kawae tun kan dare yyi nisa ta tona min asiri” Mikewa Aliyu yyi ya daka mata tsawa ba shiri tayi tsit a tsorace, yana hararanta yace “na sake jin bakin ki sae na yanke shi, ke jaririya ce da xaki dinga yi ma mutane ihu” Mami tace “A’a bae kai ga hka ba Aliyu daina mata ihu bari in maida ta kawae” Ikram ta mike tayi gun Mami tana ci gaba da kukanta tace “ni bana sonka kuma, kar ka sake xuwa kusa dani” ta karashe mgnr tana murguda masa baki, juyawa yyi ya fice, Mami ta rungumota tace “wajen Amminki xaki ko dota” Ikram ta gyada mata kai, Mami tace “to karki sake kukan xan kai ki kin ji” nn ma ta gyada mata kai snn taje ta dauko indominta ta xauna kusa da ita ta ci gaba da ci, fridge Mami ta bude ta dauko mta juice ta bude ta xuba mata a kofi, snn tace “maxa ki gama cin abincin ki ina xuwa kin ji” Ikram ta kuma gyada mata kai snn Mami ta fita, falo ta sauka gun khaleel ta ga ko ya ci abincin, ta gansa xaune yana kallon American film, ta ce “kaci abinci son” Khaleel yace “na ci” tace “Aliyu ya tafi ne?” bae ce komai ba sae ga Aliyu ya shigo rike da ledan Ayaba, Mami tace “na ma yi xaton wucewa kayi” yace “ban tafi ba, snn ya karaso cikin falon ya xauna” kwanukan da Khaleel ya ci abinci Mami ta kwashe a dinnin tayi kitchen da su, Aliyu ya faki idonta yyi hanyar stairs, khaleel ya bi sa da kallo har ya haura snn ya tabe baki ya ci gaba da kallonsa, bae tarar da Ikram a dakin ba, sae karar saukan ruwa da ya dinga ji a bayi, yace “Ikram” a dan tsorace tace “ehh, gani nn” yyi hanyar bathroom din da sauri ya ganta tsaye karkashin shower duk tayi jagab, tace “kaga fa wanke hannuna na xo yi kawae sae wnn ruwan ya fara xuba a jiki na kuma Anty Ihu xata min ynxu” ya janyota yace “ba ki jin magana ikram” ta xumburo baki tace “to ni ce” mika mata towel yyi yace “cire kayan ki daura” tace “to fita” juyawa yyi da sauri ya fice tare da cewa “na fita” ta cire kayan ta fito daure da towel ya dauko mata daya daga cikin kayan da ya siyo mata ya bata ta sa, tana ganin Ayaba ta shiga tsallen murna, yace “to xo muje falo ki ci” tana rike da ayabarta suka sauko falo, Mami na kitchen tana wanke wanke, Aliyu ya xaunar da ita kan rug shima ya xauna, Khaleel sae kallonsu yake ta gefen ido yana dan buga kafa a tiles, Ikram ta mike tace “ya xa mu xauna a kasa bayan ga kujeru ni saman kujera xan xauna” bata jira me xae ce ba ta haye kan kujera ta xauna ta shiga bare Ayabarta, Mami ta fito daga kitchen tace “me ya sami kayan jikin ki Ikram?” Ikram na nuna Aliyu tace “shine ya canja min” Mami ta juya tana kallon Aliyu da ya bude baki yana kallonta, kan mami tace komai yyi saurin cewa “bathroom fa ta shiga ta kunna shower Mami” Mami bata kuma cewa komai ba ta haura sama, Ikram ta juya tana kallon Khaleel da ya kura ma TV ido duk da ynxu kam ba sanin abinda ake yi yyi ba don duk a takure yake, ta juya tana kallon Aliyu tace “ni kace ma wancan ya tashi ya wuce bana son ya xauna a nn” Aliyu yyi dariya yace “je ki gaya masa” ta mike ta isa kusa da Khaleel tana kallonsa tace “ka tashi ka bar mana wajen mu” daga kai yyi yana kallonta ta murguda masa baki, tace “nace ka tashi” turata yyi da karfi ji kke rigijib a kasa, ta fasa ihu tana kwala ma Anty Kira, ya mike ya tsallaketa xae wuce Aliyu ya sha gabansa yana masa mugun kallo yace “me tayi maka?” Muryar Mami suka ji tana cewa “yau na shiga uku wae wani abu na damunku ne” Aliyu ya turasa da karfi shima, Khaleel yyi kansa a fusace Mami ta daka masa tsawa tace “wuce sama Khaleel,” fuu ya wuce sae ga shi ya sauko rike da makullin motarsa yyi hanyar kofar fita. Mami kasa cewa komai tayi har ya fice, karfe goma da rabi Aliyu yace xae wuce gida, Ikram dae nata kallon cartoon kusa da Mami, yyi ma Mami sae da safe bayan ya dauki makullin motarsa snn ya daga ma Ikram hannu, ta mike da sauri tace ” ina xa ka?” Mami ta jawo ta tace “gida xae tafi gobe xae xo kin ji dota” Ikram ta fashe da kuka tayi gun sa tace “ni dae bana son ya tafi ya barni binsa xanyi, to nn ba gidansu bne” da kyar da kyar Aliyu ya lallaba Ikram ya tafi don bae son jarabar Mum dinsa. Ta gama cin kukanta jikin Mami tayi bacci wajen karfe sha biyu knn na nyt,
[2/25, 08:28] Zjy: ~Ikraam

Back to top button